← Book details Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 20

Sashe 14

Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harta kusa Gama Sha nanfa hankalinta Yayi gida Gashi babban tashin hankalinta na batasan sunan unguwar su Mom ba bare ta tari adaidaita tace ga Inda sai kaita sosai ta Fara muzurai duk Wanda suka shigo su fita har magriba masu wajen dai basuce da ita kala ba ganin duhun magriba ya Fara ya sanyata Fara hawaye Ta sadda kanta tana kuka.

Bangaren mom ba k'aramun Tashi Hankalinsu Yayi ba musamman Maman Katsina ko gida Bata koma ba wasa wasa magriba isha'i ba Sabren ba labarinta Gaba daya unguwar ba inda ba ajeba Amma Bata Nan hankalin su gaba daya Yayi mugun tashi musamman mom Kadan ya Hana Bata fashe da kuka ba ta ce "yarinyar Nan karta jamun masifa ta bace na shiga ukku Daman nasan yawo zata tafi yasa na hanata kudin Nan Ina ta sani a garin Nan ".

____ lura da ita ya sanya ma aikatan wajen nufar wajenta suna tambayarta Lafiya take kuka Kuma tun dazu Taki Tafiya.

"Kuka ta Kara Fashewa dashi ta ce "Nima bansan Gidan mu ba"Kamarya bakisan gidanku ba to wa ya kawoki?nina kawo kaina Amma bansan inda Zan koma ba "

ta karasa fada Tana rushewa da Kuka Duk tambayar duniyar Nan sunyi Mata Amma bata Basu amsa ba ,sai Kuka take a jikin wata arniya Sama sama Taji shigowar wani wajen gaba daya Taji ma aikatan wajen sun b'ige da gaisheshi cikin girmamawa dagowar da zatayi ko 'karewa saurayin kallo batayi ba ta saki arniyar ta ruga wajenshi ta baya ta makalkaleshi tare da Fashewa da Kuka ta ce.

"Yaya shine ka tafi ka barni "Mamaki ne ya Gama cika Anwar shi kuma Ina yasan wanna yarinyar da zata makalkaleshi har Tana kiranshi da Yaya,kafin Yayi magana d'aya daga cikin ma aikatan ta ce "Sorry ranka ya Dade ai bamuyi tunanin sister ka bace Bata sanar Mana ba ce Mana kawaii tayi ta bace".

"Baice uffan ba sai kokarin ture Sabren yayi Kara makalkaleshi tayi Dan ba zata sakeshiba ya tafi ya barta zaune cikin arnan Nan da Bata sansu ba su Saida ita".

"tsawar Daya daka Mata ce ya sanyata sakinshi ba shiri kamar ta fad'i k'asa saboda rud'u ganin Yayi hanyar fita Ne ya sanyata binshi da gudu Yana Shirin shiga lafceciyar motarshi ta riko rigarshi ta baya Lokaci guda ya juyo fuskarsa murtuke ya watsa Mata harara ya ce "me Zan Baki kike Bina sanina kikayi?

"Lokaci guda ta fashe da Kuka tare da Kara rike rigarshi ta baya sosai ta ce "Ni bansanka ba Amma Allah bazaka tafi ka barni ba a saceni Bansan kowa ba "

"Mamaki gaba daya ya Gama cika Anwar Karewa karamar yarinyar kallo Yayi kafin yaja tsaki ya shiga da gudu ta zagaya ta bude wajen zaman banza ta shiga cikin sweet voice dinsa ya ce "Ke wai ina Zan kaiki Zaki shigomun mota haka kawaii Bansankiba"?

turo Baki gaba tayi cikin shagwaba ta ce "To Gidan da nazo zaka kaini Mana Ni bansan gidan ba?da zakizo Nina kawoki?

"a a a bakai ka kawoni ba Amma Kai zaka maidani "ta Fad'a Ta na turo Baki"Shi tsawon Rayuwar Anwar baitaba ga ikon Allah irin haka ba ya lura yarinyar matsala take Neman bashi "meye sunan unguwar?.

Ya jefo Mata tambayar"jujjuya idanu tayi kamar zatayi tunani kafin ta juyo ta kalleshi Tana kwabe fuska ta ce.

"Nima bansan sunan unguwar ba katsina ne dai saika tambaya kace Gidan su Mom d'ina ko Kuma kace Gidan su Maman Katsina kayi sauri Dan Allah Yaya Choculate Nasan mom Dita nachan Nata nemana please yawwa kuma sunan maman mom din tawa Hajja,sunan Baban Nata Ne ma na manta Naji ance ya mutu Da dadewa........✍️

*Tofa sabren wannan kwatance haka dalla_dalla*😛

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_🤙
[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*

Arewabook👉@Miss Hajo✍️

🅿️.............*15 & 16*

"Saida bayanin nata ya so bawa Anwar dariya ya fusge ya ce"waye zai gane kwatancen Nan naki,,ki fad'amun yanda Zan gane kina batamun time".

Shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka ta ce "To nima Bansan sunan unguwarba Yaya beauty Amma muje zangane bi hanyar chan ta fad'a ta na nuna Masa bayansu"

Duk yanda Anwar yaso fisgewa Saida ya danyi murmushi sosai yanayin yarinyar da yanda take magana ya basa Dariya ,kafin yabi hanyar da ta fad'a ,.

Hanyoyi ya dinga bi da ita sai sunyi nisa ta ce ba Nan bane a sauya sosai Anwar ya Fara gajiya ya lura shiriritar dashi yarinyar keson yi Parking Yayi tare da juyowa ya kalleta fuska ba wasa ya ce.

"Saukarmun a Mota tunda bakisan Inda zakiba Ina da aikinyine."Sabren najin haka ta fashe da kuka tare da Fara Masa diddire_diddiren kafarta a Mota Tana kukan sangarta ta ce.

" Allah bazan saukaba saika maidani gidanmu so Kake a saceni a yankani ayiwa mom Dina da dad asara nidai saika kaini gida".

sakato Anwar Ya yi Ya na Kallon ikon Allah ,Ya na ganin sangartattun Yara Amma tunda yake bai taba ga Mai sangartar wannan yarinyar ba tsaki Yaja a ranshi Dan ya tsani yaga Yara na sangarta"To Ni sani na kikayi,idan fa nidinma D'an yankan Kaine haka kawai kin makalemun to Bari na kaiki wajen yankan Kan ba shikenanba"

Ta tsinkayi muryarshi Lokaci guda ta hadiye kukan kallonshi tayi sosai ta Kare Masa kallo kafin ta turo Baki gaba ta ce.

"Ai nasan Kai ba D'an yankan Kai bane bakayi Kama dasu ba "ohh Daman har Kama garesu"ya Fada Yana tada Mota ya bi wata hanyar ko Allah zaisa a dace"Eh Mana Ni ai Dana gansu Ina ganesu ".

shiru Yayi Mata Jin hakan ya sanyata itama yin shirun"tsit motar ta dauka bakajin Komai sai sautin Gidan radio kallonshi ta dingayi haka kawai saita dinga ganin Yana yanayi da mom d'inta musamman idanunsa chocolate skin dinsa kasayin shiru tayi a hankali ta ce ".

"Yaya Beauty kaima D'an Nan garin Ne?Eh"ya Bata Amsa a takaice"To Kai inane gidanku?"duniyar sama"ya sake Bata amsa"kenan Yanzu Samar zaka koma?"Eh ko kina zuwa?Mak'e kaf'ad'a tayi ta ce "Umm umm injema ko Kai aljani ne "ya sunan mamanka wlh kanamun yanayi da mom d'ita ?

ta Kara jefo Masa tambaya"Dan tsaki yaja ya ce "kin fiya surutu parrot "harara ta galla Masa Tere da juya Dara daran idanuwanta "daidai ya juyo wara idanu yayi ya ce"Ni kike harara"Kauda Kai gefe tayi ta ce "Ni bada Kai nake ba "cigaba yayi da driving dinsa Daidai zai gitta ta wajen wasu masu gashin kaza idonta ya Kai wajen cikin d'aga murya ta ce.

""wayyo Yaya Beauty Dan Allah kaza ka sayamun "ganin Yana Shirin wucewa ya sanyata rirriko hannunsa Kadan ya Hana ta chaza musu accident ba shiri ya taka birki cikin d'aga murya ya ce "Waike Baki da da hankali,da Kika kadamu fa"ya Fada Yana sakar mata Tsawa "Kuka ta fashe dashi kamar ya daketa ta ce "To ba Saida nace ka tsaya ka sayamun kaza ba"tsaki yaja ya ce.

"ba a saya Ajiyar kud'in Kika bani,wlh idan bakiyi wasa ba Zan saukeki a tsohon Daren Nan daga haduwa dake kin likemun saikace na had'a dangi dake Duk kin chazamun Kai sai gararamba kike sanyani inayi a gari".

"cikin shagwaba ta ce "To Daman nace Kai danginane mema zai had'ani dakai Had'uwar joint kawai Ni ka saimun kazar bashi idan mukaje ba biyanka zanyi ba daga Rance ai ba kyauta nace ka sayamun ba?.

",Oh haka kikace to bazan ranta ba Kuma daga wajen Nan indai har Baki gano Gidanku ba Zan saukeki ki nema ke kadai"naji Yaya Beauty wlh indai ka saimun kazar sannan Zan gano Gidan sannan ma Rance Ne zakaban da munje gida Zan amsa wajen Mom d'ina na baka".

Banza Anwar yayi Mata Tare da fita ba ayi minti ukku ba ya dawo tare da leda batare da ya kalleta ba ya aje Mata Kan Cinya cike da murna ta ce.

"Thnks Yaya Beauty"cigaba da driving yayi ya nufi wata hanyar ko Allah zaisa a dace Yana tuna sunan da ta lakaba Masa Yaya beauty ko gidanwa ya Zama yayanta in Banda kawaii macece idan Ya sauketa baisan wani Hannu zata fad'a ba da tuni ya sauketa shawara ya Yanke in har Bata gano ba gidan ganin 11pm harta wuce gwara kawai ya kaita Gidan Radio.

Sabren bude kazarta tayi tahau ci sosai naman yayi Mata dadi har wani lumshe Ido take ta gefen Ido Anwar ya kalleta ya GirGiza Kai Yana jinjina wautar yarinyar kawai batasanshi ba ta makale masa to da ace shidin mugu Ne fa ya tabbata da Bata fada hannu ba gari ba da komai zai iya faruwa,.

Tana cikin ci taga zasu wuce wajen da ake Saida Fruits da juice marairaicewa tayi ta na kallonshi ta ce "Uhm Yaya beauty Dan Allah ga fruits Nan ka sake rantamun sai ayi lissafi"wata harara ya banka Mata ganin haka ya sanyata Fashewa da kuka ta Fara diddira kafa "tsaki yaja baisan Lokacin da ya sakar Mata tsawa ba Wanda haka ya Kara rudar da ita ta Kara Fashewa da kuka ".

.OMG ya Fada Yana dafe saitin kansa tare da duba agogo yaga karfe Sha Biyu saura tsaki yaja ya fita ya sayo Mata tare da cilla Mata cikin sauri ta amshe tare da aje naman kazar fakar idonsa tayi tare da yi Masa gwalo,tunani yayi kawai gwara ya kaita Gidan radio Dan ya gaji da gararanba da ita a gari karta jaza Masa masifa,wani tunani ne ya fad'o Masa kallonta yayi ya ce "Baki da number wani naki da kika hardace a Kira".?
Chapter 14 · 0% Book details