Sashe 19
Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin fauzy na da shekara shida a lokacin ne kuma Allah ya k'ara azurta Aysha da wani cikin, cikin da yafi na fauzy girma duk da dama cikin fari bai fiya girma ba. Amma dai wannan girmansa sosai dan har sai da Umma ta samo mata wata mata mai suna hindu domin take taimaka mata sabo da zama dak'er tashi daker. Lokacin da cikin ya isa haihuwa sun je awo hindu ta rakata direba ya kaisu sai kawai nak'uda ta tashi nan take aka shiga da ita labour room bata dau dogon lokaci ba ta haifo y'ay'anta tagwaye mace da namiji. Sosai Aysha ta yi murna dan ko da akayi scanning d'aya aka gani Allah ya boye d'ayan,sai bayan ta sauka ta kira Kb da Umma ta sanar musu. Kb daga kasuwa asibitin ya taho direct murna kamar ya goyi Aysha Umma kwa sabo da kara bata zo asibitin ba, amma Kb da ya kira Daddy ya sanar masa sai gashi shi da Hajia itama ta ji twins ne sai washe baki take har da yiwa Aysha sannu. Bayan ta huta aka sallameta daman lafiya ta haihu dan haka suka tafi gida, suna zuwa bayan tayi wanka ta kira Hafsa da Husna ta sanar musu. Da yamma sai ga Umma da wasu makotansu guda biyu, sai kuma kakannin Aysha na wajen uwa kowa sai sam barka yake. Ranar suna yara suka ci sunan Hajia da Daddy ana kiransu Amir da Amira.
BAYAN SHEKARA UKU
A lokacin fauzy na da shekara tara twins kuma na da shekara uku, amma kuma maimakon abubuwa su sauya na daga halayyar Kb sai abubuwa suka kara cab'ewa domin yanzu sai ya koyo tsabagen wulak'anci da wata iriyar izza duk abinda Aysha tayi bata iya ba kuma wulakantata ba komai bane a wurinsa duk kuwa da bashi girma da take kuma bata tanka masa duk iya abin da zai mata sai dai gani da ido 👀 ji da kunne👂 in ma ta ga bata so yaran su ji abinda ke faruwa sai ta yi ta lallashinsa tana bashi hak'uri duk kuwa da ba ita ke da laifi ba. Gashi dai ba wani abu ta canja ba dan idan ka ga Aysha ba zaka taba cewa ita ta haifi su fauzy ba gashi kullum cikin ado da kwalliya take. Amma a hakan babu abin da Kb ya raga mata dan tana zaune ma sai yake waya da y'an matansa amma ko ci kanka bata ce masa abin da take yi kawai danne zuciyarta take domin ita yanzu ta fi mai da hankali ga tarbiyar yaranta domin shi Kb ba tarbiyar yaran bace a gabansa shi kawai duniya ce da matan da ke cikinta suke gabansa ,wanda hakan yasa yake ganin matarshi da ya ajiye a gida ba komai ba. Dan yanzu wasu ne matan sabbin zubi ya yi, dan hatta Zuly yanzu ta yi aure .Ni ba kulawar miji ba ta dangin miji kullum jiya i yau amma haka nake hak'uri tun ina b'oyewa Ummata har ta kai ta kawo ina gaya mata komai dan bani da wacce ta fita sai dai ta yi ta ban hak'uri akan in dage da addu, a komai ya yi farko yana da karshe. Ga yaran yanzu da shegen wayo komai kake hankalinsu akan ka shi yasa nake nusar da shi amma shi da je ba tarbiyar yaran ce a gabansa ba babu abin da ya dameshi da yin abu gaban yaro sannan baya tunanin yin abu gaban yaro yana sa yaro ya fahimci irin rayuwar da ake a gidansu. Bugu da k'ari kuma idan har mahaifi na yiwa mahaifiya abu gaban y'ay'anta tofa yaran sukan ji haushin uban nasu, haka zalika mahaifiyar.sai dai abin da mahaifiyar za ta yi shi ne ta yi k'ok'ari wajen ganin bata biyewa mijin gaban yara dan kar a taru a zama d'aya. Fad'a gaban yara ba k'aramar muhimmiyar rawa yake takawa ba wajen kawo rashin jituwa ga d'aya daga cikin mahaifa wanda yaran suka fihimci ana shiga hak'k'insa. Sannan uwa uba rashin ba da power ma na sanya a raina wanda aka hana power misali mahaifiya tana zartar da hukunci uba ya dakatar da ita a gaban yaran ya nuna bayaso ta yiwa yaran fad'a ko kuma duka, to wannan na sanya yaro ya raina uwa haka zalika kema uwar idan kina yi yaron zai raina mahaifinsa tunda yana gani idan ya miki abu ma babu abinda zaki masa tunda mahaifinsa zai hanaki zartar da komai.
A wata ranar asabar ce muna zaune da yara ina koya musu karatu tun da yau ba makarantar boko, islamiya kuma sai karfe uku ,Abban su fauzy ne ya shigo falon nawa cikin shirinsa na fita kasuwa. Yaran ne suka ruga suna murna sun ganshi wuri ya samu ya zauna ya dora Amir a cinya d'aya Amira ita kuma fauzy dama rubutu take yi. Kallon fuskarsa na yi na ga babu alamar walwala ko kad'an dan haka nima ban ce komai ba dama tun da na kwaso kayan breakfast ban koma sashen nashi ba.
"Tun da ba makarantar boko ki shirya su ku je ku gaishe da Hajia" Gaba na ne ya ba da rass jin abin da ya fada dan ya san dai Hajia ba k'aunar in je gidanta take ba, amma sabo da mahaifiya take a wurinsa sannan musu ba d'abi, a ta bace yasa na ce masa.
"To insha Allah zamu je mu gaisheta"
"Gaskia ni dai bazan je ba Hajia bata min dariya su Amir kawai take kulawa"Fauzy ta fad'a tana kumbura baki, domin itama k'iyayyata ce ta shafeta a wurin Hajia suma su Amira dan albarkacin sunan su da aka saka musu ne take k'aunarsu.
"kar in k'ara jin maganar nan a bakinki"na ce ina bata rai yadda zata fahimci ta yi ba dai dai ba, duk da nasan tabbas yaro na son mai jan shi a jiki.
"Ke ku duka zaku je" Abin da yace kawai ya mana sallama yaran suka rakashi bakin mota, nikwa daga nan inda nake zaune na masa Allah kiyaye ko amsawa bai yi ba nima na fafa ne kawai dan na san ba amsawar zai yi ba.
Misalin karfe sha d'aya muka gama shiryawa ,napep muka hau dan yau direba baya nan. A bakin get aka sauke mu muka tura kofar muka shiga tun da muka shigo gabana ke fad'uwa. Part din Hajia muka wuce nocking muka yi aka bamu izinin shiga, shiga muka yi d'auke da sallama babu wanda ya amsa sallamar sai Hajia da take ta yiwa Amir da Amira oyoyo Ummulkhairi kwa kallo d'aya ta mana ta d'auke kai dan tun lokacin da ta dawo daga kd daga baya ta samu wani Alhaji mai bala, in kud'i ta aura matarsa d'aya ta taka Ummulkhairi a rashin mutunci dan daga k'arshema sai da ta mata dukan mutuwa sannan tasa Alhajin ya saketa daman shima irin masu auri saki ne, to shi ne fa ta dawo gida da zama sai kuma ta mayar dani kishiyarta duk da daman kishiyarce tun da ta tab'a auren mijina.
Wuri muka samu muka zauna ni da Fauzy.
"Hajia barka da hutawa ina kwana" na ce xike da girmamawa.
"Hajia ina kwana"Fauzy ma ta gaisheta. Banza ta mana tana ta yiwa su Amir magana.
"Kin gani Mama shi yasa na ce bazan zo ba kin ga ko magana bata min ba kuma na gaisheta ta kyaleni kema ta kyaleki"
"Yimin shiru"Nace ina harararta. Hajia kwa tsayawa ta yi da wasan da take yiwa su Amira ta ce
"To da wa ya gayyaceku? Ni na ce ku zo mun gida da sassafen nan ko karyawa baku yi ba? Ban da shishshigi da neman gindin zama, ai na fad'a miki bana k'aunarki kuma bazan tab'a kaunarki ba! "Hajia ta ce tana nuna Aysha da yatsa.
"Mama tashi mu tafi"Fauzy ta ce tana kama hannu na.
"Ke fitsararriya me suffar uwarta, daman kema bance ki doso in da nake ba ai gadan talauci gadon tsiya"Hajia ta fad'a tana zazzarewa Fauzy ido.
"Haba Hajia ki yi hak'uri shi yaro me ya sani, kawai dai itama tana so ki ke janta a jiki kamar yadda ki ke yiwa sauran y'an uwanta"
"A ah lalle kin yi baki, har ni ki ke gayawa magana ina fad'a kina fad'a? Ku tashi ku fice min daga gida"ta ce tana nuna mana kofa da hannu.
Haka muka fito ni da Fauzy dan su Amir basu biyomu ba raina sai kuna yake bana jure ka yiwa d'ana abu musamman da Fauzy ke ta kuka. Motar Kb na shigowa ta Ummulkhairi ta biyo bayanta, fitowa ya yi suma suka fito Ummulkhairi Amir sai Amira.
"Ya Kb barka da dawo wa" Ummulkhairi ta ce tana aika masa murmushi.
"Ya na ganki da su Amir halan su kad'ai aka kai wurin Hajia? "
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*_______________________________________*
🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨
Short story
Story & written by
MAMAN AFRAH
Page
40
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
"Ba su kad'ai aka kai ba gyatumarsu ta je dasu shi ne ta shuka rashin arzik'i ta taho ta baro su a can"Ummulkairi ta ce tana kanne ido d'aya.
"Bangane ba ita Aysha ce ta je ta yi rashin mutunci" Kb ya ce da mamaki.
Aysha kwa da ke tsaye sakin baki ta yi galala tana kallonsu.
"Eh mana har fa zagin Hajia ta yi"
"Zagi "ya fad'a a zafafe.
"Wlh kwa dan Hajia har da hawaye ta yi na takaicin zagin da Aysha ta mata...