← Book details Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 20

Sashe 10

Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayartace tayi ringing Tana dauka Sudais yace ki fito "K'aramun beil Baki kawai ta yafa kafin ta Sanya wani combust Mai shegen kyau jikin madubi taje ta Dan shafa hoda Kadan kallon kanta tayi a madubi yanda tayi wani masifar kyau murmushi tayi tare da fitowa cikin sand'a tabar gidan kar mom ta jita Tana fita ta iske Sudais ya faka mota a k'ofar gida wajensu ta nufa ta na dariya ta ce .

"Manyan Yara Ashe da gaske ka iya mota Aiko Nima saika koyamun"Big girl ake gaya muku wannan show haka zamu yaki people fa "Far da Ido tayi ta ce "ya son ranka "faruq Daya daga cikin class mate d'inta ya ce "Kai wankan Nan fa Yayi tawajena kodai hada ciko"Harara ta b'alla masa ta ce "Shafa kaji".

Duka dariya suka kwashe Affan ya ce "Wlh ki daina wannan Saran ta shafa muji d'innan da Kika tarko wani shafawa zaiyi"Dako ya shafowa uwarsa da ubasa kwanan sell ta fada Tana bude murfin motar tare da shiga Tace "Kuyi sauri mu biya mu d'auki zey ta shirya.

"Saida suka biya suka d'auki zey kafin su wuce yawonsu guri guri wet learn park and garden suka Fara nufa sosai suka shakata a park d'in suka Sha hotuna kafin su wuce admiral Park Shima sun jima suna shirme da Shan ice cream da hotuna har bayan magriba Kafin su wuce gida ikon Allah ne kawai yamaida kowannensu gida saboda Kasadadden tuk'in D'an koyon da suka hau Dan kwananshi Biyu da Gama koyon motar.,

Saida ta shigo gida ne da danji wani iri tasan mom saitayi Mata fad'a sosai akan yawon da ta tafi tun azahar Ganin motar Dad a parking space ya Sanya hankalinta kwanciya tare da kutsa kanta cikin Palourn...

*KATSINA STATE*
_Ta Dikko 'Dakin Kara_

Gaba D'aya masarautar ta kauraye da bushe bushe da kide kide na maroka,motoci ne na alfarma kwara Biyar suka kutso cikin masauratar Wanda shigowarsu ya k'ara sanyawa gurin ya hargitse da mabusa,.

busa ake sosai irin ta gidan sarauta tare da kirari ta ko wani bangare "D'an sarki ,jikan sarki magajin sarki D'aya tamkar da dubu sha kundun mahassada,an buga dakai an barka Jan Zaki mai bawa maza tsoro,.

,kaid'inne Mai firgita namun Daji taka Lafiya yariman da Babu kamarsa ,saukarka Lafiya asalin jinin sarauta ,mazan fama,takawarka Lafiya D'an Uwar gida Hajiya Aisha fulanin mai martaba Uwar sarki Kuma matar sarki barka da zuwa shalelen Mai Martaba ,Kuma shalelen masarautar katsina da kewayanta Ganinka sai Mai sa'a,kaid'inne dai Mai firgitasu,.

kirari ake sosai Ana bushe bushe da kid'e_kid'e Sojoji ne sunkai Goma suka fito tare da zagaye motar da yake kowannensu fuskarsu murtuke ba alamar imani a cikinsu suna rik'e da bindigu Nanfa waje ya Kara kaurayewa da sabon kirari D'aya daga cikin sojojinne ya bud'e murfin motar tare da kamewa ya sarawa Wanda yake ciki kafin suma sauran su kakkame tare da sarawa da jinjinar ban girma Saida akayi kusan 10 minutes kafin ya zuro kafarsa D'aya wacce ke dauke da Wani tsatsadan cover shoe Wanda ko mahaukaci ya kalli takalmin yasan mallakarshi sai manyan gaske Wanda suka Isa, saidai Yayi kusan two minutes kafin ya zuro dayar kafar A hankali Yake fitowa daga Motar cike da Tsantsar tak'ama da izzah "Ai sumar tsaye nayi cin Karo da........✍️

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_🤙
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN*🧸

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*

Arewabook👉@miss Hajo✍️

🅿️............*11 & 12*

Cin Karo da kyakyawar fuskarsa mai dauke da tsantsar kwarjini da haiba Gaba Daya jikinsa a mummurde yake daka kallesa kaga kakkarfan gaske Kyakyawane ajin karshe Wanda tsayawa kwatanta Kyawunshi ma B'ata baki Ne Dan page D'aya Yayi Mana kad'an mu bayyana ainahin surar wannan bawan Allah wannan Shi ake kira da ainahin mijin novel(lol)Kyakyawane na bugawa a news Ba Fari bane irin chocolate colour dinnan ne da fatarsu har wani glowing take,gaba Daya kyakyawar fuskar tasa zagaye take da lallausan sajen da yasha g'yara kallo Daya zakayiwa sajen kasan ba k'aramun g'yara yake Sha ba duba da irin yanda ya kwamta luf bakin sajen har wani shining yake,dogon hancinshi kamar an zana idanunshi ko kallo Daya zaka yi mashi ka sadda saboda wani irin kwarjini da haiba(,Nayi sakato Ina jinjina Tsantsar kyau da Allah Yayi a wajen wannan bawan Nasa, Bansaniba Ashe har ya wuce saurin binsa Nayi hada had'awa da gudu Dan dauko muku rahoto yanda ya kamata).

Tafiya yake irin ta jinin sarauta Taku yake cike da izza har Lokacin masu kirari da bushe bushe Basu bari ba Wanda Jin hakan yake tamkar ana d'iga Masa digon darma a kansa dan a rayuwarsa inda Abunda ya tsana Bai wuce hayaniyar jama'a da irin wadannan abubuwan masu hawa ka ,

baiyi Wata Tafiya Mai tsayi ba ya Isa ga fadar Mahaifinsa Mai Martaba Alhaji Salim muhmod ko ban fad'a ba kunsan dai yanda kyau da tsaruwa yake na Gidan sarauta musamman Aje ga fadar Mai gayya Mai aiki ,gaba Daya hakimai,da Yan fadar sarki suna zazzaune.

sosai aka shiga yiwa Yarima barka da zuwa Fuskar Yarima da Annuri ya karasa ga kujerar Mai Martaba Wara Masa Hannu Yayi Inda ya shige ya lafe a jikin mahaifin nasa yanajin Wata nutsuwa Na saukar Masa sauran fadawa da Y'an zaman fada gaba Daya watsewa sukayi saboda dokar sarki ce Indai Yana magana da iyalansa Bamai Zama a wajen musamman Kuma *Yarima Anwar* da yake star a wajensa ,.

a hankali Mai Martaba Ya dago dashi daga jikinsa tare da shafa kyakyawar fuskarsa ya ce "Soja na barka da zuwa nayi farinciki matuka da Allah ya dawomun dakai lafiya da kuma nasarar da kukayi a yaki munga irin karramaka din da akayi sannan ina tayaka murnar karin girma da ka sake samu shiyasa a Koda yaushe nake matukar Alfahari dakai my son Allah dafa maka akan komai"Ameeeeen Abba na nima Ina matukar Alfahari da Kasancewarka uba a gareni fatan munsameku lafiya"gaisuwa sukayi irin ta soyayyar d'a da uba Kafin ya Tashi ya wuce Bangaren mahaifiyarsa.,

Tungada shigarka Bangaren Uwar gidan sarki Hajiya Aisha Fulanin sarki mahaifiyar Yarima Anwar zakasan ka shigo daular masarautar,Palour ne D'aya bayan Daya zakayi ta wuce su kowannensu Kuma shake yake da Abun duniya kayan alatu,da Kuma kaya irin na Gidan sarauta ko wani daki lik'e yake da kyawawan hotunanta ita da Mai martaba gaba D'aya ,Hadiman dake aiki a Bangaren Saida suka k'ame ganin shigowar, Yarima Anwar kowannensu na kawo irin tashi gaisawar tare da dukursawa kowa Yayi k'asa da kansa ba Wanda ya Amsawa tafiyarsa kawaii yake Cikin izza da takama.,

Saida ya karasa Babban palour Wanda ya take wad'ancen komai da kyau Aljannar duniya kenan Mahaifiyarshi dake sanye cikin Lafceciyar Alkebba Mai matukar Kyau da daukar hankali sanye take cikin tsatsatsadan lace Mai masifar kyau Tana ganin shigowarsa ta Mike tare fadada fara'arta ta na ware Masa Hannu ta ce.

"Oyoyo my son ur welcome ,sannu da zuwa Mazan fama namijin duniya na oyoyo "Lokaci guda ya saki wani lallausan Murmushi Tare da rungume mahaifiyar tasa yanajin guminta wata irin nutsuwa Na k'ara sauko Masa ,."cike da farinciki ya dago tare da dago da fuskar mahaifiyar tasa Yana Murmushi ya ce "miss You alot Mamy na".

yanayin yanda Yayi maganar ma kadai ya Isa ya saukarwa da Mai sauraro kasala cikin wata zazzak'ar murya Mai cike da nutsuwa.

"Murmushi Mamy tayi ta ce "Miss You too Soja na muje ka ci special girkin da na Sanya akayi domin Kai kadai" I can't eat anything now I want to rest mammy anjima idan na huta zanzo naci".

ya fad'a Yana D'an langabewa "kardai har Yanzu kana Nan da rashin son cin abincin Nan naka son "murmushin gefen Baki Yayi Wanda ba kowa zai fahimta yayishi ba ya ce"Ina ci Sosai Mamy na ko Kinga na rame Ne"Girgiza Masa Kai tayi ta ce".

"A a a a kyau ka k"ara ta fad'a Tana latsa wayarta tare da yin Kira ta ce "Ku shigo ku gaisa mun gama.gaisawar"Saboda girmamasa da ake Indai Yana magana da Mamynsa tofa ko kannansa Basa Zama wajen har sai sungama".

Tana sauke wayar Y'an Mata su Biyu suka shigo Palourn kallo D'aya zakayi Musu kasan sud'in jininsa ne D'aya Bazata wuce 22 years ba sai d'ayar bazata wuce 17 years ba "Kowaccensu da fara'arta ta shigo Palourn cikin girmamawa da nuna Farincikin dawowarsa Sukayi welcoming nasa tare da dukursawa har k'asa suka gaishe sa ,ya Amsa Musu tare da tambayar lafiyarsu Suka Amsa Masa da Alhamdulillah"Tare da Kallon Mufeeda ya ce "Ya school d'in hope kina maida hankali ko ?".

Tana fara'a ta ce "Ina mayarwa Sosai Yaya Ai munshiga s s two Yanzu"Yana latsa waya Ya ce "Karatun naku baya sauri"wara idanu tayi sai Kuma tayi Dariya ta ce "Yaya na zata haka za kace Yayi gudu fa?.

Shiru yayi mata Hakan bai dameta ba Dan tasan yayan nasu ba mutum bane Mai fiya doguwar Magana idan yaso "Maryam dake zaune gefensa ta ce "Yaya Ni baka Tambayeni ya school d'inba Ina maida hankalin?.

Ba tare da ya dago ya kalle Ta ba ya ce "a a a karki maida Tunda Position ake rubuta muku"Yar Dariya tayi ta ce"Uhm to Nima dai Ina maidawa Dan Second semester dinnan Bani da c o ko Daya" good girl"Ya Fada Yana jinjina Mata da Hannu.

"Yana mik'ewa ya kalli Mamy ya ce "Na wuce Part d'ina Zan huta'"Okay a biyoka da abincin kenan"Eh Nan da 2hours, Mufee ko Maryam su kaimun "
Chapter 10 · 0% Book details