Sashe 5
Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy ya hadiyi miyau da kyar, Hajiya Nasara kuwa a ranta cewa ta yi, ta san za a rina, don tuntuni ta yi zargin Taufeeq shi ne matsalar Kulsumu.
Baffa ya ce,
Ko za ki fadi dalilin ki, tunda Allah ya hana hukuncin da babu hujja?
Kulsumu ta yi shiru, Daddy ya ce,
Kulsumu feel free to talk, we are all here for you.
Idan mun amince da hujjojin ki ba za a daura auren nan ba
Tausayin iyayen Taufeeq ya kama Kulsumu, amma haka ta rufe ido ta fadi abubuwan da ta gani a cikin firij din sa.
Ta kare da cewa,
Ina tsoron auren ko da mashayin wiwi ne, balle giya.
Ina tsoron halin da zan fada a gaba, da kuma ranar da
yanmu za su gane dabi'ar mahaifin su, su zarge ni da zaba musu mai wannan dabi
a.
Amma in Yaya Taufeeq ya ce na yi masa karya, yana iya rantsewa ba haka ba ne
Tsit!
Ka ke ji a falon, yayin da Taufeeq ya sunkuyar da kai yana hada zufa.
Bai taba tozarta a rayuwar sa irin yau ba.
Bai taba zato watarana asirin sa zai tonu ga iyayen sa ba, bai taba zaton abin da Kulsumu ta gani kenan ba ya hargitsa ta haka.
Tun farko shi me ya kai shi kiran ta zuwa gidansa ya kasa hakurin a daura musu aure?
Yau ga abin da ya janyo wa kansa.
Hajiya da Daddy ne suka tsura masa ido, Daddy ya yi karfin halin cewa.
Da gaske ne Taufeeq?
Ya kara yin kasa da kansa kamar ya roki kasar ta tsage ya shige.
Hajiya Nasara ta ce,
Da gaske ta ke ko sharri ta yi maka?
Cikin tsananin nadama Taufeeq ya ce,
Ba ta yi min sharri ba.
Tabbas ta gani din.
Amma Mum don Allah ku yi min afuwa, wallahi ban dade da fara sha ba
a komawa ta Lagos ne don in samu in rage tunanin ta, a lokacin da ki ka ce sai na jira ta for some years
na ga cewa ba zan iya jiran ba, shi ne na nemi abin da zai yi assisting dina, amma wallahi daga yau Mum na bari, na bari har abada, ba zan sake ba.
Tsautsayi ne
Goggo ta kawar da kai, jin hawaye na son zubo mata.
Tausayin Nasara ya yi bala
in kama ta ganin halin tashin hankalin da ta fada lokaci daya.
Daddyn Taufeeq kuwa kada ka so ka ga fuskar sa a lokacin sabida tsananin fushin da ke cikin ta.
Ya ce,
Taufeeq, sabida mace ka zabi ka sha GIYA, ka saba wa Ubangijin ka?
Duk tarbiyyar da uwarka ta yi maka?
Ba ka sha giya a Turai ba sai a Nigeria Muhammad Taufeeq?
Hawaye Taufeeq ya soma, ya ce,
Daddy na yi kuskure, na yi nadama, zan yi istigfari, amma don Allah kada ku hana ni auren Kulsum, wallahi daga yau na bar giya har abada!
Hajiya Nasara ta mike hawaye fal idon ta, ta ce,
Maganar aure tsakanin ka da Kulsumu babu ita, na soke ta har abada.
This is your punishment, ka je ka yi karatun-ta-nutsu.
Don mai shan giya bai iya rikon aure sai dukan mata.
Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi
Goggo ta ce,
Ku yi masa afuwa mana, don Allah ke Kulsumu ba kya afuwa?
Da Allah ba ya afuwa gare mu da tuni bai kifar da duniyar ba?
Dukkan mu masu kuskure ne, sai ake so in muka gane kuskuren mu a karbi hanzarin mu.
Ki yi hakuri tunda ya ce ya bari
Kulsumu ta girgiza kai tana hawaye.
Ba zan iya ba Goggo, tunda Hajiya ta ce a yi hakuri, to a yi.
Zan taya Yaya Taufeeq addu
a Allah ya ba shi wadda ta fi ni
Daddy ya ce,
Goggo a bar maganar nan, Taufeeq has to be punished don gobe ya gane ba duk abin da ka ke so sai ka same shi dole ba, a kuma lokacin da kake so.
Ya je ya yi karatun-ta-nutsu, ranar da ya tabbatar ya zama mutumin kirki ya dawo ya auri Kulsumu, amma aure gobe babu shi
Ya mike shi ma ya fice.
Hawayen idon Taufeeq suka gangaro, ya ce,
Don Allah Baffa ku ba su hakuri, ina son Kulsum ba zan iya hakura da rashin ta ba
Baffa ya ce, "Taufeeq yanzu sun dauki zafi, ka bari su huce.
Ba za su saurare mu ba.
Ku tashi ku je, Allah ya yi muku albarka
Duk yadda Taufeeq ya yi don ya kebe da Kulsumu ya samu ya lallashe ta ta ki fitowa daga dakin Goggo, har Daddy ya yi kiransa domin su tafi cikin Kano su kama hotel su kwana, gobe su biyo su dauki Hajiya Nasara su wuce, don lokacin magriba ta kusa ba za su iya kama hanya ba.
Haka Taufeeq ya bi bayan Daddy, yana mai jin karshen duniyar sa ya zo.
Yana mai hasaso yadda rayuwa za ta koma masa babu Kulsumu.
Ya yi nadama sau ba adadi, nadamar da ya tabbatar iyayen sa ba za su karbe ta a wannan lokacin da suke cikin tsananin fushi da shi ba.
Sun idar da sallar isha, Hajiya Nasara na kwance a dakin Goggo, zazzabi ya rufe ta, Goggon sai ba ta baki ta ke, tana cewa, ta dauki abin nan da sauki kada ciwon zamani ya shige ta, yaran yanzu ai kowanne da matsalar sa, kuma Taufeeq ya yi nadama tana da tabbacin in ya auri Kulsumu ba zai sake ba.
Daga kwancen da ta ke Hajiya Nasara ta ce,
Allah ya kiyaye in hada Kulsumu da mai shan giya, kuma tunda sai ya samu Kulsumu ne zai bari ya je ya yi ta sha, Kulsumu ta riga ta tsere masa
Sallamar yaro suka jiyo daga tsakar gida, Goggo ce ta fito tana amsawa.
Ya ce,
Wai ana sallama da Baffa
Goggo ta ce,
Tunda ya tafi sallah bai dawo ba
Ba ta rufe bakin ta ba sai ga Baffan na shigowa, fadi yake,
Kai din bako ne da za ka tsaya a waje kana sallama?
Da can haka ka ke yi ba sallama ka ke yi kan ka tsaye ka shigo ba?
Ya shigo, bakon na biye bayan sa.
Hasken farin wata ya haska wa Goggo fuskar Yarima Turaki, gabadaya tsakar gidan su ya dauki kamshin sassanyan turaren sa, a idanun Goggo har tsayi da girma ya kara, fatar sa sai sheki ta ke a cikin hasken farin wata, ga wata shadda mai maiko da ya zuba sai walainiya ta ke (Excelcior), ya dora hula wadda ta dace da shaddar jikin sa ruwan toka, hannayen sa biyu zube cikin aljihu kamar yadda ya saba.
Sai faman sunkuyar da kai yake, yana murmushin da da ka gani ka san na rashin nutsuwa ne.
Dazun nan da safe yaron nan Sadi makwabcin su Kulsumu da ya sa ya dinga yi masa dakon zuwan ta Gaya ya fada masa ta zo har da marikan nata, kuma ya ji kishin-kishin gobe ne za a daura auren ta.
Duk abubuwan da ke gabansa haka ya zubar da su ya taho Gaya, bai samu jirgi da wuri ba shi ya sa isowar sa Gaya ke nan ko gidan su bai shiga ba ya zarto nan, don ya ga ko da abin da zuwan sa zai amfana masa.
Har gobe jikin shi yana ba shi zai samu Kulsum, zai dawo da ita cikin rayuwar sa komai daren dadewa.
Ganin ta da ya yi a Lagos ya kara tabbatar masa Ubangiji na nufin wani babban al
amari a tsakanin su.
Goggo ta ce,
ah!
Turaki ne tafe?
Yayin da Baffa ya shimfida masa darduma ya zauna, Goggo ta shigo ta zauna a gefe suna gaisawa.
Baffa ya dube shi ya yi murmushi, ya ce,
To alhamdulillahi, da ma yanzun nan da ka gan ni na dawo, gidan ku za ni wajen Maimartaba, in gaya masa in har yanzu kana bisa ra
ayinka na neman komen Kulsumu, gobe ka kawo sadaki a mayar maka da matar ka
Turaki ji ya yi tamkar zuciyar sa ta yi tsalle ta fito daga kirjin sa, sannan ta kuma yin wani tsallen ta koma muhallin ta.
Ya ji shi tamkar yana yawo a kan gajimare, duk da haka bai gaskata kunnuwan sa ba, domin wani abu ne da ya zo masa bagatatan tamkar saukar aradu, ya bugi zuciya da kwakwalwarsa a lokaci daya.
am Baffa
me ka ce?
Ya tambayi Baffa don dai ya samu wannan karon zuciyar sa ta karbi tabbacin maganar.
Baffa ya sake maimaita masa, ya ce,
A da, gobe za a daura auren ta da dan uwanta, to amma an samu matsalar da ta sa aka fasa, sabida haka in har yanzu kana kan ra
ayin komen, ni a gobe zan yi wa Kulsumu aure, da ko ma waye, jama
ar da na tara ba ni da bakin sallamar su
Baffa bai yi aune ba sai ganin Turaki ya yi ya fuskanci gabas ya yi sujjadah.
Murmushi Baffa ya yi don ya fi kowa sanin wahalar da yaron ke yi a kan neman komen Kulsumu, ko sati daya ba a yi ba ya zo, amma bai gaya masa ta kusa aure ba, don ba ya so ya karya masa zuciya.
Ya yi musu hidima mai yawa ta kayan abinci kamar yadda ya saba, Allah ya sani!
Tun farko ya fi so Kulsumu ta koma wa Turaki, kunyar Hajiya Nasara ce ta sa ya amince da zancen Taufeeq.
Bayan ya dago daga sujjadar Baffa gani ya yi hatta kyawun fuskarsa ya karu.
Ya ce,
Baffa "na gode" ta yi kadan ta bayyana godiya ta.
Na gode Baffa, Allah ya yi muku duk abin da ku ke so a duniya da lahira.
Ya jikan mahaifa, ya ja kwanan ku.
Yanzun nan zan je na fada wa Maimartaba da Umma, kuma a daren nan ba sai gobe ba za a kawo sadaki
Mikewa ya yi zai fita, jikinsa har rawa yake.
Baffa ya ce,
Bari a kirawo Kulsumun mana ko gaisawa ne ku yi
Turaki ya juyo daga bakin kofa gaban sa na faduwa, ya ce,
ah Baffa, kyale ta za mu gaisa gobe.