← Book details Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 20

Sashe 4

Kulsum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don haka ta sauko kafafun ta daga gadon karfen Goggo, ta karbi ledojin da Baffa ke mika mata.

Ya juya ya fita yana fadin,
Ki ci ki yi wanka da sallah, sannan mu zauna in ji me ya faru kin ji Kulsumu?

Ki kwantar da hankalin ki, da raina da lafiya ta babu abin da zan kasa yi miki
Wadannan kalaman na Baffa su suka sanyaya mata zuciya.

Har ta samu karfin gwiwar cin naman sosai.

Da ma tsakanin ta da balangu akwai kyakkyawan aminci.

Ta shanye furar gabadaya wadda ba'a cika mata sukari ba, sannan ta tashi ta je ta yi wanka ta dauro alwala.

Sai da ta rama duka sallolin da ke kanta, sannan ta ji nutsuwa ta soma shigar ta.

Sai da Baffa ya dawo sallar isha sannan ya kira Kulsumu a dakin sa.

Ta shigo sanye da hijabi ta zauna ta rakube abin tausayi.

Baffa ya ce,
Kulsumu?

Ta ce,
am Baffa
Ina so ba tare da kin boye min komai ba, ki gaya min duk abin da ya faru.

Mene ne dalilin tahowar ki daga wajen marikan ki kwanaki uku kafin daurin auren ki ke kadai tun daga Lagos?

Kulsumu ta share hawaye, ta ce,
Baffa auren ne na fasa
Baffa ya hadiye fushin sa da razanar sa, ya ce,
A wane dalili, ko ko don ki wulakanta dattakon mu, ki saka hairan da sharran?

Hawaye suka zubo wa Kulsumu, ta ce,
ko daya Baffa, sai don in tserar da kaina daga sake zawarci a shekarun girmana, bayan wanda na yi a shekarun kuruciya ta, in zaba wa
yana uba na gari, in kuma yi jihadin ceton tarbiyyar
ya na a can gaba
Baffa ya kasa fahimtar ta, sai ya ce,
kai tsaye ki gaya min, me ya faru?

Kulsumu ta sunkuyar da kai.

Baffa zan fi so a ce yana zaune zan fada, don kada ya samu damar cewa na yi masa sharri.

Sannan Hajiya da Daddy kada su zarge ni da munafuntar su
Baffa bai ce komai ba, sai ya yi shiru yana nazarin kalaman ta, amma hankalin sa ya tashi sosai, don ya kasa cankar inda zancen ta ya sa gaba.

Kira ne ya shigo wayar Baffa a lokacin.

Yana dagawa ya ce,
ga Nasaran nan ma
.

Ya amsa suka gaisa a mutunce yadda suka saba, sai dai ya ji muryar ta ba yadda ya saba jin ta ba.

Ta ce,
Baffa, Kulsumu Gaya ta taho?

Baffa ya dubi Kulsumu, sannan ya ce,
ga ta nan a gabana
Wata irin ajiyar zuciya Hajiya Nasara ta saki a fili, ta jero alhamdulillahi sau uku.

Ta juya ta ce da su Goggo,
Kun ji Kulsumu na Gaya
Goggo ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta ce,
Idona idon Kulsumu
wannan yarinya ta dauki alhakin mu, ni Taufeeq na fi tausayawa, dubi yadda ya fita hayyacin sa sabida neman ta, wannan sakarci da me ya yi kama?

Ki kamo hanya tun daga Legas ba tare da sanin kowa ba?

Hajiya ta nisa, ta ce
Ku daina fadan nan Goggo, ni na tabbata Kulsum cikin hankalin ta ta ke, akwai muhimmin abin da ke damun ta da ya sa ta aikata hakan.

Da ma gobe za mu tafi Gaya dukkan mu ko mene ne za mu hadu a yi maganin sa, Daddy sai ranar daurin aure ya yi niyyar tafiya, amma gobe zan sa shi a gaba mu tafi tare gabadaya har Taufeeq din
Hajiya Nasara ta kira Malam Hadi ta ce da shi, mutanen
Yalleman kada su zo Abuja, su zarce Gaya su ma gobe can za su tafi, an fasa yin kamu da wunin a Abuja.

Taufeeq na shigowa ta gaya masa Kulsum na Gaya,.

Zama ya yi jabar!

A kan kujera ya rasa abin da ke masa dadi.

Me ke damun yarinyar nan ne tamkar mai motsuwar kwakwalwa?

Hajiya Nasara ta dube shi ta kasan idanu kafin ta yi magana cikin bacin rai.

In ma wani abun ne ka yi mata wanda har ta zabi ta koma wajen iyayen ta, kada ka yi tunanin za ka yi amfani da ni ka cuce ta, ita din marainiya ce kuma amana a hannuna.

Zan yi adalci ne na gaskiya a tsakanin ku
A jigace Taufeeq ya dago ya dube ta, he is looking helpless tun tafiyar Kulsum, tun jiya yake cikin tashin hankali da wahalar da Kulsum ta sabbaba masa.

Shi kuwa me zai yi wa Kulsum da har za ta zabi barin su?

Babu komai cikin zuciyar sa a kanta sai tsananin so da kaunar ta.

Iyakar tunanin sa ya san bai yi mata komai ba.

Ko dai Kulsum ta fasa auren sa ne shi ya sa ta ke tsiro da wadannan bakin halayen?

Wani abu da shi kuma ba zai taba lamunta ba, ya yi saken da Kulsum za ta kubuce masa.

Shi kadai ya san wahalar da ya sha kafin ya samu kanta, ko me ta ke so zai yi mata
amma ban da fasa aure!

Washegari tun asubah suka kamo hanyar Kano a cikin babbar (Land Cruiser) din Daddy, Taufeeq ke jan motar, Daddy na gefensa, Hajiya Nasara da Goggo suna baya, Nasmah ba ta biyo su ba sabida ba za ta iya jure tafiyar mota ba, za ta jira su har su dawo tare da amarya in an dauro aure.

Mujaheed sai goben zai bi su ya samu daurin aure.

Karfe goma sha daya na safe suna cikin Kano, daga nan suka dauki hanyar Gaya.

Wajen karfe daya na rana Taufeeq ya kashe mota a kofar gidan Malam Jibo.
(Daga can nesa da su, wani gajeren saurayi ya fiddo waya jikin sa har rawa yake, ya lalubo lamba ya kara a kunnen sa).
*** *** ***
Daga inda ta ke kwance a kan gadon karfen Goggo tana jiyo sallamar su daya bayan daya.

A hankali ta runtse ido tare da kiran sunan Allah.

Goggo ce ta fara shigowa dakin ta haska ta da tocilan kasancewar dakin ba haske.

Kwafa ta yi tare da cewa,
Kin kyauta abin da ki ka yi.

Shin Kulsumu ke karamar yarinya ce, ko ko goyon ki ake yi?

Kin bi kin daga wa bayin Allah hankali babu gaira babu sabar.

Yanzu ga shi kin taso su bagatatan, wai kina cikin hankalin ki kuwa?

Kulsumu ta gyara kwanciyar ta ba ta ce wa Goggo komai ba.

Ta yi bambamin fadan ta har ta gaji, Kulsumu ba ta tanka mata ba.

Hajiya Nasara ce ta shigo ta bude tagogin dakin da Kulsumu ta rurrufe, haske ya wadaci dakin.

Ta ce,
Fadan nan ya isa haka Goggo, ki bari su Daddy su dawo sallah sai mu zauna da ita mu ji damuwar ta.

Na san Kulsumu ba za ta yi abubuwan da ta ke yi haka kawai ba
.

Sannan ne Kulsumu ta samu lafiya daga sababin Goggo, ta sauko ta yi wa Hajiya Nasara barka da zuwa, tare da tambayar Nasmah.

Hajiya Nasara kallon ta kawai ta ke tana mamakin yadda ta zabge cikin kwana biyu kacal.

Ta ce,
Nasmahn da ki ka kusa sa wa nakuda lokacin ta bai yi ba.

Ki ka jefa su a tashin hankali, ai ba ki da guts na tambayar ta.

Amma Kulsum ko ma mene ne ki tsallake ni ki taho tun daga La
gos har Gaya ke kadai?

Gaskiya ban ji dadi ba.

Na dauka ni ce mutum ta farko da za ki fara dosa da kowacce damuwar ki?

Kulsum ta yi kasa da kai, ta ce,
Ki yi hakuri, ba zan sake ba Mum
.

Iya abin da ta fada ke nan.

Don bata da kalaman kare kan ta.

Bayan kowa ya yi sallah mazan sun dawo daga masallaci, Baffa ya yi musu shimfida a falon sa.

Tunda suka shigo Taufeeq ke raba idon ganin Kulsumu amma ko inuwar ta bai gani ba.

Har sai da Baffa ya yi wa Goggo umarnin a kirawo Kulsumu.

Daddy na zaune kusa da Baffa, Taufeeq a kusa da shi, sai Hajiya da Goggo daga kusa da kofar dakin.

Kulsumu ta yi sallama ta shigo kanta a kasa, ta ja mayafi ta rufe fuskar ta.

Daga kusa da Hajiya ta zauna ta ki yarda ta kalli bangaren da Taufeeq yake, wanda ke cikin dukkan damuwar duniyar nan, ya rasa abin da ke damun ta.

Ya bi ta da kallo har ta nemi wuri ta zauna.

Baffa ne ya bude taron da addu
a, sannan ya ce,
Na ji dadi da ku ka zo bakidayan ku, domin na yi-na yi da Kulsumu ta fada min abin da ya taso da ita haka afujajan tun daga Lagos har Gaya ita kadai, ta ki gaya min.

Ta ce sai Taufeeq yana zaune
Ya gaya musu a halin da ta zo masa jiya na jigata da fita hayyaci, sannan ya dube ta, ya ce,
To Kulsumu, ga Taufeeq ga iyayen sa, ga kuma mu kakannin ki wadanda ba ki da wanda ya fi su, muna so ki gaya mana abin da ke damun ki, ko hankalin wadannan bayin Allah ya kwanta a ci gaba da shirin daurin aure
Kulsumu ta muskuta, ta ga cewa wannan ita ce damar ta ta karshe, idan ta yi shiru Baffa ya fusata da ita, ko ta zo daga baya ta fada ba zai saurare ta ba.

A cikin ranta kuma sai ta ji tausayin Taufeeq ya darsu mata, don ita ta san irin masifaffen son da yake mata.

Amma dole ta fadi abubuwan da idanun ta suka gane mata, ko da a ce zai musanta hakan.

In ba haka ba hankalin ta ba zai taba kwanciya da shi ba.

Ke muke saurare Kulsumu, duka wajen nan babu bare, kamar yadda babu abokin wasan ki, idan ba ki da damuwa ki fada mana mu kama abubuwan da ke gaban mu
.

In ji Goggo.

A hankali muryar Kulsumu ta fito, ta ratsa kunnuwan su.

Baffa, na fasa auren Taufeeq, ku yi hakuri
Goggo ta yi shiru tana mamakin karfin halin Kulsumu, shi kuwa Taufeeq dagowa ya yi a firgice ya dube ta.

Duk da bai yi sa
ar ganin fuskar ta ba.
Chapter 4 · 0% Book details