← Book details Kulsum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 27

Sashe 3

Kulsum Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda gimbiya hafsatu ta karanta wasikar sumy, sai cewa tayi karta damu dama maza basu da tabbas, itama tayi mamaki yadda yayi ta zubar da kudi kaman bai san ciwon suba, indai aure takeso zata iya naima mata wani ta aura kodan ta huce haushi.
Kursum tace haba gimbiya kamata ace kin naimo mijin nata ayi magana,tunda da hadin bakinki akayi auren nan kuma ai kinsan kawunsa, gimbiya tace tab aini yanxu ko nayi trying number kawun bai shiga kashe wayar take
kuma yarinyan ita da kanta ta nuna shi take so kuma xata aure shi, toh miye laifina aciki.......ki fice min yanxu nan marar kunya, wato kece da bakin magana ita da aka saka bata zoba sai ke, wawiyar banza.
Kursum ta fice ranta abace,bata taba ganin zalamar miyar mata irin gimbiya ba, ita dai kanta kawai tasani......

Ta koma dakinsu, har lokacin sumy kuka take duk ta rame ta fita hayyacinta lokaci daya, kursum tace mata dan Allah ki bar kukan nan haka, indai ina raye a duniya toh saina naimo shi na daukar miki fansar abunda ya miki, koda kuwa zaiyi causing life dina, dat is a promise, sau daya nataba ganinshi amma bazan taba mantawa da face dinshi ba......
Tana taba sumy baki hardai ta hakura ta barwa Allah komai..

*Bayan wata biyu*

Sumy sai rashin lafiya take ga zazzabi da weakness da take ji ga yawan amai , shiyasa gimbiya ta kaita asibiti, doctor ya mata gwaje gwaje ya gano tana dauke da cikin wata biyu.......aka sallamo su suka dawo.
Gimbiya ta kirawo kursum ta gayamata sumy na dauke da cikin wata biyu, sai data girgiza da jin wannan xancen, yanxu ya sumy zatayi idan tasan tana dauke da cikin wanda yama manta da zamanta, gimbiya tace ga test result din saiki bata ki kara kwantar mata da hankali, kinsan mai karamin ciki batason tashin hankali gudun kar ciki ya zube.
Ta karba sum - sum ta fice, tasamu sumy na karatun al-qur'ani, sai da tajira ta idar sannan ta mika mata test result din, sumy ta karba ta duba saida gabanta ya fadi tace wake dauke da ciki ? Kece kowa?
Kursum tace kinsan dan Adam ajizine, duk yadda ubangiji ya tsara aka ke faruwa babu wanda ya isa yaja da ikon Allah, komai na duniyan nan jarabawa ce, Dan Allah kiyi hakuri ki yarda da kaddaran da Allah ya daura miki, sumy tace meke faruwa ne ? kinsani a duhu fah.

Ciki gareki na wata biyu sumy, kece keda cikin ba kowa ba, hawaye kawai sumy take tana addu'an Allah yasa hakan yafi alheri agareta, kursum tace amin.

Daddy ne ke tuki hankali kwance, yana murnan yau zai ga diyar shi tilo a duniya, wajen shekara guda rabon daya ganta..

Ya iso makaranta, har visitors lodge (inda iyaye ke zama idan sunzo ganin ya'yan su) aka kaishi, aka tura kiran sumy tazo dad dinta yaxo.....ita da kursum suka je wajen daddy suka gaishe shi, gaban dad sai da yafadi ganin yadda sumy ta rame sai haske data kara sosai, yace kursum, sumy bata da lafiya ne? Kursum tayi shiru ita dai tarasa dalilin daya sa idan tana gaban baban sumy take jin wani iri, kaman akwai wani connection tsakanin ta dashi.........kukan sumy ne yadawo da ita daga tunanin da take, tana kuka tana ba daddy labarin abunda ya faru tun daga auran ta har izuwa yanxu da take dauke da ciki, daddy kasa magana yayi sai hawaye kawai, gaskia ya tausayawa sumy ba kadan ba, duk laifin hajiya hadiza ne, da yanxu sumy na gida agabanshi hankalinta kwance.
Yana taba sumy hakuri akan karta damu jarabawa ce ta ubangiji, komin wuya akwai dadi, ya ajiye masu shopping din daya masu sa'annan ya masu sallama zai koma kano, karshen shekara zai dawo ya dauketa, ya dauko makudan kudi yabasu suna ta godiya..

Daddy kam yayi niyyan kwana biyu, amma bazai iya jure ganin sumy halin da take ciki ba, shi kanshi daurewa kawai yake amma ranshi a bace yake, aka ya tattara ya koma kano,

Hajiya hadiza na hakimce a parlour a zaune tana jiran shigowan daddy gidan, dan ta kwarara mai buhun bala'in data saba akan yaje ganin yar tsintuwo bada izinin taba....
Yana shigowa ta gane muryanshi da sallaman da yayi bata ma damu da yanayin shi ba, ta hau zaginshi damai rashin kunya ta ko ina, daddy kam kasa magana yayi ma saboda bakin ciki ta riga tamai yawa, nan take shikam ya yanki jiki ya fadi sai jin faduwan mutum tayi tim akasa.....😳😳

Ta kwallawa samira (yar aiki) kira maza ta fito Alhaji ba lafiya, samira ta fito da gudunta tana hajiya, alhaji ne ya fadi da alama ma rai yayi halinsa.
Hajiya a rude tace "samira kiramin wayar shehu nasan baiyi nisa ba,kirashi mukai alhaji asibiti.....

Baba shehu da sauri ya iso gida,suka sa alhaji a mota sai asibiti
likitoci sun yi iya kokarinsu, amma rai yayi halinsa (kulli nafsin za'ikatul mauti), abun tausayi hajiya da baba shehu sai kuka suke yau sunyi babban rashi.
Doctor yasamu baba shehu da hajiya ya tambaya su ya akayi suka bari har zuciyan alhaji ya buga alhalin sunsan yana da ciwon zuciya, hajiya tayi tsuru tsuru bata ce komai ba illa kukan da take tayi dan tasan tabbas itace silan ciwon zuciyan alhaji, yanxu gashi ya tafi ya barta, kuka kawai take tana nadaman abunbuwa data shuka mai........

Nima kasa rubutu nayi saboda mutuwan daddy ba karamin girgizani yayi ba...... Rip😭😭😭

[10/14, 8:11 PM] Badee Social: 🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺🌺

🌺🌺 By ~Xarah Bêê

Page 2⃣6⃣ ~ 3⃣0⃣✨

*Kano*

Mutuwa daddy ba karamin girgiza jama'a tayi ba, mutane da dama sun sanshi da halin kwarai da taimakawa talakawa, Sam ba ha'inci ko xalinci a lamarin sa......mutane sai shigowa ta'aziya suke, baba shehu na daga waje yana amsan gaisuwa...
Hajiya kuka kawai take dakyar take ma iya amsa gaisuwan da ake mata, hajiya mario ce tadawo gefen ta tana kara bata baki akan tayi hakuri addu'a ya kamata tamai bawai kuka ba.
Zainab ma tayi rashin daddy ba kadan, dan daddy ne kadai yake kwabarta da mata nasiha sosai game da yanda tadau rayuwa da zafi, yau gashi tayi babban rashi. Tana kaunar shi tamkar shiya haife ta..
Har gida yazid yaje yama xee ta'aziya, ya tausaya mata sosai dan yasan yadda suka shaku da daddy ba kadan ba, wani irin sonta ya karaji a zuciyan shi....har dakin hajiya yaje ya mata gaisuwa, ta amsa ba yabo ba fallasa dan yanxu tadan rage kukan nata, dazai wuce ta bashi sako ya kaiwa mairo tare da shi mai Albarka. ........yazid kam yana jin haushin yadda hajiya ke cewa umman sa mairo sai kace a kauye Ina laifin maryam ma......😠😠😠

Bauchi
Yan makaranta kam sai shirye shiryen xana jarabawa shiga ajin karshe ake babu wasa kowa ya dukufa da karatu, sumy kam ciki ya shiga wata tara, haihuwa ko yau ko gobe, "Sam bata da labarin mahaifinta ya rasu wata bakwai da suka wuce.
Kursum da gimbiya kadai suka San da rasu war shi, sunki sanar matane akan lalular da take tare shi. Sun fiso saita haihu sannan su gaya mata.....

Bayan kwana biyu, sumy ta tashi da nakuda mai tsanani, da gudu kursum ta kira gimbiya sukai rushing dinta zuwa hospital , Allah yasa haihuwan taxo mata da sauki ta haife kakkyawan baby gal wanda babu bambamci da ubanta kaman an tsaga kara an karya...washe gari likita ya sallamo su suka dawo...
Ranan suna ba wani bidiri akai ba, duk da gimbiya ta gayyato mutanan ta, yarinya kam taci suna hanifa son kowa kin wanda ya rasa.
Sumy kam sai murna take, ba karamin son hanifa take ba, dan yanxu tama daina jin haushi mijinta asalima ta yafe mai duk abunda ya mata...tana fatan Allah ya hada hanifa da ubanta wata ran.
Kursum ce ta shigo daki ta kwantar da hanifa da tayi bacci, tace akwai abunda nakeson gayamaki sumy amma kiyi hakuri bamu gayamaki ba tun lokacin saboda cikin ki, Allah ya yayiwa daddy rasuwa tun wata takwas da suka wuce....
Innalillahi wai inna'ilaihi raji'un kawai sumy take furtawa, kuka take na tashin hankali shikenan daddy ya tafi ya barta yanxu bata da wani gata, yanxu ya zata koma gida da zama, dan bata manta da azabar da tsanar da hajiya ke mata ba tun tana karama, hawaye kawai take tana Allah yaji kanka da rahma daddy......Kursum kam tashi tayi tabar dakin dan bazata iya ganin kawarta cikin yanayin da takeba.......itama tasan tayi rashin daddy ba kadan ba, dan shine ya mamaye mata gurbin uban da bata dashi.

*kano*

Gaba daya family din daddy sun hallara a parlour din gidan tare da lawyer (alkali) sa dan karanto will (wasiha) da alhaji ya bari kafin ya rasu......
Baba shehu kam sai murna yake dan yasan dole yasamu abu mai tsoka, dan tun rasuwar daddy ya maida kanshi managing director din oil company dinsa.
Mommy da xee suma suna zaune suna jiran barrister yafara bayani..
Barrister shu'aibu ya fara da addu'an sannan ya fara bayani yace tun lokacin da alhaji yakamu da ciwon zuciyan yasan bazai dade ba, shiyasa yazo ya sameni ya bani takardar nan, acewarsa duk ranar da baya duniya yanaso acika masa burinsa dake rubuce anan......barrister ya Bude yafara bayani kaman haka
Ni Alhaji Tanimu Bawa na damkawa ya'ta sumayya dukiyata kashi hamsin acikin kashi Dari, sannan na bata matsayin managing director na oil company dina da kuma gidan da muke ciki duk na mallaka mata su.
Acikin kashi hamsin daya rage na bawa hajiya hadiza kashi ashiri, kashi goma na bawa Zainab, kashi goma na bawa shehu sai sauran kashi goma akai masallaci da gidan marayu.
Ina fatan iyalaina zasu cikamin burina , sannan banyi haka danna matawa wani ko wata rai ba.....bissalam

Barrister ya gama karantawa sannan ya mikawa mommy takardar, yace alhaji yamai xancen nan da shekera daya atura driver yaje ya yaje ya dauko sumy daga makaranta, mommy tace to insha Allahu xaai haka, barrister yamasu sallama yatashi ya tafi.
Chapter 3 · 0% Book details