← Book details Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 20

Sashe 18

Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mama ni banason Nan din ki maidani wajen mom da dad "to naji za a mayar dake Amma yanzu kuje Ki huta' ko?kafin ta kalli mufeda tace "ga Yar uwarki Nan Kuma kanwarki Nasan kinganeta tunda Kuna Dan gaisawa za a shigo da kayanta ki kaisu dakinki kuje ki Bata Abinci tayi salla tayi wanka".

"tohm Mamy ?ta fada kafin ta kalli Sabren ta ce "Muje ko sis?Zata Sanya kuka mamy ta Had'e fuska ta ce "Kika sanyamun kuka Zan fasa maidake ?Cikin sauri ta hadiye kukan Tana goge hawayen ta ce .

"Na daina"Kama hannunta mufe tayi suka shiga bedroom d'inta ita ta ha'da Mata ruwan wanka da kanta bayan ta fito daga wanka kallon mufe tayi ta ce "Ina kayan nawa"Akwatinta da tun zuwan mom yola suna Asibiti ta had'o mata kayanta aka shigo dasu ta janyo tare da budewa ta ce.

"gasunan"Budewa tayi Daman duka kananan kayane cikinsu ta Sanya wasu mararsa nauyi Tana gamasa ta Haye gado Tana kallon gefe ta Lula duniyar tunani"Mufe ita ta rufe kayan kafin ta ce "Bazaki Tashi Kiyi salla ba Sabren Mamy tace a hanya la'asr tayi muku ga magrib itama har anyi"ba ayin sallar ta fada Tana rufe idonta "Dariyar mufeda tayi ta ce "sallar ce bakiyi kome?ba a saniba Yar ba'ka kawai"Dariyar mufe ta Kuma sawa ta ce "Au a kaina Zaki huce fushinki kenan to Yi Hakuri yar Farar danginmu ".

shiru Sabren tayi na Yan wasu Lokaci Jin mufe Bata Kuma magana ba ya sanyata juyowa kallonta tayi Tana salla Tashi tayi zaune Saida mufe ta Gama sallar kafin ta ce.

"waike kadai na gani a Gidan ko duk anmusu aure?a a a Yaya Maryam Taje bikin wata friends d'inta Shiyasa Baki ganta ba "To ina Aunty Farida wadda mom ta Tab'a ban muka gaisa da ita tace itace first born din Mamn katsina .

"Tana gidanta Kano take Aure kardai itama Baki Santa ba"zaro idanu tayi irin a mamakance ta ce "kaiii Wai har anmata aure"Dariyar mufe tayi ta ce "Eh Mana koni Lokacin da akayi bikinta Banda wayau ke Kuma Lokacin ko yayeki ba ayiba Yanxu Haka babban d'anta yayiki tsawo"Allah da gaske?Eh mana lokaci guda ta washe fuska ta ce.

"Kice Ina da abokin wasa"Dariya sosai mufe tayi ta ce "ke Yanzu Baki wuce wasa ba Sannan ma da d"an zumunki zakiyi wasan"Harararta Sabren tayi ta ce "Ehmana Ina ruwanki"To naji Amma yanxu Tashi Kiyi salla kinji Yar kanwata".

Tilla Mata pillow Sabren tayi ta ce "ba ayi din Tashi muyi game a wayarki Dan Allah"bazan bada ba indai bakiyi salla ba Kuma Ina dasu Amma sai kinyi sallah jin haka ya Sanya Sabren mik'ewa faka_faka tayi sallar ta salamce tahau gado suka hau buga game sosai mufe tayi mamakin kwarewar game irin na Sabren duk game din da suka shiga ta iya Shi ita kanta a Dan zaman da sukayi na yan montuna ta tabbatar da ba k'aramun Wasa bane a ranta Suna Cikin game Daya daga Cikin hadimar Mufe ta shigo ta shaida Mata Hajiya na kiransu suje suyi dinner da to mufe ta amsa Mata Sabren hankalinta Yana wajen game Dakyal mufe ta samu ta Amshi wayarta suka fito tare da Sabren d'in.

a tsararren dining area din dake shake da manyan kuloli na alfarma suka tarar da mamy da Maryam Suna dinner karasawa wajen sukayi tare da Jan chairs suka zauna "Kallon Sabren Mamy tayi da Fara a fuskarta ta ce "Kici abinci sosai kinji ".

"Dan murmushi Sabren tayi ta ce "To Mamana"Maryam ce ta dakata d'aga cin abincin da take tare da Kame Baki ta ce.

"Mamy kardai Yar aunty Amina ce ta girma Haka ,Rabona da ita fa tun Tana 8years ko 5 "ai Dole kice bakisan Yar uwarkiba mararsa zumunci Wai Kuna cousin sister's Amma bakusan juna ba ai hada laifin Aminar da Bata zuwa da ita kuma again ba zumuncin zuwa inda suke ba Kuke ".

Sosa Kai maryam tayi ta ce "Ba Haka bane Mamy Yanzu ai inshallah zamuyi zumuncin kafin ta kalli Sabren ta ce "sannu ko kanwata kinsanni Ai Ni ko?Make kaf'ad'a Sabren tayi tare da kallon mufe ta ce "Kice Bazanyi magana da ita ba yanzu".

Dariyar Maryam tayi ta ce "To menayi"Tana tuttura Baki Gaba ta ce "Bake Ce kikace Baki gane niba bayan Ni Ina zuwa Saida na tambayeku"Sorry my kanwa Nina Isa nak'i ganeki Wasa nake maki my sweet sisterta dawo nanma ayi kaunar zumunci".

ta fada Tana janyo hannunta tare da zaunar da ita kujerar gefenta "Lokaci guda Sabren ta saki fuska tare da yin Murmushi Dan a rayuwarta ba abunda takeso sama da Yan uwa idan taje gidan friends d'inta taga yayyunsu da kannansu sosai abun ke burgeta sabanin ita da take ita daya Tana kallon Maryam ta ce.

"Aunty Kema Ai yayata ce ko?eh Mana yayarkice ni Mai matukar kaunarki my sister "Cike da farinciki Sabren ta ce "yeee Nima Ashe Ina da yayyu kamar su Affan Amma meyasa bakwa zuwa Inda muke"Murmsuhi Maryam tayi Mata ta ce "muna zuwa Lokacin Baki wayau shiyasa Amma Yanzu ai kindawo Cikin mu ko ?Make kaf'ad'a tayi ta ce.

"a a a wajen dad Dina zan Koma saidai idan ku kun yarda ku bimu"Amma ai zakiyi Mana kwana biyu indai kina son muma mu bikin?shiru tayi na Yan mintuna kamar Mai tunani kafin ta ce"To na yarda Amma gidanmu zaku Koma da Zama"Mamy Ce tayi murmushi sosai take so da kaunar Sabren a Cikin ranta yarinyar nada shiga Rai over ta ce.

"Yanzu dai ki Barmun daughter taci Abinci ai kuna tare saikuje kuyi ta hirar Taku"Mufe ce ta kalli Maryam ta ce "Aunty daga zuwanki harkin kwacemun fada wajen sis"Dariya Sabren tayi tare da yi mata gwalo ta ce "Ke ai kanwata ce"Duk Dariya sukayi kafin su Fara gabatar da dinner dinsu Sabren taci wannan taci wancen Har Saida ta KoshI kafin ta mike Tana kallon mamy ta ce.

"Mamyn katsina Ki kiramun Mom d'ina"Tirkashi Mamy ta fada a ranta kafin a fili ta ce"Bata sayi layi ba Amma dazu ta kirani a wayar wani Dr sun Isa lfy Suna ma Asibitin gobe za a Fara duba lafiyar dad din naki kije ki kwanta gobe da safe kunyi wayar".

Nan fa Sabren ta ce Bata San wannaan ba kuka ta fashe dashi tare da bajewa Kasan tiles tahau diddira kafa sai an Kira Mata mom d'inta ba lallashinta da ba ayi Mata ba Amma ta tubure ta ce.

"indai ana son na hakura sai an sayamun ice cream"Dakuwa many tayi Mata ta ce "Gidanku keda ice cream din katuwar wofi kitashi kije ki kwanta ko na zaneki ".

"to ki maidani gidanmu Nidai Allah sai ansayamun ice cream"ta fada Tana cigaba da diddira Kafa Maryam da Mufe Dariya kawai suke Mata dansu Basu tab'aga Sangarta irin wannan ba katuwar budurwa na acting din Yan yaye.

"Maryam ce ta ce "chab akwai aiki Gaba Keenan to Nidai na tafi saida safenku"ta nufi sashenta Tana Dariya yayinda Mufe itama Tana dariyar ta shiga lallashin sabren Amma kamar zuga ta ake Mamy ganin ba sarki sai Allah yarinyar tayi nisa ga wani ihu da take Tana Shirin Tara Mata mutane a dauka ba lafiya ba ya sanyata lallashinta tare da aikawa a sayo mata ice cream Din.

ana kawowa ta Mike kamar ba itace ta Gama murje murje ba ana Mika Mata ta goge hawayen tare da Fara Dariya Ta kalli mamy ta ce "Thnks Mamy na"kafi ta Ruga da gudu d'akin Mufe "girgiza Kai Mamy kawai tayi tare da kallon Mufe ta Mika Mata d'ayar robar ta ce.

"Saida safe ki tabbatar Tana cika salla nauyin Dana Dora Miki kawai akanta"Dariya Mufe tayi ta ce "to Mamy inshallah Zan kokarta Naga kamarma batasonyin salla Dan dakyal tayi dazu"Haka Uwar tacemun batason yin sallah Sai taga dama Shiyasa na Dora Miki Bangaren Nan naji da sauran "Tana Gama fadar Haka ta shige sashenta yayinda Mufe ta wuce sashensu itama Tana ta Dariya ita Daya Dan ita Gaba daya maganar Sabren ma yanda take komai a sangarce Dariya yake Bata.

Cikin sati guda Sabren ta Fara sabawa da Yan uwanta soboda irin yanda suke janta a jikin da nuna Mata kulawa musamman Mufe Sannan hankalinta yadan Fara kwanciya kasancewar kullum sai sunyi waya da mom ta wayar Mamyn katsina tanajin lafiyar dad d'inta Sannan Suna video call ,dangane da shiriritarta ba abunda ya ragu Yanzu babu abunda yafi damunta Daya wuce Zama waje Daya yanda ta Saba da yawo jinta take kamar a Kaya take,.

Sanye take Cikin blue din jiens tare da farar t-shirt ta Sanya farin combost d'inta hula Ce kawai a kanta ganin ba kowa a Palour mufe da Maryam Suna school Mamy Kuma Bata fito ba ya sanyata Cikin sauri ta fita d'aga part din, wani lumshe Ido tayi Koda taji hasken Rana sosai take karewa masarautar kallo Wanda sai Yanzu take Gama ganinta,kowa harkar gabanshi yake hakan ya sanyata Fara zagayawa Yawo ta shigayi ta shiga Nan ta fita Chan .

Tana Cikin Tafiya Taji tayi Karo da mutum Kadan ya hana ta fad'i cike da tsabar masifa ta ce "uban uban wani shegen ne ya Bugeni"Haidar dagowarshi kenan cike da zafin nama niyyarshi ya wanke wacce Yar rainin wayan ce har da Zata zageshi ".

Saranda yayi ba shiri Cin Karo da kyakyawar fuskar da tunda yake tsawon rayuwarsa Bai taba cin Karo da kyakyawa ba kamar yarinyar da yake gani gabansa, sakato yayi Yana kallonta kamar wani statue,irin kallon da yake Mata Ne ya Kara kular da Sabren cike da masifa Ta fara jaraba "Kai makahone ko baka da hankali da Zaka Bugeni Sannan ma shine ka tsaya kana kallona ko?.

Murmushi Haidar ya sakar Mata tare da. Cewa "Am sorry pretty ban gani ba Kiyi Hakuri"wata harara ta Dalla Masa tare da Had'e fuska sosai ta ce "Ai bansan wani Abu Hakuri ba malam ,sai ka biyani diyyar Bugeni da kayi Kasan dai ko a kotu kudinka sun haura dubu dari biyu ko?.
Chapter 18 · 0% Book details