← Book details Idan Rana Ta Fito Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 19

Sashe 3

Idan Rana Ta Fito Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

11.Mata da yawa suna bada lbrn halin maza na rashin kirki ko cin amana, ko kuma sakacin alkawari, niko zan bada lbrn rike alkawarinshi gami da yafiyarsa.Ki lura Husna, Bello Tahir bai ta6anuna min cewa mahaifina yasa a harbe shi ba, kuma an harbe shin ya yi jinya amma bai nuna min ba, sai da ya taho Sajan yake fada mana tare da ke."Sannan mahaifiyarki'yar uwarta ce dubi abinda ta mishi amma hakan bai sa shi juya baya daga gare mu ba ni da ke.Hasali ma sai tattalinmu gami da nuna kuluwarshi gare mu. Kalli irin kudin da yake kashe mana."Husna ta ce,"A gaskiya Anty Basma kin gama dace shi ne dalilin da yasa ki ka ga ina son Bilal, don wasu da'iun Bros rin nashi ne."Basma ta ce,"Na Allah in yaso sai ki ga ya shirya lmrnkun auri juna.""Allah yasa haka ne."Duk abinda Basma take fadi kan Bello Tahir haka ne, har cikin ranta ta ba shi dukkan gaskiyarta, duk abinda ya ce gare ta gaskiya ne.Ta yi matukar yarda dashi, shi kan shi in yatuna da batun Jidda gabanshi yana matukar faduwa, sai ya samu kanshi da da ya sanin auren da ya dedo ma kanshi, amma kuma in ya tuna da halin Jiddan ke ciki sai yaga cewa taimako ne, fatan shi daya Allah ya shige mishi gaba kan niyarsata alkhairi.Yana cikin mota kan hanyarsa ta dawowa gida Dady ya kira shi yana sanar da shi cewa.""Bello an bani mata, ina nufin shawarar da ka bani nayi kanta. Yanzun haka zuwa ranar Jumma'a zaa daura aure, kuma ta tare."M.B ya ce,"Kai amma fa nayi murna sosai,amma ka bincika sosai ko?" 12.Ya yi 'yar dariya."Na bincika mana Bello, Bazawara ce amma yarinya ce haihuwarta daya, mijintaya rasu ne."M.B ya sake cewa da mahaifin nasa."Ka bincika dalilin mutuwar mijin nata ko?"Saboda cutuka da suka yi yawa yanzun."Ya ce,"Eh hadarin mota ne."Yar limamn anguwar mu ce tana da hankali sosai, hakanan ga duk binciken da nayi bn ji wanda yafadi aibunya ba.""Alhamdulillahi,­a gaida mana Anty sai in mun zo."Yana isa gida ya taras da su Basma sun dawo daga Mkrnt, duk kansu suna zube kan kujera. Da sauri Basma ta taso ta rungume shi tare da mishi sannu dazuwa, Husna ta mishi sannu da zuwa. Ya zauna a gajiye ga yunwa.Basma ta zauna kan cinyarshi tana cewa da shi,"Darlingyunwa muke ji sai yanzun Helin ta dora abinci, kaje ka amshe ta don ka fi tasauri kuma naka yafi dadi."Yasa bakinshi ya dan tsotsi le6enta tare da cewa.""Na gajiMy Dear,nima in so samu ne in hau cin abinci yanzun."Dukkansu da Turanci suke magana tun zuwan su k'asar ba sosai suka cika yin Hausa ba."Ta ce,"To kaje ka taya tamana."Ya sake manneta a jikinshi."Basma ke da Husna ya dace ku koyi dafa abincu fa, musamman ke Hunsa in ni na jure baki sani ba ko wanda za ki aura ba zaya jure ba.""To kuwa Brother in ba zaya jure ba sai dai ya yi ta cin Indomie."Dukkan su suka sa dariya."Ya ce,"Na tuna Dady fa ya yi aure."Husna ta zaro idanu.""Aure kuma Bros?""Uhmhm!Ba a dai daura ba sai ranar Jumma'a."Ta ta6a baki, Basma kuma ta ce,"Budurwa?""Yariny­a ce amma ta ta6a aure."Husna ta ce, "Ni kam Bros ka ce mishi ya hkr ya dawo da Hjy.,Ganin yadda ta 6ata rai tamkar zata yi kuka sai ya ce,"Tozan shawarce shi amma kin san ba lallai bane ya yarda."Husna ta ce," In ma ba zaya dawo da ita baya hkr da auren ya auro karamar yarinya ta raina mu?" [29/09 9:29 am] Inna👬👫: 13.Dariya Husna ta bashi, ya dai gano cewa kishi ne ke damun Husna. Waton tana kishin mahaifiyarta."Dady bai isa ya zauna haka ba tukunna batare da wadda zata dafa mishi abinci ba."Ta zum6oro baki."To baga kuku ba?""To in mun yi waya zan fada mishi, ko kuma ki kira shi ma."Ta ce,"A'a kai ne zaka fada masa don ya fu jin maganarka.""To zan fada, ki ka ce in ce mishi kina gaidaAntynmu ko?"Husna ta sake turo baki.Basma tana dry tana kalon fuskar M.B, ta sumbaci wu yanshi tare da cewa.""Honey kana k'ara kunna Husna ko?"Helin ce ta katse su da cewa"Ta shirya musu tebur."Shi kam M.B ya kanci abincin Helin ne kawai don yunwa, amma ba wai don dadi ba, su kuwa su Basma har da santi.¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤Ran­ar Juma'a kuwa bayan an tashi daga Sallar Jumma'a aka daura auran Alhj Tahir da Amaryarsa Fatima, wadda aka fi sani daNana, kuma a ranar ne ta tare a gidanta wanda yasha gyara tare da cana dukkan Ma'aikatan gidan.Rayuwa sosai su Dady suka shiga Shimfidawa shi da Nana, lallai namiji damaan ce namjin yana tsufa ta wani gefe ya kuma lkcn karfinshi ke kara zuwa ya dinga jin shi tamkar saurayi.Nana zata shaida hakan.14.Ni kam ina nan zaman jiran miji har an sa kimanin wata 6 ni da Baba ya ce nan da wata 3 har an kara 3 ga matsi da nake fuskanta daga gurin Baba Gaje fiye da da.Ga Hinde tunda ta haihu aiki ya karu gurina, wankin kashi, goyon yaron mai suna Zubairu, du in da zani dashia baya, ko talla har ma wani lkcn ya ki uwarsa sai ni.Binto ma ta haihu 'yarta budurwa sunanta Jamila, matar Ado ma tana nan da nata cikin.Shi kuwa M.B baya son zuwa Najeriya ne sbd batun auranshi da Jidda wanda kusan shi ne ya janyo ma kansa, amma in ya yi wani tunani sai yaga kamar bai yiwa iyayanshi da ita kanta yarinyar adalci ba, inya san ba zaya iya ba me ya kai shi cewa za ya yi?"Koda yaushe cikin saka wannan lmr yake, daga karshe ya tattara lamuranshi ya mikasu ga Mahaliccinshi, duk abinda ya faru da shi ya yarda daga Allah ne kuma zai amsheshi hannu bibbiyu [29/09 9:32 am] Inna👬👫: 15.Cikin haka kwatsam sai gashi aiki ya taso mishi daga gurin aiki an tura shi Najeriya, alissafin shi aikin zai dauke shi tsawon sati 2amma an bashi sati 4, don haka sai ya yi tunanin yin amfani da damar ya cika alkawarin da ya dauka duk da dai Lagos aka tura shi aikinki.#NIGERIA!Ya sauka Najeriya a Abuja, watanshi 9 kenan rabonshi da kasar.Ya sake hawa wani jirgin don zuwa Lagos. Cikin taimakon Ubangijinshi a kwana gomaya kammala aikin shi, ya nufi Kano.Kafin ya bar Lagos din sai da ya hada lefenshi tsaf,a kwatuna ne guda biyar da dan karamin su cikon na shida.Ya bi jirgi ne zuwa Kano sannan ya yi shatar mota zuwa gidansu, kafin ya karaso ne ya kira mahaifinshi ya sanar dashi cewayana shigowa yanzun nan don ya iso Kano din.Dady ba ya gida amma ya kira Nana yashaida mata zuwan dan nasa.Lokacin da yashigo gidan bayan ya sallamimai tasi, 'yan aiki suka kwashi kayansa zuwa ciki.da salla,a ya shiga falon, babu kowa ya sake yin sallma tare da zaunawa kan kujera.Ta fito tana sanye da atamfa 'yar Ingila da bakin hijabi a kanta.Kyakkyawar mace mai cikar mutunci, da fara'a ta tare shi tare da cewa "Kai ne tafe?"Ya yi murmushi."Ni ne Anty."Bata samu matsala ba don bata baringidan babu abinci. [29/09 11:21 am] Inna👬👫: 16.Nan ko ta shirya masa abinci kan tebur ta zo ta ce"To Bello ga abinci fa sai dai Allah yasa kana cin rin shi domin namu ne na gida."Ya ce,"Anty kenan, ai ni na fi son komai nawa inda zai yiwu in yi amfani da na gidan ba ma abincin ba."Ya ci gaba da cewa,"Ba mu gaisa ba sai batun abinci." Ta ce,"To ai zamu gaisa tunda gida kazo."Tuwo ne na shinkafa da miyar shuwaka, yaci tamkar kar ya koshi don dadi, ya jima baikoshi haka ba. Yana idar da sallah Dadynshi yanashigowa.Ya dubi mahaifin nashi da murmushi cikin tsokana."Dady kai ne kayi k'iba haka?"Dariya suka sa har Nana.Dady ya ce,"Aikin Antunka kenan, cika miniciki take yi da kalolin girkinta."M.B ya ce,"Na lura don nima na shaida haka.""Yaya ya zo babu su Husna?"M.B ya ce,"Ai ya zo Lagos kuma ya kammala aikin.""Allah ya taimaka,ina fata dai ka taho da shirin ka na zuwa kauye, don Babanka Maigari da kansa ya zo kwanaki don jin yanda ake ciki, na kumatabbatar masa da ka iso da sati guda za a soma biki."M.B ya share zufar da ta feso mishi, sannan ya dubi mahaifinsa.""Kayan can lefe da shi na taho."Dady ya ji dadi tareda cewa Allah ya yi masa albarka.Shi kuwa ya ce,"Anty Nana ki duba duk abinda babu sai a zuba, sannan a yi mata dunkunan kayan da za da zai samu duka." Ta ce,"To, sai dai a raba ma Teloli."Nan ta shiga dubu kayan.Rantsattsun lesuna ne da shaddodi da kuma atamfofi duk na karshen kudi, takalma da gyalulluka zuwa after dress ba a magana. 17.Anty Nana ta yabakaya, sannan ta ce, "Sai kayan shafa zuwa kayan ciki irin su siket." Ya ce,"To Anty sai ku shiga kasuwa, yarinyar dai k'arama ce ina tunanin ba ta wuce sha shida zuwa sha bakwai ba."Anty Nana ta ce, "To za'a siyo. Sai batun dunkunan a dinka duka?""A dinkesu kawai don can ba su da wasu Teloli."Dady ya ce,"Haka ne."Bayan sun gama wannan babin sai Dady ya ce,"Ka sanar da Basma kuwa?""A'a sai nan gaba saboda wasu 'yan dalilai."Haka da dare sundawo daga Sallar Isha'i su da Dadynshi suka samu abinci kusan kala 4, kowanne dai-dai cin mutum uku. Nan fa M.B ya shigaruwan ido ya ma rasa wanne zai ci, nan ya ci wannan ya ci wancan ga kunun aya da kwakwa da dabino, ga so6o.Ya dubi Nana ya ce,"Anty Nana ina ma a nan nake."Duk suka saka dariya.Abinda ya k'ara birge shi da matar mahaifin nasa shi ne, yanda take matukar girmama shi da yin tsantsam da duk wani abu da tasan zai sosa masa rai.Cikin dare yana kwance gefensa na da tunanin Basma yake yi wadda ba su dade da gama waya ba yanzun.Yana son ta bayason abinda zaya sosa ranta. Yana tunanin ranar da zata ji ya sake aure ba tare da ta sani ba.,Gashi ta yarda dashi duk wata gaskiya ta ba shi, tana makutar sonshi.Ya tuna sanda zaya taho, rungume shi tayi tana kuka, kuka sosai da kyar ya sha kanta dama kwana biyu kafin ya taho ya shiga kasuwa da su sun siyi duk wani abu da za su bukata kafin ya
Chapter 3 · 0% Book details