Sashe 17
Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Story & written by
MAMAN AFRAH
Page
36--37
A gigice Ummulkhairi take kallon fuskar Kb tana zazzare idanu, nan take hawaye ya fara zarya a kumatunta.
"Ahayye to yanzu dai ba mijinki bane sai asan nayi umma ta gaida ashshe"Zuly tace tana fashewa da dariya.
Juyawa Ummulkhairi tayi ta kalleta ga zafin mari ga na saki sannan itama tana kara mata da wani abin haushin.
"Baby zo mu wuce uzurinmu tunda komai ya kare kuma"Zuly tace tana kama marfin motar ta shiga. Shima juyawa ya yi ya shiga ba tare da ya k'ara magana ba. Jan motar ya yi a 360 suka bar layin. Ummulkhairi jin jiri na d'ibanta yasa ta karasa jikin motar ta jingina, da taimakon dafa jikin motar ta karasa ta ciro makullin motar rufe motar ta yi, tasa kulle d'an sahu ta tsaida dan kwata kwata ba zata iya tuk'i ba.
Tun da ta shiga d'an sahun take aikin kuka, kuka take sosai dan ta rasa dame zata kwatanta halin da ta shiga yanzu cikin lokaci k'ank'ani, mai napep d'in ke bata hak'uri akan koma me ya sameta ta fawwalawa Allah.
"Dalla malam ka yi abin da ke gabanka"ta fad'a a zafafe.
"Ikon Allah, Allah baki hak'uri"ya ce tare da maida hankali kan tuk'insa. Banza ta masa .dai dai k'ofar gidan data nuna masa ya tsaya a ransa yana kissima lallai dole tayi abin da take so indai a gidan nan take," to ko me yasa ba, a yawo da ita a mota? "ya tambayi kansa. Sauka tayi ta bude k'aramar kofar zata shiga,
"Hajia baki sallame ni bafa" ko waigoya bata yi ba bare ya sa ran zata masa magana, bare har a kai ga bashi hak'k'insa da ya buk'ata.
"Allah ya isa ki je na barki da Allah "ya ce tare da jan dan sahunsa ya bar wurin dan ua san ko shiga gidan ya yi yace a biyasa ba lallai hakan ya samu ba karshe ma ido ua juye da mujiya.
Tana shiga gidan da wani uban ihu ta hau stairs domin cimma Hajia, d'akin Hajia ta shiga babu ko sallama.
"Lafiya dai na ganki haka waye ya mutu?"
"Hajia wallahi ya sake ni"ta ce tana fad'awa kan cinyar Hajia.
"Ya sake ki garin yaya haka ta faru?"
Nan Ummulkhairi ta kwashe komai ta fad'a mata.
"Me ya kai ki, bayan kinsan sharadin da boka ya gindaya? "
"Wallahi na manta Hajia"ta ce tana k'ara fashewa da kuka. Haka Hajia ta yi ta lallashinta ta ce zata san abin yi bayan tasan bokan ya ce duk wanda ya yi kokarin maida auren sunan shi gawa.
*********
A can gida kwa lokacin da ake ta tafka wannan kitimir mira, ita kwa Aysha tana can ta baiwa Hanatu Fauzy tana zaune da littafin addu, o i a hannunta tana karanta azkar din yamma bayan ta gama ta dinga jero addu, o i akan Allah ya shiga lamarinta dan ta san ba mantawa ya yi da ita ba yana sane da halin da take ciki. Gamawarta ke da wuya ta aji ye littafin ta jiyo dirin mota amma ba tasan ko motar waye ba tsakanin Ummulkhairi da Kb dan tasan duk din su basa nan. Ta ji lokacin da ya fita, yana fita itama ta fita a tata motar.
"Assalamu Alaikum " Kb ya ce wanda basu je ko ina da Zuly ba ya ji yana so ya ga Aysha shi ne ya ajiye Zulyn ya nufo gida. Jin muryar Kb cikin falonta, da mamaki kwarai a fuskarta take kallonshi mutumin da a shekara biyu bai shigo dakinta ba amma yau shi ne ya shigo har da sallama fuskarshi a washe kamar gonar audiga.
"wa alaikumus salam"Ta amsa har lokacin bata bar mamaki ba.
"Eesha nah "ya fada yana rungumota jikinsa difff ta yi kamar an dauke wuta jin ta jikin mijinta da rabon da ya rabeta tun kan Abbanta ya bar duniya, tun cikin Fauzy bai da girma, tun sanda ta je gidansu yini ta dawo ta tarar dashi a d'akin Ummulkhairi. Kokarin kwace kanta take daga gareshi jin hawaye na neman sakko mata, riketa ya yi da karfi yadda ba zata iya k'wacewa ba.
"I miss you"
Banza ta yi dashi bata masa magana.
"Haba Humairana yanzu ba kiyi missing dina ba" jin abin da ya ce yasa wasu zafafan hawaye zubo mata
Shin wace macece zata ce bata yi missing din mijinta ba tsawon shekara biyu da watanni??? Alhalin tana cikin gidansa kuma da igiyar aurensa a kanta
Shin ko kwana biyu a kace mijinki zai a dakin kishiyarki ranar bakinta ya kike ji??? Bare kuma a dauki har kwananki a had'a mata tsawon shekaru🥲😭 dole zaki ji babu dad'i dole zaki shiga damuwa, dole zaki ji kunci da tashin hankali.in banda ma na rik'e Allah ina ta addu, ar samun sassauci da tuni na kamu da hawan jini ko ciwon zuciya irin tabargazar da ku ke a gabana!!!
"Ki yi hak'uri matata kar ki rik'eni a kan hakan wlh bansan komai game da hakan ba"ya fad'a yana shinshinar turaren jikinta, wannan furucin nasa ne ya dawo da ita daga sak'ar zucin da ta ke.
Kalamai ya ke masu taushi da sanyaya zuciya, masu tsaga b'argo da dukkan sassan jikin mutum, ba tasan ya akayi ba sai ji ta yi an yi sama da ita😕 kwantar da kanta tayi a kafadarsa bai zame da ita ko ina ba sai kan gadon bedroom d'inta,anan na juya dan ban so na shiga hurumin da ba nawa ba. Sun nunawa juna so da kuma k'auna sunyi kewar juna marar misali, sai dai muce Allah ka rabamu da wanda zasu shiga tsakaninmu da masoyanmu ameen. Sosai Kb ya kwashi gara😝sabo da Aysha irin matan nan ne da basu da budewa dan ko da ta haihu kamar ma bata haihu ba, dan ma da mutuwar mahaifi🥲 shi yasa ba, a mata gyara da wuri ba. Kakarta ke sakata shiga ruwan bagaruwa, bayan ta fito ta shiga na magarya, da wasu ruwan itatuwa dake gyara gaban mace ya hanashi lalacewa ko da haihuwa nawa za ta yi. Kuma lokacin ma an mata wasu hade hade masu kyau da daka mai kara ni, ima da gumba haka ta tafi da kayanta bayan wanda aka yi ta matsa mata tana sha sabo da tana cikin damuwa.
Tun da ta dawo ta tarar da Ummulkhairi a matsayin matar Kb kuma Kb ba ta ita yake ba sai ta tattara kayan ta ajiye, amma da yake ma, abociyar shan markad'ad'd'iyar kankana da madara da zuma ce dan kawai ta kan sha hadin dan ta ji dad'i a ranta sannan yawancin kullum akwai kunun aya a friege dinta, gashi bata taba tsarki da ruwan sanyi wannan ya hana ni, imarta daskarewa. Sai ana kiran magrib komai ya lafa suka shiga wanka tare suka d'auro alwala, suka yi sallah.sai sannan Ayshan ta tuno da Fauzy ganin shiru shiru hannatu bata kawota ba. Itama hannatun ta ga lokacin da Kb ya shiga sashen Ayshan shi yasa ta yi ta jan fauzy da wasa har dai kuma ta ga fauzyn na jin barci ta goyata da ta yi barcin ta kaita d'akin da take ta kwantar da ita.
Tun daga wannan ranar Kb ya dawo da kulawa ga Aysha soyayya babu kama hannun yaro, duk da ta lura har yanzu yana tare da yan matansa dama an ce mai hali baya fasa halinsa, sai dai itama kuma da tasan halinsa sai ta sha maganin zama dashi.ga wani had'i yar uwa matuk'ar ki ka yi zaki ga kyansa na san sai kin dinga yi tsabagen kyan da yake dashi.
* Ki samu kankanarki mai kyau kwallo d'aya.
** Sai kwakwa kwallo d'aya.
*** Dabino kamar na naira 100
****kanamfari dai dai misali kamar dai na 50.
Yadda za ki yi, ki samu wuk'a ki huda kankanar, kamar yadda masu sayarwa keyi idan suna so su ga ko kankana na da kyau, ma, ana a mata v shape. Amma ki yi mai dan girma sabo da kayan da zaki zuba a ciki. Ki cire k'wallon dabinonki, sai ki daka shi ya yi laushi, shima kanamfarin daka shi za ki yi, ya yi laushi, sai ki fasa kwakwar ki zuba ruwan kwakwar a cikin kankanar ta inda kika huda ta. Sai ki gurza kwakwar a magogin kub'ewa, bayan kin gurza ki juyeta cikin kankanar hakama kanamfarin da kika daka, sai dakakken dabinon shima ciki zaki antaya shi. Ki dannasu su shiga, sai kisa wannan wurin da kika yanke ki maidashi jikin kankanar ki rufe, ki sanya a friege ta yi kamar 30 minute, sai ki fitar ki yankata wannan kayayyakin su gauraya ko ina sai ki cinye abinki😋 Zaki ga kyau kamar me dan Allah y'an uwana mata a jarraba a gani sai an gwada akan san na kwarai🤝💃
*********
Bangaren Ummulkhairi da gyatumarta Hajia dan wahala bayan sun je wurin bokan ya ce aure ya kare, amma basu daddara ba, suka yi ta zuwa wurare da dama amma abin babu labari. Dan yanzu ko gidan Kb ya je ko kallo Ummulkhairi bata ishe shi ba, sannan bokan ya gargadesu akan kada su yarda Su fad'awa Daddy mutuwar auren domin hakan ne zai yi sanadiyyar karyewar asirin da ke jikin Daddy.Jin haka yasa Hajia kama bakinta tare da gargadar Ummulkhairi akan kar ta kuskura ta fad'awa Daddy, haka kuma Hajia ko Kb bata taba tuntuba da maganar ba, dan bata so sanadin hakan Daddy ya san maganar.
Wannan k'in yiwa Kb maganar ne yasa Ummulkhairi jin haushin Hajia sannan tasha alwashin fad'awa Daddy dan yasa Kb ya maidata gidanshi.