← Book details Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 21

Sashe 3

Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To shikenan tunda kina ganin koda kn rama bazaki huce ba,bari a dakko madoki ki rike a hannunki sbd tsaro ,domin kuwa kina bude wannan bakin naki kika zageni wlh wlh wlh kinji na rantse da Allah hr sau uku,to duka zan sanya miki kinga sai ki rama da madokin naki.dukanki zanyi yadda gaba ko zagin na miki masu maiko bazaki tarki ramawa ba.in dakeki in ga wanda ya tsaye miki,da banda hauka da rashin tarbiya ya za,ayi mace da tarki zagin miji,wannan abinda kike ba komai bane illa rashin ilimi da kuma wayewa,shisa naso na auri mace wayayya mai matakin ilimin boko babba,ba irin naki ba karatu iya secondry scul ga irin ta.........

"Kabeer cin fuskar ya isa haka da kasan da wayayyun matan ka barsu ka aureni?shin kasan da masu babban matakin karatun Bokon ka barsu ka aureni? Sannan ni nasan bani da wanda zai tsaye mn dan ka dukeni,sai dai Allah yana gani kuma shi zai mana hukunci ranar gobe ,kuma kome mutum ke takama dashi Allah ne ya bashi kuma muma Bai manta damu ba amma ka sani ni bazan zauna inayin zagi in zaga ba da miji da Kuma doki in duka ba,domin zaman ya tashi daga zaman aur
Ya zama zaman bariki dan haka gobe gdn mu zan tafi yanzu ma dan dare yayi"ta fada ta cigaba da kuka.

"zaman bariki?"ya fada yana binta da kallo.juyawa tayi zata fita daga cikin dakin,ta koma daya dakin nata domin dakuna ne guda hudu masu dauke da bayi akayi da tangamemen falo.

"Hakan yayi tunda hakan kika zaba ,to kije na sakeki saki daya,kuma idan kn tashi tafiya goben karki sake ki daukarmin yaro ko daya ,kije gdn naku da kika dauka gida,zakisan ba kara Mn rufa miki asiri nayi ba,dana aureki,indai zaman gidane da Kuma zawarci ga fili ga .mai doki.ni Kuma zan samo wacce zata Maye mn fiye da gurbinki"ya fada yana doka wani uban tsaki tare da juyawa ya fice daga dakin gaba daya.

Aysha dake tsaye ,tayi mutuwar tsaye tun lokacin daya furta kalmar saki a gareta ,ya datse alakar auratayya dake tsakaninsu,tun lokacin jinta da ganinta suka dauka na yan sakanni.kuma bata samu damar furta komai ba ,har sai da taji karan banko kofar falonta da yayi da mugu mugun karfi kamar zai karya kofar,durkushewa tayi a wurin tana sakin wani marayan kuka,mai bn tausayi,lallai kalmar saki bata da Dadin sauraro ga macen da mijinta ya furta mata duk da daman ta gaji da zaman gdn kuma zatayi Murna idan ya sawaqe mata kodan idan tana da rabon yin rayuwar farinciki a gaba,itama ta ji dadi da ni,imar aure,dk da tasan tabbas akwai kalubale a kowane gdn aure amma dai tasan ba kamar GIDAN MIJINTA BA dk da haka sai taji zuciyarta hr wani daci daci take,lallai sakin aure bashi da dadi shisa kenan al,arshin ubangiji yake girgiza idan aka yishi,shisa ubangiji baya son saki,gashi dai halal ne ,amma Kuma halal dn da ubangiji bayaso.

Ummanta ce ta fado mata "yanzu umma Ya zataji idan taji kabeer ya sakeni?"ta yiwa kanta wannan tambayar.
"Kiyi hkr umma wlh hakurina ya kare a gdn nan,tabbas idan naci gaba da hakuri wataran bakinciki ne zai kasheni,kuma shi ba damuwarsa bace,wata zai nemo yaci gaba da rayuwa,keda yarana kune da asara"ta fada tana kwantawa a wurin,wani tashin hnkalin na Baibayeta data tuna Rabuwa da yaranta bare ma yace karta tafi masa da yaro ko daya.juyawa tayi rubda ciki tana danne saitin zuciyarta da hannunta,yadda take jin tana bugawa d sauri da sauri ga wani ciwo da taji wurin nayi.

"Lallai kabeer yau ni ka SAKA,ni din da kace bazaka iya rayuwa idan. Babu ni ba?nice fa kace bazaka taba rabuwa da ni ba,kai ne fa ka kasa hakuri in cigaba da karatu bayan nayi Candy,kana ganin kamar idan bamuyi aure ba wani zai iya zuwa ya rabamu da juna.haka na hkr mukayi aure sannan ka Hanani karatun a gidan naka,haka na hkr sbd farincikin ka sbd biyayyar aure,sbd na faranta maka.amma yau dk babu wannan alkawarurrukan na kafin muyi aure ashe dk ka manta da komai?"ta fada tana komawa rigingine ta maida tafukan hannayenta kan fuskarta, ta rufe idanunta tana jin yadda hawayenta ke kwaranyowa kamar an bude fanfo.

*FARKON LABARI*

Malam saleh dan asalin garin roni ne,dake jihar jigawa,iyayensu su biyu suka haifa Kuma
Suka mutu suka barsu shida yayansa salisu.a lokacin saleh yana da shekaru goma sha biyar shi kuma salisu na da shekaru ashirin ,sun taso a Hannun kakarsu ta wajen uba wato iya a,i.ta nuna musu kulawa bayan rasuwar iyayensu hkn yasa suke ganin kamar ma basuyi maraicin iyaye ba.

Tunda salisu ya kammala karatun secondary school bai cigaba da karatu ba,lokacin ma mahaifansu Nada rai sai kawai yake aiyukan karfi yana taimakawa iyayensa,sbd suma ba wani hali garesu ba ,Mutane ne masu karamin karfi.Bayan rasuwarsu ma bai sha wahala ba wajen taimakawa dan uwansa tare da kakarsu ba.

A haka hr wani makocinsu ya masa mgn yace yayi shawara da kakarsa akan zai tafi dashi kano ,ya nuna masa sana,a yakeyi dn ya samu halin cigaba da rike Nauyin dake kansa.haka kwa akayi yake bn Makocinsu kano ya nuna masa sana,ar sai da kayan gwanjo,sannan ya bashi wurin zama a gdn shi sbd yana d gida a kn daman anan yake da zama kawai dai dan asalin garin roni ne.matarsa ma bata da matsala dan haka salisu ya yaso a hannunsu ,yana sana,ar sa,da Allah ya sanya albarka sai gashi har dila yakan karba ya bude Idan ya siyar ya dauke ribar ya hadawa masu kayan kudinsu,dan dama makocinsu Rabi,u shi ya hadashi da abokinsa mai bada dilar gwanjo bashi.

Ana nan salisu idan ya kwashi sati biyu ko uku yake tafiya roni ya gano su iya a,i da saleh ,ya kai musu abubuwan bukata.a haka har yayi jarin kansa yake bude dila tashi ta kansa.

Bayan shekara biyar

Lokacin salisu har ya samu yarinya a makotan gdn m.rabi,u mai suna zainabu ,suka dai daita aka sanya musu rana aure ,a inda m.rabi,u ja shige masa gaba,ya kama musu hayar gida
a yan kaba,daman shima a lokacin yana da shekaru 29 haka bayan tarewar zainabu yaje roni domin dawowa da iya a,i da saleh daman so yake idan yayi muhalli ya dawo dasu kusa dashi ,haka kwa ya dakkosu suka dawo gidansa da zama daman daki biyu ne sai iya a,i ta shiga daya su suna daya shi kuma saleh da zauren gdn da wani dan daki mai kamar shago ,ja shiga ciki.

Tun daga lokacin salisu ya so ya nunawa dn uwansa harkar gwanjo amma yaki ,tunda shima dai iyakarshi sec din ,da suka dawo kano ma yace shi ba yanxu xaici gaba da karatu ba shi adai daita sahu yakeso yake ja,haka dn uwan ya kaishi aka bashi Adaidaita yake ja yana kai musu blance.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya hr zainabu ta haifi yarta,aka sanya mata suna hasiya,sunan mahaifiyarsu salisu ne.yarinyar ta taso cikin gata da kulawa,sosai saleh yake son yarinyar komai ya samu ihsan dake haka suke kiranta.Yarinyar tayi wayo tana yawonta ko ina.

Wata rana da saleh bazai taba mantawa ba a rayuwarsa itace ranar wata Alhamis bayan ya tashi daga aikin adaidaita misalin karfe shida na yamma,daman shi bai fiya aikin dare ba ,bayan ya shigo gida da dare suka sha hira a dakin iya a,i sunayi suna cin naman daya siyo musu su kulli daya su salisu kulli daya,ihsan kuma ice cream,a lokacin da yake yiwa iya a,i sallama zaije ya kwanta,salisu ma ya shigo anan ya fasa tafiya suka zauna suna ta hirarsu,har iya a,i tana cewa shima saleh ya samo mata a masa aure suna da dariya.haka suka yiwa juna sallama kowa yaje ja kwanta.can cikin dare saleh yana barci yake jin kuka da ife ife,da sauri ja bude idanunsa,tasowa yayi da gudu ja fito daga dakinsa dake zaure ,yana fitowa yaga gaba daya cikin gdn naci da wuta ,wutar hr ta fara shigowa cikin zauren ,saurin bude kofar gdn yayi ya fita a rude kuma a gigice yana neman taimako.

Gaisuwa gareku
Queen fulani
Hanoupa
Mmn islam
Mmn jidda
B.jarda
Mame yusuf
😍♥️♥️♥️

🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨

Short story

Story & written by

MAMAN AFRAH

MARUBUCIYAR
RAYUWAR MARYAMU

AND NOW

GIDAN MIJINA

Alhamdulillah I am back again🤗

*SADAUKARWA GA BABANA UBANGIJI ALLAH BASHI LAFIYA👏👏*

Page 7_8

Kururuwa saleh Keta faman yi ,yana neman agaji da kuma dauki daga Jama,a,bubbuga gidajen dake makotaka dasu yake,ya buga nan ya dawo ya buga,can kan kace meye wannan mutane sun taru ana ta kokarin kashe wutar.wasu ruwa suke dakkowa daga gidajensu wasu kuma da ruwan kwata suke kashewa,kafin kace me an kusa kashe wutar,dan lokacin da yan fire Service suka zo kadan suka tarda wutar

Bayan an kashe wutar aka shiga fito da gawarwakin,domin gdn yayi kurmus sai kaurin hayaki dake tashi,haka aka fito dasu gaba daya sun kone babu wani mai sauran rai a cikinsu🥲(UBANGIJI KA MANA TSARI DA WUTA,YA ALLAH KA HARAMTAWA WUTA CIN NAMAN JIKINMU DUNIYA DA LAHIRA AMIN).mutane kowa na fadin albarkacin bakinsa,wasu suce ko tsakace ta hada gobarar ,wasu kuma suce wutar nepa ce tayi spark,Allah ne masani .shi dai saleh yana kan gawarwakin a durkushe yana kallon ikon Allah.kuka yake dk ya zama kamar tabi tabi dn ma dai yana ambaton" innalillahi wa inna ilaihir raji,un"Gasu nan a laye akan babbar tabarma dake gdn makocinsu aka shiga dasu,yaya salisu,iya a,i zainabu,da kuma ihsan.tab lallai dan adam ba kowa bane shi ,shine ke daukan kanshi wani abu.

Washe gari aka musu sutura aka kaisu makwancinsu,tun a ranar da daddare m.rabi,u ya ya tafi da saleh gdnshi dan daman kawai a kofar gida aka dn zauna ake karbar ta,aziyya.suma yan uwan zainabu a can gidansu zasuyi zaman makoki ,sbd gdn bashi da kyan gani ma.haka saleh ya dawo wani shiru shiru dashi dn sosai mutuwar ta tabashi,sai dai ya zauna yayi shiru sai da m.rabi,u ya dage sosai akanshi da Addu,a tare da nasiha sannan ya dn fara sakarwa yana dan walwala
Chapter 3 · 0% Book details