← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 20

Sashe 1

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Normal Table
No List
0Header Char_b50fc32c-980c-4784-9af9-7ffdbee6fa27
header
0Footer Char_e6efe823-6ea5-49dd-a740-d9006ff1e3c1
footer
KULSUM
3
Littafin
SUMAYYAHABDULKADIR
[email protected]
SADAUKARWA
Ga dukkan matan da ke fama da lalurar 'nocturnal enuresis'(fitsarin kwance) a gidan aure.

GODIYA
Godiya ta musamman ga Nura Sada Nasimat sabida jimirinsa na bin rubutuna kafin bugawa da bada shawarwari.

Allah ya raya mana zuri
a rayuwa mai albarka.

JINJINA
Ga daukacin mambobin TAKORI'S ONLINE FORUM, littafin Kulsum ya jinjina muku, ni da ku hadin Allah ne.

Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah.

You are my source of inspiration.

GARGADI
Banyar da a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ba tare da iznina ba, tun daga radio, facebook, whatsappp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne, kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'I Wali.

KULSUM-3
Har tana tuntube, saura kadan ta fadi
ta samu ta rike marikin kofar ofishin ta yunkura ta fice da mugun sauri.

Ba ta tsaya a ko
ina ba sai a jikin motar Taufeeq.

Babu inda ba ya rawa a jikin ta, ta tabbata Turaki ne ta gani ba mai kama da shi ba.

Fatan ta a lokacin kawai shi ne ta hango fitowar Taufeeq su bar asibitin gabadaya, amma har aka shafe mintuna goma babu Taufeeq ba mai kama da shi.

Sai can ta hango su su biyu suna tahowa a tare, da shi da Turakin, sai waige-waige suke yi.

Rasa inda za ta sa kanta ta yi, sai kawai ta daddage ta taka da gudu ta boye a bayan wasu shuke-shuke.

Daga inda ta ke tana iya hango su har cikin motar Taufeeq suke dubawa, daga baya Turaki ya juya cikin tafiyar nan tasa ta
yan saraki ya koma cikin asibitin, Taufeeq kuma ya dauko motar sa ya tuko a hankali yana bin gefen hanya da idanunsa, tana iya hango tashin hankalin da ke shimfide baro-baro a kan fuskar sa.

Sai da ta ga ficewar sa daga get din asibitin, sannan ta fito daga bayan shuke-shuken ta zo bakin get domin ta fice ta tari taxi zuwa Victoria Island gidan Sakeenah.

Tana zuwa get masu gadin suka taso suka kulle get, suka koma gefe suka fuske, suna kiraye-kirayen waya.

Wani mugun takaici ya kama Kulsum, ko kallon arziki ba su yi mata ba, amma sun kulle kofa sun hana ta ficewa.

Ba'a jima ba ta ga mota kirar Acura na fitowa daga cikin asibitin zuwa inda suke.

Tun daga nesa ta gane mai tukin nan cikin tsananin nutsuwa kamar bai son taka kasa.

TURAKI ne.

A wannan lokacin ba gilashi a idon sa, wannan ya ba ta damar gane shi sosai.

Da gane irin canjawar da ya yi.

Juyawa ta yi ta karasa gaban masu gadin ta soma rokon su su bude mata kofa.

Ko daga ido su kalle ta ba su yi ba, har motar Turaki ta iso ta yi parking a gaban ta kamar za ta take mata
yan yatsun kafar ta.

Zama ya yi cikin motar yana kare mata kallo.

Ga wani makalallen murmushi a gefen bakin sa.

Ya bude motar ya fito gaba-gadi, rataye da falmaran din bakaken suit din jikin shi a kafadun sa.

Gaban ta ya zo ya tsaya suna fuskantar juna.

Kallon ta kawai yake da idanun nan nasa da ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu.

Yayin da ta yi kicin-kicin da fuska, za ka rantse da Allah bata taba sanin fuskar da ke tsaye gaban ta ba a tsayin rayuwar ta.

Malam lafiya?

Kulsum ta yi tambayar, muryar ta na rawa, tana mai dojewa kallon tsakiyar lumsassun idanun sa.

Na zo fita ka sa an tare ni, na ci bashin ku ban biya ba ne?

Ba ta yi aune ba ta ji hannun ta cikin na Turaki, shidewa ta kusan yi na wucin gadi, kafin ta tantance me ke faruwa, ya ja ta tana tirjewa ya bude motar shi ya sanya ta, tare da rufe kofar da key din hannun sa.

Ya zagaya ya shiga mazaunin sa ya tashi motar.

Masu gadin suka wangale masa kofa ya fice, suna daga masa hannu cikin girmamawa.

Tafiya kawai yake bisa shimfidaddun titunan garin Lagos ba tare da Kulsum ta san inda aka nufa da ita ba.

Malam sace ni za ka yi?

Malam ina ruwan ka da ni ne?

A ina ka sanni?

Malam ni matar aure ce ko ba ka gan ni tare da miji na bane?

Tambayoyin Kulsum kenan ga Turaki, cikin rawar muryar da ke gab da rushewa da kuka.

Idan stiyarin motar ya ba ta amsa, to mai tukin motar ma ya ba ta, inda ta ke wannan bai kalla ba, sai sharara gudu yake, amma makalallen murmushin da ke kan tattausar fatar bakin sa ya kasa bacewa.

Kulsum ta soma bugun gilashin motar da duka hannayen ta, fatan ta gilashin ya fashe ko da zai yanke ta ne, ta yi ihun da mutane za su ji su kawo mata dauki.

Amma ta lura gilashin motar ko sound ba ya badawa kuma ko za ta shekara tana bugunsa ba zai fashe ba.

Kawai sai ta fashe da kuka tana kiran Goggon ta da Baffan ta.

Abin da ya yi matukar bai wa Turaki dariya.

Ya dube ta da lallausar murmushi ta gefen lumsassun idanun sa, cikin rada ya ce,
Saura Batulu da Umma!

Idanun ta cike da kuka, amma hararar shi ta ke, daidai lokacin da suka kawo wani check-point na
yan sanda.

Daga murya ta yi sosai tana kwarara ihu ba ta san cewa murya ba ta fita daga gilashin ba.

Sai ta daga hannuwa tana yi wa
yan sanda alamar da ta sa daya daga cikin su ya zo jikin motar tare da kwankwasa gilassan, Turaki ya sauke glass a hankali ya kuma nuna masa katin shaida (I.D card) na shaidar aikin sa, nan da nan dan sandan ya yi baya yana daga masa hannu, ya yi sama da gilassan motar da sauri ya sake shan round ya shiga unguwar Ikoyi.

Kulsumu ba ta bar kuka ba, don ta gane in ma sata ce Turaki ya gama sace ta.

Sun wuce kyawawan gidaje kamar guda biyar kafin su shiga wani kyakkyawan lodge mai hawa daya.

Maigadi ya zo ya bude, Turaki ta zura hancin motar sa cikin gidan.

Ya yi parking a rumfar adana motoci wadda ke dauke da wasu motocin guda biyu, ya kashe motar tare da sakin ajiyar zuciya.

Ya dubi Kulsumu wadda ta ki dagowa daga cinyoyin ta balle ta san inda ya kawo ta.

Sautin kukan ta kadai ka ke ji a motar, kamar wadda aka gaya wa sakon mutuwar iyayen ta.

Kirjin sa ne kawai yake dagawa yana sauka da sauri-da-sauri.

Wani lokacin excitement zai iya haifar da bugun zuciya.

Mutum ya fadi ya mutu farat daya.

To hakan ce ta faru ga Turaki, wanda ke ganin komai da ke faruwa da shi yau kamar a mafarki
wai shi ne da Kulsumu a gabansa!

Idan mafarki yake yana rokon Allah kada ya farkar da shi daga wannan mafarkin, har sai ya ga karshen sa, har sai ya gan shi tare da Kulsum matsayin ma
aurata a karo na biyu.

Ashe duk mahaukacin neman nan da yake wa Kulsumu tana cikin kasar Nigeria, a garin da yake yawan rayuwa?

Allah shi ne shaida kan babu abinda ya wahalar da shi a duniya irin neman da yai wa Kulsumu, shekaru dai-dai har guda hudu.

Shi Allah da yake Gafurur-Raheem ne, yau ga shi ya tankado keyar Kulsumu ya kawo mishi ita har cikin ofishin sa.

Shin shi wane irin wawa ne da zai yi saken da za ta sake kufce masa???

If you are done with the cry (idan kin gama kukan) ki wuce mu karasa ciki
A matukar fusace Kulsum ta dago ta dube shi, idanun ta a rufe sabida bacin rai, ta ce,
Da wacce hujja zan bi ka inda ban sani ba?

Me ye hadin ka da ni?

A ina ka san ni, ko na yi maka kama da
yammatan da ake daukowa bisa titi a garin Legas a kawo su guest house ne?

Kyabe baki ya yi, ya ce,
Ni ma ban san me ye hadin nawa da ke ba, kuma ba ki yi kama da
yammatan bisa titi ba, sannan nan ba guest house ba ne, gidan mutane ne, hujja ta ta cewa ki bi ni ciki mu zauna mu yi magana ta nutsuwa ita ce; kin yi min kama da matata ne, matar da ban saki ba har gobe, amma na neme ta na rasa
Ya karasa maganar da kasalallen murmushin sa na gefen baki.

Ina so in tabbatar ne, I just want to confirm ko Kulsumu na ce wannan....I just want to confirm idan matata UmmuKulsum da na rasa nake nema ce
I just want to confirm idan reaction dinta saboda gani na a inda ba ta yi tsammani ba, yana nufin itama ta gane ni ne take pretending....ko kuwa wani abin ne daban ya firgita ta ta ke gudu tana neman mafaka
Kafin ya rufe baki Kulsumu ta amsa,
ni ban gane ka ba, babu wani sani da na yi maka.

Ban sanka ba, ban taba ganin ka ba, sannan ni matar aure ce, kuma tare da mijina ka gan ni, amma ka sa aka rufe min kofa saboda tozarci, saboda ka sato ni ka kawo ni guest house.

To tsakani na da kai Li
ilafi dubu
Turaki ya yi wani murmushi, wani tattausan murmushi da rabonsa da yin emotional murmushi irin sa ba zai iya tunawa ba.

He salute her courage!

Yau ji yake babu wanda ya kai shi sa
a a duniya, babu wanda ya kai shi samun cikar buri.

Ashe zai ga Kulsumu komai daren dadewa!

Sai dai kuma watakila ganin nata ya zo at a wrong time, idan har abin da ta ke fadi gaskiya ne na cewa (wanda suke tare mijin ta ne).

Idan har wannan ikirarin nata gaskiya ne, shi ya ya zai yi da rayuwar sa?

Saboda ita ne har yau bai kara aure ba.

Saboda ita ne har yau babu diya macen da ke burge shi.
Chapter 1 · 0% Book details