← Book details Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 20

Sashe 16

Khadijatul Sabren Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Rufamun bargo Amina sanyi nakeji,"Hankali tashe mom ta ce"To Dadyn sabren please ka Tashi Muje asibiti "Ki Rufamun zan samu sauki "Tana rufa Mai ya Kara cewa ta rufa Masa wani Saida ta rufa Masa bargo har ukku chan Cikin muryarshi da Bata fita ya ce "yayemun bargon Nan Amina zafi nakeji har Cikin Kashi na ji nake kamar ana huramun wuta a Cikin jikina zafi Aminaaaaa"ya fadada Cikin dauriya Yana Jan Aminaaaaa da karfi".

Iya rikicewa mom ta rude batasan sanda ta fashe da wani irin kuka ba ta ce "innalillahi wa Inna ilaihiraji'un meke faruwa dakai Mustapha?.........✍️

*Domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536*

_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

_*Miss Hajo ce*_ 🤙
[12/9, 9:17 PM] ~Miss Hajo~: 🧸 *KHADIJATUL SABREEN* 🧸

```MALLAKAR```

*HAJARA L SADEQ*

Arewabook👉@Miss Hajo✍️

🅿️..........*17 & 18*

Dad bai iya bata amsa ba sakamakon gushewar da hankakinsa ya fara saboda tsananin azabar da yakeji Gaba d'aya mom ta rikice a matukar rudewa ta Haye gadon tare da tallaboshi Taji jikinshi zafi rauuuu kamar wuta "sunanshi kawai take Kira Tana jijjigashi saikuma ta fada jikinshi ta fashe da matsanancin kuka.,

Tunda Sabren ta Tashi takejinta sai a slow fir tak'iya ta karya ita gida takeso Ba yanda Maman Affan ta iya sai rabuwa tayi da ita ta wuce gida a ranta Tana nazarin Daman sabren nada iskokokai kuwa?iyayenta sun sani kokuwa?.

Ba k'aramun Tashi Hankalin Sabren yayiba a yanda ta tarar da iyayennan nata Bata ta'ba ga kukan mom irin haka ba ga dad a sume jikinta "wani k'ara ta fasa Wanda shiya dawo da mom hankalinta da gudu ta ruga tare da rungumo dad ta fashe da kuka ta ce "Mom what happened to my dad mom meyasamu dad Dina jikinsa kamar wuta ".

Sai sannan mom ta lura da dad a sume yake Dan numfashi ne kawai zai tabbar da Yana Raye "Dakyal mom ta iya jarumtar mik'ewa ta janyo wayarta Cikin sauri,rasa Wanda zata kirama tayi aje wayar tayi tare da janyo gyalenta a rude. Ta ce "Taimakamun Mu kaishi asibiti baby bar kukan zai samu lafiya yi sauri "Sabren da ta Mak'alk'ale dad Ta na kuka ta ce "To mom Dan Allah mom Kar dad Dina ya mutu Nima mutuwa zanyi mom Ina sonshi sosai karki Bari mu rasashi".

Ta karasa fada Cikin wani irin kuka da tunda take Bata Tab'a irinshi ba da taimakon get man aka saka dad Mota mom tayi driving dinsu Basu zarce ko Ina ba Sai FMC Fedaral Medical center har suka Isa hospital din Sabren kuka take mom ko tashin hankalinta da take ciki Baya musaltuwa da komai mijinta mafi soyuwa a ranta uban yarta Kuma babban masoyinta Cikin halin mutuwa ko rayuwa Idan tatuna irin soyayyar da sukayi da dad saita fashe da kuka ba addu'ar da take in Banda Allah ya Tashi kafadunshi.

Emergency aka nufa dashi Sabren rungume mom tayi ta na kuka Mom Bata iya lallashinta ba sai kukan ita ma take,basuyi tunanin Kiran kowaba saboda Gaba Daya kansu ya fasu Wasa wasa Tun safe likitoci suke Kan dad Duk wani gwaji da za ayi Masa anyi Masa Amma basu ga Komai ba game da abunda ke damunshi Gado suka bashi tare da bashi Yan taimakon da ba a rasa ba,bayanin Dr yayiwa mom Akan basuga abunda ke damunshi ba Amma Sun kwantar dasu za a cigaba da gwaje gwaje har Allah yasa a dace da ganin ciwon.,

Yinin ranar asibiti suka yini cikinsu ba Wanda ya iya Shan ko ruwa Sabren ko kuka kawai take gwarama yanzu mom ta dake Tana lallashinta,Around 8 suna zaune sunyi jugum Sabren na gadon da Dad yake Mom na Kan kujera tayi tagumi,Cikin kuka Sabren ta kalli mom ta ce.

"Mom yaki Tashi har Yanzu please kice ya Tashi Ina son magana dashi mom "Bata iya Bata amsa ba sai hawaye kawai take ganin haka ya Sanya Sabren Fashewa da kuka ta fada jikin dad "Sai Lokacin mom ta iya daga Baki Cikin muryarta da ta gaji da kuka ta ce.

"Ki daina Hawa kansa kina Masa kuka baby zaiji sauki insha Allah ki dinga tofa Masa Addua sannan ki Tashi muyi salla mu roki Allah Shi kadaine zaiyi Mana maganin damuwarmu"Cikin sauri ta ce "To mom "tare sukayi Salla sun Jima suna Addu'ar Allah yabawa Dad lafiya kafin mom ta janyo wayarta "Mom wazaki Kira?cewar Sabren"Su Baba Zan Kira Nafada musu halin da Ake ciki?Bata Rai tayi sosai ta ce.

"Mom karki Kirasu Ni banason ganinsu,banason su da dad d'ina Allah ko kin Kirasu saina koresu"?Saboda me baby me yasa Wai bakya son Su baba bayan kinsan dai yayace wajen kakanki kuma kusan ita ta Riki Babanki tun bayan rasuwar iyayensu matsayin kakarki take Sarai kinsan da Haka Meyasa wai bakison dangin babanki?Ni ba kakata bace Allah kiyaye tazama kakata ,Maman Dad ta rasu tun Yana yaro yabani Labari bayan Nan mahaifinsa ya rasu Taya ta Zama kakata ".

"

Girgiza Kai kawai mom tayi tana dannawa mahaifiyarta Kira ta sanar da ita rashin lafiyar mijin nata Akan su tayasu da Addua sosai Hajjar mom ta rude ita kanta Jin Wai ba asan Kan ciwon ba.

Washegari mutane Duk sun Fara sanin halin rashin lafiyar dad sosai mutane ke tururuwar zuwa dubiya mom takira baba ta fada musu halin da ake ciki tun a Cikin wayar take kuka ba ayi ko awa guda ba sai gata Ta na kuka da shaftar majina Tana ganin dad ta fashe da kuka ta ce.

"Shikenan Na shiga ukku Ni lami D'ana Mai taimakona shine.a Cikin halin Nan?Na shiga ukku na lalace Shikenan asirina ya tonu Mustapha Kaine ci na kaina Sha na ,Kai NE suturata,kaine rufin asirina Dana y'ay'a na idan ka mutu Bansan wani Hali Zan shiga ba?.cike da masifa Sabren ta hayayyako ta ce .

"Kece dai Zaki mutu badai Dad Dina ba da Allah yiwa mutane shiru kinzo Kin ishi mutane da ihu Wama ya kawoki Asibitin Nan?tsawa mom ta daka Mata ta ce Zan B'ata Miki Rai baby dan Baki da kunya Babar kike fad'awa Haka ".

Baba ko Cewa tayi "Ba Cewa nayi zai mutu ba y'ar Nan Mutuwar Mustapha ai tonon asirina ce Kiyi Hakuri"Dogon tsaki Sabren taja tare da Kauda Kai tana ballawa Baba harara dake ta shafce majina "Sadiya ce ta shigo itama Da nata kalar haukan Zubewa tayi a k'asa Tana wani irin kuka ganin Masoyin nata da take da burin mallaka tun yarinta Cikin wani Hali batasan sanda Tafara sabbatu ba Tana cewa.

"Karka tafi ka barni Mustapha Dan Allah bakasan kalar son da nake maka ba ,nidin masoyiyarkace ta Hakika ,karka mutu ban cika Burina na aurenka ba "kafin ta fashe da wani irin kuka marar dadin sauraro ,ba Sabren ba hatta mom Saida ta firgita Jin kalaman Sadiya Ganin Tana Shirin yin gadon dad zata rungumoshi mom batasan sanda ta zabura ba Tare da zuwa ta bangaje sadiya Tana aika Mata da harara ta ce.

"Meye Haka fad'awa jikinshi zakiyi ko me?Sadiya Gaba daga hankalinta Baya gabanta Saida ta Tab'a wuyan dad Taji sanyi k'arai "wata irin zabura tayi ta ce "Amina Jikinsa ya fara zafi kafin yayi sanyi yanzu"Mamaki dauke da fuskar mom ta ce "Ya akayi Kika San jikinsa Ya Fara Zafi?"wayyo Allah na sadiya Innalillahi innalillahi"ta fada Tana Dora hannu a ka kafin ta fita daga d'akin a matukar rude gabaki d'aya da Kallon Mamaki suka bita ".

D'iyan BaBa magidanta maza biyu ne suka shiga Shamsu da Balarabe "Mom har Lokacin ta daskare a zaune Sabren ko Wani irin tafarfasa takeji zuciyarta nayi kamar zata tsage gida biyu a duniya idan da Wanda ta tsana Basu wuce su BaBa ba, Gaishe da mom sukayi Cikin ladabi tare da yi Mata ya Mai jiki "Suna yiwa Sabren magana Dakyal ta iya bude Baki tace "Sannunku"Baba ce ta ce "Ko gida kike zuwa ki Shirya Ki Dan huta' Amina tunda gamu Kuma ga Yan uwansa sun kula dashi".

Girgiza Kai Mom tayi ta ce "A a a baba Zan zauna Zan aika a dauko Mana abunda muke bukata "ganin baba Taki Tafiya NE ya Sanya Sabren Jan tsaki tare da Tashi tabar d'akin Gaba Daya ta koma waje ta zauna Kan chairs ta Had'e Kai da gwuiwa ta. Na hawaye.

Daren ranar mom ta Kira Uncle Ahmad don ta fada Masa halin da ake ciki Koda ta fada Masa Rashin lafiyar dad sosai ya nuna tashin hankalinshi tun a cikin wayar saidai yacewa mom Yanzu Haka yana Shirin b'arin kasar zuwa Australia wani muhimmin aiki Amma idan yadawo zaikira yaji halin da ake ciki".

Washegari Y'an yola sukazo duba dad Ciki hada maman katsina da maman Mom da Kuma yayyu da kannan ta sosai sukaji dadin zuwansu kowa yazo Saiya tausayawa halin da dad yake ciki numfashine kawai zai tabbatar da Yana raye Dan abincima da ruwa ta na'urori ake basa gashi babban tashin hankalin har Yanzu an Gaza gano abunda ke damunsa.".

Aunty sadiya ko tunda ta tafi basu Kara ganinta Asibitin ba ,sosai mom take kashe kud'i a hospital dinnan a aljihunta Gaba Daya harta rame Ga rashin cin abinci ga tashin hankali kwanansu Yan yola biyu Suka juya Banda Maman katsina da tace zata zauna Suyi jinyar Tare bazaiyu a bar y'ar uwarta ita kadaiba da wannan jinyar tunda Daman sunsan dangin dad ba wani kula dashi suke ba Abun hannunsa suke so sosai hakan yayiwa mom da Sabren Dadi Dan Koba Komai Tana kwantar musu da hankali itake tilasta musu da sai sunci abinci.
Chapter 16 · 0% Book details