← Book details Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 20

Sashe 8

Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Salati mom tayi ta ce "Kanwar Baban naki kike fad'awa hakan dan Baki da mutunci sabren"Mom ta Tana nufota Aunty sadiya duk ta tsure tsoro take Kar aje sabren taga abunda ya zuba dukda tasan Daman yarinyar ba kaunarsu take ba Bulala Daya mom ta tsala Mata ta charger waya Wanda ihun data kwalla Duka Saida ya kewaye Dakin wani irin ihu take kamar ana zarar ranta Aunty sadiya dukta rude ta ce.

"dan Allah Kiyi Hakuri Aunty Yarinta ce Ni wlh banjima komai ba"Haba Sadiya akanme komai tayi sai ace yarinta yarinyar Nan ba fa Yarinya bace da za ace a shekarunta Bata San darajar manya ba,sabren ihu kawaii take hange take wata barnan zatayiwa mom wacce zataji ciwo fiye da yanda Taji na bulalar.,

hango abinciccikan da ke jera a dining tayi tasan mom ba abunda ta tsana sama da barnan abinci Aiko ba Inda ta nufa Tana ihun kukan sangartata sai dining Tana zuwa ta hau watsi da komai Dake dining din miyar ta dauka Tare da watsawa a farin carpet din palour aunty Sadiya da suka nufo wajen hankali tashe mom da Dora hannu aka tace na shiga Ukku sabren abincin da tun safe nake wahalar girka sa Kika zubarmun miyar da Nayi ta kwana ukku Kika watsarmun ita Wasu hawayen bakin ciki NE suka zubowa mom saboda bakar wahalar da Tasha Ai Bata San lokacin da ta furta Cewar"Yanda Kika wulakanta abincin Nan wata rana saikin nemeshi da idonki kin rasa Dan ubanki".

( da yawa wasu iyayen fushi na sanyasu ga fad'awa yayansu mugayan kalamai na Baki wanda saisun Manta ma bakin ya dinga bibiyar yayansu saboda ance bakin uwa dafi ne Allah yasa iyaye su gane su dinga Kai Zuciyarsu nesa yayinda yayayensu sukayi musu wani Abun da basuji dadinshi ba Allah sa mu gyara). wayar wuta Mai kauri ta wawuro tare da nufarta da ita sabren na ganin haka ta kwalla ihu tare da nufar hanyar kofa

mom ta Mara Mata baya Dan Yau Mai raba ta da ita sai Allah sabren hankalinta duk ya tashi bude k'ofar palour tayi ta kwasa a guje Maigadi ya Mike Yana tambayarta Lafiya saijinshi yayi kasa sakamakon bangajesa din da tayi mom Kira take,.

",yusha'u karka barta ta fita ka rik'emun ita kafin ma yusha'u ya Mike ta bude k'ofar get d'in ta Kara kwasawa a saba'in Bata nufi ko Ina ba sai gidan su Affan..........✍️

*Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536*

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*

Arewabook👉@Miss Hajo✍️

🅿️.............*9 & 10*

Yanda ta shiga gidansu Affan Ne a guje ba ko hula ga ko uniform Bata cire ba ya Sanya Mamansu dubanta ta ce"Lafiyanki kuwa Baby ya haka Naga ko uniform Baki cire ba "Tana murza Ido ta ce "Mom nayiwa laifi shine zata dakeni na rugo "

"Daman na sani uwar yar laifi jeki Dakin abokin naki Yana ciki"Turo Baki gaba Tayi ta ce "Ni yunwa nake ji mama"murmushi kawai mama tayi ta na kallon budurwar yarta ta ce "tashi ki zuba Mata abinci"Saida taci Abinci ta koshi ita da Affan kafin su Mike su shiga wasan da suka Saba mama nayi musu mitar sun Girma da wasa ba Wanda ya kulata cikinsu.

Aunty sadiya ihu ne kawai batayi ba saboda takaicin bakincikin asarar da sabren tayi Mata dama ce babba ya samu wacce Bata taba samun irinta ba Amma tsinanniyar yarinyar ta B'ata Mata shiri ta tsinewa Sabren yafi dari a ranta ba shiri ta jawo Jakarta tayiwa mom bankwana Tana cewama ta jira Dad ya dawo Amma Bata saurareta ba.,

________Tana Isa Ba sallama ta fad'a gida Kamar ta fasa ihu tayi dabas ta zauna baba dake taunar goro ta ce "Lafiya sadiya meya faru"Baba komai ya lalace yarinyar Nan Allah tsine Mata albarka ,baba kituna bakar wahalar da Nasha na tsallaka Nigeria na je har gari ya na marad'i ki duba Nissan tsakanin yola da marad'i Banda ciwon wahalar da Nasha naje wajen malamin Nan na amshi maganin Nan Wanda ya tabbatar mun matsawar suka cishi shikenan komai zai rikice zaiji ba wacce ya tsana sama da ita bazasu Kara Kwana Daya ba zai saketa ,ba, na samu babbar dama na saka Musu a abinci kawai yarinyar Nan ta zubar da miyar gabaki daya gashi Duka maganin ne na Sanya"ta karasa fad'a hada hawayen Takaici.,

Salati BaBa tayi ta salamce ta ce "Kai anyi lalatacciyar Yarinya kijimun shegiyar Yarinya tsinanniya yar asara shiyasa kikaga na tsani yarinyar Nan da uwarta Bana kaunar Yan iska yanxu kenan komai ya lalace"

"Komai Mana ya lalace BaBa na rasa wani irin shegen taurin Hali ne da tsinanniyar Aminar Nan Asirin munyi munyi ba nasara ,Yanzu fa tuna da Asirin Nan Na kwanaki da Boka yayimun kuma shima an tabbatarmun da aikinshi kamar yankan wuka Shima ba nasara "

"Lallashinta Sosai BaBa tahau yi ta ce "Ki kwantar da hankalinki y'ata Dole ne Amina tabar gidan Nan idan Kuma tak'i ta Taki ajalinta zanga uban waye bokan ta a kasar Nan Dole ki Auri Mustapha Kuma kiyi yanda kike so dashi ba y'ar katsinawa ba ita Tana takama da ta Gama dashi bayabin umarnin kowa sai nata To ko Yar maguzawace sai na gwada Mata zaren ba kalar yadin bane barni da ita d'iyar kirki "

"Sai sannan sadiya hankalinta ya Fara kwanciya Kallon Baba tayi ta ce "Ya banji girbin yaran ba"Tabe Baki BaBa tayi ta ce "Malalacin uban su yazo ya tafi da su"..

______"Lafiya palourn Naga ya firgice haka ga Miya kacha kacha meyake faruwa"?

Dad yake fad'a shigowarshi kenann Palourn",Mom da kuka ne kawai batayi ba Dan Takaici ta ce.

"Daman na'ki gyarawa ne dam kaga abunda yarka tayi da idonka sabren ta lalata gaba Daya abincin danayi "ta karasa fad'a kamar ta saka kuka.,

"Subhnallahi daughter tayi Aikin wannan kenan to Amma nasan dai haka kawai bazatayi haka ba me kikayi Mata".

Sakato mom tayi Tana kallonshi cike da Takaici Ta ce "Ohh tambaya ma kake me akayi Mata bama fad'a zakayi Mata ba to wlh yau bazan Kuma shiga kitchen nayi girki ba saidai Duka gidan muzauna a haka ".

Murmushi dad Yayi ya ce "Sorry my menah me Yayi zafi yanzu mu gyara wajen sai muje joint muci abinci muyi order na dare shikenan ko yanzu Ina daughter?.

Sai sannan mom ta danji sanyi kafin ta Mike ta ce "Ta tafi yawon da ta saba ta san dukanta zanyi ba zata dawo gidan Nan Dan wasa ba"Barema Bata dakuwa tunda ga dad dinta"Harara mom ta galla Masa yayinda Shi Kuma yasa dariya.,

Har magriba sabren Bata bar gidan su Affan ba Saida suka ci abincin dinner kafin Mamansu Affan ta kalleta ta ce "Baby tashi ki wuce yayarku ta rakaki dare nayi Kar mom ta nemeki ko?.

Make kafad'a tayi Tana turo Baki ta ce "Mom wlh Duka na zatayi Ni bazanje ba "to wayace kiyi Mata laifin tashi muje Ni na rakaki kar su nemeki dakyal ta Yarda maman Affan ta rakata Tana makale jikinta har suka Isa Palourn Tana ganin mom ta Kara tsorata ganin irin hararar da take aika Mata Lokacin Basu jima da dawowa daga unguwa ba ,dad na ganinsu ya fadada fara'arshi maman Affan Tana zauniya ta ce.

"Biko Nayo Amina ayi Hakuri Kar a daketa tunda ta tsorata murmushi Mom tayi ta ce "Saida ta tasoki kenan Aunty ai Daman nasan Tana chan in bandake Allah da saina daketa Amma taje taci arzikinki ygd "bayan sun Gama gaisawa har dad maman Affan ta wuce gida Sabren ko jikin dad taje ta daddareshi Dan karma mom ta daketa.,

After two weeks Dad ya koma wajen aikinsa Lokoja kasancewar babban immigration ne Yanzu Haka Yana gab da taka matsayi babba dalilin Zuwan Shi course din sati biyun nan dad ya kasance mutum ne mai sa'a tun yarinta hakan yasa kowani course yaje tofa saiya yi nasara(Zakuji tarihin waye dad a Nan gaba) gidan duk Yayi Musu ba Dadi musamman sabren hakan yasa mom ke Kara janta jiki yanzu ko laifi tayi Mata saidai ta tsawatar Mata ko tayi mata addu'ar Shiriya.

,.kasancewar Dad Bai Saba Tafiya Yana barinsu ba duk wajen aikin da za ayi post nasa tofa tare yake Tafiya da iyalan nasa Duka basufi wata biyar da dawowa yola ba da Zama dalilin mom na Cewa hada zaman kudu yake Kara rikirkita tarbiyar Y'ar tata yasa ta kafe Akan Dole yola zasu zauna a gidansu da idan sunzo hutu suke sauka ganin ta kafe ya Sanya dad hakura yake Tafiya Amma duk sati biyu saiya dawo koma k'asa da Haka Dan Daidai da Second daya bayason Nesa da iyalan nasa.

Tana kwance a saman lallausan carpet dinsu Tana note wayar mom dake gefenta tayi ringing dubawa tayi taga ansaka "Aunty Aisha "Cikin sauri ta dauka Tana dariya ta ce.

"Hello Auntyn katsina"Wanakeji kamar baby"Dariya tayi ta ce "Nice Aunty kedama Kika Manta Dani inajinki ko waya kuke da mom bakya nemana sannan kin daina zuwa gidanmu"Ina Ni ina mantawa da Y'ar diyata guda Yakike ya school din ya Kuma rashin ji Yana Nan ko andaina".

Turo Baki gaba tayi ta ce "Nasan Mom ce take muku gulma ta take cewa Banaji inaji itace dai kawai ta Saba jaraba ai dad Bai taba cemun Mai rashin jiba sai ita "

"Ke banason wannan maganganun naki mararsa kan gado da har yanzu Baki iya gaisuwa ba ina Maman Naki Take Kai Mata wayar"Mik'ewa tayi ta ce "Bari nakai Mata wayar Maman katsina Ina yaranki Yama sunansu na manta sunansu Mufidat kawai natuna kice Musu Ina Gaishe su".
Chapter 8 · 0% Book details