← Book details Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana Shan gwanda ta ce "umm na haddace ta mom" ta Fada muryarta Bata ma fita sosai sakamakon cika Mata Baki gwanda da tayi,".

"Daman kinsan Akwai number a kanki kikayi ta sanyani gararanba sai kace kin samu driver"mancewa nayi fa Yaya beauty "ta Fada hankalinta kwance tuni damuwarta ta gushe tunda ta samu abunda takeso"karki Kara cemun wani Yaya beauty "ya Fada Yana Had'e girar sama da ta kasa tare da Mika Mata wayarsa ya ce Sanya ki Kira ki tambayeta unguwar".

Amsa tayi ta Sanya numbobin mom ringing biyu mom ta daga lokacin ta gaji da kuka Dan har Gidan radio an tafi badawa cigiyarta "Hello mom baby ce "Lokaci guda mom ta zabura ta Mike ta ce "Baby Ina kikaje ,kika tayarmana da hankali kina Ina"Bata bawa mom amsa ba sai Cewa tayi "Ya sunan unguwarku mom"Cikin sauri mom ta ce "Layout"layout"ta Fada Masa Masa kafin ta katse wayar ta goge number mom ta Mika masa.

Cigaba da ciye ciyenta tayi har batasan sunzo unguwarba ,kina iya gane gidan Yanzu ko sai an kirata tunda na Kula kwalwar Taki chunkushe take bakya ganewa daga gani ko a class"Harara Sabren ta balla Masa tare da turo Baki gaba wara idanu yayi Yana nuna kanshi ya ce.
"Ni"?
To menayi a cikin Daren Nan harma idonka yagane maka"

ta Fada Tana turo Baki tare da karewa unguwar kallo Kasancewar akwai hasken glove ya sanyata gano k'ofar Gidan su Mom wata Nauyayyar Ajiyar zuciya ta sauke gabanta ne ya fad'i tuno bashin da taci na uban sayayyar da yayi Mata kayanta ta Had'e a leda guda Tare da bude murfin motar ta fita da gudu kafin ta juyo da karfi ta ce.

"Yaya beauty Daman wayau nayi maka naci banza ,na koshi,sannan kayi yawo Dani a gari Daman so nake Naga gari kuma Kayimun sayayya da kudinka nagode saimun had'u a lahira Dan bazaka Kara gani na ba har abada ba garin nake ba "Tana Gama fadar haka ta Kara kwasawa a guje.

Anwar ya rasa Dariya zaiyi ko haushi ,baitaba haduwa da wacce tayi wasa da hankakinshi ba irin wannan yarinyar babban haushinshi na dagangan ta Bari ya dinga yawo da ita,Wanda baisan ta fada Masa ne kawaii saboda tsabar shakiyanci,sannan maganarta ta taci banza ita ma taso bashi Dariya ga haushin shi na ashe layin su Hajja ne ma tun farko Rashin sani juya Kan motarshi yayi Ya wuce Kai tsaye spare Gidansa Dan baya shiga cikin masarauta muddin dare yayi.

Sosai mom sukayi mamakin ganin Sabren Ita hankalinta kwance Su kuma gaba Daya ta tayar musu da hankali Dan maman katsina ko gida Bata tafi ba koda suka tambayeta Bata boye musu komai ba sosai maman katsina ta Kara jinjina wautar da rashin ji irin na Sabren kawai ta makalewa wani batasanshiba danma Allah ya taimaka mutumin kirki ne da ta hadu da na banza ya lalata Mata rayuwa fa Fada sosai maman katsina tayi Mata akan yawo,da Kuma yarda da wadanda Bata saniba kafin mom ta Dora nata Tana ganin haka ta shigewarta daki ta kwanta ta jima Tana dariyar wayan da tayiwa mutumin Nan yayi Mata sayayya Tana ta Dariya har bacci yayi awon gaba da ita.

Washegari Anwar ya wuce Lagos wajen aikinsa bayan yasamu Sanya albarka daga wajen iyayensa Bangaren hajiya talatu ko bataso hakan ya faru ba saboda Akwai maganin da Boka ya Bata akan tilas ya cisa a abinci kafin mako guda maganin zai daina aiki to gashinan Kuma ya tafi Dan ko bankwana baije yayi Mata ba sai text yayi Mata saboda Kiran gaggawa Daya samu daga wajen aikinsa.

Mom rage kwanakin da zasuyi tayi Dan ba k'aramun tsorata tayi da b'atan Sabren ba tasan ba saduda take ba hakan yasa kwanansu shida ko gidan Yan uwanta Bata zagaya ba tayi musu bankwana driver' da Daman Yana Nan ya wuce dasu Wanda murna wajen Sabren har baka suna Isa gida ko ciki bata shige ba ta ruga Gidan su Affan sosai suka hau murnar ganin Juna suna rungume juna Affan Yana Fada Mata yanda yayi missing d'inta Shi ya rakota har gida bayan yayiwa mom Sannu da zuwa dashi ya Taya mom ta gyara Gidan da ya danyi datti abun Tafiya da sukayi Dan Sabren Cewa tayi ta gaji.

Wannan karinma da dad yazo satinshi biyu haka yakoma ba abunda ya shiga tsakaninsu da matar tasa sai Dan wasanni Dan Sabren ta k'asa ta tsare babu ta yanda zasu kebe sannan ko bacci take indai sukayi niyyar wani Abu sai ta farka cikin satin Ne mom ta Fara rashin lafiyar zazzabi da ciwon ciki.

Yauma kwance take sosai ciwon cikin nata ya matsa Mata gashi Taki fad'awa dad Sabren da ta hado Mata tea ta zauna gefenta cike da kulawa ta rungumota ta tadata zaune ta ce

"Sannu mom ga tea din "GirGiza Mata Kai tayi Ta ce "jira ya Dan lafa"Aje tea din tayi ta ce "Wai mom ciwon cikin me kike kwana biyun Nan sannan jikin kima da zafi fa ko dai ciki gareki kani zakiyimun Daman Ina sane tun ina karama idan nace kiyimun Kane kikecewa zakimun Allahsa Kanin ne zakimun mom shine ko?"

"Saida ciwon cikin ya lafa mom ta Gama had'a zufa kafin ta dauki ruwan tea din Tasha "Kwabe fuska Sabren tayi ta ce "Mom Baki bani Amsa ba "Dan Allah yimun shiru Sabren please banason surutu".cewar mom.

"Sannu to?yawwa Baby"momy Saura wata nawa ki haihun Dan na Fara shirya dinner da zamuyi da friends dina"dafe Kai mom tayi ta ce "Zaki dameni baby cemiki nayi haihuwa zanyi"turo Baki gaba tayi ta ce"Ai nasani Mana bakyason ki fadane Kuma Bari naje nayiwa dad albishir ta Fada Tana rugawa tare da janyo wayarta Ta dannawa dad Kira.

Yana Dauka cikin d'oki ta ce "Dad Albishirin ka"Goro babyn dad"Mom nada ciki zata haifamun k'ani "Wara idanu dad yayi sosai cike da farinciki ya ce "da gaske baby wannan babban albishir ai kin chanchanci tukuici Mai tsoka Ina mom din Taki maza Kai Mata wayar '"Tana Dariya ta ce.

"Ai dad tukuicina kawai shine ka kaini Dubai da England da Paris tare da India mu hadu da aditi sharma saboda ita ce best actress d'ita "ta Fada Tana mikawa mom wayar daga Bangaren dad ya ce "Sweetheart Daman Akwai wannan babban albishir din Baki fad'amun ba ,wannan abun farinciki haka".

"Mom ji tayi kamar me wani gamin saita rasa Wanda yafi wani tsakanin sabren da dad "Hmmmmm ya wajen aikin".

kawai tace "Kamarya hmm ya Zaki chanza magana please wata nawa,kinje hospital an dubamun lafiyarki kuwa?waiko baka karya ba dadyn Sabren Kai Yanzu ko ce maka akayi Ina da ciki saika yarda ,ana haihuwa ba mahaifa Daman?Sannan kodai a Ruwa akeshan cikin ban sani ba kamanta shekara biyu da wani abu rabona dakai?".

Lokaci guda murnar dad ta koma ciki A sanyaye ya ce"sorry na Manta hakane sweetheart Gaskiya Nima Hakuri na yazo karshe Jibi ki shirya tarbar mijinki Ina Nan zuwa jibi saimu shirya yanda zamuyi da daughter".

Sosai mom Taji wani Dadi a ranta suna Gama waya da dad ta mikawa sabren wayarta.

kamar yanda dad ya Fada ranar ya dawo Sabren da mom sosai sukaci kwalliyarsu kamar ko yaushe idan zai dawo an shirya Masa lafiyayyun abinciccika Sabren na lik'e jikinsa Tana da dokin ganinsa Yana shafa kanta suna ta hirar y'a da uba mummy tayi serving dinsu wanda a Baki ya dinga feeding din Sabren harta Koshi kafin itama tayi feeding dinshi mom ce ta ce.

"Nima ban yarda ba to oya ayi feeding Dina "Dariya sukayi Sabren ta ce "To Mom Bari mijinki yayi feeding dinki".

dakuwa mom tayi Mata yayinda dad da ita suka sa Dariya cikin farinciki suka Gama dinner dinsu kafin Dad ya kalli agogo Karfe Tara na dare ya gani da Ido yayiwa mom sign ta ankare Kallon Sabren tayi ta ce.

"Babyna Muje na kaiki Gidan Su Affan Samira tayi maki kitso saiki kwana a chan"Jin zata kwana gidansu affan ya sanyata murna haada tsalle ta ce.

"To mom muje"Ajiyar zuciya mom ta sauke har dad dad ya ce Bari na rakata ke zauna "Dad ya rakata har gidansu Affan kafiin yayi hug d'inta tayi mishi bye bye tare da Saida safe ta shige cikin Gidansu Affan .

Affan shine matsayin sallamarta Tana shiga suka Taba ta ce "Albishirka besty yau gidanku Zan kwana zamu jima muna game a tab yau saina gwada maka kwarewata "Dariya yayi ya ce.

"Wayarki dai Akwai charge ko "Ehmana tun safe na cikata "Maman su Affan ce ta ce "Au ba kitson da mamanki tace a Miki ba zakiyi ba kenan ta game ma kike"Dariya tayi ta ce "Mama kitso da Daren Nan saidai gobe Tana Gama fadar haka taja hannun Affan suka zauna a k'asa suka Fara buga game Hankalinsu kwance ,girgiza Kai mamansu Affan tayi Tana jinjina wannan kawancen tun yarinta zataga ranar da aure zai raba tasan dai ansha kuka.,

Kashe wayoyinsu mom sukayi saboda gudun wata matsala......bayan komai ya lafa kamar sarar mom Koda yaushe Bata kwanciya ba tsarki wanka ta maza taje tayi tare da dauro alwala dad ko Wani baccin dadine da ya Jima baiyi irinsa ba ya kwashesa ba irin yanda mom bata tasheshiba Akan ko alwala ce ya Tashi yayi Amma ya k'iya haka dai ta hakura suka kwance like da juna.

Bangaren Sabren harsun kwanta karfe Sha Daya ita da samira Taji ta kurma wani uban ihu yayyun affan manya Dakyal suka rirriketa zabura kawaii take Tana wasu maganganu da basusanma wani yare ne ba gashin kanta gabaki d'aya ya warware zabura take sosai Tana neman fusgewa mamansu affan da Ihun ya tasheta da ita aka hadu aka dinga tofa Mata adduoi tare da Sanya Karatun alkur'ani wani irin gunjin kuka take Tana jujjuya Kai Tana hawaye adduoi sosai aka shiga tofa Mata Dakyal suka samu wajen 1:00am abun ya lafa ta Fara sauke ajiyar zuciya kafin ta lafe jikin Maman Affan ta koma bacci kamar ba itace ta Gama fisge fisgen Nan ba".

____Da wani irin masifaffen zazzabi Mai zafin gaske dad ya Tashi Gaba Daya hankalin mom Duk ya Tashi baitaba ciwon da ya hanashi yin sallar asuba ba sai wannan sosai jikinshi yad'au kerma,Yana kakkarwa ya ce.
Chapter 15 · 0% Book details