← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 20

Sashe 18

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In dai diaper ce ta sa min mata kuka, sai a bar ta, babu dole
Kulsum ta shafe hawayen ta, a hankali ta ce, "Ba kukan diaper nake ba, kuka nake don tausayin ka, ka auri wahala...

Ka auri kazanta.

Yet ba ka taba nuna min gazawar ka ba.

Ba ka taba nuna kyama a gare ni ba.

Don Allah Prince ka kara aure...

Wallahi na amince, in ba haka ba sai alhakinka ya hana ni warkewa".

Murmushi Turaki ya yi, ya ce, "Well, mu bari after surgery in ba ki warke din ba sai ki zabo min mata na aura.

Amma ni ba ni da idon kallon mata.

Mai fitsarin kwancen kawai ido na yake iya hangowa".

Za ta iya cewa ba ta taba jin kalmar da ta yi mata dadi a rayuwar ta irin wannan ba.

Ko da kuwa Turaki ya fada ne don ya faranta mata kadai ba don haka abin yake a zuciyar sa ba.
*****
Washegari aka shiga da Kulsum dakin tiyata.

Bayan sun yi wata irin sallama da mijin ta Turaki 'very emotional'.

Ya sumbace ta a goshi da hanci.

Ya ce, "Insha Allah lafiya za ki tashi Kulsum, kuma da yardar Allah wannan shi ne karshen wahalar ki".
*** *** ***
A rayuwar Dr.

Ibrahim Takai, bai taba yin 'surgery' ko 'kidney transplant' an samu kuskure ba, to haka ma a wannan karon yana kyautata zaton samun nasara a aikin da ya yi wa Ummu Kulsum.

Amma ba za a gane hakan ba sai nan da wata daya.

Kulsum za ta ci gaba da zama a gadon asibiti.

A wannan lokaci jinyar duk wata kulawa da soyayyah Kulsum ta same su daga mijin ta Turaki.

'The one in million husband', wanda ta ke fatan har a lahira Allah ya tashe su tare matsayin abokan rayuwar juna.

Bayan 'surgery' da jinyar wata guda, sun ci gaba da zuwa 'check up' a asibitin 'Royal Berkshire' hannun likitan da Dr.

Ibrahim Takai ya yi 'referring' din su, wato Dr.

Kennedy baturen Worcaster, shi din 'kidney and bladder specialist' ne da ake ji da shi a asibitin nasu.

Yayin da Ibrahim Takai ya koma Illinoise wajen Rayhanar sa,bayan ya gama aikin da ya kawo shi Reading.

A duk sanda suka zo 'check up' Dr.

Kennedy na fada musu aiki ya yi kyau.

Akwai ci gaba sosai, da taimakon Ubangiji wannan karon Kulsum ta rabu da lalurar 'Nocturnal Enuresis'.

Ranar 'check up' din su na karshe likitan ya yi murmushi ya dube su.

"Congratulations Mr. and Mrs.

Abubakar Turaki Abdullahi, your wife is finally saved from bed-wetting". (Matar ka ta kubuta daga lalurar fitsarin kwance).

Ya kara murmusawa ya ce yana bai wa Dr.

Abubakar shawarar ya dauki hutu domin ya murmure daga jinyar nan da ya sha, su je garin Chelsea su huta.

Dariya Turaki ya yi ya dubi Kulsum, wadda ta sadda kai kasa, hawayen farin ciki na zuba daga idanun ta.

A haka Turaki ya kama hannunta suka bar gaban likita bayan ya yi masa godiya sosai.
*** *** ***
"Shi ke nan yanzu kuma sai mu fara shirin zuwan amarya tunda uwargida ta warke?" Turaki ya fada a lokacin da ya zura mukulli yana bude kofar 'apartment' dinsu.

Kulsum ta yi gumm!

Kamar ba ta ji shi ba.

Ya sake maimaita abin da ya fada, ta dauke kai ta shige dakin ta.

Wanka ta yi, ta yi kwalliya irin wadda tun zuwansu U.K ba ta taba yi ba saboda rashin kwanciyar hankali.

Ta yi alkawarin ingantawa Turaki daren yau da dukkan iyawar ta, domin nuna masa godiyar ta ga dumbin lkhairin sa da soyayyarsa gare ta.

Wata irin doguwar riga ta saka mai bin jiki da aka yi da yadin 'velvet', ta bi fatar jikin ta ta kwanta lambam.

An tsaga ta tun daga idon sawu har zuwa gwiwa ta yadda santala-santalan kafafunta suka fito 'freely' in tana tafiya.

Ta feshe jikinta da turaren nan na mata mai dadin kamshi COOL WATER (Davidoff).

Gashin kanta da ba wani yawa ne da shi ba sai salki da cika irin na fulanin Gaya ta raba biyu ta tufke shi gefe-da-gefe.

Ba ta taba shafa 'lip-stick' ba tun auren ta da Turaki sai yau.

Ta shafa shi kalar 'light pink' samfurin avon.

Ta taje gassun idon ta da girar idon ta da 'mascara' nan da nan fuskar ta ta zama 'cute' ta yi kyan da ba ta taba yi ba.

A hankali Kulsum ta ke taku kamar a filin fashion-parade tana ta faman shige da fice a gaban Turaki, wanda ya baza takardu a falo yana ta aiki cikin 'macbook' din sa.

A hankali ya cira kai ya dube ta za ta wuce rike da robar 'ice-cream' a hannun ta.

Ya dan kara girman idanun sa yana kallonta sosai.

Bai san sanda ya ce,
"...Come here baby...".

Ta rangwadar da kai, "Ba aiki ka ke ba Prince?"
Ya ture 'macbook' din gefe, ya ce,
"Na ce ki zo koh?"
Ta tako a hankali tana shan 'ice-cream' din ta debo kadan ta nufo bakin sa, yayin da shi ba ta wannan yake ba, kokari yake don ganin ya zuge zib din rigarta gabadaya, yana fadin.

"A duniya akwai mai hakuri iri na?

Quite three months ba tare da mata ta ba...".

Kulsum ta sakar masa komai, tare da inganta masa daren yadda ya kamata.

Ita kanta wani abun bata san ina ta koyo shi ba.

Ta dai sa wa ran ta ne za ta yi komai don ta faranta wa Turaki.

Rayuwar ta kacokam fansa ce ga farin cikin sa.

Daren ya kasance musu tamkar a ranar suka taba kusantar juna, ya shige cikin darare masu dumbin tarihi da suke adanawa a kundin rayuwar su.

Washegari suka shirya suka tafi Chelsea, kwanan su uku a 'hotel' din 'The Chelsea Harbour Hotel' suna gwangwaje soyayyah zallah, ko wayoyin su kashewa suka yi.

Sai lahadi da daddare suka bi 'train' suka koma Reading.

Rayuwar auren Kulsum da Turaki kenan, rayuwa ce wadda aka gina bisa soyayyah, kauna ta fisabilillahi da yarda zallah, wadda biro ya yi kadan ya bayyanata.

Sun gina rayuwar auren su ba don kyale-kyale na rayuwa ba.

Babu sirrin junan su da ba su sani ba.

Yo mijin da ki ke yi wa fitsarin kwance ya wanke ai zance ya kare.

Turaki ba ya boye wa Kulsum komai da ya shafe shi, ko da a fannin aikin sa ne.

Da hankulan su suka natsa ne ya gane Kulsum na da matsala a ido.

Sai lokacin ne ya tuno zuwansu European Eye Hospital a Lagos ita da Taufeeq, ya tsare ta da tambaya kan me ya kai ta ranar?

A nan ne ya san matsalar idon Kulsum ta tun haihuwa.

Mai abu da abunsa, wani ma ya yi rawa bare dan makadi?

Tuni ya sa ta a gaba da bincike da gwaje-gwaje, a nan ya gano tana dauke da matsalar da suke kira amblyopia (lazy eye), wanda magunguna na digawa (eye drops) kadai zai magance shi ba sai ta saka gilashi ba.

Tun daga ranar ya soma diga mataeye drops masu kyau har suka washe.
*******
Ranar ta kasance juma'a, da wuri Turaki yake dawowa gida.

Ya shigo a matukar gajiye, Kulsum na zaune ta bararraje tana shan 'ya 'yan 'strawberries' in zai iya tunawa yau wajen sati guda ke nan ba ta da abinci sai 'ya'yan 'strawberries'.

Ta kashe shi da murmushi, ya ce, "Kulsum are you alright?

Cin wannan abun naki ya yi yawa fa".

Ta yi narai-narai da ido, "In ban ji shi a baki na ba sai in ji saliva (miyau) ya cika min baki".

Murmushi ya yi ya aje jakar hannun sa da falmaran din 'suit' din jikin sa akan kujera.

"Then, you are subject to P-t (pregnancy test)".

Zaro ido ta yi abin dariya, "Haba Prince!

'yar yarinya ta da ni za ka yi min wannan fatan?"
Dariya ya yi, ya iso gare ta ya mikar da ita tsaye.

Ya jingina bayanta a jikin sa ya daga rigarta da hannun damansa yana shafa shafaffen cikin ta cikin shauki.

"In mace ce, Batulu ce.

In namiji ne Abdul'Ahad ne.

Su suka taimaka min na same ki 'for the second time', a lokacin da na riga na sa a raina na rasa ki, ciwon son ki kuma shi ne zai yi ajali na.

Sun ba ni 'support' din su dari bisa dari tare da tabbatar min ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

With Almighty Allah everything is possible".

Kulsum ta yi murmushi, ta ce, "Ni dai ban fada maka ina da ciki ba".

Ya ce, "Amma kin iya sa miji a daki kina k......".

Da sauri ta kwace jikin ta daga nasa ta yi daki, tare da sa yatsun ta biyu ta toshe kunnen ta.

Turaki bai yi shiru ba sai da ya karasa mata.

Ya kuma tabbata zahiri Kulsum na da karamin ciki na watanni biyu, lokacin da Turakin ya gaji da ciye-ciyen ta ya kai ta 'lab' aka auna fitsarin ta.

A wannan satin suka shirya zuwa Manchester wajen su Sajeedah.

A 'train' suka tafi zuwa Manchester.

Sajeedah da Abdul'Ahad suka shirya musu tarba ta musamman za su yi weekend (hutun karshen mako) tare da su.

Amma kasancewar gidajen U.K kanana ba 'spare room' dole sai a 'hotel' suka sauka.

Da safe wanka kawai suka yi suka shirya Abdul'Ahad ya zo ya dauke su zuwa gidan su.

A can suka yi 'breakfast', Kulsum da Sajeedah suka wuni hira, Sajeedah na kara wayar mata da kai a kan rayuwar duniya gabadaya.

Da yamma suka debe su a motar Abdul'Ahad don su zaga da su cikin Manchester, inda suka ziyarci 'Greater Manchester, Castle Field, National Football Meseum, Man City and Man United' da suke jin labari.

A karshe suka dire a 'university of Manchester' jami'a mai tsohon tarihi.

Sun rabu kamar kar su rabu, a lokacin cikin Sajeedah watanni bakwai.

Burin Sajeedah ya cika ta zama 'best friend' din Kulsum, abin da ba ta taba yi a rayuwar ta ba (kawa) bayan Batulu.

Ba tare da shawara da ita ba Turaki ya cike mata 'application' na neman gurbin karatu.

Babu jimawa 'admission' dinta ya fito, ya kawo mata har kan cinyar ta.

Kulsum ta daga takardar tana karantawa a hankali.
Chapter 18 · 0% Book details