← Book details Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 21

Sashe 10

Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Barka da sakkowa daddy"kb yace yana murmushi.

"barka dai auta ko kuma auta ya girma yanzu"daddy yace da zolaya yana dariya irin tasu ta manya.

"ay daddy yanzu ya girma ba shine autan ba"ya abdullahi shima ya fada yana dariyar

"daddy ay gaba da baya nine auta"kb ya fada yana zumburo baki.gaba daya falon dariya aka saka banda jamila da tayi karamin tsaki da ba wanda ya jita sai hajia,itakwa aysha murmushi tayi kanta har lokacin a sunkuye.

"a toh shikenan mun ji kai ne auta"cewar daddy yana samun wuri ya zauna.

Bayan kb ya gaishe da daddy aysha ma mikewa tayi taje har gaban daddy ta tsugunna har kasa ta gaishe dashi cikin mutuntawa da kuma girmamawa.amsa mata yayi yana mai jin dadin tarbiyar yarinyar yana kuma godewa Allah daya bashi suruka kamar aysha lallai har gobe yana alfahri da ita a matsayin matar dansa kabeer.komawa tayi kasa wurin zamanta ta zauna ,a yayin da mutum uku suka bita da harara,hajia ummulkhairi,da kuma facalarta jamila suna jin haushi da yadda take.ita dama jamila ta gaishe da daddy tun sanda sukazo sai dai tana daga kan kujerar da take zaune ta gaishe dashi,

A alhamdulillah nagode Allah daya bamu rai da lpia ,ina kuma kara gode masa daya bani iko da dama na taraku domin mu tattauna magana wacce nake fata ta kawo gyara akan gyaran da nakeso ,ta kuma zama sanadin gyaruwar komai kamar yadda nake son hakan ya kasance.

gyaran murya yayi kafin yaci gaba da bayani.

wato shi ubangiji shike iko da kowa da kuma komai,shike bayarwa kuma shike hanawa.yanayin yadda yaso a lokacin daya so,duk wanda kaga Allah ya bashi to shi yaga dama ya bashi bawai dubara ko wayon mutum din ne yasa ya samu.kuma kowa dana ne yadda kowace uwa ta dauki ciki tsawon wata tara ta kuma shayar tsawon watanni tara kamar yadda yazo a alqur,ani mai girma cewa (ciki da kuma shayarwa watanni talatinne)dan haka kowace uwa haka tasha wahar haifar danta ta kuma shayar dashi da kuma wahalta masa a rayuwa.kuma babu wata uwa da bata son danta kowace uwa ka gani akwai soyayyar danta dankare a zuciyarta,dan haka kowa da kaddararsa mai kyau ko marar kyawu.sannan kowane mutum an rubuta masa arzikinsa da ajalinsa da aikinsa sannan da makomarsa tun kan yazo duniya duk wanda ka gani da arziki Allah ne yayi nufin ya bashi,haka kuma duk wanda ka gani a talauci haka shima Allah yakeso ya ganshi dan haka wulakanta wanda kafi da wani abu ba naka bane wala ilimi daukaka,mulki ,ko dukiya .dan kaima duk wannan abubuwan daka mallaka anan duniya zaka barsu da zarar mala,ikan mutuwa ya ziyarceka shikenan daga kai sai farin llikkafaninka wanda dashi ake kai kowa kabari mai kudi ko kuma talaka.kai ko ba,aje ga mutuwa ba wata rana zaka wayi gari ka rasa koma menene kake takamar ka mallakeshi.

Domin rayuwar nan ba tabbas ba gareta ,yanzu zaka ga mutum ana jimawa ace maka ya mutu🥲mutum ba komai bane wlh shi yake daukan kansa wani daga an zare maka rai shikenan ka zama gawa kuma a lokacin za,ayi jana,izaarka a kai ka makabarta a saka a rami a rufe shikenan daga kai sai halinka.dan haka nake jan hankalinku nake kuma ankarar daku a matsayinku na iyalaina daku bi duniya a sannu domin bata da tabbbas ko kankani! mu guji duniya Allah zai so mu ,sannan mu guji abin hannun mutane suma mutane zasu so mu.shiru yayi yana bin fuskokinsu da kallo yana kuma karantar yanayinsu gaba daya.duk sunyi shiru da alama kuma zancen na shigarsu domin gaba daya sun yi sanyi.
Abu na gaba da nakeso na yi magana akansa shine akan zamantakewar auratayya ,ku mata kuyi biyayya ga mazanku ,kuma mazan kuyi adalci a zamantakewarku.sannan hajia inaso ki sani cewa aysha surukarki ce kuma yarinyace mai biyayya,sannan kuma dama Allah ya rubuta ta a matsayin matar kabeer tun kan tazo duniya.dan haka ki yiwa Allah ina rokonki ki da ki karbeta a matsayin suruka.sannan inaso ki sani ba komai da mutum keso ko kuma yake son kasancewarsa ba yake samu sai abinda Allah ya kaddara.yau kusan watanni kenan da aurensu amma ko sau daya baki taba sanyata a idonki ba karfa ki manta itama 'ya ce kuma uwa da ubame suka haifeta kuma suma suna sonta kamar yadda muke son namu yayan,dan haka ina rokonki daki sakar mata fuska ki kuma karbeta a matsayin suruka domin rayuwa bakasan mai gaba zata haifar ba.sannan baka san mai maka rana ba sai Allah."yana kaiwa nan ya koma ya jingina da jikin kujerar

Hajia ce ta fara magana"insha Allahu za,a gyara kamar yadda ka bukata kuma naji dadin wannan nasiha daka mana. Allah ja da kwana"ta fada a zahiri a ranta kuma tana raya tabbas ya gama zubar mata da girma a idon aysha,kuma ita bazata taba karbarta a matsayin suruka ba.

"insha Allah daddy zaka samemu masu aiki da abinda ka fada"cewar ya abdullahi a ladabce.

"daddy tabbas nasiharka ta taba min zuciya lallai kafin a samu mahaifin da zai zaunar da iyalansa yana fadakar dasu domin gyara rayuwarsu,domin su dace duniya da lahira za,a tona,in Allah ya yarda zaka samemu masu aiki da maganarka.Kabeer ya fada yana kallon daddy.

"daddy munji nasiharka kuma muna godiya sannan zaka samemu masu kiyayewa"cewar ummulkhairi.

"daddy mun gode kwarai da nasiharka garemu"jamila tace a takaice.falon ne yayi tsit kamar ba kowa.

"Yata ke bazaki ce komai ba"daddy ya fada yana mai kallon aysha da kanta ke duke har loakcin.dago kanta tayi tayi sannan ta fata bayani.

"daddy hakika ina alfahri da kai a matsayin uba kuma suruki a wurina ,sannan kuma wannan nasiha da kuma fadakarwa sunyi tasiri sosai a zuciyata,babu abinda zance sai dai ina maka ftn alkairi a dukkan lamuran rayuwarka,ina kuma addu,a ubangiji ya maka jagoranci ya baka rai da lpia yasa kayi kyakkyawan karshe ya kuma maka sakamako da gidan aljanna"tana kaiwa nan tayi shiru.daddy kwa tunda ta fata magana yayi tsai yana kallonta yana kuma yaba kaifin basira da iya magana da kyawawan lafuzza da ayshan keyi wanda gaba daya cikinsu babu wani wanda yayi magana makamanciyar tata.har hajiyar ma.ita kuma hajia da jamila dama ummulkairi sai binta suke da harara a inda ya abdullahi da kb suke ta jijjiga kai suna murmushi alamar ayshan ta burgesu.

"ah alal hakika nayi matukar farinciki da abubuwan da kuka fada Allah mana jagoranci gabaki daya"daddy yace tare da rufe taro da addu,a dan dama yayi hakane sbd aysha da bata taba koda zuwa gidan surukan nata ba ,da kuma hajia dake nuna batasonta dan kasancewarta ba yar kowa ba ma,ana basu da abin duniya.daga haka kowa ya musu sallama ya fito aka bar daddy da hajia suna tattaunawa.ummulkairi part din hajia ta wuce ranta bace ganin kb da aysha sun jera suna ta magana suna murmushi ,hakama ya abdullahi da jamila data wani manne masa kamar zata koma cikinsa wai ita a dole zata nunawa aysha ita wayayyiya ce.haka sukayi sallama kowa ya shiga motarsa mai gadi ya bude musu get suka fice kowa ya kama hanyar gidansa.

A haka rayuwa taci gaba da kasancewa cikin farinciki da kwanciyar hankali a tsakanin kb da aysha a haka har suka shafa watanni shida da aure.a lokacin ne kuma aysha ta fara rashin lpia ana zuwa asibiti gwajin farko aka gano tana dauke da cikin wata guda sosai kb yayi murna da samun cikin,sai dai cikin yazo da laulayi sosai wanda haka yasa kulawar da aysha ke bawa kb ta ragu domin yawancin kullum bata da lpia wannan ne yasa kb ya koma soyayya da yan matansa dumu dumu wanda daman ya dai ragene amma koda sukayi aure da ayshan bai fasa ba yana boye matane kawai.

soyayyar da yakeyi da yanmatansa tasa ya daina baiwa aysha kulawa ,idan ya dawo daga kasuwa yayi wanka yayi kwalliyarsa ya fice sai kuma kwanciya zai dawo dan abincinta ma bai fiye ciba ya gwammace idan ya fita ya dauki budurwarsa suje su ci abinci mai rai da lpia mai tsada.wannan halayen da kb ya fara fito dasu sune suka sanya aysha cikin tsananin damuwa domin ya daina kulata ta kowace fuska,idan ya dawo ta masa sannu da zuwa sai kawai ya daga mata hannu ya fice ya barta a wurin.in ta tambayeshi ko ta masa laifine sai yace shi ba wani abu data masa kawai ya gajine ta barshi ya huta,kai gaba daya rayuwar ta sauya har dai aysha ta fara tunanin ko dai cikinne bayaso,dan yanzu ko mu,amalar aure sai ya dau lokaci baiyi da ita ba.amma a haka ko zai kai karfe nawa bai dawo ba sai ta jira dawowarsa kuma koda ya dawo ba wani kulata yake ba,wani lokacin ma ita ke kwanciya a jikinsa domin suna hawa gado yake juya mata baya sai dai ita ta rungumoshi saboda sosai cikin ke sanyata jin shawa,a amma haka zaiyi biris da ita kamar bai jita ba haka zata hakura ta kwanta a jikinsa wai ko ta danji sanyi sanyi da saukin abinda take ji.

Haka aysha ta kasance cikin damuwa kullum da abinda ke damunta kai hatta abinci sai daya fara fita ranta tayi baki ta rame ga laulayi ga damuwa duk sai duniyar ta mata kunci,ko gidansu taje mahaifiyarta tayi ta tambayarta damuwarta amma tace babu komai domin bataso ta sanyata a damuwa ita kuma mahaifiyarta sai take tunanin ko laulayin cikinne ke sakata damuwa sai tayi ta mata nasiha .to indai kaga aysha ta saki jiki tana hira to sai dai in gida taje dan yanzu kb ko loacin zama da ita bai dashi bare kuma har yayi hira da ita.
Chapter 10 · 0% Book details