← Book details Idan Rana Ta Fito Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Idan Rana Ta Fito Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

6.Sai da na gama talla sannan na shiga gidansu Binto, tana zaune tsakar daki nayi sallama na shiga. Sama'ila yana shan kunuya ce,"A'a Kuluwa ce?"Cikin murmushi na ce, "Ni ce kuwa. Binto sannu wai cikin nan naki da girma yake haka ma na Hinde."Ta ca,"Don Allah ke kin cika shirme, zauna mana."Na zauna muka gaisa da Sama'ila, ya miketare da cewa,"Ya tafi Gona."Binto ta yunk'ura zata tashi, ko rakiya zata yi masa? Sai ya ce"Zauna abinki na hutarki.""Allah ya tsare ya bada sa'a."Ta ce mishi.Ya yi murmushi ya ce,"Amin Kuluwa sai anjima."Na ce,"To sai anjima."Binto ta dube ni."Kin san Yaya Ado zai zo hutu kwanan nan kuwa?""Kai! Da gaske?""Allah kuwa." Ta tabbatar min.Ta turo min wani kwano."Ga d'umame nan ki ci ga kuma kunu cikin wancan kwanon shan."Na ce,"To bari in ci, nasan kona koma gidad'an ruwan kokon ma da kyarzan samu tunda Hinde ta zo."Binto ta ce,"Har yau dai abin na Hinde ya k'i ne?"Nace,"To Binto yaushe kuwa lamura zausudai-daita, ko yaushe Baba Gaje tana shiryamata yanda zata ci mutuncin uwar miji da shi kansa miji. Binto ban ta6a rik'e su BabaGaje cikin raina ba ina ga shi ne Allah ya yi min wata sakayya."Ta dube ni da kyau."Wani abunne ya faru?"Na gyara zama na fara kora mata duk yanda muka yida Baba jiya. Murna gurin ta ba a magana.Sep 4Aisha Ummu Shureim Sa'eedMsmart BG Zee Town7."To ya ya ba ki tambayi Baba ba kin ji ko wanene?"Na ce,"Na kula baya so in sani ne, ana shi zaton ba zan yarda ba k'ila tsoho ne."Binto ta ce,"Insha Allahu ma ba tsoho ba ne.""Ni ko nakasashshe ne ma na gode Allah, tunda ya d'aga ni daga gaban Baba Gaje. Sai dai fa Amana na baki bana so ki fada ma wani, don su Baba Gaje ba su sani ba.""Ai ko babu mai ji, sai dai zan so ki fadawaHaja, nasan zata yi murna sosai.""Daga nan can zan nufa."Haka kuwa nayi.Ina shiga dakinta ta tare nida fara'a muka gaisa. Cikin zumudi na shiga karanto mata abubuwan da suka faru. Jin baba bai gaya min ko wanene mijin ba yasa Haja yin shirutare da nuna min bata san komai ba akan auren.San da na ce mata "Ina zaton tsoho ne ko yana da nakasa shi yasa baba ke 6oye minko zan ki.Sai naga Haja ta kwahe da dariya tare da cewa."In Allah ya yarda ma yaro ne."Na ce,"Ko wanene ma Haja in dai Musulmi ne ya yi min.¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤An­ samu kusan sati 2 da faruwar lmrn, rannan sai ga Dija Aminyar Baba gaje."Ina gibdin murhu ina jiyo su lkcn da take cewa da ita."Kawalli kin ji lbrn da na samo gidan Hassi?"Ta sake nisawa tare da rik'e bakinta.""In ko haka neGaje kin yi sake."Gaje ta ce "me aka yi kuma? Ko kina nufin batun Hinduwa?"Dija ta gyara zama.""Tabbbas ba ki
[29/09 9:19 am] Inna👬👫: Idan rana tafito

n8.Dariya Baba Gaje tasheke da ita har da kwarewa, sannan ta ce da Dija.""Don Allah ina ki ka samo wannan lbrn k'anzon kuragen?Ai ko cikin mafarki haka ba zata ta6a faruwa ba, bare gaske."Dija tayi 'yar dry tare da cewa."Ke dai bincika a hankali, domin kuwa za su iya 6oye miki."Cikin rashin yarda da zancen take dariya da cewa"To zan bincika, don ance ba a k'inta mu2m. Amma bisa gaskiya shirme ne wannan zancan." Ta nuno ni da yatsa."Dube ta fa sai ka ce dabbar daji, tayimiki kama da mu2m wadda za a duba ace ana so har ma a aura?"Dija ta shek'e da dry."Wa yaga Mujiya."Da suka fito zata tafi sai ta ce"Tambayar ta mu ji."Baba Gaje kuwa sai cewa ta yi."Kuluwa da gaske aure Babanki zai miki?"Na dube ta sannan na ce,"Yaushe?"Nan suka shek'e da dariya.Dija ta ce,"Har da saurin tambaya taji batun barin gidan nan, babu inda zaki."Baba Gaje ta ce, "Ina kuwa zata, aure sai dai ki ga wasu nayi. Yanzun ma ai kin yi bandaro tunda duk sa'o'inta sun yi aure.Da za su yi sallama ne Dija ta sake jadda matacewa ta tuhumi Babana. Bba gaje ta ce,"Ki daina damun kanki, "k'arya ce kawai,amma zan tuhumi 'yan uwansa tynda in ya6oye min ba zaya 6oye ma 'yan uwansa ba. ai sune za su bada ta."Suka yi ban kwana ta tafi. Cikin zuciya na ce,"Allah ya shirye ku in madu shiryuwa ne,in kuma ba masu shiryuwa ba ne Allah kai kasan yadda za ka yi dasu.Duk in da Baba Gaje tasan zata samu lbrn auren nawa ta bincika amma bata samu komai ba, daga k'arshe dai ta tattara ta watsar da batun
9.Cikin satinne sai ga Ado, na sha mamakin ganin yanda Ado ya yi kyau tamkar shima dan birni ne. Har gidanmu yazo yagaida Baba, kuma ya saka wani yaro ya kira ni na fito muka gaisa, na ce,"Ya birni ka gankakuwa Ado?"Ya yi dry tare da kallon jikinsa.""Kemaai kin kusa zama 'yar birni."Da sauri na ce, In ji wa?"ya sassauta murya."Kina nufin za ki 6oye min ne? Ai na samu lbrn auranki.""A can birnin mijin yake." Nayi saurin tambayar shi.Ya yi 'yar dariya tare da cewa,"Gaskiya kina da sa'a Jidda, duk kauyan nan ke ce ki ka fara samun miji daga birni."Cikin dariya na ce,"Ni fa dan san ko a ina ne mijin yake ba, ban san ma irin shi ba."Ado ya ce,"Za ki san shi, ke dai ki yi ta addu'a Allah zaya dai-daita miki lamuranki."Na ce,"To na gode, ai lamura ma sun somagyaruwa."Baba Gaje ta fito."Kai me ka ke yi gurinta?Ban raba ku ba?"Ya ce,"Na zo ne ai mu gaisa."Tasa bayan hannu ta mauje ni tare fa ce min"Karya kawai, wuce ciki."Ado ya dube ta cikin rashin jin dadin abinda ta yi min."Bana da kin daina nuna hassadar ki da k'iyayyar wannan yarinyar ba ki san irin baiwar da Allah ya yi mata ba, k'ila nan gaba inuwarta zaku sha ke da 'ya'yanki.Nan ko ta shiga jaraba tare da tsine-tsine. Ado ya ce,"Ki dai yi tunani Baba,in babu duniya dai akwai lahira." Ado dai ya manna mata hauka ya tafi.Sai zuma bala'i take duk makota sun taru wai kan me Ado zai ce mata ita da 'ya'yanta za su sha inuwar Kuluwa?"Wacece Kuluwa?"Ko uwarta ma wacece har ta mutu bate ita.Ta gaji ta wuce cikin gidan, nan ko ta shiga jibgata wai ko'ina naje sai in dinga zaginta, sai da ta barni kwance sannan ta ce in zo indebomata ruwa."¤¤¤¤¤¤¤¤Su M.B ana can soyayya ba dama ne, duk wani tattali suna yiwa juna.Tuni kuma sun soma zuwa Makaranta.Sep 4Aisha Ummu Shureim Sa'eedMsmart BG Zee Town10.Basma tana yin duk wani abu da ta san zata faranta masa rai, haka shima. Ta fannin abinci ne yake da matsala, in yana gida ya kanyi irin wanda ya iya suci, in kuwa ba shi da lkc dama suna da masu aiki.Rayuwarsu abin sha'awa, Husna ma ta kiraHjyrta ta shaida mata suna tare da Brotherdin su a America, kuma tuni ta soma zuwa Mkrnt. Nan take Hjyr ta shiga zaginta tare da cewabata da kishin uwa ta nuna maya cewa Bello yafi ta kenan, duk da tozarcin da ya yimata. To ta gaggauta baro shi ta dawo ta yafe ta itama kamar yanda suka yafe Basma.Husna bata katse mahaifiyarta ba sai da takai aya sannan ta ce,"Hjy magana ta gaskiya Brother ba shi da laifi, duk da abubuwan da ku ka mishi bai sa ya ta6a nuna min ba, haka nan bai ta6a min hirar abinda ya faru ba. Hsali ma shi ne ya somamin albishirin cewa yasan va za a tsare ki ba, kuma hakan e ta faru."Hjy ta ce,"Na gode kin dai nuna min cewa Bello ya fini."Ta ce, "Ba haka ba ne Hjy. Dady ba zaya yarda in dawo gurinki ba haka nan zama gidanmu babu dadi tunda ni kadai ce in Dady ya fita.,Sannan kuma Bilal Hjyr sa ta ce ba zaya aur ni ba, saboda abin da kika yi.Ni kuma gaskiya zaman gurin ya ishe ni, ina jin dadi a anan gani ga Anty Basma.,Tsaki Hjyr taja sannan ta ce, "TO shikenan ki zauna ke da makiyan nawa, tundasun fini mahaifiyarku." Ta kashe wayarta."Kuka Husna ta saka, nan Basma ta shiga lallashinta tare da cewa, "Wata rana zata gane, Kuma zata yarda cewa mijina mai gaskiya ne.
[29/09 9:28 am] Inna👬👫: Idan rana tafito
Chapter 2 · 0% Book details