← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 20

Sashe 10

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba inda ba su shiga ba, har ran ta ta yaba da gidan, sai dai farin cikin ta ragagge ne duk da kasancewar ta mallakin sa, tunda da Turaki za ta yi rayuwa a cikin sa, wanda ba shi da gurbi ko kankani a zuciyar ta yanzu.

Ko son ganin sa ba ta yi.

Umma ta aiko musu da abincin karin kumallo a manyan warmers, suka zauna suka ci ita da Batulu.

A lokacin ne baki suka soma zuwa
yan ganin daki da
yan ganin kwaf!

Yan uwan Turaki da
yan zuri
ar su duk sun zo.

Wadanda ta saba da su a baya, da wadanda sai yanzu ta san su.

Har dare suna hidimar baki ita da Batulu, sai da aka zo daukan Yayar su Magajiya
yar wajen Hajiya Saratu, sannan Batulu ta bi su suka tafi da alkawarin gobe kafin ta koma Kaduna za ta biyo su yi sallama, ta kawo mata Nurain da Zunnurain
yanta ta gan su.
*** *** ***
Turaki bai shigo gidan ba sai karfe tara na dare.

A matukar gajiye yake, a kan dining ya samu abinci cikin warmers, ya debi wanda zai iya ci, ya koma kujerar tsakiyar falo ya yi zaman sa, ya kunna talabijin ya kamo tashar da yake so, wato CNN, ya koma cikin kujera yana cin abinci yana sauraron labarai.

Bai damu da ya je inda ta ke ba, amma zuciyar sa da idanun sa so suke su gan ta, ko da kuwa rikici za su yi, ba zai iya kwana bai san halin da ta ke ciki ba.

Mikewa ya yi zuwa dakin nata.

Ya murda kofar ya ji ta a rufe.

A hankali ya ce,
Ummukulsum, bude min kofa
Banza ta yi da shi ta ci gaba da shimfidar gadon da ta ke yi.

A ran ta ta ce,
Yadda ka aure ni ba da sani da amincewa ta ba, haka za ka gaji da ni ka maida ni inda ka dauko ni".

Ya sake tausasa murya,
Kulsum kada ki yi abin da zai fusata ni, idan na shigo dakin nan...

Sauri ta yi ta je ta maida mukullin jikin kofar, yadda ko ya zira nasa ba zai budu ba, wato ya doke ta sannan ya hana ta kuka saboda zalunci?

A lokacin da ta ke neman jin kan sa, kulawar sa da soyayyar sa bata samu ba sai yanzu da ta daina bukata?

Hakan kuwa ya yi, domin dakin sa ya koma ya dauko bunch of keys na gidan gabadaya, ya zo ya yi ta gwadawa, amma ya ki shiga.

Nan ya gane makullin ta bari a jiki.

Ya yi kwafa.

Ya ce.

Ni da gidana a ke rufe min kofa?

Ki yi kina sani, ranar da zan rama tana nan zuwa
Kulsum ta yi murmushi ta san ta shaka masa.

A zuciyar ta ta ce, "da na ce gidana ne?

Dadin abin ba daga bola ka tsinto ni ba
Turaki kwana ya yi da wannan bacin ran, washegari ba ta fito ba sai da Batulu ta zo yi mata sallama tare da yaran ta.

Suka yi sallama cike da begen juna.

Kuma a ranar ne Malam Yusha
u ya kawo mata dukkan kayan ta na sawa da na amfani, da takardun makaranta daga Abuja.

A daren ranar Turaki bai neme ta ba, ya sa a ran sa ya fita sabgar ta, don shi duk wata hanya da za ta kawo raini tsakanin sa da kowa bai son ta.

Balle iyalin sa.

Duk da hudubar da Abdul
Ahad ke ta yi masa na cewar, kwantar da kai zai yi, girman kai ba nasa ba ne a halin yanzu, ya aje sarautar sa da mulkin sa a gefe ya lallashi Kulsum, laifi har ba iyaka ya san ya yi mata, amma ya san shi ba zai iya ba, yana tattalin girman sa sosai.

A tunanin sa in har zai samu su kebe cikin nutsuwa ya san ta duk hanyar da zai bi ya wanke laifin sa a aikace, amma ba ta irin hanyar da Abdul
Ahad ke so ba.

Shi Ba-sarake ne, wanda ya gaji sarauta gaba-da-baya ba haye ya yi ba.

Kulsum ta je ta yi ta yi, ranar da ta gaji za ta bari ne.

Domin wannan karon auren su na har gaban abada ne, don haka tun ranar bai kara zuwa ya buga mata kofa ba, ita kuma ba ta fasa shigewa tun yamma ta kulle kan ta ba.

Da ma ita in ta ci abinci karfe shida na yamma shi ke nan kuma ba ta kara ci sai breakfast din washegari.

A haka suka zauna ba mai shiga harkar dan uwan sa har tsayin kwana biyar, ya kama washegari ne hawan angoncin da Turaki ya shirya da abokan sa da
yan uwansa maza.

Kuma a ranar ne Abdul
Ahad ya iso, abin mamaki tare da Sajeedah.

Bai gaya masa ba don ta ce surprise ta ke son yi musu.

Ba za ta iya hakuri ta zauna ba ta zo ta ga Kulsum din Dr.

Abubakar ba.

Ta zama kawar ta ta farko daga bangaren matan abokan su.

Turaki da kansa ya raka su wajen Umma da wajen Maimartaba suka kwashi gaisuwa, Umma ta dade tana jin labarin Abdul
Ahad a wajen Turaki.

Ba karamar tarba tasa aka yi musu ba, aka kai su guest house din Maimartaba, amma sai Sajeedah ta ce ita Allahnbur wajen Kulsum za ta sauka.

Abdul
Ahad ya harare ta, ya ce,
kin taba jin inda aka yi masauki a dakin amaryar da ko sati ba ta rufa ba?

Ta ce,
Dear, ni ba zan hana su amarci ba, akwai sakonnin da zan bata ne.

And I want to be her first friend from Reading
Turaki ya ce da Abdul
Ahad ya kyale ta, in sun yi wanka sun huta zai zo ya dauke ta zuwa wajen Kulsum din, amma a can karkashin zuciyar sa cike yake da zullumi da taraddadin tarbar da za ta samu daga Kulsum din, shi kansa a me yake gare ta balle wani nasa?

Gabadaya ta canza daga Kulsum din da ya santa, saliha mai sanyin hali, ta rikide zuwa wata halittar daban.

Kamar ba ta san girman hakkin aure a kan ta ba.

Laifi ya san ya yi mata, amma ta ba shi da ma mana ya wanke kansa?, Ya ba ta hakuri kamar yadda Abdul
Ahad ya ce, su fahimci juna su manta baya?

Babu dan Adam din da ba ya kuskure a rayuwar sa.

Sai dai shi zaman nan da yake tare da Kulsum cikin gidan sa, duk da babu wata alaka mai dadi a tsakanin su, ya fiye masa gabadaya lokutan rayuwar sa a Reading dadi, sanin cewa ita din mallakin sa ce, kuma tana cikin dakin auren sa, shi ne babban kwanciyar hankalin sa.

Bai aure ta don biyan bukatar gangar jiki ba, sai don ita din bakidayan ta yake so.

Fatan sa Allah ya nuna masa ranar da zai sake mallakar Kulsum a shimfidar sa, ya wanke gabadaya laifukan sa na baya ta hanyar da shi kadai ya san ta, ta hanyar da shi kansa ya san unexpressable ce.

Shi ne kuma kadai maganin taurin kan Kulsum.

Da wannan tunanin ya iso gida, ya adana motar a inda ya saba adana ta.

Cikin rashin karsashi ya nufi dakin Kulsum.

Cikin sa
a ba ta kai ga rufewa ba kamar yadda ta saba, don a lokacin ta ke sallar la
asar ma.

Yana shiga ya rufe dakin da makullin da ke jiki ya zare shi, ya rufe toilet shi ma ya zare.

Ya hada su duka ya zuba a aljihun rigar sa.

Kulsum na sallah tana jin duk abin da yake yi.

Gaban ta ya yi mummunar faduwa da ba ta san dalili ba.

Turaki ya kishingida a gefen gadon ta yana kallonta with lingering emotion a zuciya da idanun sa.

Rabon da ya sanya ta a idanun sa yau kwana hudu ke nan.

Haka kawai ta hana musu morar amarcin su da kuruciyar su, sabida wani fushin ta wanda bai karewa.

Kin sallamewa ta yi, in ta sallame sai ta tada wata, bayan kuma ya san bayan la
asar ne ba lokacin nafila ba ne.

Wato dai wadannan sallolin don shi aka kirkire su, ba don Allah ba.

Murmushi ya yi ya mike ya saki labulayen dakin gabadaya, ya kashe kwan lantar ki ya kunna A.C.

Dakin ya bada wani irin dim, sanyi mai dadi ya fara ratsawa a jikkunan su.

Rigar voile din da ke jikin sa ya cire ya saura daga shi sai singileti da wandon jikin sa, ya yi kwanciyar sa a gadon Kulsum, yana fadin,
Yau daga ni sai ke, sai Ubangijin da ya sanya min soyayyar ki.

Ki kashe ni ki huta Kulsum, ya fiye min wannan silent killer punishment din naki
Ya dau filo ya rungume, ya yi kwanciyar sa.

Kulsum ta rasa inda za ta sa kanta, ta yi sallolin har kafafun ta sun gaza daukar ta, sallolin da ta tabbatar babu lada a cikin su.

Ba ta yi aune ba ta dan zauna tana hutawa, sai jin ta ta yi a hannun Abubakar-Turaki.

Gabadayan ta ya sure ta ya haye gadon da ita, ya ja duvet mai laushi ya lullube su, bayan ya rungume ta tsam-tsam a cikin kowacce kusurwa ta jikin sa yadda bazata iya kwacewa ba.

Kafin ya soma kissing din ta wholeheartedly ma'ana da dukkan zuciyar sa.

Ya ja tunga da lips dinsa cikin nata, amma duk da ta soma ficewa a hayyacin ta a dalilin deep kisses din Turaki, ba ta fasa kokarin kwatar kanta ba.

Ba abin da ta tuno a lokacin sai ranar su ta farko, ranar da Turaki bai taba tausayin ta ba
ranar da ya tabbatar mata ba ya son ta, ya tara da ita ne a bisa tilas.

Nan da nan ta fara protest, wasu hawaye masu zafi na bin gefen fuskar ta.

Turaki ya ji dumin su a kan fuskar sa, ya sassauta daga tsattsauran rikon da ya yi mata, ya sake kissing din tausasan labbanta softly.

Wadanda a lokacin suka koma kalar light pink.
Chapter 10 · 0% Book details