← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 20

Sashe 14

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Za mu yaki wannan matsalar tare) insha Allahu.

Just relax and pray.

Yanzu zan je in ga Maimartaba akwai inda za mu je sai dare zan dawo.

Me ki ke so in taho miki da shi?"
Hawayen farin ciki suka zubo daga idanun Ummu Kulsum.

Ba ta taba tsammanin martanin da za ta samu daga Turaki ke nan ba.

Ta kara gamsuwa da cewa....this is not the previous Turaki
wannan wani sabon Turaki ne, mai dauke da kauna ta ban mamaki a gare ta.

"Ba abin da nake so sai kai Prince dina
.

Ta fada tana kwantar da kai a kirjin sa.

Kaso tamanin cikin dari na tashin hankalin ta ya kau.

Ya dan bubbugi bayan ta, ya ce,
In dai Turaki ne kin samu, I
m only yours.

Zan kawo miki waya sabida su Goggo, amma ban yafe ba in ki ka yi magana da Taufeeq
Ta lumshe ido tana murmushi, ta ce,
Ko ka yafe ba zan yi ba.

Bana neman komai daga sauran maza, you are more than enough to me.

Allah ya bar mu tare cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi
Sosai Turaki yake kissing din kowacce halitta ta fuskar Kulsumu, ido, hanci, goshi, da baki sai da suka karbi rabon su na sassanyar passionate kiss daga Yarima Abubakar Turaki.

Sannan da kyar ya janye ya gyara zaman hular sa ya fice da gudu-gudu sauri-sauri ganin sunan Maimartaba a kan fuskar wayar sa.

Kulsum ta bi shi da lallausar murmushi.

Ji ta ke kamar su dauwama cikin wannan yanayin da ba ta taba samun kanta a mai dadi da sanya nutsuwar sa ba.

Ko da ya dawo a ranar kin zuwa dakin sa ta yi, har yanzu kunyar ba ta sake ta ba.

Ta yi shirin kwanciya ke nan sai ga shi ya shigo, tun daga bakin kofa ya jefa mata harara.

Me ki ke nufi da ni ne matar nan?

Ina ta jiran ki ki zo mu cike wasu takardu, kin barni ni kadai?

Shirin kwanciya ma ki ke yi abun ki alhalin ga turakar mijin ki?

Kulsum ta langabar da kai abin tausayi, ta ce kasa-kasa.

Ina tsoron kada ya kara zuwa ne
Ya sa hannu ya dago habar ta, murmushi ya sakar mata wanda ya ratsa har cikin ruhin ta.

Sannan ya sumbaci bakin ta ya ce,
To sai me?

Har na sayo mana injin wanki da katon din hypo da na omo (Ariel).

In mun yi sai mu wanke.

Watarana sai labari
Da karfi Kulsum ta kankame shi tana wani irin kuka.

Gabadaya ya daga ta suka fice daga dakin.

Cike takardu bai yiwu ba a wannan dare, domin ya kasance daren rahma ga ma
auratan, sun raya shi har yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba.

Amma a karshe Kulsum ta ki yarda barci ya dauke ta, tana kallon Turaki yana barcin sa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali irin wanda miji ke samu idan ya samu kyakkyawar gamsuwa daga matar sa.

Sai zarya ta ke daga gadon zuwa toilet tana kakalo fitsari.

Ba ita ta kwanta ba sai da suka yi sallar asubahi, Turaki ya dube ta tana lazimi idanun ta sun yi luhu-luhu.

Ya daure fuska sosai ya ce,
Look, hau gado ki kwanta sai karfe goma na yarda ki tashi daga barci.

Wannan daura wa kai wahala har ina?

Ina ce katifa dai tawa ce ko?

Zanin gadon ma nawa ne ba naki ba?

Ta sunkuyar da kai tana murmushin maganar sa, soyayyarsa na karuwa a zuciyar ta.

Oya!

Hau ki kwanta tun ban canza manufa ta ba
Ta gane me yake nufi, don haka ta ja jiki zuwa gadon ta kwanta a dofane, ya jaquilt ya rufe ta da kansa.

Tare da sunkuyawa ya sumbaci goshin ta.

Ta yi barci kuwa sosai, domin kuwa shi ba'a cin bashin sa.

Sai dai kuma ta tashi ne again cikin yanayin da ya fi na jiya.

Turaki yana dining yana karyawa da abincin da Laraba ta tanadar musu.

Sai da ya gama ya dawo dakin, ya shiga toilet ya yi wanka ya fito yana zaben kayan da zai sa ba tare da ya san halin da Kulsum ke ciki ba.

Ta sanya kanta karkashin filo tana kuka, wanda da hawaye kawai ta ke yin sa babu sauti.

Ba ta so yau ma ya yi aikin fitsari shi ya sa ta sa hannu ta toshe bakin ta.

Sai da ya gama tsaf!

Ya fesa turarensa one man show, sannan ya iso gabanta don ya duba ko ta tashi.

Filon da ta danne kanta da shi ya dauke,
Kina so ki danne numfashin ki ne?

Gani ya yi wajen ya jike sharkab da hawaye.

Nan ya gane halin da ta ke ciki.

Fuskar sa ta nuna damuwa ya ce,
For God
s sake Kulsum, wannan kukan ne zai yi maganin lalurar?

Duk abin da na gaya miki bai shiga kunnen ki ba.

In dai a kaina ne ki ke shiga wannan halin ni kam kina zaluntata!

Damuwar ki da fitar hawayen ki sune manyan damuwa ta ba fitsari ba.

Idan
depression
ya kama ki ba zan yafe miki ba
Da kyar ta mike cikin tsananin jin kunya, ya taimaka mata ta hanyar kama hannun ta ta mike ta shige toilet.

Ya yaye zanin gadon, amma wannan katifar in ba ta sha rana ba yau akwai matsala, domin ko an goge da omo sai ta yi warin damshi.

Tana fitowa ta same shi ya balle links din hannun rigar shi ya kwance botir din wuyansa ya zage yana goge katifar.

Kifa kai ta yi a jikin bango tana hawaye.

Turaki ya yi kwafa ya ce,
Ki yi abin da ki ke ganin shi zai fishsshe ki
Duk runtsi ba zai fidda katifar nan waje ba sabida
yan aikin su, balle Laraba da yake da masaniyar ta san Kulsum na da lalurar.

Ya rasa yadda za su yi da katifar, ya dai sakar mata fanka ta sama da ta kasa.

Ya canza kayan jikin sa ya je ya shigowa da Kulsum abin da za ta ci.

Da kyar ya samu ta iya cusa dankali biyu a bakin ta.

A ran ta ta yanke ba za ta kara kwana dakin Turaki ba duk abinda zai ce mata gara ta je ta yi ta kazantar ta ita kadai a dakin ta.

Tea din nan sai kin shanye shi, in har kina son zaman lafiya Kulsum".

Ka yi hakuri Prince, ba ni da appetite, wallahi na tsani kaina!

Turaki ya tsura mata ido, kalaman rarrashi sun kare masa.

A irin wannan stage din ne mata da yawa ke haduwa da depression wanda zai iya yin sanadin suicidal thought.

Ya ajiye kofin shayin ya matsa gare ta ya rungume ta.

Ta kwantar da kai a kan kirjinsa tana ta sharbar kuka.

Ya ce,
Is o.k Kulsum, na san abin da ki ke ji.

Amma don Allah ki kwantar da hankalin ki, wannan lalura ba kanki farau ba, mata da yawa suna fama da ita, wani lokacin ma har maza.

Tun jiya na yi magana da kwararren nephrologist din da zai duba ki Dr.

Ibraheem Mansur Takai (Rayuwar Rayhana).

Za mu hadu da shi a U.K, zai zo asibitin da nake daga Illinoise (Chicago) kan wani aiki da za mu yi tare.

So relax please, stop these waste of tears, ni ko ba ki warke ba ina sonki haka!

Zan kuma ci gaba da zama da ke cikin kowanne hali, to the very end
Kulsum ta shafe hawayen idanun ta, har yanzu kanta na bisa kirjin Turaki, ta ce,
Watarana za ka gaza
watarana za ka auro wata
in ta gane zan wulakanta
zan tozarta
Hannu ya sa ya toshe mata baki.

Ban yi miki alkawarin har abada ba zan kara aure ba, tunda Ba-sarake ne ni.

Amma Kulsum ko aure ya kama ni sai na tabbata kin warke.

Ba dai in yi aure saboda lalurar ki ba, don Allah ki kwantar da hankalin ki
Kara shigewa jikin sa ta yi tana jin kanta tamkar a kan gajimare.

Turaki ya gama yi mata komai a rayuwa, Allah ya sa ya tabbata a hakan.

Now, gaya min treatments din da ki ka taba karba a asibiti, in cike a wadannan takardun zan tura wa Dr.

Ibraheem
Tiryan-tiryan ta soma gaya masa tun zuwanta Lagos gidan Aunty Sakeenah, treatments din da ta karba; pharmacological and non-pharmacological.

Result din da treatments din suka bayar.

Kwayoyin maganin da aka dora ta a kai, wato tricyclic antidepressants, tofranil (imipremine) da kuma (desmopressin acetate) da ta jima tana sha.

Ta kuma daina sha ba tare da likita ya dakatar da ita ba, sai don a tsammanin ta ya tafi ke nan.

Duka Turaki ya shigar da bayanan, sannan ya tura wa Dr.

Ibrahim ta email din sa.

Ba jimawa response din sa ya shigo, inda ya ce ya amince zai ga Kulsum a U.K sati uku masu zuwa.

Turaki yake gaya mata da ma hutun da ya dauka na aure na wata daya ne, don haka za su koma a daidai lokacin da Dr.

Takai ya diba musu.

A nan ta ke ji ya zo Lagos ne ziyarar aiki ba'a can yake ba dindindin.

Yana aiki ne da asibitin koyarwa na jami
ar Reading wato Royal Berkshire Hospital wanda reshe ne na NHS Foundation.

A nan ne ta san abubuwa da yawa game da Turaki wadanda a baya ba ta sani ba.

Har haduwar su a jami
ar Reading shi da Abdul
Ahad da irin abotar da ke tsakanin su, da rawar da ya taka wajen taimaka mishi ya same ta.

Ya dube ta ya yi murmushi,
Shi ya sa na dame ki sosai kan ki karbi bakuncin su, they are your real supporters
Yana kwance rigingine da laptop a kan kirjinsa yayin da kansa ke bisa cinyoyin ta suke hirar, a lokaci guda yana processing visa dinta ta shiga U.K as his spouse.

In ka gan su sai sun ba ka sha
awa, yatsun ta cikin sumar kansa wai kitso ta ke mishi cikin tarin kwantacciyar sumar sa duk ta duddunkule mishi gashi, ko kofar gida yau bai fita ba, duk don kada ya fita Kulsum ta koma cikin damuwar ta.
Chapter 14 · 0% Book details