Sashe 16
Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kulsum ta ce a ran ta, tabbas da ta rasa Turaki, kamar yadda ta so yin wannan babbar wauta, hakika da ta yi asara irin wacce ba a mayarwa!
Zancen zuci ta ke, ba ta san cewa ya fito fili ya shiga kunnen sa ba.
What are you saying?
Turaki ya tambaya, don bai ji sosai ba.
I said I love you
And I love you more
I can
t do without you
I can
t be happy without you too
Na gode Prince, once again, I love you with all my heart
.
Ita ce ta ke fadin soyayyar tata in theory, yayin da shi practically ya soma bayyana mata tasa.
Ta gane cewa, tata soyayyar is underestimated.
Ga masu soyayya in practice, wadanda ba sa bata yawun bakin su wajen bayyana ta.
*** *** ***
Kwanakin da Turaki zai yi a Gaya suka cika, wato wata daya.
Ya kama gobe za su tashi zuwa U.K, visa din Kulsum wadda za ta je a matsayin matar aure ga ma'aikaci ta kammala, don haka yau da yamma suka shiga cikin gida don yi wa Umma da Maimartaba sallama, daga can kuma za su biya gidan su Kulsum.
Maryam
yar Yaya Hadiza da ta dawo hannun Umma tun bayan auren Batulu ce ta sanar da su Umma na wurin Maimartaba, bayan sun gaida kowa sun gaida Fulani da jiki sun yi mata sallama tana mai sa musu albarka, suka karasa bangaren Maimartaba din.
Kulsum da Turaki suka zube suka kwashi gaisuwa.
Maimartaba sarkin Gaya kallonsu yake cike da murmushi, shi dai haka nan yake son yarinya Kulsumu kamar
yar cikin sa.
Ya ce,
Ummu Kulsum, ina fatan babu matsala, kina nan kina ta hakuri da mijin ki?
Murmushi ta yi, ta ce,
Ai shi ma yana hakuri da ni
Haka ya yi ta jan ta da hira kamar ba surukar sa ba.
Ya ce,
Za a tafi kasar Turawa a bar mu ko?
Ni dai aikin nan na Turai bana son sa Turaki, ba zan gaji da maimaita maka ba, kasar mu na bukatar likitoci irin ka, sau biyu ke nan kana min alkawarin dawowa gida gabadaya, amma sai ka kalallame ni ka kara komawa.
Yanzu kuma Kulsumun ma za ka dauke ta, mu da ganin ku sai Baba-ta gani
Turaki ya muskuta ya kara dukar da kan sa, ya ce, "Insha Allahu wannan karon zan cika alkawari, shekaru uku za mu yi mu tattaro komai mu dawo gida.
Allah ya kara maka yawan rai, na yi alkawarin ni da iyali na ko birnin Kano ba za mu je ba, a nan Gaya za mu kafa rayuwar mu har mutuwa.
Ina da burin bude asibiti idan na dawo, ga UmmuKulsum ma ma
aikaciyar jinya ce za ta taya ni kula da komai.
Fatan mu dai a bi mu da addu
Ran Maimartaba Sarkin Gaya ya yi fari tas!
Ya ce,
Albarkar mu na tare da ku, albarkar uwa da uba, ba za ku taba tabewa ba
Umma ma da ke gefe tana ta kallon su sun mata kyau a fuska, sun dace da juna.
Turaki ya yi aure wanda ta ke so, kuma hankalin ta ya kwanta da shi, don haka ba ta da sauran damuwa a yanzu.
Umma, ke ma ki sa mana albarka
.
In ji Kulsum.
Umma ta yi murmushi,
Ai Maimartaba ya hada har da tawa, kada albarkar tamu ta yi muku yawa
Kowa sai da ya murmusa.
Ta ce,
ku tashi ku je gidan su Kulsumu ku yi musu sallama kada dare ya yi sosai
Suka mike a tare suna godiya.
Goggo tana nan?
Jibo na kiran ta a zaure
Kulsum ta make murya ta fada daga tsakar gida.
Goggo na lazimi ta jiyo ta, ta yi dariya da murmushi duka a tare.
Baffa Jibo ne ya fara fitowa daga dakin sa.
Ya nunata da dan yatsa.
Wannan Jibon dai ya fi karfin ki, in ma zawarcin sa ki ka zo
Ta ce,
Haba!
Kayyasa!
Wane mutum!
Ina da sardidin likita na a gefe, me zan ci da tsoho baki duk goro?
Turaki ya sunkuyar da kai yana dariyar su.
Goggo ta fito ta shimfida musu tabarma, farin ciki ya cika ta, yau Kulsum ce tare da Turaki suna masu farin ciki da juna.
Ya Allah ya kara mata tsawon rai, ta dauki jikokin su.
Addu
ar da ta ke yi a zuciyar ta ke nan.
Ko da Kulsumu suka shiga daki da goggo, ba ta gaya mata fitsarin ta ya dawo ba.
A wannan gabar ta rayuwar su ta amince suna bukatar kwanciyar hankali.
Ta kuma kwana da sanin babban tashin hankalin su a rayuwa fitsarin kwancen ta ne.
Duk wani support da encouragement (karfin gwiwa) ta gama samun shi a mijin ta abin kaunsr ta (Turaki).
Ba abinda fada musun zai haifar sai tashin hankali a gare su.
Kulsum ta kira Baban ta ta yi masa sallama, sabida Turaki ya ce gobe kafin su wuce Abuja za su fara zuwa 'Yalleman su yi wa Baban sallama, nan Goggo ta ke gaya mata ya kira ta dazu ya ce ba ya gari, ya je Maiduguri kan wata harka da ya samu.
Tausayin Baban ta ya cika ta, mutum ne shi mai kokarin neman na kansa don rufuwar asirin iyalin sa.
Ta roki Allah ya ara mata dama ko yaya ne watarana iyayen ta su huta a karkashin inuwar ta.
Duk da cewa ba cikin wahala suke ba.
Ta gaya wa Goggo, Turaki ya ce gobe ta Abuja za su tashi, don haka za ta biya gidan Hajiyar ta.
Ba su bar gidan ba sai karfe sha daya na dare.
Tunda suka koma gida suka fara hada kayan su.
Washegari karfe shidda na safe suka dauki hanyar Abuja.
Daga Kulsum sai Turaki a motar.
Yana tuki tana gefen sa, tana so ta yi barci don barcin ta na jiya ragagge ne, ta kwana tana hada kayan su.
Amma tana yaki da barcin don kada tsautsayi ya sa ta fitsare masa mota.
Da ma ta yo guzurin lipton din ta, shi ta yi ta sha har da su nescape duk don su hana mata barci.
Turaki na tuki ba tare da ya juyo ba ya ce,
Wai wannan shan shayin na mene ne?
Ko dai
.
Ya ki karasawa yana murmushi.
Kulsum da bata dago inda ya sa gaba ba ta ce,
Ko dai me?
Ni don ya korar min bacci nake shan sa
Da mamaki ya ce,
To a kan me ba za ki yi barci ba?
Ana raba jikin dan Adam da barci ne?
.
Kawai ta ce, ai it is embarrasing ta gaya masa tana tsoron jika masa mota ne.
Hannun hagun sa ya mika ya kwantar mata da kujerar ta.
Please sleep baby
.
Yana iya hango fargabar ta cikin kyawawan idanun ta.
Ya kuma san me ta ke fargaba din.
To Ummu Kulsum, mece ce mota?
Barcin ki ya fi ta muhimmanci a waje na
Tana lumshe idanu cike da barci ta dube shi cikin shaukin so.
Mutum kamar mai gani har hanji?
Ya daga mata gira tare da kashe ta da wani kyakkyawan murmushi da ya ratsa har cikin ruhin ta.
Help me and sleep
(taimakeni ki yi barci).
Kulsum ta lumshe idanun ta, kafin dan lokaci barci ya dauke ta.
Cikin taimakon Allah ba ta yin ba har suka shiga Abuja.
Yana kokarin shiga da su hotel din Rockview ta ce,
Prince, don Allah mu je in gaida Hajiya ta, ban yi mata sallama ba
Ya ce, shi sai ya yi wanka da sallah ya huta.
Kuma sai ta tabbatar saurayin ta ba ya gidan sannan za su je.
Ta yi narai-narai da ido.
Ya ya za a yi in san yana gidan ko ba ya nan?
Shi da gidan su?"
Ya yi fuska ya ce,
Ki kira ki tambaya".
Dariya ta yi ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska.
Da ma ka cire shi a ran ka, ni ban taba son sa ba, irin son da ka ke tunani.
Ina son sa ne a matsayin sa na dan uwa na na jini, kuma shi ma ya sani, ya sha fada da bakin sa;
Ki taimake ni kada ki kara ambaton Turaki a gabana, zuciya ta za ta buga Kulsum
Turaki ya yi wani lallausar murmushi yana murza sitiyarin motar sa cikin gwanin ta.
Wato har zance na ki ke masa Kulsum?
Ashe kina so na duk da laifuka na gare ki?
Ya fada cikin sanyin murya.
Kulsum ta kare fuska da mayafin ta,
Hatta Hajiyar mu da Goggo, sun san irin son da nake maka Prince".
Turaki ya mika hannun damansa ya kama nata ya matse shi sosai a cikin hannun sa.
To say I thank you
is not enough to express the feeling
.....
Daidai lokacin da suka adana motar a parking lot.
Ya mika hannu ya bude mata kofa, jakar hannun ta kawai ta dauka.
Turaki ya wuce gaba ya je ya kama musu daki.
Ta lifter suka bi zuwa dakin nasu.
Duk abubuwan da ya lissafa sai da ya yi su; wanka, sallah, hutawa sannan suka fito don tafiya (Brains&Hammers) wato gidan Hajiya Nasara.
Hajiya Nasara kadai suka samu a gidan, karshen farin ciki ta yi shi da ganin su.
Ta sa Serah ta shirya musu abinci.
Turaki duk ya kasa sakewa saboda surukuta, amma haka ta matsa musu kan sai sun ci abinci.
A dakin ta da Kulsum ta shiga domin su gaisa sosai Hajiya Nasara ta kasa boye farin cikin ta, ta ce,
Na ji dadin yanayin da na ganki ciki Kulsum, na kuma tabbata Turaki na kula da ke yadda ya kamata.
Madallah
Nan Kulsum ta ke gaya mata sallama ta zo ta yi mata za su wuce U.K can inda Turaki ya ke zaune, ba ta san lokacin da za su dawo ba.
Farin cikin Hajiya Nasara ya karu, ta ce,
Ai kuwa zama bai gan ni ba, bari in tattara miki kayan girki, don a can ba za ki samu irin su ba
A waya Hajiya Nasara ta kira Dr.
Sakeenah da Nasmah duk ta gaya musu tafiyar Kulsum.
Nasma ta shiga EDD dinta, Taufeeq na Lagos, kayan amfani masu yawa Hajiya Nasara ta hada mata.