Sashe 12
Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummulkhairi da yunwa ta hana ta sakat ta d'akko tsummar k'afarta ta nufo sashen Aysha,ko sallama babu haka ta afko falon tana shigowa idanunta su ka sauka a kan farar kyakkyawar fuskar Aysha da ta yi fayau da ita ga hancin nan kamar wanda a ka kara masa tsawo,baka hango komai sai gashin idonta da su kaeyi zagar zagar suka kwanta kamar ma ba barci take ba,gashin girarta kwantacce da kuma sajenta ,da gashin dake gaban goshinta duk sun kwanta sun kawata fuskar sosai ganinta haka ya tada hankalin Ummulkhairi kamar dai yau ta fara ganinta,ai idonta na sauka a kan gashin daya mata kama dana larabawa ko kuma indiyawa sai da zuciyarta ta yi wani tsalle kamar zata fito daga k'irjinta,sosai tayi mamakin ganin gashin Ayshan yarinya kamar wata yar shugaban kasa gabadaya alamomin jin dadi ne a tare da ita sai kawai taji ta raina kanta, gaba daya ayshan ta fita komai da komai kyau ,diri da cikar kirji anya kuwa ya Kb zai yarda ya aureta dan wanda ya ajiye mace kamar wannan me zai yi da ita kuma? tunowa da ta yi Hajiya za ta saka shi dole ya aureta sai ta ji hankalin ta ya dan kwanta,dan yanzu ma Hajiya ta aiko ta tazo ta yak'i soyayyarta ta samu gurbin zama a zuciyar yayanta dan idan yana ganinta yau da gobe dole zai ji yana sonta dan hakane ma suvka yiwa Daddy karyar Kaduna zata je shine ta tattaro kayanta ta taho nan.Wani haushi ne ya turniketa ta yi kan Aysha a zafafe kamar zata hauta da duka
"Ke malama ina abincina ai wallahi tunda a gidan yayana ki ke dole ki girka ki bani,in ba haka ba in sanar da Hajiya wallahi". Ta fad'a tana rike k'ugu da hannu biyu.
Aysha da kanta ya wani sara da k'arfi jin wannan hayaniyar da Ummulkhairi ke tsaye a kanta tana mata kamar ta mata wani babban laifi yasa ta daga yatsan ta ta mata nuni da karamin foodflask d'in dake dauke da indomie sai kuma bowl mai k'wai a ciki ta rufe da wani bowl din.Ita dama ba za ta dauka bane ta kai mata har dakin da take kamar wata uwarta.'Daukar kwanukan tayi tare da doka tsaki ta juya ta bar falon.
Da yamma wajajen karfe hudu da rabi sai ga Husna ita da Hafsa sun zo,suna shigowa su kayi ido hudu da ummulkhairi da taci ado kamar mai zuwa biki ansa riga da sket na material dinkin ya kamata ansha maje up ga daurin dankwali,sai dai fuskar duk tabon kuraje na man bilicin da ake kwanbalawa.Sallama suke amma ta musu banza ta juya ta shige dakinta tana wani juya mazaunai da gaba daya suke manne jikinta kamar cingam babu wani tudu duk da tana da jiki amma bata da hips sai fadi tayi wani himgimgim.Dariya ma taso basu sai dai mamaki ya hana su dariyar dan suna tunanin kar dai Kb aure ya kara,basu gama jimamin ba Aysha ta fito tana musu maraba.Falo su ka shiga tun kan a gaisa suke jero mata tambayar wacece suka gani ita kwa cewa ta ke dan Allah su bata ledar kayan kwalam din taci kafin aje ga fadin wa suka gani.
"Ga shi nan, ke da komai na duniya kike daukansa ba komai ba"
Hafsa ta fada rai bace, ta tura mata ledar karba tayi ba tare da tayi magana ba ta bude ta fid do alewar madarar ta fara ci kamar yar yunwa dama wuni guda babu abinda taci,sai da taci sosai kafin ta dauki goruba daya dan gaba daya gorubar ma an banbashe mata,gurgura ta farayi sannan ta sanar musu wacece suka gani.Sosai su ke bala'i wai a kan me za ta yarda ta zauna mata a gida bayan a kwai aure tsakaninta da Kb,kuma ko kwalliyar nan ai dan a burge Kb a ka yi ta,ita dai ba tace musu komai ba ta d'auki ledar kayan da suka kawo mata tace su biyo ta d'aki.Suna shiga bedroom din suka zube a kasan capet nan aysha ta shiga basu labarin canjin da ta samu daga Kb tunda ta fara laulayin ciki da kuma abubuwan da ta gani jiya a cikin wayarsa.
"Subhanallah! Gaskiya kina cikin damuwa wannan wace irin rayuwace, wai wasu mazan su keyi ? Ka dauki matarka ba a bakin komai ba,sanna ka fifita matan waje a kanta bayan ita tafi cancanta da ta samu kowace kulawa daga mijinta.,sannan ma da dududu ma yaushe a ka yi auren da har matsaloli irin wannan za su kunno kai cikin zamantakewar auren?". Hafsa ta ce rai 'bace.
"Hakane ,amma ni kuma ina ganin abubuwan da kika gani ba wai suna nufin kb na neman mata bane ,kin san yanzu zamani nan wasu mazan ba wai sai suna zina bane su ke hulda da mataye barkatai ba ,a'a wasu ma kawai dan suke soyayya dasu kawai suna jin dadi suke tara yan mata da yawa,kuma ma yanzu wasu matan marar sa kamun kai ba komai bane dan namiji ya rike musu hannu ko kuma ya rungumesu gaba daya abin yazo da zamani da kuma karshen duniya sai dai kawai mace ta dagewa mijinta da addu'ar nema masa tsari da matayen banza idan kuma d'iya mace gareta ta nema mata tsari da samarin banza". cewar Husna.
"Ni wallahi abin ne ya bani mamaki ya kuma shallake tunanina ,ban taba zaton yadda Kabeer ke nunamin so da kauna har ya tara mata haka bila adadin nifa na san abinda na gani".
Aysha ta fada kamar za tayi kuka tunawa da tayi har hotuna ta gani ya na rungume da mace,yanzu ace wanda ta za'ba abokin rayuwarta sannan ma yanzu tana dauke da cikinsa zai zama abokin rayuwarta shine yake irin wannan abu.
"Aysha kenan! Shi fa namiji haka ya ke son mata a halittarsu yake ,sai dai na wani yafi na wani,kuma da kike bayanin yana sonki ya kuma tara mata,shifa namiji da kike gani da ace za a bashi matan duka duniya ace mallakinsa ne amma kuma a ware guda daya ace ba tashi bace wato banda ita a mallakinsa to wallahi da gabaki daya hankalinsa zai maida kan wannan guda dayar,ji zai yi duk duniya ita ya ke so, ita yake muradin ya san wacece to haka namiji yake amma kuma ana samun wanda zaki ga basu damu da kula kulan yan mata ba amma fa basu da yawa gskia"
Cewar Hafsa tana kallon Aysha da idanta ya ciko da kwalla.
"Humaira ki yi hak'ur ki cire damuwa a ranki ko dan abinda ke jikinki,ki nunawa kb kamar ma ba ki san me yake yi ba, Sannan uwa uba ki dage da addu,a Allah maji rokone "
Husna tace tana dafa kafadarta.
"Shikenan nagod aminai na gari kuma insha Allahu zaku sameni mai aiki da shawarwarinku"
Aysha tace tana murmushi.
Ummulkhairi dake jikin window din bedroom din Aysha ta gama jin duk abinda suka tattauna tayi saurin barin wurin ranta fari kal.
Su kuma falo suka taso suka dawo jin dirin motar kb,sallama suka mata su kace zasu tafi leda ta dakko cike da kayayyakin kwalliya da turaruka sai 5k ta basu sa hau d'an sahu.Rakosu tayi anan suka hadu da kb suka gaisheshi ya amsa da sakin fuska anan ta dakata da rakiyar ta juyo su kuma suka tafi,tana juyowa tayi ido hudu da ummulkhairi ta tare gaban kb sai wani fari take da ido tana wani tsuke baki shi kuma sai washe baki yake kamar gonar auduga,hakan bai bata mamaki ba sbd yanzu ta gama sanin halinsa.Karasowa ta yi itama ta tsaya a gabansu.
"Barka da dawowa sadaukina"
Ta fada tana kashe masa ido daya dan taba ummulkhairi haushi.Sakin baki yayi ganin Ayshan tayi wani masifaffan kallo irin na yan bariki,harshe yasa ya lashi labbansa sannan yace
"Barkanki dai ishana"wani kululun abune ya tokarewa ummulkhari a makoshi.
"Mu je na watsa maka ruwa ko kwa yi bankwana da gajiya"
Tace tana mika hannu ta kamo hannunsa ,tasa daya hannun ta ruko k'ugunsa shima nata kugun ya riko suka tafi suka bar ummulkhairi tsaye da baki sake,ita Aysha tayi hakane da gangan dan ta cusa mata haushi shi kuma KB yama manta da ita a wurin😜
ummulkhairi dakinta ta wuce ta fada kan gado ta fashe da kukan bakin ciki
MAMAN AFRAH😍🥰😘 MAMAN AFRAH😍🥰😘
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*_______________________________________*
🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨
Short story
Story & written by
MAMAN AFRAH
Page 30--31
Sai da tasha kukanta ta koshi,sannan ta kira Hajia a waya ta shaida mata duk abin da ke wakana.Hajia taji dadin labarin da Ummulkhairi ta bata,na samun matsala tsakanin Aysha da Kb amma kuma kwata kwata bata ji dadin yadda Ummulkhairi tace ya biya Ayshan har sun tafi sun barta tsaye ,amma kuma tasan tunda dai akwai matsala tsakaninsu to tabbas da yiwuwar Ummulkhairin zata samu gurbin zama a wurin Kb.Sai dai itama Ummulkhairi ba tayi gigin fadawa Hajia cewar yana tare da wasu matan ba kamar yadda ta ji Aysha na baiwa kawayenta labari domin matukar Hajia ta san yana mu,amala da yan mata barkatai har ma yana iya rungumarsu to tabbas akwai matsala dan zata tsawatar masa ne akan abinda yake.Hakane ma ya bata damar boyewa Hajia domin tayi amfani da wannan damar tashi ta son mata ta ringa shiga wacce zai ke daukan hankalinsa har dai ta kai ga cimma nasara kamar yadda ta yiwa kanta alkawari,shisa da ta tashi fadawa Hajia tace akwai gagarumar matsala a tsakaninsu,amma kuma bata san wace iri bace.Bayan sun gama waya da Hajia a nan ta kwanta tana ta sake sake akan abinda ya faru yanzu tsakanin Aysha da Ya Kb ,tana tunanin yadda zata bullowa al,amarin har dai ta samu mafita ta tashi tana wani murmushi da ita kadai ta san ma,anarsa.