← Book details Idan Rana Ta Fito Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 19

Sashe 4

Idan Rana Ta Fito Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dawo., Ya basu mota ya kuma ce baya son suje ko'ina sai Mkrnt, ya tsorata su da cewa kada su ga ba ya nan sucanza dabi'u ya saka abinda duk inda suka je za ya mishi bayani. 18.Duk sun yarda musamman Basma wadda ta tuna abinda ya faru baya. Ya yi murmushi da ya tuna yanda suka tsorata tare da rantse mishi cewa ba za su canza ba.Ya janyo filo ya rungume yana me tuna lallausan jikin Basma tare da kamshinta, kanta ya soma sanin wacece mace, don haka baya wasa da ita. Ma'ana baya son abinsa zai sosa ranta, nashi ganin tafi dukkan wata mace a bayan kasa.Cikin kawana 2 duk wani abu da lefen ke bukata ya kammalu, hatta dinkunan.Ya jinjinawa Anty Nana, don ta tsaya tsayindaka don ganin komai ya hadu.Sajan Sani ne ya ja motar zuwa Garkosukadauki wasu daga dangin mahaifinsa, sannan suka nufi kauyan su Maigari.Gidan Maigari suka sauka, sun ci sun sha sannan suka kuma dunguma zuwa gidan Amarya.¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤­¤¤¤¤Ni ina zaunebutu- butu gidin murhu ina yiwa Hinduwa dimamen tuwo, ga danta a bayana yana ta kuka hancinsa dam da majina, sai muka ji tsayuwar motoci.Babana ya fito ya tare su tare da yi musu sannu da zuwa.Sajan ya shaida ma Baba cewa lefena sukakawo, tabarma Baba ya amso nan makotanmu shi da kanshi ya shigo ya same su tsattsayemutan gidan sai kallonsusuke yi.Baba Gaje ce ma ta zo tana baje jayayan hakoranta tana cewa,"Sannunku bayin Allah, daga ina?"Sai kuma ta hango matan Maigari nan taketa nufi gurin su tana cewa,"Lafiya?"A'a wai na ce lafiya?"Kafin su yi magana Baba ya shigo da tabarma nan suka amsa suka shimfida suka zauna 19.Ya ce,"Gaje kawo ma baki ruwa."Da yake bata san dalilin zuwan su ba, nan ta nufi dakin Jama'a don aron kwanon sha, sbd Baba Gaje dai bata da abin kanta.Bayan ta kawo musu ne ta nufo inda ni ke ta zubamin rankwashi iya karfinta har sai da na gigice tare da cewa,"Tashi a nan uwar kallon tsiyakada ki sa su amai da wannan warin naki."Na mike na nufi cikin daki." Daga ciki ina jin lkcn da matan suka shaida ma su Baba Gaje cewa lefen Jidda suka kawo. Gaje ta fiddo da dukkan idanunta waje tareda cewa," Wacece me wannan sunan, kunanufin Kuluwa?"Suka ce,"Eh."Ta ce,"Kunyi 6atan kai, ina ga dai Kuluwar gidan Me jakai ce."Matan Maigari suka ce"Ta nan gidan ce ba 6atan kai muka yi ba.",Da saurita iso dakin ta janyo ni zuwa gabbansi."Kun ga fa irin tamu Kuluwar, wane mahaukaci ne zai ce yana sonta?Koko Birni suna matsalar Kuluwa ne ba su da masu sunan. 20.Baba ya yi tsaki sannan ya ce ma bakin "Toan gode muku."Matan Maigari tare da sauran bayin Allah da suka zo tare dai mamaki ya hana kowa magana.Suka mike suka ce,"To su daikan za su tafi."Baba ya kawo kudi ya ba su ya ce,"Ga tukuici."Suka ce ba za su kar6a ba, ya ce,"Su amsa ai haka ake yi, sannan suka amsa.Suna fita nan fa Baba Gaje Faifan bala'i wato ita muguwa ce har da za a dinga 6oyemata abu?"Lallai kuwa za a ja da ita.Yau kam sai ta ji dalilin da za a 6oye mata auran Kuluwa, ko ba ita ce ta haife ta ba ai ita ce taci kashinta ta kuma ci fitsarinta. Saiyau naga fushin Baba inda ya ce,"Karya ki ke Gaje!"Ya bugi kirjinshi "Ni nenan na ci kashin Jidda na ci fitsarinta, ke tauye ta ki ka yi tare da bautar da ita kin manta ne?"Ta ce,"Haka ka ce?""Eh,na fada."In ji Baba.Ta rasa me zata ce, sai ta zari mayafinta ta yi gidan Dija.Tana shiga tarushe da kuka tamkar waddaaka ce mata uwarta ta mutu.Dija ta taso tana sallallami, tana fadin."Kawalli me ya faru?"Cikin kuka riris take sanar da Dija cewa,"Ashe batun auran Kuluwa gaske ne?"Dija ta dafa kirje tare da cewa,"Kai haba?"Gaje ta ce,"Wallahi kuwa, ga lefe can an kawo Adaka ce kusan guda 6 ban ma ta6a ganin irin ta ba."Dija ta ce,"Wanene kuwa mijin?" 21.Gaje ta ce,"Ina zansani?Ni dai ba ruwana da harkar su kayan su ma ba dai dakina ba, kuma ko zan tafi tsirara ba dai su zauna lafiya da mijin ba."Dija tasa hannu ta dafe mata baki tare da cewa,"To sarkin shirme an ce miki ana fadane, batun ki ce ba ruwanki da biki bai ma taso ba, kin san halin kauyan nan ba su iya tsegumi ba.Yanzun a zaga gari da ke ace kina bakin ciki, yi kokari ki danne in yaso 'yan bori na sun ishe su.Za mu sa su turo musu Aljannu su hana su zaman lafiya,ko ya dinga ganinta a Dodo kin gani dole neya sako ta."Gaje ta ce,"Kin kawo shawara, sai dai Allahyasa na iya dannewa, in ga wannan Bakin cikin."Dija ta ce,"Za ki iya mana muje gidan yanun sai ki nuna cewa kin zo ne ki gaya min mu zo muga kaya daga nan sai ki aika duk Jama'a su zo su gani, ki nuna murnarki ki danne komai."Sai ga su sun dawo kafin su dawo ma gidanya soma cika nan kuma aka rasa yanda za a bude akwatuna.Sai da aka aika gidan Maigari sannan aka zo aka bude.Ba Baba Gaje ba, hatta Dija ta ji bakin ciki kayan, gashi matan Maigari sun dawo su ne ke daga kayan saboda sata, dankunne da sarkan ma ba su bari kowa ya ta6a ba, sun dai nuna suka ce daham ne dashi za sutafi.Cikin abin da bai fi sa'a biyar ba lbrn kayanaurena ya zaga har makotan kauyan sun soma samun lbr.Wasu da yawa da yawa in za su yi kwatancena kucakar gidan Wanzamai sukece min, shi yasa ba a sha wuya gurin gane ni ba.Dija da Baba Gaje cikin daki suka tara ni sai na gaya musu wanene mijin, na dinga rantsuwa kan cewani ban san shi ba............ [29/09 11:22 am] Inna👬👫: 21.Hinduwa kuwa kuka ta kwana yi wai Baba ya samo min miji a birni ita ya k'i samo mata.Hakan ya k'ara d'aga hankalin Baba Gaje dama akwatunan shagonsa suke kwana ta ce d'akinta ba guri. Sauran matan gida kuwa suna tsoranta.Matar Yaya Auwalu ma har da had'a ni da Allah wai in fad'a mata ko wanene mijin, wallahi ba zata sanar da kowa ba, na ce nima nan bn san shi ba, k'ila ma nakashsshe ne, ta ce haba?"Na ce Allah to in ba haka ba wa ki ka ga zaya aure ni?Nan kuwa matar Auwalu ta je ta sanar da su Baba Gaje cewa mijin nawa nakashasshe ne, wai ta lalla6a ni na gaya mata.Nan kuwa zance ya shiga yad'a gari, kai wasu ma har cewa suka yi K'ila dai irin 'yanshan jinin nan ne da yake ana cewa suna yin amfanin da Mahaukata, to wai ya ganniya zata Mahaukaciya ce.Babana ya tafi ya sanar da dangin mahaifiyata ya ce da wan mahaifiyata ya dace su zo don kula da kayan aurena da aka kawo, ya dawo kamar yau washe garinsuka zo."A lkcn Baba ya 6ulo da shagonsa ta cikin gida aka kulle k'ofar waje.Nan dangin mahaifiyata suka zauna, hakanya dad'a k'ona ran Baba Gaje don dai Dija tana tausarta."A na sauran kwana 3 daurin aure Baba Jummalata tsafe min kai, ni kaina na tsorata da irin kwarkwatar da ke zuba dagakaina, kalkashin suka sa suka wanke min kaina sai naji tamkar an cire min kayan nauyin nedaga kan nawa.Ana saura kwana 2 daurin aure Baba yaje suka sayo min kayan d'aki, ranar ce kuma aka saka ni a lalle.23.Gidan k'anwar su Babanmu muke zaman lallan, itama a tsorace ta amshe mu don duk 'yan gefen Baba Gaje ne. Kawaye kuwa har da wadanda ba su ta6a min magana ba, duk sun zo sun shiga bikina. Ban san abokan ango ba bare in dago ko wanene Angon nawa, komai da Angawaye za su baiwa Amare daga gidan Maigari akekawo shi.An saba kajin alibidi guda 2 ake kawowa, sai ga nawa guda 10. Kai komai nawa ya fita daban, ana gobe daurin aure mijin nawa yaaiko da buhunan shinkafa 'yar Gwamnati da Rago tikeke, tun lkcn aka yanka shi aka shiga suya, miya aka yi ranardaurin aure da safe kuma tyn Asubahi aka girka shinkafa.Wani abin alfahari ba a ta6a yin wani taro a k'auyanmu kamar na aurena ba, ko lkcn nadin Sauratar Maigari taron bai kai wannnan ba.Motoci daga birni 'yan daurin aure ga su nan.Bayan an daura ne kuma aka shiga cin abinci, suma angawayan sun zo da abincin cikin wani d'an abu ga kuma lemon kwali da na roba.Suka yi ta ba Jama'a kowa sai sambarka dahamdala, mata kuwa ba na kauyan namu ba hatta da na wasu mak'otada kauyan namu sun lodi abinci.Sai dafawaake ana ba Jama'a, ku ce min ina Baba Gaje lkcn???24.Tana nan daki ta kasa fitowa don damuwa,kawayan ta suna tausarta, in sun fito waje kuma suyita yi mata dariya tare da cin abincinsu gamida kaiwa gidajansu.Dangin uwa ba su da na 2, sune suka tsayatsayin daka a bikin matan gida ma in tana d'aki su fito suma susa hannu in kuma ta fito sai su koma daki.Mutanan k'auyen mu ba su girgiza ba sai da aka gama d'aurin aure suka ga wanene Ango.#MuhammaduBello­ Tahir,yana sanye da shadda danya ,mai ruwan k'asa 'yar ciki da malun-malun, ya murza hula Minsta itama mai kalar shaddar Haka nan takaliminshi duk in da ya ratsa k'amshine ke tashi.Na ya durkusa gaban su Baba wanda shima ya yi wankan farar shadda malun-malun aska tara itama daga Angon nawa ya kawo masa, ya gaishesu Baba ya gabatar da shi gurin abokansa da wan Mahaifiyata, da kuma sauran 'yan uwansa.Duk sun sha mamaki, da kyar suke iya furta Allah ya sanya alheri.Shi kuwa nanya cika su da kudi, shi da su Ado suka yi masa rakiya zuwa cikin gidanmu don gaida dangin mahaifiyata.Kafin su karaso tuni lbr ya iso cewa ga Angon nan shigowa, tuni mata suka shiga baza idanu don ganin wanene Angon.Tsohon ne ko nakashasshenne??"25.Lokacin nima ina zaune cikin d'akin da dangin mahaifiyata suke zaune, sanye nake cikin leshi ruwan d'orawa na rufa gyale fari, ni kaina samun kaina da faduwar gaba lkcn da Sayyada 'yar wan mahaifiyata ta shigo tana cewa wallahi ga Angon ya shigo, mutane suka bisu da kallo ga Marka har cikin gida.Baba Gaje ma
Chapter 4 · 0% Book details