Sashe 11
Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aysha ta fara tunanin kodai kb neman mata yake duk da zuciyarta taki aminta da haka ,amma yawan tunani da take da kuma halin ko in kula yasa ta fara sanya masa ido akan dan lokacin da yake zama a gidan idan ya dawo wato lokacin dawowarsa daga kasuwa da kuma lokacin kwanciya da yake dawowa da kuma da safe kafin ya fita.na farko ta faki ido ta kalleshi ta wutsiyar ido a lakacin da yake bude pin din wayarsa domin tanaso tasan me yake a wayar ta hakane zata fara gano bakin zaren,sai data tabbatar ta gama ganin pin din bude wayar sannan ta maida kanta ta kwanta shi kuma yaci gaba da daddanna wayar har tayi barcin karya.ya dade yana ta danne danne a wayar daga bisani ya ajiye wayar akan bedside drower ya kwanta,sai data tabbatar yayi barci dan har munshari ya fara sannan kuma ya bata bayane sannan ta lallaba ta tashi da dakko wayar hannunta har karkarwa yake zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri,sanin da tayi ada wayar kb ko pin baya sanyawa sai dai yake dan kaffa kaffa amma yanzu ga pin sannan idan an kirashi yake ta wani wuri wuri da ido alamar kamar marar gskia.har ta cire pin din sai kuma wata zuciyar ta haneta da bincika wayar tana nuna mata kazantar da baka gani ba tsafta ce.har ta ajiye taji dai hankalinta bai kwanta ba aikwa ta dakko ta kuma cire pin din nan take ta fara shiga call long anan ta fara cin karo da sunaye baby1 babie luv,my heart sunaye dai barkatai wasu sun kira wasu an kirasu sosai zuciyarta keta lugude acan kasa taga kiran data mishi yana kasuwa zatace ya taho mata guiva amma ya katse kiran bai dauka ba sunan data gani a numberta shi ya bata mamaki ya kuma so ya bata dariya INDO ya rubuta da manyan harufa.fitowa tayi ta shiga gallary hutunan yan mata kala kala gasu nan ko mayafi babu duk dinkin jikinsu a matse kai wasu ma english wears ne jikinsu,wasu hotunan kb ne da yanmata gasu nan barkatai mace ba daya ba ba kuma biyu ba wani an rungumeshi wani an masa kiss gasu nan dai kamar jamfa a jos.
fitowa tayi duk da hotunan ba karewa sukayi ba,ta shiga whatsapp nan ma ga sunayen mata nan anyi chart na soyayya bila adadin hira da kalamai wanda ita tunda take dashi ma bai taba gaya mata irinsu ba.ta shiga nan ta fito ta shiga can sai data gama duba wayar kakaf sanan ta ajiyeta inda ta dauka zuwa lokacin hawaye ya gama wanke mata fuska zuciyarya sai zafi take mata,komawa tayi tanaci gaba da zubar da hawayen bakinciki wanda har sai da tayi data sani da bata buda wayar ba amma kuma ko ba kamai taji dadin budewar domin kuwa yanzu tasan waye mijinta kuma dawa take zaune take rayuwar Aure.
Haka ta kwana cikin damuwa bata samu wani barci ba,shikwa sai barcinsa yake hankali kwance.da asuba ta tashi sallah ta tasheshi shima data tafi dakinta bata sake waiwayar inda yake ba,domin haushinsa sosai takeji ko fuskarsa bata son gani ita da a iya tunaninta baza,a taba yin ranar da zata ji bataso taga fuskar kabeer ba sai gashi auren bai je ko ina ba amma an samu matsalar da ko hanyar dakinsa bataso ta kalla bare kuma aje ga kallon fuska.
Karfe tara dai dai ya gama shirinsa tsaf cikin kananan kaya da suka karbeshi sosai,wayarsa ya dauka ya kira abokinsa Aliyu domin yau ba kasuwa zai je da wuri ba akwai inda zasuje da aliyu.
"kai ya ka shirya ne"kb yace yana yar dariya .
"na shirya kai kawai nake jira"
"okay gani nan zuwa"yace tare da yanke kiran.fitowa yayi daga sashensa a ransa kuma yana mamakin rashin ganin aysha dan kullum tana nan yake shiryawa amma kuma yau gashi kimis.sashen nata ya nufa dan idan ya fita bai san lokacin da zai dawo ba kar kuma ko bata lpia.tarar da ita yayi kwance kan gado ko kayanta na barci bata cire ba,bayan kullum da sassafe take yin wanka tayi kwalliya sannan taje ta zauna ta jira har sai ya gama shirya.da sauri ya karasa bakin gadon ya mika hannu ya taba wuyanta ko zaiji zafi dan duk tunaninsa bata lpia ne,itakwa aysha tana jinsa amma bata ko motsa ba dan kanta ke mugun sara mata.
"aysha meke damunki ne?"
"ba komai"tace a takaice yayin da idanunta ke rufe dan batason ganinsa.
"okay zamu je anguwa nida aliyu daga can zan wuce kasuwa"
"Allah tsare" kafin ya kai ga amsawa wayarsa na ta kara ,yana duba mai kiran ya saki murmushi juyawa yayi yana mai daga mata hannu bai ma lura da idonta a rufe yake ba ,ya danna ok ya kara a kunne tana jiyo maganar shi
"sorry baby ba girmanki bane yanzu zamu taho......."sauran maganan bataji ba saboda ya riga da ya fice a falon.juyawa tayi ta dauki filo ta rufe fuskarta ta ringa kuka dan ta samu sauki a ranta,daga karshe bacin da batayi jiya ba yayi awon gaba da ita.can cikin barci take jiyo muryan mace na magana daker ta bude idonta da suka mata nauyi agogo ta duba 11:40 saurin tashi zaune tayi tana mamakin barcin da tayi,sakkowa tayi daga gadon ta kamo hanya dan ta fito taga mai magana
"wai ina mai tsaron gidanne"taji maganar ta doki kunnenta,tana fitowa idanunta suka sauka akan ummulkhairi sai direban hajia dake dauke da trolly da kit binsu tayi da sakakken baki😨😨
"nuna masa dakin da zan zauna ya ajiye min kayana"
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*_______________________________________
🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨
Short story
Story & Written by
MAMAN AFRAH
Page
28--29
" 'Dakin da zaki zauna kuma?". Aysha ta tambaya fuskarta cike da alamun fargaba da kuma mamaki.
"E mana! Ko ba za ki nuna ba,in zabi d'akin da ya mini? dan ma kin samu har na kulaki na tambayeki,a matsayinki na mai jire gida" Ummulkairi ta fad'a ta na wani yatsine fuska tare da d'ad'daga kai.
"Ba haka bane ". Aysha ta fad'a a sanyaye.
"To yaya ne? Koma dai menene ke kika sani"
Wucewa aysha ta yi ta nunawa direban wani daki mai dauke da toilet a ciki da komai na buk'ata,d'akin gyare yake tass kamar ma a kwai mutum a ciki.Bayan ta juyo ta ga Ummulkairi a inda ta barta tsaye,kallonta ta yi sanye ta ke da riga da wandon jeans gaba d'aya jikinta a d'ame sai karamin mayafi da tayi rolling dashi sai glases kwalba a idonta ,da hand back d'inta sak'ale a hannu d'aya hannun kuma wayarta ce.
"Ya dai? Kin ga shiga wacce ba ki iya irinta ba ko?Hmmm! Ai duk laifin Ya Kb ne daya kasa tsayawa ya za'bi macen da ta dace da shi,banda rashin sanin ciwon kai ace har karfe sha biyun rana mace ta na kwance tana barci sanye da kayan barci,maimakon a dau wanka na fitar hankali kafin miji ya fita kasuwa shima ya gani ya san ya ajiye mace ta nunawa sa'a a cikin gidansa, hmmm!" ta ce tare da juyawa ta fara tafiya a yangance ta na wani yauk'i da kwarkwasa kamar tana gaban namiji.
Ita kuwa Aysha kallon jikinta ta yi sannan ta girgiza kai ta cigaba da tafiya za ta shige dakinta ta jiyo maganar Ummulkairi.
"Ki sama mun abin da zan saka a cikina domin yunwa na ke ji"
"Ban jin dadi"
Aysha ta fad'a.
"Kamar ya ba kya jin dad'i? Ai aikin bariki tilas ne". Ta ce ta juyawa ta kama hanyar d'akin da a ka kai mata kayanta ciki.Itama Aysha juyawa ta yi ta shiga d'aki tana jin kamar zata fadi ga damuwa, ga rashin karfin jiki ,ga kuma zuciyarta dake tashi kamar za tayi amai dan k'amshin turaren ummulkairi sosai ya kara tasar mata da zuciya.
Haka ta daure ta shiga ta watsa ruwa ta fito ta dauki doguwar riga marar nauyi ta sanya,dan yanzu duk tafi jin dadin sanya su.Sallar azzahar ta gabatar dan lokacin har d'aya da mintina, addu'a ta zauna tayi sosai sannan ta tashi ta linke hijabin da sallayar ta ajiye,wayarta ta dauka ta kira no Hafsa k'awarta jinta a kashe yasa ta kira ta Husna,ba a d'auka ba har ta katse sake kira tayi a karo na biyu sannan aka dauka bayan sun gaisa ta sanar da ita dan Allah idan ta samu lokaci ta iyo mata iloka da alewar madara,sannan ta siyo mata goruba sosai Husna tayi ta dariya tana tsokanarta wai d'an baba ya yi kira dole ne tazo, a yau da yamma ta kawo mata.Haka su ka yi sallama ta kashe wayar sannan ta dauki wani dankwali ta daure hancinta dashi ta shiga kicin ta dorawa Ummulkairi indomie mai attaruhu da albasa ,ta juye sannan ta fasa kwai guda uku ta sanya albasa da maggi da curry ta soya mata ta juye ta dakko su ta ajiye a falo ta zauna tana kallo a tv gyangyad'i ta ke yi dan wani barcin ta keji sosai kamar ma ba ta yi ba, dan cikin barci da kuma kasala yake sanyata ga kuma zazzabin dake gewayata jingina ta yi a kan kujerar har hular kanta ta zame daga kan nata gashin da ta sanya ribon ta daureshi ta kama karshen ta tufke jelar ta sauka har gadon bayanta sai wani sheki yake ya bayyana.