← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 20

Sashe 11

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya kira sunan ta, ba ta amsa ba sai hawayen ta da suke kara gudu, sassanyan kamshin jikin sa na sanya ta cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa, ta daina kokawar da ta ke yi da shi duk jikin ta ya saki.

Abin da yake so ke nan, ta nutsu ta saurare shi.

Ya ce,
Ummu Kulsum ko mene ne a tsakanin mu, komai girman laifi na, ina rokon ki darajar iyayen ki ba don ni ba, ki jingine shi a gefe zuwa kwanaki uku, ki karbi bakuncin babban amini na da matar sa, wadanda suka taso takanas tun daga U.K, saboda su taya mu murnar aure
Kulsum ta kwace jikinta daga nasa, ta juya masa baya.

Har wata murna za a taya a wannan auren na rashin adalci?

Turaki ya kwantar da kai a bayan ta, ya shiga magiya da rokon ta yayin da hannayensa ke shafa kwantaccen gashin kanta, abin da bai taba tunanin zai iya ba a rayuwar sa.

Amma Abdul
Ahad na da babban matsayi a wurin sa, duk da ya san komai ba ya so ya tozarta a idanun Sajeedah kamar yadda ya tozarta a gaban Batulu, domin ya lura da gaske ta ke son Kulsumun, dole ya nemi hadin kanta kafin ya kawo ta.

Kulsumu sai ta sa masa kuka, ta ce,
Ni ina ruwana da abokin ka balle matar sa?

Ce musu ka yi auren soyayya ka yi da zan nuna musu ina son auren ka?

Ai gara ma ka fada musu gaskiya cewa, yaudara ta ka yi ka dawo da ni gidan ka
Ajiyar zuciya ya yi, ya ce,
Duk na amince, atleast forget everything sai sun tafi, sai ki ci gaba da gasa ni yadda ki ke so, in ci arzikin su.

Ko a lahira wani kan ci albarkacin wani.

Kada ki manta bakon ka Annabin ka
Ba ta ce komai ba, amma reaction din ta ya nuna sassauci, ya mike daga gadon ya kunna fitila jin ana ta kiraye-kirayen sallar magriba.

Ta ja quilt din ta rufe har kanta.

Ya yi kwafa, ya ce,
Lokacin ki ne, ki ci gaba da wulakanta ni son ran ki, ni na jawo da na saka miki ido har zuwa yau.

Da na bambanta miki da da yanzu, da ba ki raina ni har haka ba
Kyabe baki ta yi a cikin quilt din, kamar yana ganin ta.

Ya ce,
Zan dauko su idan na yi sallah, Umma za ta aiko da duk abin da za su ci.

Don Allah Kulsum ki taimake ni, irin dan murmushin nan na mata da miji da caring din da mace ke nuna wa mijin ta.

Ni kuma na yi alkawarin in sun tafi duk abin da ki ke so zan yi miki
Da sauri ta ce,
Ba abin da nake so illa ka daina shigo min daki.

Ba za ka taba samun yadda ka ke so a tare da ni ba.

Me ya hana lokacin da ni ma nake bukatar kulawar ka a baya ka kula da ni ka tausaya mun?

Ka kaunace ni?

Amma sai ka tsallake ka bar ni?

Sai yanzu don na zama mutum?

Wallahi ba zan taba mantawa da ko wane ne Turaki ba.

The vicious
the selfish
the rapist
. (Mugu, mai son kai, mai fyade).

Runtse idanun sa ya yi, ya ce,
Ummu Kulsum, ki san abin da ki ke fada min, I
m your husband no matter what, ki tuna mala
iku suna tare da ke.

Ashe da ma akwai rape a cikin aure?

Idan na ce miki nima a lokacin ban san yaya ake auratayyar bafa?

Abin da zan ce shi ne, ki yi hakuri ki hadiye komai just for three days, ......please".

Ya fada cikin roko.

Shiru ta yi tana kara boye kanta cikin quilt, ba ta son kallon wadannan idanun na Turaki, wadanda ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu.

Yau ga Turaki ta samu, amma zuciyar ta ta kasa karbar sa.

In je in taho da su Kulsum kin amince?

Please Kulsum just for three days
Ta gaji da magiyar sa, kamar ba Turaki ba, wannan Prince din mai ji da kan sa, ciki-ciki ta ce,
na amince
Sosai fuskarsa ta washe ba tare da sanin sa ba, ya yi murmushin nan nasa na gefen baki.

Inyaso in sun tafi sai a cigaba da gasa ni, ko a yi gunduwa-gunduwa da ni, Allah Sarki ni Abubakar
Ya fice yana cewa,
Ki tashi ki shirya yanzu za mu shigo
Ko amsa ba ta ba shi ba, ya bude mata toilet da kofa da ya rufe ya fice har wata irin sassarfa yake don farin cikin ya fara samun kanta.

Masaukin su Abdul
Ahad ya koma ya samu duk sun kimtsa, shi suke jira.

Sajeedah ta dauko
yar trolly din da ta zuba kayanta suka tafi.

Tun fitar sa Kulsum ta mike daga gadon, wanka ta sake yi, ta fito ta shirya sosai.

Wata shadda Ghanilla ta saka mai babban dinki senegalese ruwan goro, ta sha aiki daga sama har kasa.

Ta kawo mayafin da ya dace da kayan ta yafa.

Tana fitowa falo ta tarar Umma ta aiko
yan aikin ta sun kawo abincin da bakin za su ci.

Ta jera komai a dining ta kunna turaren oud a burner, gidan gabadaya ya dau sanyin kamshi.

Tana kokarin kunna talabijin ta ji sallamar su.

Turaki ne a gaba, Abdul
Ahad ya biyo bayan sa.

Sai wata kyakkyawar mace son kowa, wadda kallo daya ta yi mata ta gane zubinta ba na matan Nigeria ba ne.

Ta amsa sallamar su, tare da karasawa ta karbi jakar hannun Sajeedah.

Murmushi suka yi wa juna ta yi musu jagora zuwa cikin falon, amma ta kasa hada ido da Turaki, balle ta yi masa abin da yake so, don ita ba ta iya pretending a komai ba.

Yanzu-yanzu idanun ta zasu bada ita.

Sai dai ta sa a ranta ba za ta yi abin da zai bata ran shi ba, don ta lura kwarai yake ji da bakin nan nasa.

Sosai Sajeedah ta ke kallon Kulsum, ta yaba da nutsuwa da kamalar ta.

Kyau kam akwai shi, amma ba na tada hankali ba.

Irin dai na fulanin Gaya.

Farat daya ta ji Kulsum ta shiga ran ta.

Duk yadda Turaki ke son su hada ido ta ki yarda.

Ta kai kayan Sajeedah har bedroom din ta, ta dawo ta zauna a kusa da ita, sannan ta yi musu tayin cin abinci.

Gabadayan su suka hau tebir ta yi serving kowa, making sure ta fara serving Turaki first.

Wannan abu ya yi masa dadi, har ya samu karfin gwiwar yi mata magana.

Sajeedah ta ce a wajen ki za ta sauka
Ta yi fara
a sosai tana duban Sajeedah,
You are most welcome Aunty Sajeedah, na gode sosai da wannan karramawa
.

Ta fada da harshen Turanci, kasancewar ta gane Sajeedah ba ta jin hausa.

Sajeedah ta ce,
Da fatan ba zan takura wa amarya da ango ba. ina so mu saba ne, mu fahimci juna.

Wannan ne karona na farko na zuwa kasar Nigeria.

I
m Eritrean
Dr.

Abdul
Ahad ya ce,
To fadi ba a tambaye ki ba
Kulsum ta yi
yar dariya, tana son mutane irin Sajeedah, haka suke open minded, sannan ba sa bakunta a duk inda suka samu kan su.

Mazan suka koma tsakiyar falo suna hirar da ta shafe su.

Ta ja Sajeedah suka yi dakin ta.

Sajeedah ta ce,
Ni fa na sanki ba tun yau ba, labarin ki iri-iri babu wanda ban sani ba
Mamaki ya kama Kulsum, ta ce,
ke kuwa a ina ki ka san labari na?

Duk cikin harshen turanci suke magana.

Sajeedah ta ce,
Duk wanda ya san Dr.

Abubakar farin sani ya san ki Kulsum, ki gode wa Allah ba karamin so mijin ki ke miki ba.

Har ya yi rayuwar dalibtaka zuwa ta aiki a jami
ar Reading Dr.

Abubakar ba shi da budurwa.

You are his only love tun daga sanda ya rabu da ke har zuwa yau da ya kara samun ki.

Na san za ki yi mamakin dalilin da ya sa na nace sai na sauka a wurin ki.

To babban dalilin shi ne, don in labarta miki yadda Turaki ya kwashe shekara da shekaru a cikin soyayyar ki, da neman inda zai gan ki.

Babban burin kowace diya mace shi ne ta auri mijin da ke son ta, fiye da son da ta ke yi masa.

In haka ne kuwa ke kam Kulsum kin dace, sai in ce ki kara rike mijin ki da daraja, soyayya da kauna don ki kara nesanta zuciyar sa daga sauran mata".

Idanun Kulsumu suka cicciko da kwallah, ta ce,
Sajeedah, Turaki ya yi min laifi da yawa, laifin da zuciya ta ta kasa yafe masa
.

Ta labarta mata komai, na rayuwar su ta farko, amma ban da zancen fitsarin kwancen ta.

Da haduwar su a Lagos, da yadda ta gan shi a matsayin mijin ta na biyu.

Ta share hawayen ta, ta ce,
In ke ce za ki yarda yanzun da gaske yake son ki?

A lokacin da na so ya so ni, zuciya ta ta ke matukar son sa duk bai so ni ba, sai lokacin da na yi yaki da ita na fidda shi da komai nasa a rai na?

Sajeedah ta dafa kafadun ta biyu, ta ce,
Na fahimta Kulsum, shi da ma aure na hadin iyaye ai haka yake, soyayya ba ta zuwa farat daya, tana zuwa ne gradually along the way a cikin rayuwar aure.

So ki bude zuciyar ki ki karbi soyayyar mijin ki a wannan karon, ku mori rayuwar ku tare.

Ki manta da duk abin da ya faru a baya, tabbas Turaki bai kyauta ba, amma ki dauki hakan as a system of understanding one another ke da Turaki.

Ki daina waiwayen abin da ya riga ya faru, just the present.
Chapter 11 · 0% Book details