← Book details Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 21

Sashe 16

Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kb ne zaune a kan tabarma kusa da Daddy su duka sun rasa me yake musu dadi gaba daya suna so su gano dalilin kin maida hankali wajen duba Abba musamman Daddy ma da yake ganin rashin kyautawarsa amma kuma ya kasa tunano komai daya fara kokarin tunawa sai ya ji ya manta komai. Suna nan zaune suna karbar gaisuwa su da su kawu habibu, a lokacin kuma Ummulkhairi tana ta fan kiran wayar Kb amma bata shiga. Kakan Ayshan ne da aka kira aka sanar dashi saukar Aysha yazo ya zauna kusa da Daddy yake sanar dashi haihuwar Aysha. Sosai yayi addu, a da fatan alkahiri, Kb kwa sai wwni wani dadi yake ji a cikin ransa yayi y'a. Ana cikin haka Hajia ta dokowa Daddy waya akan ya dawo gida haka ya amsa mata ba dan yaso ba, har sun musu sallama zasu tafi sai kawu Habibu yace su shiga daga zaure a karbo yar su mata addu, a haka kwa akayi kawu Habibu ya kawo yarinyar Daddy ya karbeta ya mata addu, a ya mik'awa Kb hannunsa har karkarwa yake ya karbeta yarinya kyakkyawa sak Aysha kiran salla ya mata bayan sun ganta suka baiwa kawu Habibu ita ya maidata cikin gida.

Ummulkhairi da ta ga wayar Kb taki shiga hakura tayi ta shiga ta yiwa Ummar Aysha gaisuwa ta shaida mata Hajia ba lafiya shi yasa bata zo ba, itakwa Umma cewa tayi ba komai Allah bata lafiya. Daddy motarsa ya shiga dirabansa ya jashi suka tafi a inda Kb ya kira Ummulkhairi a waya ta fito su ma suka shiga mota suka kama hanyar gida, dan yanzu Daddy ba,a hayyacinsa yake ba bare ya tambayi ba, asin zaman Ummulkhairin a gidan Kb.

Daddy na komawa gida yake sanar da Hajia haihuwar Aysha, ranta ta ji ya mugun baci shikenan ta hada zuri, a da talakawa, banza tayi masa da ya gaji ya fita ya bata waje daman sashenta ya je domin mata albishir din samun jika.

Rigima Ummulkhairi ta ringa yiwa Hajia wai ta ga Kb yana wani rawar kafa, akan haihuwar Aysha karfa asirin ya karye ya fasa aurenta aikwa Hajia tace aure babu fashi nan da sati biyu za, a yi komai a gama.murna gun Ummulkhairi ba, a magana..

Kb ya koma ya yiwa ya radawa yarsa suna (FAUZIYYA) a inda ya baiwa Aysha kudade masu yawa domin ko za, a buk'aci wani abu, duk da tana cikin damuwa sai taji sanyi a ranta ganin Kb yana zuwa yana kuma basu kulawa a tunaninta komai ya gyarune bata san bisa umarnin Ummulkhairi yake yi ba dan gudun maganar mutane yasa suka shirya hakan tapi ta da Hajia hatta kayan Baby babu abinda ba, a kai ba. Sai dai kakar yar batazo ta ganta ba suma kwa basu damu ba.

BAYAN WATA BIYU

Lokacin an yiwa Abba arba, in itama Aysha ta zubar da wanka har ma an shafi kwanaki, a mak'otansu aka sama mata wacce zata ke dan mata raino, suka tattara suka koma gidansu. Komowar da Aysha tayi gidanta ya tayar mata da hankali sosai domin kuwa tazo ta tara da Ummulkhairi a matsayin kishiyarta wanda kwata kwata bata san da hakan ba part guda aka gyarawa Ummulkhairi aka jera mata kaya na gani na fada. Tunda Aysha ta dawo gidan wannan Kb bai kulata daga ita har yar tata domin kuwa su Hajia sun kara tashi tsaye akan lamuran Kb sun kara shiga tsakaninsa sosai da Aysha da kuma yarsa FAUZIYYA. Tana ji tana gani komai ya gagareta a gidan sai dai ta ringa wasa da diyarta dan take dauke mata kewa.Yanzu sun hade kai da jamila nan take zuwa suyi ta yiwa Aysha habaice habaice dan ita jamila ko cikin ma babu dan tace ba yanzu ta shirya haihuwa ba, sai ta gama more rayuwarta domin bataso ta tsufa da wuri. Shi kuma Ya Abdullahi gashi da son y'ay'a amma babu yadda zaiyi saboda Hajia ta tsayawa Jamilan. Ko wucewa Ayshan tayi sai su kwashe da dariya, amma ita ko a jikinta bata kawosi aka, saboda komai ma mutum zaiyi yanayi ne dan miji to ita kuma mijin ba ta ita yake ba.

Haka rayuwa tayi ta tafiya kullum da irin abinda Ummulkhairi zata bullo dashi wanda zai batawa Aysha rai, sannan duk wani abu da tasan zai k'untatawa zuciyar Aysha shi takeyi. Aysha kwa bata kulata iyakarta tayi ta danne zuciyarya tana yin hakuri da kyma juriya, sannan kullum bata da aiki sai karatun Alqur, ani mai girma da kuma nafilfili akan Allah ya zama gatanta ga kuma nasiha da Ummanta ke mata domin zuwa yanzu Umma ta gama gano Aysha na cikin matsala. Musamman ma da aka mata kishiya ya yin da take gidansu dan makokin mahaifinta da kuma wankan jego amma hakan baisa an jinkirta auran ba, koma baza, a jinkirta ba ai a sanar da ita.

Yanzu ta kai har honeymoon Kb ya dauki Ummulkhairi suka tafi tsawon watanni uku ba tare da Aysha tasan ko da sunan kasar da suka tafi ba bare tasan Lokacin dawowarsu sai dai komai akwai a store babu abinda suka nema suka rasa sai walwala kulawa da kuma farinciki irin wanda kowacce mace ke fatan samu a gidan mijinta. Yanzu Fauzy ta warware sosai kuma kullum kyanta sai kara bayyana yake, gata da lafiya yarinyar kana ganinta kasa Aysha ce ta haifeta. A haka har su Kb suka dawo daga inda suka tafi honeymoon. Wanda suka kara dawowa da sabon salo sosai dan rayuwar turawa kawai suke a gidan, dan yanzu zaka ga Ummulkhairi da mini sket da have best tana yawa suna rungume rungume da kisa kisai a filin gida ba ruwansu da kowa. Abu daya ne ma Aysha take jin tsoronsa shine kar su bata yar mutane hannatu yarinyar dake mata renon Fauzy. Wani lokacin haka zaki ga Kb ya goyo Ummulkhairi a bayansa amma haka Aysha zata wucesu kamar ma bata gansu ba. Wannan abin shi yake baiwa Ummulkhairi haushi domin so take ta yiwa Aysha abinda zata bar gidan domin Kb za zamto nata ita kadai, duk yanzun ma menene igiyace kawai a tsakaninsu amma bayan haka babu wani abi da yake wakana sai dai abinda hausawa ke kira da zaman HAK'URI.

BAYAN SHEKARA BIYU

Har zuwa wannan lokacin bata sauya zani ba, din kuwa babu abinda ya canja tsakanin Aysha da Kb sai shi da Ummulkhairi dake cin karensu babu babbaka. Amma kuma wani abu da Ummulkhairi bata sani ba, shi ne har yanzu Kb yana nan da kule kulen yan matansa, ita kawai Aysha ce a gabanta shi yasa bata damu da tasan komai ba tunda tana ganin ta shiga tsakaninshi da Aysha ai babu ita babu kishi da wata mace🙄

wata ranar litinin Kb yace wa Ummulkhairi zai je ta, aziyya gidansu wani abokin kasuwancinsa, ta kafe akan zata bishi amma kuma yaki yace ta zauna yanzu zaije yabdawo ba dadewa zaiyi ba. Haka ya shirya shiri irin wanda Ummulkhairi bata yarda da gidan mutuwa zaije ba, yana fita itama ta shiga motarta daya sai mata ta mara masa baya. Kb da ya gama waya da Zuly zai je ya dauketa a gidansu bai san Ummulkhairi na biye dashi ba, domin ta iya takunta daga nesa take bin motat tashi yadda bazai gane ba tunda ya san motar tata idan ta bishi a kusa kusa zaiyi saurin ganota. Tana kallo ya faka motar wata ta fito daga wani gida ,abin da ya batawa Ummulkhairi rai bai wuce yadda Kb ya fito ya budewa budurwar kofa ba, tana shiga ya maida ya rufe ua koma ya shiga ta mazaunin direba. A nan take Ummulkhairi ta hau dokin zuciya, ta kuma dau kudirin kawo karshen alak'arsu a yau ba sai gobe ba. Ganin ba,a ja motar ba zuciyarta keta mata sak'e sak'en wani abun sukeyi a cikin motar wanda ya danganci soyayya, jin gaba d'aya ta fita hayyacinta yasa ta kunna motarta ta karasa wurinsu. A dai dai motar Kb ta faka motar tata ta bude ta fito afujajan tana fitowa ta bubbuga jikin motar da mugun karfi wanda hakan yasa Kb da Zuly saurin dagowa suka maida kallonsu wurin wacce ta buga kofar.

"To karuwa! an rasa maahinshini shine aka b'uge da bin mazan mutane"Ummulkhairi tace tana kama k'ugu yayin da ta rike marfin motar da d'aya hannun.

"Karuwa! Ni kike kira karuwa? "Zuly ta tambaya tana nuna kanta da hannunta.

"Eh! An fad'a din in ba karuwa ba wane suna kike jiran na kiraki dashi? "

D'aga hannu Zuly tayi ta wanke Ummulkhairi da wani gigitaccen mari wanda yasa Ummulkhairi ta ga wulgawar wasu taurari. Itama hannu ta d'aga zata rama ta ji an rike mata hannu kallon Kb tayi da rinannun idanunta da suka sauya kala tsabar marin da tasha da kuma bacin rai. Haushi yasa ta warce hannunta daga rikon da ya mata, batayi wata wata ba ta daukeshi da mari😨😨😨 domin gani tayi ma ai ya raina mata hankali a mareta bai rama mata ba kuma ya hanata ramawa 🙃🙊 tabb lallai Aysha tana k'ok'ari tana kuma hak'uri ji yanzu dan abin da ta gani yanda ya gigita mata tunani inaga Aysha da tun kafin Ummulkhairi ta zama matar Kb ta tare a gidanta take cusguna mata🥲ashe haka take jin babu dad'i kai kaishi masifane.

"Ke kina da hankali kwa?? Ni zaki mara? "Kb ya fad'a yana koma mata kamar wani zaki. Bata ankara ba ta ji ya dauketa da wani gigitaccen mari wanda yafi na Zuly zafi da rad'ad'i a kumatu. Nan take maganar Boka ta dawo mata.

"Karki kuskura ko da wasa kice zaki kai masa hannu ma, ana ki dukeshi, komin kankantar duka matsawar kikayi haka to tabbas aiki zai lalace a take komai zai wargaje babu bata lokaci zai dawo hayyacinsa sannan babu wani aure da zai sake wanzuwa tsakaninku! "

Saurin dawowa hayyacinta tayi daga tunanin abinda boka ya fad'a mata.

"Ya Kb ni matarka Ummulkhairi ka mara🥲" tace hawaye na zuba a idonta.

"Wace matar tawa to indai nine mijinki na sakeki saki uku!!!"
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

*_______________________________________*

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Short story
Chapter 16 · 0% Book details