← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 20

Sashe 7

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya yi mai sauti ta cikin wayar, ya san albishir din ba zai wuce a kan Kulsumu ba, the only obstacle of Turaki.

To ko dai ya samo ta ne?

Ya ce,
Kunne na goma sha biyu, plus na Turaki in an hada da nawa sun zama sha hudu kenan
Dariya ya yi, ya ce,
To kai komai sai ka sa wasa a ciki?

I called to inform you yau na zama angon UmmuKulsum for the very second time, cikin yardar Ubangiji da amincewar sa
Dr.

Abdul
Ahad ya ce,
Idan wasa ka ke min, to bana so mu yi magana ta gaskiya
Turaki ya ce,
Na taba yi maka irin wannan wasan?

Well, ba ni da lokacin ka yanzu.

Zan so ka zo Gaya, akwai hawan angonci na musamman da zan shirya next week wanda ba a taba irinsa a Gaya ba.

It''s a promise da na yi da dadewa cewa duk ranar da zan yi auren soyayyah zan yi hawan angonci.

Your Horse is reserved for you (an ajiye maka Dokin ka)."
Zuwa yanzu Abdul
Ahad ya yarda Turaki da gaske yake.

At last ya samu Kulsumu, kowa zai samu lafiya.

Ya ce cikin murmushi,
Dole ne ma in zo, ko don in ga Kulsum, in ga shin me ta taka haka da ta sukurkuta min aboki shekara da shekarusaura kadan yayi asarar likatancin sa a kanta?

Murmushi Turaki ya yi, ya kashe wayar sa ba tare da ya ba shi amsa ba.

Shi kansa in za'a tsare shi ba zai iya fadar abu guda daya da yake son Kulsumu sabida shi ba, ita din bakidayan ta yake so, the whole her. (Dukkanta).
*** *** ***
Umma ta aiko an gaya wa Goggo gobe lahadi da yamma za su dauki amarya, don haka duk wani shirye-shiryen su daga yau zuwa gobe gare su.

Hajiya Nasara ta sa Sakeenah ta hado duka kayan dakin Kulsum da suka tanada ta taho da su Gaya a gobe-goben nan.

Ba ta gaya mata ko me ke nan ba, ta dai ce ta yi kokari ta zo tare da kayan, kuma kada ta gaya wa Nasmah komai kada ta dage sai ta biyo ta ta zo tana haihuwa a kan hanya.

Washegarin ranar Sakeenah ta iso da motocin kaya, Baffa ya bude dakin da ya ajiye wadanda Maimartaba ya aiko wa Kulsumu tun ma kafin auren ya juye kan dansa.

Aka hada da wadanda su Hajiya Nasara suka yi wa Kulsum aka wuce da su gidan Sarkin Gaya inda za a yi wa Kulsumu kafi.

Amma sai Maimartaba ya ce, Turaki ba zai zauna cikin gidan ba wannan karon, sassan ya yi musu kadan kuma ya tsufa, ya mallaka masa sabon gidan sa da ya gama ginawa a bayan gari, don haka can aka wuce da kayan, aka kuma yi wa su Hajiya Nasara da za su yi kafi jagora zuwa can.

Lokacin da su Batulu suka iso, Umma ta gaya musu kome ke nan.

Batulu hawaye ta dinga yi, farin ciki ya kai mata ya kawo.

Ta ce a lokacin za ta tafi gidan su Kulsumu, Ummah ta ce ba ta yarda ta je ta cikata da dumi ba, ta bari sai gobe su je su dauko ta gabadaya.

Dr.

Sakeenah ta ji abin da ya faru, ta yi bakin ciki sosai a kan Taufeeq, ta yi fatan Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi, Ya yi wa Taufeeq sauyin alheri.

Sun je sun yi kafi, suka dawo suna ta yaba tsaruwar gidan, Lami matar Malam Hadi ta rangada wa Kulsumu guda aka ta ce,
Allah ya sa kannen ki a damshin ki Kulsumu, gida kam na duniya kin yi shi, Allah ya sa na lahira ya fi shi
Kulsumu wadda tun wayewar garin yau ta ke risgar kuka, damuwar ta shi ne, wannan aure da Baffa ya yi mata mai kama da auren sadaka da mijin da ba ta san ko waye ba.

Duk maganganun da mutane ke yi a kan gidan wanda suka je kafi suka dawo ko daya bai burge ta ba. za ta fi so a ce Baffa ya yi hakuri ya kara mata lokaci ta kawo masa wani mijin, tunda ba su karbi nadamar ta a kan Taufeeq ba.

To shi wannan din an san nasa halin?

Kada dai ta yi gudun gara ta tadda zago.

Kada garin neman gira ta rasa ido.

Allah ya sa dai Baffa ba kudi ya gani ba, tunda yana ikirarin sadakin ta duk Gaya ba
yar wanda ta samu kamar sa.

Su kuma ga su sun zo suna santin gida.

Amma da ta tuna ko wane ne Baffan nata, ta san hakan ba za ta taba faruwa da shi ba.

Ba ta samu kebewa da Babanta Malam Hadi ba sai da ya zo tafiya bayan daurin aure, kasancewar shi ba zai kwana ba, amma su Lami duk suna nan sai sun raka Kulsumu dakin ta.

A zauren farko suka tsaya sabida yadda gidan ke cike da jama
a.

Ya dubi Kulsumu wadda idon ta ya yi kozai-kozai don kuka, babu wata kwalliya ta amare a tare da ita.

Haushin kowa ta ke ji, musamman Baffa.

Ko da Aunty Sakeenah ta yi mata magana kan ta canza kayan jikin ta ko hoda ce ta shafa kuka ta fasa mata.

Kukan da ya sa dole ta kyale ta, don ita Sakeenah ba ta son kuka a rayuwar ta.

Malam Hadi ya ce,
Kulsumu komai ki ka ga ya faru da bawa, da ma rubutacce ne a lauhul mahfuz, wani ba ya auren matar wani kamar yadda wata ba ta auren mijin wata.

Ki sa a ranki duk mijin da Allah ya zaba miki shi ne alherin ki.

Na ji an fasa aure da shi wannan yaron dan wajen marikiyar ki sabida wasu matsaloli da suka taso.

To dama ni tun farko na amsa ne sabida karamcin iyayen sa gare ki, amma Kulsumu na fi so ki koma gidan tsohon mijin ki.

Hausawa suka ce da sabon gini gwanda yabe, su kam ai sun sanki ciki-da-bai din ki, babu wani abu naki da zai zame musu sabo, ke ma kuma in kin nutsu kin kwantar da hankalin ki sai kin fi jin dadin gidan Sarkin Gaya.

A hankali Kulsumu ke daga kumburarrun idanun ta tana bude su a kan Baban ta.

Wai me yake nufi ne da wannan zancen nasa?

Ita ko alifun ba ta fahimta ba, ban da sunan gidan SARKIN GAYA.

Har ya yi mata sallama ya sanya mata albarka tare da yi mata addu
I masu yawa ya tafi, Kulsumu ba ta koma daidai daga razanar da ya sanya ta a ciki ba.

Maganar gidan Sarkin Gaya da ba ta fahimci musabbabin ta ba.

Ga shi har ya wuce ya tafi ba ta nemi karin bayani daga gare shi ba.

Harshen ta kamar an daure mata shi, haka ta ja jiki ta koma cikin gida kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.

Gadon Goggo ta hau ta kwanta, ta lumshe idanun ta tana sauke ajiyar zuciya.

Cikin dare ta kasa barci sai juyi a kan gadon karfen Goggo, ta tabbata ita din yanzu matar aure ce, matar wanda ba ta sani ba, ta yi sallama da Taufeeq daga cikin rayuwarta.

Kwata-kwata kwakwalwar Kulsumu ta ki yarda ta karbi zancen gidan Sarkin Gaya da malam Hadi ya yi mata, sabida tsabar ba ta kawo hakan a ranta ba.

Ta fi sa wa a ranta ya fada mata ra
ayin sa ne kawai na gidan da ya fi so ta yi zaman aure.

Ko mecece kaddarar ta tunda ita ta ki karbar Taufeeq ita ta ja wa kanta, dole ta karbe ta da hannu bibbiyu.

Amma ba ta taba lissafo wa da Turaki cikin kaddarorin da ka iya samunta ba.

Duk da haduwar su a Lagos ya bankado shafuka da yawa daga karkashin zuciyar ta da ta dade da binnewa na ciwon abin da ya yi mata.

Wai "matarsa da ya rasa bai sake ta ba".

Ta tuna statement din sa.

Ita ta san wannan ba Turaki ba ne, Turakin gaske bai taba son ta ba!

Turakin da ta sani daban yake da wanda ta gani, tunda ta aure shi har Allah ya raba su ba ta taba ganin murmushi a fatar bakin sa ba.

Amma haduwar su a Lagos Turaki har rungumar ta ya yi, ya sumbace ta passionately, duk da ce masa da ta yi tana da aure, sannan ta ga murmushin sa ya kai sau nawa, wanda ya kusa tafiya da sauran numfashin ta.

Tana wannan tunanin har aka yi kiran assalatu a kan kunnen ta.

Har aka tada sallah ta kasa motsawa, sai da Goggo ta bubbuge ta.

Ko da ta yi sallah kasa komawa barci ta yi, idon ta ya soye, zuciyar ta ma ta soye kamar soyayyar gyada marau-marau, da tunanin yau ne rana ta biyu da za ta sake barin gaban iyayen ta zuwa gidan aure.

Akwai fargaba mai yawa a tattare da ita, wadda ta cika ruhin ta sakamakon tunanin shi kuma wannan auren me za ta je ta tarar a cikin sa?

Idan lalurarta ta dawo fa?

Tunda har gobe likita bai ba ta tabbacin warkewa gabadaya ba?

Babban abin da ya sa ta ke gudun aure ke nan, ba ta so ta kuma yinsa a sake sako ta.

Sannan ba ta son terere da bankada a kan lalurar da Allah ya dora mata.

Duk da jikin ta yana ba ta ta gama warkewa, Dr.

Sakeenah ma na da tabbacin hakan.

A haka barci mai nauyi ya dauke ta, a karshe ta bingire a kan sallayar tana yin sa bilhakki, babu wanda ya tashe ta don sun lura kwanan ido biyu ta yi.

Washegari gidan aka tashi da hidimar tafiya kai amarya wanda za'ayi da yamma, Dr. sakeenah ta ja hannunta suka shige dakin Baffa kasancewar ba ya nan ya fita.

Wani fulas ta jawo ta aje mata a gaban ta ta ce, ta cinye kazar ciki tas!

Ta ba ta kasusuwan, sannan ta ba ta wasu kwayoyin magani ta ce in ta gama ta hadiye su.

Ta dube ta cikin ido, ta ce,
Na san Kulsumu ba za ki ki bin umarni na ba, na san kina girmama ni!
Chapter 7 · 0% Book details