Sashe 18
Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata ranar alhamis Hajia zata tafi bikin y'ar k'awarta da za, a yi a Abuja,dan bikin zai fara tun juma, a sai kuma lahdi za, a kammala. Ta yi ta yi Ummulkhairi ta shirya su tafi amma tace bata jin dad'i, ita kuma Hajia ganin ga yan aiki nan a gidan sannan Jamila ma yanzu nan gidan ta k'auro wai bata son zaman gidanta sabo da rainin wayau. Haka Hajia ta shirya direbanta ya wulwula da ita tare da wata kawarta suka tafi a mota daya wai basa son son tafiya a jirgi😕😜 bayan Hajia ta tafi da kwana daya ashe akwai abinda Ummulkhairi ke shiryawa domin ta kasa hak'urin rashin Kb. Part d'in Daddy ta nufa da sallamarta ta shiga, ta sameshi yana kallon news, zaunawa tayi. Gabanta na bada sautin rass sabo da fargabar abin da zai biyo baya. Amma haka ta danne zuciyarta ta fara kokarin sanar da Daddy dan tana gani ai tunda Hajia na Abuja ba wani zai sanar da ita ba.
"Ummulkhairi kina buk'atar wani abu ne? "ya ce ya yin da yake rage volume din tv.
"Daddy dama, am daman"sai kuma ta yi shiru tana sosa k'eya.
"Dama me? Ki yi magana mana me ki ke so?? "
"Daddy dama so nake na ce dan Allah kasa Ya Kb ya maidani d'akina, ya sakeni kwata kwata yanzu bai kula.....
maganarta ta yanke ne ganin Daddy ya rike kanshi da hannu biyu yana jero salati.........
MAMAN AFRAH😘🥰😻
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*_______________________________________*
🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨
Short story
Story & written by
MAMAN AFRAH
Page
38--39
"Daddy lafiya?" Ummulkhairi taa fad'a hankali tashe dan gaba d'aya yanayun nashi ya bata matuk'ar tsoro. Daddy dai bai ma san tana yi ba sai sunayen Allah yake ta ambata, ji yake kamar kanshi zai rabe gida biyu can kuma sai ya ta ga ya fara bin jikin bango yana dafawa yana d'aga kafafunsa daker kamar wanda suke a d'aure. Gaba d'aya Ummulkhairi ta gama tsorata, sai binsa take da kallo har ya shiga bayin dake can karshen falon daga korido, sai jin k'aran amai ta ke yana ta kolon amai ji tayi daman bata fad'a masa maganar ba, gashi yanzu ta janyo ya shiga wani yanayi wanda dole Hajia ta san me ya faru.
"Ummulkhairi "ta jiyo muryar Daddy kamar daga sama, dago idanunta tayi take kallonsa, abin mamaki da k'afafunsa yake tafiya ba tare da ya dafa bango ba. Ruwane a fuskarsa da alama wanke fuskar ya yi.
"Ina Hajia?"ta ji ya tambayeta duk da bata amsa kiran da ya mata ba sai binsa kawai da take da kallo.
"Ba ta tafi Abuja ba" ta bashi amsa jikinta a sanyaye dan tun da ta ji ya ambaci ina Hajia take to tabbas ya dawo hayyacinsa, tun da dai ai yasan Hajia ta tafi Abuja biki to mesa yake tambaya.
"Abuja kuma lafiya tayi tafiya bata sanar min ba? "
"Biki ta tafi kuma ta sanar maka" jim ya yi yana d'an nazari sai kuma ya ce
"Okay bari na hau sama"ya juya ya hau matakalar benen a nutse kuma kana ganinshi kasan ya dawo Daddy na asali domin lokacin da baya hayyacinsa ko magana yake sai ka ga alama kamar dai wani zautacce.Binsa Ummulkhairi ta yi da kallo har ya b'acewa ganinta.
"wayyo ni na b'allo ruwa na jik'awa Hajia aiki, kai hatta nawa aikin ma ya jik'e gashi Daddy ko ta kan maganar dana fad'a masa bai bi ba"ta ce tana mik'ewa ta fito daga part din daddy ta nufo na Hajia. Jamila ta tarar zaune tana shan ice cream tana kallo sai wani yatsina fuska take, kallo d'aya Ummulkhairi ta mata ta haye sama ba tare da ta kuma bi takanta ba.
Bayan dawowar Hajia
A lokacin da ta dawo Daddy ya fita dan haka wanka ta yi ta huta abinta hankali kwance. Shima Daddy da yake haushinta yake ji yana gani ta yi tafiya bata sanar dashi ba sai kawai bai bi takanta ba ya wuce sashensa ya watsa ruwa ya kwanta tunda lokacin har karfe tara na dare ya yi, ganin Daddy bai je inda take ba tunda tasan itace da gidan shi yake mata abinda takeso tun da ta gama dashi. Sannan ko da Jamila ta sanar da ita Ummulkhairin ta je kd bata kawo komai a kai ba tun da tasan tana xikin damuwar mutuwar aurenta, kuma tunda ita tayi tafiya bazata ji dad'in gidan ba tunda ba wani shiri suke da Jamila ba.
Tashi tayi ta nufi part d'in Daddy, sama ta haura ganin duk fitilun a kashe yasa ranta k'ara b'aci, tana ganin kenan har ya kwanta ba tare da ya damu da ya ganta ba. Kunna fitilun ta yi, ta je ta tsaya a kansa k'ememe Daddy kwa ba barci yake ba yana jinta ya watsa yinta. Hannu ta mik'a ta janye bargon da ya rufa dashi.
"Gaskia ne wato har ka samu damar kwanciya ba tare da ka je ka min sannu da zuwa ba? Ka kuma duba na dawo lafiya ko akasin haka" ta fad'a rai bace tana wani masa fad'a kamar wata gyatumarsa. Mamaki ne ya rufe Daddy wanda hakan yasa ya kasa ko da motsi.
"wai ba magana nake maka ba? Ta zafice shi kamar mai k'ok'arin kai masa duka. Tashi zaune Daddy ya yi a nutse sannan ya dubi Hajia yace
"Kin ci albarkacin y'ay'a kuma sa'arki d'aya bana k'aunar yin saki sabo da Allah bayaso kuma duk lokacin da aka yishi sai al, arshin Ubangiji ya girgiza amma wlh da a yau sai na datse igiyar da ke tsakani na da ke!!! "Daddy ya ce yana nunata da yatsa.
Gaban Hajia ne ya bada rass, ta hadiye wani yawu dank'ararre a mak'oshinta, lokaci daya wata zufa ta fara jik'a mata jiki. Gani ta yi Daddy ya koma mata kamar wani zaki mutumin da sai yadda ta yi dashi amma yau yake mata ikirarin zai iya sakinta.
"Banda rashiin sanin ciwon kai ki fice daga gidan nan ki tafi har Abuja ba tare da sani na ba, sannan ki dawo har ki ke maganar wai banje na miki ban gajiya ba, tabdi to yaushe na zama sallamamman miji yaushe na zama mijin ta ce?? "
"Tabbas da alama wannan shegiyar yarinyar ta jik'a min aiki", tace a ranta a fili kuma tace
"Dan Allah Daddyn yara ka yi hak'uri wlh nima ban san me ya hau kai na ba, kawai na tsinci kai na da fadin maganganun nan ne amma da yardar Allah bazan sake ba, kuma tafiyar da na yi kayi hak'uri nasan ban kyaut...
"Ya isa haka"yace yana d'aga mata hannu ya ja bargo ya koma ya kwanta ya barta nan tsaye. Kashe fitilun tabl yi ta zo ta kwanta,idonta biyu har barci ya lula dashi, itakwa lallabawa ta yi ta baro part din nashi ta koma nata tana dana sanin k'in raba auren Aysha da Kb da ta sani ta sanya Kb ya saki Aysha tun baya hayyacinshi, ta rasa me yasa ta manta da hakan sai yanzu ta tuna. Hmmm Hajia kenan ai indai zaka rik'e addu a wane mutum.
Waya ta dauka ta dannawa k'awarta kira bayan ta dauka take sanar da ita abin da ke faruwa nan tace mata tabbas aiki ya b'aci sosai ran Hajia ya baci. Suna gamawa ta dannawa Ummulkhairi kira wajen sau uku amma bata d'auka ba, Ummulkhairi kwa tana ganin kiran Hajia ta ki dauka..
*******
Aysha da diyarta fauzy kamar yadda suke kiranta, suna samun kulawa sosai daga wurin Kb dan yanzu basu da wata matsala ko kad'an, matsalar Aysha d'aya shi ne Zuly ita ce ta takura mata dan idan Kb yana gida tayi ta kiransa a waya idan kuma baya nan tayi ta kiran Aysha a waya tana gaya mata bak'ak'en maganganu wanda ita Aysha ta rasa a inda Zulyn ta samu numberta .sannan ko da ta sanar da Kb shiru ya mata kuma be d'auki mataki ba, dan da ya d'auka da Zuly d'in ta dena damunta a waya. K'arshe da ta ga abin nata ba na k'are bane sai ta sayata a black list, duk da haka bata daddara ba sai tayi ta turo mata da message na maganganu mararsa dad'i tana ce mata " y'ar matsiyata ta yi asiri ta rabata da masoyinta ita ta aureshi to wlh ba zata barta ta yi zaman lafiya ba indai tana numfashi sai ta rabata da Kb"Irin wannan maganganun su suke damun Aysha tana ganin ita shikenan GIDAN MIJINTA haka zai zama kullum da wacce zata tada mata hankali, tana ganin babu Ummulkhairi ashe akwai Zuly hallaw kuma bayan itama bata da masaniyar wata ba zata zo ba tunda dai shi MIJIN nata haka yake da shegen son matan tsiya🙄.
Haka rayuwa ta ci gaba da kasancewa yau zuma gobe mad'aci dama hakane yau ka ji dad'i gobe kuma akasin haka. Yanzu fauzy ta warware sosai dan har ta shiga makaranta boko da islamiya akwai direban da yake kai ta ya koma ya dawo da ita. Dan haka yanzu itama hannatu ta koma gidansu sabo da zuwa makaranta dama dan renon fauzy aka kawota yanzu itama fauzy ta zama sai dai tayi renon😄