← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 20

Sashe 17

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da wasa Kulsumu ba ta yi zancen fitsarin ta ba, ba ta so ta kara daga wa kowa hankali, wahalar da suka sha a baya Allah ne kadai zai biya su da mafificin alherin sa.

Sai karfe goma suka bar gidan, domin hira ce sosai ta shiga tsakanin Turaki da Hajiya Nasara, kasancewar su duka mazauna Birnin Sarauniya.

Hajiya ta ce, ta taba zuwa Reading Berkshire, kuma insha Allah ba da jimawa ba in sun shigo London za su zo har Reading su gan su ita da Daddy.

Ko da suka koma hotel gajiya ba ta bar su sun tsinana komai ba.

Amma Kulsum ta ki yarda ta kwanta don kada ta yi fitsari.

Ta hau kujera kwalli daya da ke dakin ta kishingida tana faman daddanna wayar ta.

Turaki ya kwace wayar, ya kuma kashe fitila mai haske ya ce,
Malama ki kwanta please, gobe asubanci za mu yi, is good ki samu barci ko yaya ne
Ta bi umarnin sa ne kawai don ta san ko me za ta ce ba zai kyale ta ba.

Suka kwanta Kulsum kalmashe cikin jikin sa.

Amma ko na sekon daya ba ta bari barci ya dauke ta ba.

Ta lafe a jikin Turaki tana sauraron yadda yake sauke numfashi a hankali, ita ina ta ga wannan kwanciyar hankalin?

Ta lura Turaki na jin dadin barcin sa, don haka ba ta nuna wata alama da za ta nuna idanunta biyu ba, har lokacin sallar asubahi ya yi.

Karfe shidda wanda zai kai su filin jirgi ya kuma tafi da motar Turaki ya zo, wani abokin sa ne Dr.

Habib mazaunin Abuja.

Sun bata lokaci wajen screening da zaman jiran jirgi ya daidaita.

Karfe goma sha daya na safe jirgin su ya tashi zuwa United Kingdom.
*** *** ***
A cikin jirgi ne Kulsum ta samu ta yi barci sosai a jikin Turaki.

Tafiyar awanni takwas a cikin jirgin British Air ta sauke su a birnin London.

Inda daga nan suka dauki taxi ta kai su tashar jirgin kasa, suka bi train zuwa garin Reading, Berkshire.

Nisan da ke tsakanin babban birni (London) da garin Reading (37 miles) ne, wato tafiyar mintuna arba
in da biyu a cikin jirgin kasa.

Reading babban gari ne mai tsohon tarihi a kan kasuwanci a yankin Berkshire (South-East England).

Gidan Turaki na cikin jerin gidajen malaman jami
ar Reading.

Mai taxi din da ya dauko su har kofar gidan ya sauke su.

Gajiyar da ke tare da Kulsum ta sa ba ta gane komai da ke cikin gidan ba sai washegari.

Gida ne a cikin Estate duka gidajen iri daya ne, masu dakuna ciki-biyu da falo, kowanne daki da toilet manne a cikin sa, sai kicin wanda kofar sa ke cikin falon, sai garden daga wajen kitchen din, mai shimfide da korran ciyayi daga sama har kasa sun yi wa gidan rumfa ruf, gidan karami ne sosai kamar sauran gidajen Estate din, sai dai ya ishi dan Adam duk wasu bukatu na rayuwar sa.

Kwanan su uku ba su je ko
ina ba suna ta fama da fitsarin Kulsumu.

Fitsarin da kamar jira yake su sauka a Reading ya kara ta
azzara.

Hutawar da suka yi niyya duk ba su same ta ba, soyayya an jingine ta a gefe saboda Kulsumun kwata-kwata ba ta cikin hayyacin ta saboda damuwa da tashin hankali.

Ita babbar damuwarta shi ne Turaki zai tsane ta.

Yayin da shi kuma damuwar sa ita ce damuwar da ta ke jefa kanta a ciki, wadda yake tsananin tsoron kada ta taba brain dinta, ta jawo wata matsala wadda ta fi ta fitsarin kwance.

Ya kira Dr.

Ibrahim Takai kan appointment din su na ganin sa, ya ce za su hadu a asibitin nasu Turaki, wato Royal Berkshire Hospital ya zo ziyarar aiki ne daga Illinoise teaching hospital na watanni uku a asibitin koyarwa na garin Reading.

Kulsum ta yi tsai da idanun ta tana kallon Dr.

I.M Takai, ta dauka za ta ga mutum wanda ya manyan ta kamar likitan ta na Lagos, sai ta ga sardidin mijin na Rayhanah Baban Asma
u matashi tamkar nata mijin.

Sun dade suna magana shi da Turaki, da turancin su mai accent wanda ba duka ta ke fahimta ba.

Ya yi mata tambayoyi masu yawa tana ba shi amsa.

Ta kuma gaya masa sunayen magungunan da ta ke sha a baya, da dukkan treatment din da ta karba daga hannun likitan ta na Lagos.

Dr.

Ibrahim ya dube ta sosai, sannan ya ce,
Ina tsammanin kina da karamar mafitsara ko blocked urethra (mafitsara tosasshiya), zan yi miki test har guda hudu; na farkourinalysis, inda za mu dauki sample na fitsarinki mu duba infection acikin sa ko sauran urinary tract infections.

Test na biyu da za mu yi shi ne urine culture, inda za mu tura sample na fitsarin ki zuwa lab don duba ko akwai bacteria ko yeast a cikin fitsarin ki.

Sai test na uku shi ne uroflowmetry, inda za ki yi fitsari a cikin special funnel da za mu ba ki, mu auna yawan fitsarin da ki ke yi and how quickly it flows out.

Sai test na karshepost-void residual urine measurement; wannan test din zai nuna yawan fitsarin da yake ragewa a mafitsarar ki ba tare da ya fito ba duk lokacin da ki ka yi fitsari.

Idan muka yi duk wadannan gwaje-gwaje, za mu gane what are the possible causes na nocturnal enuresis din ki.

Za mu gane blocked urethra ne ko pelvic organ prolapse, ko kuma matsalar daga structure din mafitsarar ki ta ke (wanda na fi tsammani), ko enlarge prostate ne ko urinarytract stones ko infection na mafitsara.

Ki ci gaba da non-pharmacological treatment irin na baya, sannan inaso ki gaya min abubuwa guda hudu.

Karfe nawa ki ke bed -wetting?

Yawan fitsarin da ki ke yi (kadan ne ko mai yawa)?

Yawan abin da ki ke sha kafin kwanciya barci?

Sauran alamomin da ke nuna za ki yi fitsari?

Kulsum ta fada masa duk abin da ya tambaye ta iya sanin ta.

Doctor Takai ya ce,
To yanzu za ki shiga toilet ki ba mu fitsarin ki, mu auna mu gani, sannan akai lab, gobe sai ku dawo mu ga me result ya nuna
Washegari karfe goma na safe suna gaban Dr.

Takai, nan ya gaya musu result din gwaje-gwajensu ya nuna Kulsum na da karamar mafitsara.

Za ta sha magunguna masu karfi ba irin na baya ba na tsawon sati biyu, derifenacin (enablex), oxybutynin (ditropan), tolterodine (detrol) da kuma trospium chloride.

Idan ba ta daina fitsari tsayin wata guda ba za su dawo.

Dole sai an yi surgery.

Sunan surgery din da za'a yi
Bladder augmentation
Dr.

Takai ya ce,
s an operation that makes your bladder larger, which raises the amount of urine it can hold (aiki ne da ake yi wanda zai kara girman mafitsarar ki, ya kara yawan fitsarin da za ta iya rikewa)
Da wannan suka baro gaban likita Takai bayan Turaki ya sayo duka magungunan da aka rubuta musu.

Haka kawai Kulsum ke jin wata irin gamsuwa wannan karon da treatment din gawurtaccen nephrologist Ibrahim Takai, domin kwata-kwata bai yi kusa da wanda ta samu a Lagos ba.

Wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta.

Magungunan sun fi na baya karfi nesa ba kusa ba.

Sai da ta yi sati daya ba ta yi fitsari ba ko sau daya da ta fara shan su.

Murna wurin Kulsum abin ba'a cewa komai, amma Turaki kallon ta kawai yake.

As a medical doctor jikin sa yana ba shi karshen ta dole sai an yi surgery din nan.

Ya koma aikin sa tuni, don haka ita kadai ta ke wuni a gidan, Sajeedah da Abdul
Ahad sun bar Reading sun koma Manchester inda aka yi wa Abdul
Ahad transfer.

Turaki ya mata alkawarin in hankalin su ya kwanta sun gama da asibiti za su je musu har Manchester wajen su.

Ilai kuwa bayan kwana goma sai ga shi ta sake yin fitsari, wanda alama ce da ke nuna cewa, karshen ta surgery zai tabbata.

Turaki bai gaza ba wajen karfafa mata gwiwa kan cewa yana tare da ita cikin kowanne hali, yana son ta a duk yadda ta ke.

Sati hudu suka cika suka koma gaban likita, ko a ranar ma sai da ta yi fitsari, don haka Dr.

Ibrahim Mansur Takai ya sa musu ranar surgery kwanaki biyar masu zuwa.

*****
Ana i gobe surgery din Kulsumu kasa barci ta yi, gani ta ke in ta shiga dakin tiyata ba za ta fito da sauran numfashi ba.

Turakin ta zai zama mallakin wata a bayan ran ta.

Ta yi kuka, ta yi kuka har ta ji babu dadi.

Ko da Turaki ya dawo aiki a ranar ya fahimci ta ci kuka ta gode Allah.

Bai yi kasa a gwiwa ba wajen wanke damuwar ta da nau
ikan soyayyar sa masu tsayawa a zuci.

Da ya fita sai ga shi ya dawo da sinkin adult diaper (pampers din manya) don su huta da wankin zanin gado, duk da yanzu ba ya taba katifar su sabida water mattress ce.

Dr.

Takai ne ya ba shi wannan shawarar ya ce, hakan zai fi musu sauki, after intercourse din su ta sanya diaper idan non-pharmacological treatment ya ki aiki a jikin ta.

Kulsum ba ta taba jin madaukakiyar kunya a duniya irin ta yau ba.

Wane embarrassment ne ya wuce miji ya sanya maka diaper?

Ta jinjina wa Turaki a zuciyar ta, ta amince samun kamar sa cikin maza dubu sai an tona.

She is indeed among the luckiest women on earth (tana daga cikin mata masu sa'a a duniya), amma shi din ko a jikin sa, gaya mata ma yake,
Ba shi ke nan mun huta da wankin bedsheets ba?

Ita dai kunya ba ta barta ta ce komai ba.

Da idanun sa yake lalubo idon ta wanda ya cika taf da hawayen tausayin Turaki.

Ta fi tausayin shi akan yadda ta ke tausayawa kanta.

Ita ke fitsari, amma shi ke cin wahalar sa.

Da suka hada ido ya daga mata gira, a hankali ta ce,
Na gode Prince
Sai ta fashe da kukan tausayin kanta.

Turaki ya janyo ta barin jikin sa yana fadin.
Chapter 17 · 0% Book details