← Book details Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 20

Sashe 1

Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

[12/8, 2:35 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN*🧸

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*

Arewa book👉@Miss Hajo✍️

*MARUBUCIYAR*
👇
< *Komai muk'addari ne* >
< *K'addarar soyayyya ta* >
< *Najmat Abiy* >
< *Ni da Yaya Arman* >
< *Auren wata Tara* >
~And now~
< *KHADIJATUL SABREEN* >

بسم الله الرحمن الرحيم

TEAM GAWURTATTU BIYAR✨🔥
________________________________

*GODIYA*

_Ina Godiya ga Allah ( s w a ) da ya k'ara bani ikon Fara rubuta wannan littafin Mai taken *KHADIJATUL SABREEN* tsira da aminci su k'ara tabbata ga Annabi Muhammad ( S A W) tare da ahalinsa da tsarkakkun sahabbansa,Ina rok'on Allah ( s w a )yanda na Fara rubutun Nan lafiya ya sa na Gama lafiya cikin amincewarsa da yardarsa Allah bani ikon rubuta abunda zai amfane Ni ya amfani al'umma ko bayan Raina,Allah ya tsari alkalamina da rubuta abunda yake ba Alkhairi ba,Allah yafe Mani Dukkan kura Kuran da zanyi a rashin sani zanyi amfani da wannan damar wajen nuna tsantsar Godiya ga d"aukakin masoya nagode kwarai da zallar soyayyarku gareni Ina matukar alfahari daku a duk inda kuke ALKHAIRIN Allah Yakai muku har Gadon baccinku farincikinku shine nawa masoyan asali miss hajjo takuce ta har abada Ina fatan Shima wannan littafin zaku so Shi ku kaunace Shi fiye da yanda kuke Cikin kaunar littafai na na baya nagode kwarai da nuna soyayya love you all my fans_ 💃💃💃

*GARGAD'I*

```Ba yarda wata ko wani yayi amfani da wani Bangare ko ya juyamun labari ko sayarmun ko edit da dai sauran abubuwan rashin adalci littafin Nan mallakina ne Ni Hajara L Sadeeq (Miss Hajo) muddin haka ta faru Zan d'auki tsatsauran mataki```

*GAISUWA*

_Dubun gaisuwa a jinjina ga d'aukakin members na novels group miss hajo Ina matukar alfahari daku Ina ji daku irin sosai d"innan Tatattun masoya Allah yabar kauna da soyayyya ina yimuku fatan Alkhairi Gabaki d'ayanku,dan ban Isa iya lissafo sunanku ba ,Tare da Daukakin members na kungiyar jarumai writers d'aya tamkar da dubu,Alkhairin Allah yakai Muku har gadon baccinku ina yinku Kuma ina kaunarku fiye da yanda Kuke Cikin nunamun_

```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM```

🅿️.........*1 & 2*

Matashiyar yarinya ce wacce a shekaru bazata wuce shekara Goma Sha d'aya ba sanye take cikin wata y'ar karamar y'ar kanti da ta tsaya Mata iya gwuiwa tsalle_tsalle kawai take Ta na wasanta hankali kwance A compound d'in tsararren Gidan da ya had'u Dukda bashi da wani girma na azo a gani Amma Gidan ya tsaru da shukoki ga tsarin gidan ya had'u Wanda kallo d'aya zakayiwa Gidan kasan mamallakin Gidan Yana Da Hali Sosai parking space din Gidan bazai wuce d'aukar mota biyu zuwa ukku ba,.

,part d'aya ne Gidan Wanda komai Yana ciki sai d'akin Mai gadi dake gefen jikin hadad'd'en get din Gidan dake zageye da wayar security,gefe guda Kuma motoci da kekuna tare da tarkacen abubuwa na wasan yaran tundaga kan Lilo,da sauransu Sosai nayi mamakin tilin kayan wasan dake wajen ba abunda babu na wasan Yara,tayi wasa da wancen tayi da wancen kafin tahau kekenta ta Fara jagaye Gidan dashi,.

Mai gadi dake Zaune Yana Jin radio Ganin Tayo wajenshi da Keke ne ya sanyashi saurin tashi ba shiri Yana komawa gefe Dan yasan k'aramun aikin ta ne ta bigeshi Saida yaga wucewarta kafin ya Girgiza Kai ya ce "Allah ya shiryeki yarinyar Nan"

Wata matashiyar Mata Ce ta fito daga cikin part din sanye take cikin tsadadden doguwar rigar Leshi da yasha d'inki ubansu ,Doguwace Mai madaidaicin jiki black beauty ce Masha Allah kyakyawa dukda shekaru basa boyuwa Amma a k'alla bazata wuce shekara talatin ba zuwa sama kad'an Amma hutu da gayu da Jin dad'i Dana Lura sun zauna a wajen bazaka kalleta kace takai shekarunba,.

Kai tsaye wajen Da taga Yarinyar tayi da keken ta nufa cikin sauri tayi sand'a ta kamota tare da rik'e keken ta ce "Tun d'azu nayi maki magana Kizo na Sanya maki Kaya ki tafi islamiya shine Kika gudo Nan to maza,wuce muje kishirya Dan gidanku Kullum saikin sani ciwon kai Akan islamiya".

Juyowa tayi tare tsatsareta da Dara daran idanunta masu matukar d'aukar hankali tubure fuska tayi kamar zata Sanya kuka cikin shagwababbiyar fuskarta da na Lura fuskartama gaba d'aya ta shagwab'e ce ta ce "Ni Mom bazanje ba na gaji ki rabu da ni "ta k'arasa fad'a Tana Shirin fashewa da kuka ".

Sai Sannan na kare Mata kallo kyakyawa ce sosai ta bugawa a jarida Fara ce Sosai Haskenta har wani shuni_shuni yake,Tana da round face Tare da manyan idanunta Wanda sune babban abunda ya k'ara fito Mata da ainahin kyaunta,hancinta madaidaici da yayi das da kyakyawar fuskarta,sai d'an k'aramun bakinta Daya chuno gaba Masha Allah shine kawai abunda zaka kalla yarinyar ka ambata saboda wani fitinannen kyau da Allah yayi Mata (Gaskiya za ayi budurwa a Nan Na fad'a a cikin zuciya ta) Doguwace y'ar Charas da Ita Bata da k'iba sannan Bata da rama ,lalllausan bak'in gashin kanta da akayi Mata kitso shuku ukku an Sanya beat masu matuk'ar d'aukar Ido duka gashin kan Nata ya saukar Mata har kasan k'eyarta Ni kaina Saida nayi mamakin yawa da silb'in gashin saika d'auka attachment ne aka Sanya saboda yawanshi Duk inda kyau yake yakai kyau to dai yarinyar Nan takai a kirata da kyakyawar k'arshe shuwa Arab kenan(Na fad'a a cikin zuciya ta Dan Ni kaina kyaun yarinyar Saida yaso ya zautar Dani kyau kamar aljana lol).

"Cikin sama da murya Mom ta ce "Kinma Isa kik'i zuwa islamiya Sabreen yaushe rabon ki da islamiya kusan sati guda kenan ko Dan Kinga na kyaleki na zuba Miki Ido ubanme kike a gidan da bazaki je makaranta ba awa guda kuntashi,saikinje wlh ko Kuma na lillisaki a gidan Nan tunda Mai d'aure Miki d'in ganinshi Yana hanaki zuwa School d'in baya Nan"

Ta fad'a cikin y'ar Tsawa Tana kamata tare da sauketa daga kan keken "Jin abunda mom ke cewa NE na saitaje makaranta Wanda ba abunda ta tsana sama da zuwa islamiya ya sanyata tirjewa tare da zaunewa a wajen ta Fara kuka da burgima a wajen kamar wacce akawa bugun mutuwa Sosai take kuka Tana cewa Bata zuwa.

"Takaici Duk ya Isa mom inda sabo ta saba da sangartar y'ar Tata Wanda Duk mijin ta ne ya sangartata ita kanta tasan bilhak'k'i matsayinta na uwa Tana iya bakin k'ok'ari wajen Ganin ta bawa y'ar Tata ingantacciyar tarbiya Amma abun ya gagara Kota Fara Daddynta saiya ruguza Mata ta rasa yanda zatayi da wannan bahagon halin na y"artata Wani irin zafi takejin ranta Gashi dai Tana ji Tana Ganin ilimin addini Yana neman gagarar tilon y'artata Sa'anninta hada Wanda suka kusa sauka Amma sabren hizif biyar cikakke Bata kawo maka Shi sangarta da b'aci da wasa da Jan magana Shi kad'ai ta iya".

"Numfasawa tayi daga wanna tunanin da ta lula tasan duka baya yiwa sabren da duka yanayi Mata da tuni ta shiryu dukda ita kanta ba ason ranta take dukan Nata ba durkusawa tayi tare da kamo hannunta ta fusge Tana kuka ta na cewa

"Daman nasan bakya Sona Dad kawai ke Sona Shiyasa kike yimun Tsawa Kuma saina fad"a Masa idan baya nan kina duka na "ta karasa fad"a cikin kuka kamar wacce aka daka",.

Cikin lallami da lalashi mom tace "Sorry Mom D'in Dad Ba tsawa nake maki ba Ina sonki Nima kamar yanda dad dinki ke sonki,kiyi hakuri muje na saukeki a school nasan Kema kinason kiyi karatu ki hardace Qur'an kizama babbar malama ni da dad muyi alfahari dake ko daughter na to yi hakuri tashi muje na kaiki idan muka dawo Zan saya maki manyan chocolate"

Turo Baki tayi Tana murza.idonta ta ce "Mom malamin Ne mugu Ni banason zuwa "Had'e fuska Sosai mom tayi ta ce "Kinga Ina lallamaki shiyasa kike b'atamun lokaci ko?Turo Baki tayi Tana cigaba da murza idanunta"mom ji take kamar ta daketa hakanan take daurewa Tana wannan lallamata d"in Dan batason ace sai duka Ne kad'ai zatayi Abu saboda Shi saboda ba abunda take tsoro sama da tab'a.lafiyarta amma Dole ta tsoratata cikin fad'a ta ce,.

"wlh Zan zaneki Sabren ,Dan iskanci waike yarinya ce da za ace Kullum saikin bani wahala Akan komai,jibi Sa'anninki fa akan idonki haka suke da iyayensu Meyasa kikeson bani wahala Sabren komai sainayi fafatu akanki ,kinsamun ciwon Kai kafin kiyi to wlh Zan dake ki yanzunnan tunda bakisan lallami ba duka Kika sani"

Jin abunda mom ta fada ya Sanya sabren tsorata saboda tasan halin mom Sarai zata iya zaneta musamman taga dad bayanan kuma ta rantse bazataje islamiya ba hakan ya sata saurin Mikewa tsaye Tana kallon mom ta ce "Zanje to Amma saidai ki d'aukomun kayan makarantar Ni bazan shiga ciki ba"

"A wajen Zaki sauya kayan me cikin yayi Miki da bazaki koma ba uwar kinibibi"mak'e kafad'a tayi ta ce"Ni dai Indai kina son naje saidai ki d'aukomun kayan nasa a nan"Girgiza Kai mom tayi tare da cewa "Allah ya shiryeki ya kawomun lokacin da Zan huta da fitinarki Akan islamiya kin b'atamun sama da mintuna Talatin"kafin ta juya ta shiga ciki da niyyar ta d'auko Mata kayan,.

Ai SABREEN na Ganin mom ta shiga ta kwashi k'afa da gudu ta ruga tayi bakin get ta fara kokarin bud'e k'ofa Mai gadi daga dakinshi Jin Kara ya sanyashi cewa.

"waye"Ai Tana Jin haka tayi sauri ta bud'e k'ofar tare da kwasawa a guje Tana dariyar wayan da tayiwa mom gida Mai kallon gidansu ta nufa kwankwasa k'ofar tayi da karfi Wanda ba shiri Mai gadin ya taho da sauri ya bud'e Yana Kallonta yasan Daman wanna aikintane bubbuga get kamar zata b'alla cikin Gidan Kai tsaye ta nufa Tana Dariya a parlour ta tarar da maman su Anesa "wajenta ta nufa ba gaisuwa ba komai ta ce"Momy Ina Anesa" "Suna makarantar islamiya sabren ke meya hanaki zuwa ".
Chapter 1 · 0% Book details