← Book details Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 21

Sashe 5

Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hmm aunty ay kinsan mutane ne ynzu kansu kawai suka sani basa tunanin wani,indai mutum yasan yana da abin duniya to taka wanda bashi dashi ba komai bane.dan dai tace yayi attempting dn tsayawa,ta taho alamar zai bata hakuri yasan ya aikata ba daidai ba, Amma Wlh badan haka ba idan da zan yi ido hudu dashi sai na masa fiye da abinda ya mata.su masu kudi gani suke talaka bashi da gata shi ba kowa bane"kawu habibu ya fada yana cika yana batsewa.

Murmushi aysha tayi tana tashi ta ajiye plate dn data ci abinci ta shiga daki domin dakko jakar islamiyarta.

"Yanzu dai ay shikenan tunda wacce aka yiwa abin ita ta hakura,tunda kai bakada hakuri komai aka maka sai ka dau fansa,fisabilillahi rayuwa ta iyu a haka habibu,komai fa na duniya dan hakuri ne,duka ma duniyar nawa take"abba da fitowarsa kenan daga bayi ya fada yana ajiye butar hannunsa.

"Wannan haka yake Allah dai yasa mufi karfin zukatanmu" cewar umma.

"Amin"abba da kawu habibu suka fada a tare.

Aysha ta fito ta musu sallama domin tafiya islamiya,sakon gaisuwa ta bada a fadawa kakaninta.fita tayi ta barsu suna dan tattaunawa,ita kuma ta kama hanyar makaranta.

A Bangaren kabeer da zuky kwa bai zame ko ina ba sai a kofar gdnsu zuly,tun da suka baro Inda ya fallatsawa yarinyar kwata bai kuma cewa uffan ba.itama zuly ganin babu fuska yasa ta kama bakinta,sai dai lokaci zuwa lokaci takan juya ta kalleshi.tunda suka taho babu abinda yake sai cika baki da iska yana hurar da ita,sai kuma ya sauke ajiya zuciya.yana tsayar da motar ya koma ya jingina da kujera,Zuly ce ta juyo gaba daya ta kalleshi Kafin ta fara mgn.

"Haba kb wai dn allah mesa ka damu kanka da abinda ya faru,kwata ce fa kawai ka watsa mata shima bawai da gangan ba,to amma kuma kazo kana damun kanka kamar wani wanda ya kade mutum ya mutu,kawai ka manta da ita ka dawo Normal ,yarinyar da ganinta kasan yar gdn talak.....

"Stop it! Dalla malama fitar min a mota"ya mata rai bace yana hayayyako mata.

Zuly data saki baki tana zuba kamar lalataccen fanfo,jin ya doko mata wata tsawa ya sanya ta tsorata.saurin bude kofar ta fita a hanzarce,ta rufo masa kofar jiki na rawa dn tasan halin kb ba mutuncci yanzu sai ya shuka mata tsiya.
Ganin ta bar masa jakarta ya bude kofar ya iyo cilli da ita,rufe kofar yayi,reverse yayi ya figi motar a 360.

Zuly da har ta kama karamat kofar get din gdnsu,taji faduwar wani abu dimm,dake ko karan bude kofar da kb dn yayi bataji ba sbd tana rufe masa kofar ta juya tayi tafiyarta,dn tasa ba karamin aikinsa bane ya bula mata kasa ya kara gaba abinsa.ganin jakarta ce ya jefo mai tarin buks da handout wadanda take siya take ajiyewa dan ba wanda take karantawa daga ciki kawai tana siyane dn ta yiwa iyayenta basaja.dan bata shiga ko shiga class iyakarta bn samari,suyi ta zuwa Shopping da zuwa wajejen shakatawa daga karshe a dawo da ita gida.

Yanzu ma daga scul suke kb yaje ya dakkota dan dukunsu B.U.K suke karatu sai dai ba department daya suke ba. Yatsina fuska tayi tare da tabe bakinta , tace

" mayen mata kawai kai dai ba damar kaga mace sai
kace kana sonta ,banda shegen son mata ni banga abin so a wannan kwailar yarinyar ba" ta fada tana jan tsaki, juyawa tayi taje ta dakko Jakarta ta shigewarta gida.

Zulaihat wacce ake kira zuly yar gdn alhaji abdulrazzaq ,mahaifinta yana da kudi sosai sai dai mutane ne wanda sukasan abinda sukeyi .domin kudin da suke dashi bai sanya sun kasa baiwa yayansu tarbiya ba,saidai zuly bata jin mgn dan cewa tayi indai ba kasar waje babanta zai kaita ba bazatayi karatu ba.shi kuma yace dole sai dai tayi karatu a nigeria,dn bazai kai mace karatu waje ba,ita kuma dk yayunta mazane kuma dk cikinsu ba wanda yayi karatu a nigeria,shisa take gani babanta yayi son kai,dn haka bayan ya samo mata admisson a B.U.K
aikwa take yaudarar iyayen dan ba karatun take ba ,su kuma basu da masaniya akan abinda take aikatawa dan har bn maza takeyi ,tana iskancinta ba tare da sun sani ba.(Allah ka shirya mana zuri, a ka mana katangar karfe da zina ameen).

Kabeer tunda ya bar kofar gdnsu zuly yake so ya danganta da gdnsu,shi dai yanaso ya gskata cewar wannan yarinyar ba mutum bace in ba haka ba ya za,ayi tunda ya hadu da ita ya rasa Sukuni a zuciyarsa, shi da bai fiya sanya damuwar kowa ba a zuciyarsa,amma gashi ynzu ya sanya damuwar yarinyar da bai ma santa ba to idan dai ba mutanen boyen bane suka ajiye masa damuwar a ransa ba mesa hkn zai dameshi?"gashi kwa da ranar nan tabb babu tantama ma aljanu ne"wani bangare na zuciyarsa ya fada,daram damm gabansa ya yanke ya fadi,wani gumi ya tsatstsafo masa,tissue ya cira ya goge gumin."kodai tausayinta ne ya kamaka ganin ka mata rashin kyautawa amma kuma ta hakura ba tare da ta tsaya bama bare tace uffan"wani sashen na zuciyarsa ya kara fada.wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke,dan yadda da batun da zuciyarsa ta fada masa yanzu.

A dai dai wani tangamemen gida tsaya,tare da sakin wani uban horn,mai gadin ne ya dan leko domin ganin mai horn din ganin motar gdn yasa yayi saurin tura get dn ya bude.shigowa yayi ya samu wurin da aka tanada dn ajiye motoci yayi parking.kafin ya bude kofar ya fito yana maida kofar ya rufe,mai gadin ne ya karaso yana masa sannu da zuwa,hannu ya daga masa ba tare da yayi mgn ba.hanyar part dn sa ya nufa,Ko me ya tuna kuma ya juya ya nufi sashen hajiya lubabatu,kofar falon ya tura shigowa yayi ba kowa a falon sai tv dake ta faman aiki,zubewa yayi akan kujera ya dan kwantar da bayansa ajikin kijerar sanyin ac na ratsashi.zamansa keda wuya sai ga hajiyar tana sakkowa daga stairs,sanye take cikin lace da aka yiwa dinkin buba tayi daurin dankwali ture kaga tsiya,hannunta rike da waya.har ta sakko bata lura dashi ba sai data zo cikin falon.

"Autana yaushe ka shigo gdn bn sani ba?"ta fada tana zama a kusa dashi .

"Yanzu"ya fada a shagwabe yana maida kansa kan cinyarta ya kwantar.

"Ya na ganka haka ko karatun ne ya maida kai haka,ko kuma yunwa kake ji"ta fada tana shafa kansa.

"babu komai kawai na taho daga scul shine a wani layi na fasawa wata kwata shine abin ke damuna"ya fada Yana marairaicewa.

"To banda abinka meye na damuwar baka bata kudi taje car wash a wanke mata motar,ay indai akwai kudi to babu damuwa dn kudi sukanyi komai,idan nace komai ina nufin komai"cewar hajiya tana kallon fuskar kb.

"Bazaki gane ba hajiya yarinyar fa ba,a mota take ba"

"A me take"tayi saurin katseshi.

"A kafa"

"Kafa fa kace?to meye dn ka watsawa mai tafiyar kafa kwata,ai daman dole mai tafiya a kafa ya rakabe mai mota ya wuce indai ba hasada ba,ko kuma anaso a samu na siyen garin kwaki shisa ake tarar mai mota ya fatsa tunda ai shi dai mai akwai bazai bada hakuri ba saidai ya bada abin duniya wato kudiiii"

"Hajiya itafa wannan yar yarinya ce karama kuma ni ne da laifin ba ita ba tayi kokarin kauce mn amma na watsa mata kuma da kike maganar abin duniya wlh yarinyar ko tsayawa batayi ba tayi tafiyarta"

"Bata tsaya ba"Ta tambaya fuskarta dauke da mamaki.

"Eh"ya bata amsa a takaice.

Amma autana anya kwa mutum ce,a wannan zamanin da mutane ke cikin babu,wasu kamar su kwata ace an watsawa mutum kwata ya tafi ba tare data maka tsiwa ba ko tace sai ka bata kudin sabulu?
Saurin tashi zaune yayi daga kwanciyar da yayi,ya kama hannayen hajiya duka biyu ya rike

"Wayyo hajiya nima nayi wannan tunanin ,wayyo Allah nah kar taje ta shiga jikina ta cutar dani"ya fada tsoro fal fuskarsa.

"Kai ba lallai bane ba aljana ce kasan talaka ma akwai masu wadatar zuci watakil tana da hakuri ne,shisa ta tafi ko kuma taga mai mota ba Sa,an fadanta bane kar aje karamar mgn ta zama babba"hajiya ta Fada dn ta kwantar masa da hankali amma a ranta tayi mamaki kwarai dn ita dk tunaninta talaka babu abinda yake bukata a Hannnun wanda ke da wadata Sama da kudi.

"Haba yauwa hr naji dadi,me za,ayi da mutanen boye"ya fada yana jin karfin gwiwa.ganin hajiyar ta zare ido ya gane yayi baranbarama.
"A,ah ba me za,ayi daku ba nake nufi"ya canja maganar ,dn kar aljanun nan da ake ciwa na gida su jishi ,dariya suka sanya dukansu,suna mikewa suka tafi domin baiwa cikin haqqinsa.dan lakacin sun san Yaya abdullahi ya dawo da kuma daddy.
🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Story & written by

MAMAN AFRAH

*Ku* yi *hkr* *na* *jina* *shiru* k *wana* *biyu* *sbd* *wani* *dalili* *ngd*😍

Page 13 &14

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHM

" Nace aikin me ta maka da zaka biyota da kaya har gida"abba ya fada yana bin kb da kallo.

"Wlh abba babu aikin dana masa dan Allah ka yarda dani"aysha ta fada wasu hawaye na bin kumatunta.

"Bake aka tambaya ba rufe mana baki mai arahar hawaye"umma tace tana harararta.

"Da kai fa ake ka tsaya kana karewa Mutane kallo"cewar umma tana aikawa kb wata Uwar harara dn bataso ko kadan yaga fuska a Wurinta sbd gaba kar yayi gigin kara tare mata yarinya a Hanya.

"ba dan wannan Babyn da kuka ajiye ba ku kun isa kpu ganni ma,bare har ku samu damar fada min magana.ya fadi hakan a zuciyarsa ,a zahiri kuma sai yace"Wlh abba babu wani aiki data min kaji ma da kanta furta haka da bakinta"kb yace yana Maida fuskarsa ta salahan Mutane dan su kara yarda dashi.

"To Meye amfanin bayar da Kaya,tunda bata Maka wani aiki ba?ko ladan aikin ne ya fara zuwa a gaba kake so ta maka aikin ?"umma tace tana kama tsantsa tare da karkata kai.

"Nifa kamar yadda na fada cewa babu aikin data mini,kuma haka ta fada da bakinta bata mini aiki ba.kuma babu wani aiki da zata min anan gaba kawai zan bata ne dan Kyautatawa kum..........
Chapter 5 · 0% Book details