← Book details Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 20

Sashe 19

Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fada Tana tsatsareshi da manyahn Idanunta "Barema Ke kyakyawa ai sai dubu dari biyar"ya fada Yana Dariya"Harararsa tayi ta ce "ba wani dadin bakin da zakamun nayi maka ragi ka biyani diyyar da Robar ice cream guda ukku tare da gasashshiyar kaza ,da Kuma Kwallon kwakwa ukku"Dariya sosai haidar yayi kafin ya ce "Su kawai Kike bukata pretty ?Tana Harararsa ta Ce"Eh idan Kuma baka siyamun ba Kara Zan kaika wajen Sarki ".

"Ah ah yi Hakuri ba akai ga Haka ba kyakyawa tare zamuje ko Kuma jirana zakiyi na dawo"Tana Zama wani dakali ta ce "Jeka dawo Ina Nan"Haidar har ya Isa Mota yana juyowa Yana kallonta har kusan faduwa yayi sosai yarinyar ta shiga ransa lokaci guda bai taba ga yarinyar da ya kamu da tsananin sonta cikin kankani lokaci ba kamar wannan yarinyar ,ga dressing dinta ma yayi mugun Tafiya dashi".

Sabren ko Yana Barin wajen ta hau Dariya tare da cewa "Banza gara hotiho kawai har na Masa wayau"Tana Nan zaune Har Haidar ya dawo sosai tayi mamakin hada abunda Bata fada ba ma ya saya Mata "Amsa tayi Tana Shirin Tashi ya ce "Baki fad'amun ba to sunanki pretty"Tana wani yatsine fuska ta ce "Shima na kud'i ne"To nawa za a sayarmun"ban shirya saidawa Yanzu ba "binta Haidar yayi ganin Tana neman b'arin wajen tare da Cewa "kina son na dinga saya Miki wannan abubuwan kullum?.

Dan ya lura kwata kwata Bata da wayau "lokaci guda ta juyo Ta ce "Da gaske?Da gaske Mana Amma Sai kin yarda kin Zama kawata "Kare Masa Kalo tayi kafin ta ce "Amma ai Kai babba ne Ni friends Dina duk ba manya bane"To ba so kike na dinga saya Miki kayan Dadi ba ko su kananan friends din naki suna saya Miki"Shiru tayi Jim kafin ta dago ta kallesa ta ce "a a basa sayamun na yarda to "Good girl My friends wani Bangaren Kika zo Wai Dan Nasan dai ke bakuwace a Gidan Nan"

"Bangaren su Mufeda Ni diyar sister mamansu ce"Okay nagane to mu dinga haduwa a Nan ko gobe ma da la'asr mu hadu anan zanyo Miki sayayya?Sannan karkicewa Hajiyar Ni friend dinki ne"Harara ta Galla Masa tare da Cewa.

"To sannu Daddyna kake bani wani umarni kamar wani uba na"Kafin tayi Gaba "wani dogon numfashi Haidar Yana gabaki Daya kafafuwanshi gagaranshi dauka sukayi bai bar wajen ba har saida yaga bacewarta wani sanyayyen murmushi ya saki cikin kasalalliyar murya ya ce " I love you so much my pretty...

A dakinsu ta baje ta dinga ciye ciyenta Tana ci Tana dariya ta ce "Gaskiya garin Nan duk Basu da wayau,jifa garan ya zaci da gaske nake yayo mun wannan sayayyar ,Allahsarki ko Ina Yaya beauty Shima da nayi mashi wayau yayi ta sayamun abubuwa Rance "Kafin ta kwashe da dariya.

Wanda Zata iya ci taci kafin ta Sanya wasu Fridge wayarta ta janyo tare da Kiran affan sosai suka Sha hira cike da kewar juna affan ne ya ce.

"Ina wannan Babar da kika cemun ba Kakarki bace ,kusan kullum sai sunzo suyi ta buga Gidan inaji jiya Mai gadinku ya ce musu bakowa Gidan karkiga jarabar da ta dingayi Tana ta zagin mom dinki Wai Zata sayar Mata da d'a Kinga zagin da suka dingayiwa mom dinki ita da wannan lutetiyar".

"tsohuwar banza ce ai Dan Allah Affan idan ta Kara zuwa Ni na sanyaka ka harbeta da kwari da baka ko ka kad'e shaggu a kekenka Sannan karku sake ku fada musu inda su Mom da dad suke"Dariya sosai Affan yayi ya ce "Kai besty Kakartaki Nidai ba ruwana"Uwar kakata Allah kiyaye wannan munannar ta Zama kakata, banza Ni har ka batamun raima sai anjima",
Baccine ya kwasheta bayan Gama wayar.

Tunda Sabren ta Tashi taga ana ta Shirye Shirye part din na musamman tare da girki kala kala ita dai taga Shirin wannan yasha banban da Wanda ake kasa Shiru tayi hakan ya sanyata kallon Maryam dake gefenta Tana Danna Laptop ta ce .

'"Aunty Wai Shirin me ake tayi Naga tun safe gashi Yanzu har kusan la'ars ba a gamaba "Yaya Anwar ne zai shigo gari shiyasa"Waye to yaya Anwar din?.

ta tambaya "Shima yayankine daga Aunty farida saishi saini sai mufe Shima Nasan Baki sansa ba"Shima Kuma d'an mamyn katsina NE?Cike da kosawa da tambaya Maryam ta ce "Eh jekiyi salla ko azahar bakiyi ba "Make kafada tayi ta ce.

"Banyi to sai anjima"Wai meyasa Kika fiya Wasa da salla baby kefa ba Yarinya bace kin Isa ki fad'awa wasu "Turo Baki Gaba tayi ta ce "To Nidai nace Miki Yanzu bazanyiba kafin ta Haye gado ta janyo wayar Maryam tahau buga game,sanin ba yin zatayi ba ya Sanya Maryam kyaleta taci gaba da aikin da take.

Kamar ko yaushe duk zuwan da zaiyi tofa sai yasha bushe_bushe da kiraye_kiraye Wanda tun bayason abun harya hakura Dan ba yanda zaiyi Dole ,Sanye yake cikin manyan kaya irin na gidan sarauta masu tsananin masifar kyau saboda fad'an da mai martaba yake masa akan zuwa da kananun kaya ya sanya yanzu yake zuwa da manyan kaya kamshi ko duk inda ya gitta sai wajen yajima Yana kamshi Kai tsaye Bai zarce ko Ina ba Sai part din Ammynsa ,.

*Hajiya Talatu*

Ganin irin Shirin da ake a masarautar ne ya tabbatar Mata Yarima Anwar Yana tafe hakan ya sanyata fita tun safe ita da Ummul kulthum Tafiya sukayi Mai nisa Saida suka shiga har kasar Niger domin zuwa wajen sabon malamin da sukayi,.

magunguna ya Basu sosai ya ce"d'aya kina komawa Gidan ki turare d'akinki dashi Gaba Daya muddin ya shaki hayakinnan tofa aiki ya Gama sai yanda kikayi dashi ko uwarsa Bata Isa ta fad'a Abu ya tsallake ba".

"Kafin ya fiddo wani ruwa a kwalba ya mikawa Ummul khairi ya ce "Ke Kuma wanna Lokacin da zai shigo ki wanke fuskarki ki tabbatar Kunyi Ido hudu dashi tofa zance ya kare da kanshi zai dinga bibiyarki harsai kinja Masa aji ,Kafin ya dauko wata kwalbar turare ya ce "Wannan Kuma ki shafa sa Shima ki tabbatar ya shaki kamshin ba k'aramun Aiki muka Sha ba wajen hada magungunan Nan Sha Yanxu Ne magani Yanzu da kanku zakuzo Kuna mini godiya Amma akwai sharad'i guda Kar a sake maganin ya Tab'a k'asa Koda Wasa Kar ya ta'ba k'asa Dan k'asa itace makarin hadin magungunan muddin ya taba k'asa Aiki ya b'aci"bama zai Taba ba malam nagode Allah saka da alkhairi kafin ta dauko makudan kud'i ta Aje masa ta ce "tukuicinka Yana Gaba malam sai aiki yaci Yanzu muna sauri na tabbatarma da Kila ya iso saimun dawo.

____"Irin tarbar da yake samu a Koda yaushe ita ya Samu a wajen mamyn Nasa da kanta ta dinga b'ara Masa ayaba Tana basa Hira suke sosai irin ta d'a da uwa,Daga ita saishi a Palourn mamy ce ta ce "Wai ya maganar transfer taka kuwa gwarzona nifa nafison ganinka kullum kusa Dani bana son nesan Nan"Yana murmushi ya ce "Mamy keda Abba kunki Hakura da transfer Nan,Inajin Dadin aiki a chan ne shiyasa ,ya mai jikin tun Kuna abujar naso naje na duba sa Sha anin Aiki ya Hana Yanxu Suna madinar har Auntyn?

"E to da sauki za ace Amma har Yanzu dai Bai farfado ba"Cikin nuna rashin Jin dadinsa ya ce "Allahsarki Allah ya bashi lfy Ina Yartasu kuma"Amen ya Allah khadija Tana Nan na taho da ita Tana ciki Daman Ina tason kazo muga wace Makaranta yakamata a kaita saika kaita s s one tunda tayi jsce".

"inaga ammy kowace ma da an kaita da a jira zuwana ba ma "ya fada cike da ladabi"Girgiza Masa Kai tayi ta ce"a a a Kasan harkar karatu Dole saida namiji ai ba kurewa lokaci yayi ba "To shikenan mamy inaga mezai Hana a hadata da Mufeda kawai kamar zaifi"?Eh Daman Dole a hadasu Makaranta Daya da wani Dan y'artawa dai Har Yanzu akwai Saura"to shikenan' gobe Saita Shirya tare da Mufe naje na kaita din tunda Gobe Tuesday".

Tunawa da har la'asr ta wuce ya Sanya Sabren tunowa da maganarsu da Haidar ya ce zai yo Mata sayayya yau Aiko ba shiri ta Aje laptop din Daga ita sai hula ko takalmi Babu ta ruga a guje Mamy ganin fitowarta da gudu Cikin daga murya ta ce.

"Ke Khadija Ina zaku haka Cikin gudu "Ina Sabren bama ta saurareta ba tuni tayi Gaba Hankalin Anawar na kan mamy baima ganta ba yaji dai 'Karan gudu Sabren gudu ta dingayi Tana haki a zatanta mamy ta Sanya an biyota Daidai Mama Talatu ta shigo Tana niyyar nufa Bangarenta rike da kullum magungunan Data rike a hannu gudun matsala Daidai Sabren dayo wajen ji kake Gam ta tunkudeta Gabaki Daya magungunan suka baje a k'asa sabren ko bama ta tsaya tabi takantaba tasandai ta Buge mutum Amma batasan ko Meye ba.

"wani irin ihu mama talatu tayi tare da Dora hannu aka tsundumawa Sabren zagi tahau kutuntumawa Wanda babu dadin ji Takaici Daya ishi kulthum kuka ta fashe dashi ta ce shikenan duk tafiyar da wahalar da mukayi ta tafi a banza Kai Amma Allah tsinewa tsinanniyar yarinyar chan ko Yar gidan uban wacece,"Mama talatu ko Zaman Yan bori tayi .

Sabren Saida takai inda suka hadu da Haidar kafin ta tsaya Tana haki ,Haidar Daman Yana wajen Cikin sauri ya taso Yana tambayarta meyasa tayi gudu Haka Dan yasan tazarar tsakanin Part din Mamy da Nan nasu hakan yasa basama wani haduwa Dan idan ba dalili ba wani ma saisuyi wata Basu hadu ba Tana haki ta ce "Mamy Dan karta Sanya a biyoni shiyasa nayi gudun"Ohh sorry my pretty ya fada Yana son taba hannunta Yana tsoron karta masa jaraba dan ya lura jarababbiya ce.

"Saida ta Gama hak'in kafin ya Bata sayayyar da yayo Mata tun a Nan ta bude robar ice cream tare da Fara Sha har wani lumshe Ido take Dadi yakai Mata Karo da wannan abun Haidar ya samu damar kamo hannunta a hankali cike da barikanci ya ce.
Chapter 19 · 0% Book details