← Book details Kulsum Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 27

Sashe 11

Kulsum Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Office din baba Shehu ta wuce, yana zaune yana waya ta banko kofa ta shigo tana kuka, ba shiri ya ajiye wayan ya karaso gabanta yace zainab kukan mi kike ? Ina kika shiga kwana biyu ban ganki ba ?" Cikin kuka ta tsara mai komai har zuwan su bauchi, baba Shehu yayi dariya yace halina dake u ar alwyz crazing bakya Abu da tunani, "ta bata rai tace Baba ka daina cemin am crazing ina da hankali, I don't knw y mutane ke cemin banda hankali, yayi shuru yana tunani, koda ya auri jamila (maman zee) tana da mental illness harta rasu, shiyasa sumtymz zee take abu kaman mai hauka, ya nisa yace ," am sorry auta ta....ta kyalkyale da dariya tace to baba yanxu miye mafita, yace karki damu zan tura private detective dazai binciko miki komai akan ta, tun daga ranar da aka kaita school din, abunda kikeso kenan koh ?da fara'arta tace eh, yace toh yanxu abu biu zakiyi idan kinaso komai ya tafi daidai, da sauri tace me ? Yace dole ki nunawa yazid kin hakura dashi sannan kuma kija Sumy ajiki yadda bazata gane abunda kike shirin yiba, ta kwalalo ido waje tace"gaskia baba bazan iya, yace toh ke kikasani tashi ki tafi,"ta ma rairace fuska tace na yadda xanyi, yace toh ki wuce gidan kafin in zo tace OK ta fice da murnan ta...... Shima sai murmushi yake dan perfect tym yake jira ya kawar da Sumy once n 4 all.

Washe gari, hajiya na zaune a parlour tana cin abinci, zee na kallon TV, kursum ta sauko zata wuce office kusan kwana biu bata jeba, ta gaishe da hajiya ,"ta amsa a yatsine ne ,zee dake gefe tace my sis har zaki tafi,kursum da taji maganan bambarakwai,tace eh ta masu sallama ta fice.

Zata shiga mota taji hayaniya abakin gate, ta karasa wajan da sauri, mai gadi daya hango tana zuwa, ya kalli matar dake tsaye da Da niki nikin akwatuna, yace yauwa ga madam Sumy nan zuwa kwayi magana dan bazan bari ki shiga gidan nan ba,"gimbiya tayi shewa tace gidan nan shiga daram.

Tana leka waje sukayi ido hudu da gimbiya hafsatu,dam gabanta ya fadi ,gimbiya data gama tsorata tace baki mutu ba dama........
Da sauri kursum taja ta gefe ta tace mi ya kawo ki gidan nan, gimbiya tace aike xan tambaya kin mutu miya kawoki nan,INA Sumy ? Kursum tace ai Sumy CE ta rasu bani ba, yanxu haka yan gidan sun dauka nice Sumy, long story ne idan mun zauna xan baki labari ,"ta bude Jakarta ta zaro makudan kudi ta mikawa gimbiya tace ga wannan ki koma bauchi yanxu nan, zamuyi waya......gimbiya ta kece da dariya tace Ai baki isa ba, babu inda zani, kursum tace koki tafi ko in kira securities su fitar dake daga nan, "ta kara kecewa da dariya tace ai ke zabi ya ragewa, ko ki barni in zauna a gidan ko kuma inje in tona miki asiri,kinga dagani harke mun rasa , balle ke da baki da wajan zuwa.

Kursum data gama kulewa tace Baza ki zauna a gidan ba, kiyi abunda zakiyi. Gimbiya tace toh zakiga Abunda zanyi kuwa, ta bangaje maigadi ta shige gidan da gudunta, Agigice kursum ta bita tana cewa tsaya!! Tsaya!! Muyi magana, amma ina.....gimbiya tayi nisa batajin kira, harta karaso bankin parlour ta tura kofa ta shiga........

Tashin sense 😳😳

*Xarah Bukar*😘

*Dedicated to Bady social*

~Luv u all~😘😘
[10/15, 9:06 AM] ‪+234 903 484 0427‬: [06/09 10:53 AM] Xarah Bukar ✍🏻✍🏻: 🌺🌺🌺 KURSUM 🌺🌺

🌺🌺 by ~ Xarah Bee

Page 5⃣6⃣✨

Hankali kwance ta tura kofan ta shiga da sallaman ta, hajiya ta amsa tace waye ? Zee ta juya taga gimbiya, tace baiwar Allah aida baki zoba kin kiramu ta waya, sai sannan gimbiya ta gane zee, itace marar kunyan nan da sukazo naiman labarin sumy, taja tsaki tace bansanki ba kuma ba wajan ki nazo ba, hajiya tace zee kinsanta tane ? Zee tayi shuru, hajiya tace bakuwa gurunwa kikazo ? Caraf kursum ta shigo tace gurina tazo, kuma a gidan nan zata zauna, hajiya tace bazata zauna ba, Ai nan ba hotel bane daza ki kawota, gimbiya tace haba hajiya nice fa gimbiya makarantar da Sumy tayi harta girma, yadda na kulan miki da ita bai kamata ki Kore niba, "ran hajiya ya gama bacci, wani irin tsanar gimbiya taji a zuciyar ta,aranta tace wato matar nan itace ta maida min kursum abun tausayi ko kaya bata siya mata. Ta nisa tace koda kike riketa aiba kyauta bane kudi aka baki, na baki minti biyar ki ficemin daga gida.....

Gimbiya ta kalli kursum tamata signal kotasa baki ko kuma ta tona, " kursum tayi Gyaran murya tace gaskia hajiya saidai kiyi hakuri, dole gimbiya ta zauna agidan nan, tunda gidana ne, "hajiya data gama fusata tace to na yadda ta zauna amma ba nan tare damu ba, ki kaita can bangaran masu aiki ta zauna, kursum zata kara magana hajiya ta daka mata hannu tace nagama magana, ta dogara Sandar ta tahau ra sama.......kursum tace nizan wuce office ta fice,da sauri gimbiya tabi ta tace amma dai hajiyar nan bata da mutunci, kursum tace karki CE haka dan kuwa bata da matsala, kiyi hakuri ki zauna a part din masu aiki kafin insamo mafita, idan kika Kama kanki zakiji dadin zama da ita, makauniya ce ba gani take ba,gimbiya tace kina nufin duk kwalliyan datayi da uban dauri da bakin glass din bata gani ? Tace kwarai kuwa,tun wajan shekaru 18 da suka wuce tasamu matsalan ido, gimbiya tace shikenan ki tura masu aikin su gyaramin dakin, kursum tace toh kayan ki ma xansa ashigo dasu, xan wuce aiki saina dawo.

Gimbiya ta koma parlour ta zauna, zee ta kalle ta taja tsaki tace ashe bakin ku Da ita shiyasa kika ki bamu details akanta, gimbaya tace yarinya ni kike jawa tsaki ? Zee tace eh mana ke wace CE ? Gimbiya ta mike taje har gabanta ta kama mata kunne gam tace idan kina takama ke yar bariki toh ni sunana na biyu bariki, ki kiyaye ni danni ba tsarar wasanki bace,kina jina ? Zafin da taji yasa Ba shiri tace eh naji kisake mun kunne, saida taga kunnen yayi jajir sannan ta saki ta koma kan kujera ta baje, "da sauri zee ta tashi tace muguwa ta gudu sama...........

Agurguje plz........

Kursum ta koma bakin aiki, takan kiran inna taji ya hanifa, tsakanin ta da yazid sai wasa buya bata barin su hadu dan ta tabbatar ta kamu da son shi. tsoranta daya bai wuce kar asirinta ya tonu ba.

Hajiya ta warware sosai, bata shiga harkan kowa a gidan kullum tana makale adaki, kursum tana shigowa gaisheta ta bata magani.

Yazid ya kanzo gidan ganin kursum, amma sai dai yasha zama a parlour bata fitowa, idan yagaji ya tafi....

Zee kuwa basu da aiki ita da meerah sai clubbing da shaye shaye, takan yi kwana biu bata kwana gida ba, ta fita harkan yazid ko sun hadu bata kulashi, dukda sonshi na nan daram azuciyar ta, har dakin kursum take shiga tayi ta janta da hira kaman gaske.

Baba Shehu na nan da kudirin sa, burinsa ya kawar da Sumy,amma ya rasa yazeyi.

Gimbiya hafsatu ko yaushe tana main house abaje a parlour bata da aiki sai tsegumi, kowa haushin ta yake ji agidan, tunda taga Baba Shehu take shishige mai, ita adole tasamu mijin aure, shi ko kallon bata ishe shi ba.....

Bayan sati biyu

Umma ce taxo gidan tayi knocking kofa, gimbiya dake kallon TV taja tsaki ta tashi taje budewa, ta bude suka gaisa da umma, umma tace amma ke bakuwa ce koh? gimbiya ta Kare mata kallo tace wata sabon gani hajiya maryam ai bazan taba mantawa da fuskan kiba, umma ta kwalalo ido waje tace ina kika sannni nikam bansan kiba......gimbiya ta kece da dariya tace Ai dole kimanta ni, 18 years ago kika kawo min kursum tana jaririya kokin mata ne? Umma ta bata rai tace banganeki bane, me kikeyi a gidan nan ? Tace zama nazoyi mana Ai Sumy daliba tace, umma tace toh yanxu babu komai tsakani na dake, tunda kursum ta rasu, karki kara gani na kice kin sanni, gimbiya tace haba hajiya miya yayi zafi haka, ki bari muyi zumunci mana," tayi banza da ita ta wuce sama dakin hajiya.

Gimbiya tace lailai matan nan,aiko saina juyo xancen da zakuyi, sadaf taje bakin kofan dakin ta kasa kunne...

Hajiya tace ashe zaki zo, na dauka kokin mata dani, umma tayi dariya tace yanxu ma agurguje nazo Alhaji na gari Shiyasa kika jini shuru ,ya karfin jiki ? Hajia tace da sauki sosai, Ina son dinki kwana biu baizo ba.......umma tace indai yazid ne anjima kina iya ganin shi, ta duba agogo, nizan wuce office sai munyi waya,"tayi sallama da hajiya ta fice.
Chapter 11 · 0% Book details