← Book details Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 20

Sashe 5

Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wow tubarakalla Masha kinyi kyau sosai sweetheart ta karfi da yaji dai kin hanani Kara Aure"Lokaci guda mom ta Had'e fuska tare da Kauda Kai cikin shagwaba ta ce "Yanzunma ai saika k'ara tunda ba hana ka ba nayi"Dariya dad yayi ya ce "Maida wuk'ar wasa neke Amarya Kuma uwar gida ai Daga ke ba k,'ari kin rufe ko Ina kinyi Kaka gida Ina dake wazan kalla har ta burgeni ke kad'aice a cikin zuciyar daddyn Sabren kinsan da haka",.

Murmushin Jin Dadi mom tayi Tana karajin kaunar mijin Nata ta musamman "Sabren ce da hankalinta duka na kansu ta shagwabe fuska tare da Kallon dad ta ce "Dad kace ita kad'aice nikuma fa"wara idanu a tare Mom da dad sukayi kafin Suyi dariya dad ya ce.

"a. A a Ina nufin ke kad'aice Baby Bakijiba"Cikin sauri ta Fara dariya tare mikawa dad hannu suka Taba ta ce "Nima Kai kadai Ne dad Mom na dariya ta ce"Ni Kuma fa?Make kafad'a tayi ta ce "Ke ai mun B'ata duka na kike Kuma kina yimun tsawa'"Dariya dad ya dinga yiwa mom yayinda itama Tana dariyar ta ce "zasu Had'e".

A tare suka gabatar da dinner dinsu Bayan sun gabatar da sallar isha'i a tare dakyal mom taja hankalin sabren wajen kunna Mata game a wayarta da haka dad ya samu yaje ya yi Wanka ya shirya sunjima suna hira a palour cikin tsantsar kauna da burgewa sai wajen 11 bacci ya dauke sabren a palour a hankali Dad ya dauketa ya Mayar da ita dakinta kafin ya kashe Mata glove ya fito suka nufi nasu bedroom d'in Shida matarsa abun son sa,

Dad Baiyi minti Biyar da kwantar da ita ba cikin bacci taji ana Daddab'ata Cikin sauri ta zabura Ta tashi waige waige ta fara ga duhu da ya baibaye ilahirin d'akin kuka take so ta fashe dashi Amma ta kasa saboda tsabar rud'u fitilun Dakin taga sun kawo gabaki d'aya ilahirinsu yayinda taji Kuma sun dauke haka suka Fara Mata su kawo su dauke da gudu ta Mike tare da rugawa a guje ta wuce bedroom d'in su Mom a lokacin suna Shirin kwanciya sukaji fadowarta Bata zarce ko ina ba sai wajen Dad Tare da Mak'alk'ale sa ta Fara kakkafewa A matukar rude suka Fara Tambayarta lafiya Bata iya Basu Amsa ba sai da ta Gama rudewar kafin ta Fara sauke Ajiyar Zuciya a tattare Cikin rud'u mom Ta ce.

"meya faru fada Mana sabren"dad ma cewa yayi "Lafiya daughter meya faru"Sai sannan ta iya daidaita nutsuwarta cikin shagwaba ta ce.

"Dad a wajenku Zan kwana Ni bazan kwana Ni kad'ai ba"Ran Mom b'ace Ta ce " da girmanki da komai Zaki kwanta tsakiyarmu da chan da baya Nan ba ke d'aya kike kwana ba saikin gansa ki kawo sabon iskancin Nan".

'daga Mata hannu dad yayi akan tayi shiru kafin ya dukursa ya kamo hannun ta ya ce"Kiyi Hakuri muje na rakaki ki kwanta baby na Har Kiyi bacci ko "kuka ta Fara tare da murza Ido ta ce "Dad bazan koma ba dodo yake tsoratani Ni wajenku Zan kwanta",.

ta k'arasa fad"a Tana cigaba da kuka Jin haka ya Sanya mom Jan dogon tsaki tare da juyawa ta koma gado bata sake ce da su komai ba ,dad ko Numfashi yaja tare da cewa"Shikenan bar kukan zomu kwanta".

"Sai sannan ta sauke Ajiyar zuciya tsakiyarsu Dad ya kwantar da ita zuciyarsa chunkushe da tunannika kala_kala,Mom ko juya musu baya tayi cike da takaici ba ayi 5 minutes ba sabren tayi bacci Saida daddy ya tabbatar da tayi bacci kafin ya Mike zauna.

"Amina "ya Kira sunanta a hankali,shiru tayi Bata Bashi amsa ba,nasan kina jina ki taso muyi magana ,sai sannan Mom ta juyo tare da Mik'ewa zaune kamar Mai Shirin yin kuka ta ce "Ina jinka"Saida yaja Numfashi kafin ya ce"
"

"Kin tab'a Jin alamun tsoratarwa a Gidan Nan,na kasa gane wani irin tsorone Yarinyar Nan take cewa ana Bata tun kafin na tafi me Hakan ke nufi".

Tuni hawaye har sun wankewa mom fuska ta ce "Karya take dear wlh ba wani tsoro da ake Bata tunda ka tafi ita kad'ai take kwana a d'akin in Banda Rana Daya da muka kwana tare Shima ba dalilin tsoro ba iskancine kawai me yasa da bakanan Bata cewa ana Bata tsoron sai sanda kake Nan wata biyu fa kenan Yarinyar Nan ta na bijiro Mana da wannan sabon iskancin Kuma idan munje Dakin nata muga Lafiya qlau, kaikuma kana biyeta Ai Shikenan sai muyi ta kwana taren mu ukkun da gard'amemiyar budurwa shekara Sha biyu y'ar j s s one gado d'aya tunda burinta kenan har mahadi ya bayyana ".

ta k'arasa fad'a Tana goge hawayen da suke zubar Mata tare da sake juya musu baya wasu sabbin hawayen takaicin na sake zubar Mata.....cikin kwantar da murya Dad ya ce.

"Kiyi Hakuri Dan Allah Amina mu bi al'amarin Nan a sannu har mugano kan matsalar tsoratata d'in da take fad'ar anayi ya Fara bani tsoro.

"Takaici ya Hana mom batace dashi komai ba Dan harshi duka jinsu take Tana Jin haushinsa wata biyu kenan a haka.....dakyal wani wahalallen bacci yayi gaba da ita dad ko dukda gajiyar dake tattare dashi bai hanashi tashi ya jera nafiofilu ba kafin Shima Baccin ya daukesa.

Washegari around 9:Am zaune suke a dining Momy tayi serving dinsu Kasancewar week end sabreen Bata zuwa makaranta,

Sabren sai labarai take yiwa dad yayinda dad ke biyeta dukda Yana lura da yanda mom keyin Abu kamar marar lakka nanko baisaba ganinta haka ba.

,Bayan sun Gama ne Ganin hankalin sabren baya kansu Ta na palour Tana game a laptop d'inta ya Sanya dad Kama hannun mom tare murzasu ya ce",

"Meke damunki My Menah Naga kinyi sanyi ko nayi wani laifin ne"Kirkirarren murmushi mom Ta saki Dan tasan ba abundanda ke tayarwa da dad hankalina sama da yaga ta sauya ta ce "Bakomai Dear".

Murmushi yayi tare da Kama hannunta suka Mike a tare Ya ce "Muje ciki sainaji meye matsalar ko?murmushin Jin dad'in mom Tayi Tana sauke boyayyar Ajiyar zuciya "ta Mike,.

,Suna shirin shiga ciki suka jiyo katuwar sallama a palour sabreen na Ganin BaBa ce ya sanyata murtuke fuska Tare da yatsineta kamar taga Kashi ,.

Mom ko da dad saurin sakin hannun juna sukayi ba tare da komawa palour kowanne da fara'a dauke da fuskarsa ,Cikin ladabi suka dukursa suka gaishe da Baba Tana amsa musu Cikin washe Baki cikin muryarta ta tsaffi ta ce "kwana biyu Naga Mustapha bakaje ba hankalina duk ba kwance ba Hakan yasa nace bari na leko naji ko Lafiya?.

"Lafiya qalau Baba ai tun tafiyar Nan Dana fada maki nayi sai jiya na dawo"Allahsrk ka jima kenan d'an kirki andawo Lafiya",

"Alhmdullh BaBa ya muka sameku ai da ma Baki wahala kinzo da kanki ba Daman yanzu nake shirin lek'a ku"A a a d'an Nan ai gwara da nazo da Naga lafiyarku da ta Jikata da Bata zuwa inda nake" .

murmushi dad yayi ya ce "Insha Allah zata dinga zuwa ganinki akai_Akai,sabreen najin haka ta Mike tare da Jan dogon tsaki ta yi hanyar waje,tsawa mom ta daka Mata ta ce "Dan gidanku Baki ga baba bane tun dazu kik'i gaishe ta ba!! ".

dad da sabreen na kasa banbance Wanda yafi wani rud'ewa,turo Baki gaba tayi tare da juyawa tayi hanyar waje zata fita Hankali kwance ta ce "Baza'a gaishe ta d'in ba ina ruwanki ",

dad ko cikin fushi ya ce "Wannan wace irin tsawace kikeyiwa yarinyar Nan Amina saiki rud'ar mata da kwalwa haba! Dan nayi Mata magana akan rashin gaishe da kakarta shine nayi laifi?cewar Mom Tana Masa k'uri da Ido"Baba tayi sauri ta ce "Kunga karku wani damu Yarinta ce Nan gaba da kanta ma Baku sani ba zataje har inda nake"....

Sabreen Kai tsaye gidansu Anesa ta nufa suka hau wasa kafin ta wuce gidansu Affan a chan ta ci ma abinci Rana Dan wasa ya kad'i hankalinta har yamma suna yawon wasa gida gida ita da abokin yawon nata...

.BaBa ita ce bata bar gida ba sai bayan magriba Wanda dad ya dauketa a mota Dan ya wuce da ita gidanta da ke jimeta local government Wanda minti Sha biyar ya kaika daga Yola zuwa chan kusan ma Had'e suke.,

Saida mom ta Gama lafiyayyen girkinta kafin hankalinta ya koma ga sabreen Kallon agogo tayi taga har seven eleven,Saida taja numfashi kafin ta Mike Tana Jin ciwon wannan yawon na sabren akuyar daure ta samu sake shiyasa yau tayini a waje Bata ganta ba...

.Mai gadi ta aika ya lalleka gidajen da take zuwa su taho tare...a gidansu Ummy ya samesu suna cikin fad'a da yayar Ummy dakyal Mai gadi ya rabasu Dan chan cikin gidanma basusan wainar da ake toyawaba dakyal ya shawo kanta ta bishi gida Tana ta hure huren hanci a Dole antab'ota.....

...kallo Daya mom Tayi Mata ta Kauda Kai taci gaba da lazumin ta zaunawa tayi kan sopa Tana ta hure hure Ganin mom ta kyaleta Ne ya sanyata Mik'ewa tare da zuwa kusa da mom kamar zata fashe da kuka ta ce "Ina dad mom"

"ajiyarshi Kika bani "Kuka ta fashe dashi har da birgima a haka dad yashigo Hankali tashe yayi kanta yahau Tambayarta lafiya daughter Sai sannan ta sauke Ajiyar zuciya tare da lafewa jikinshi kamar wata jaririya ta ce "dad wannan Matar ce"

"Me tayi miki"ya tambayeta mamakinshi mom Tayi a zatonta ko baiyi Mata fad'a ba zai nuna Mata abunda tayi ba daidai bane Amma sai tambayarta yake me tayi Mata a ranta tace wannan da matar uba ce ke ruk'onta tuni aurenta sunanshi matacce uwartama ana tuhumarta bare matar uba"

"Tsawa take yimun dad Bata Sona"Ta karasa fada Tana hawaye lallashinta dad ya dingayi Wanda Hakan har haushi yabawa Mom da kanshi ya Bata abinci Daren ranar ma su ukku suka kwana......

After two days sabren ta dawo daga islamiya Wanda dad da kanshi ya dauketa Bayan ya biya ya saya Mata ice cream da manyan choculate suka wuce gida da Daren around 10pm sun zauna a dining Area mom Tayi serving din kowannensu Kallon abincin sabren tayi tare da yatsine fuska ta kalli dad ta ce.
Chapter 5 · 0% Book details