Sashe 15
Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana cikin gidan amma Kb ko ta kanta baya ba, dan ita wani lokacin ma sai tayi kwana biyu bata ganshi ba, kuma koda ta ganshin ma sai dai daga nesa,kai koda suna zaune da Ummukhairi Ayshan ta zo wucewa yi yake kamar ma bai santa ba.Akwai wani lokaci da taje ta tambayeshi zata je duba mahaifinta da bai da lafiya cewa yayi kar ta kara zuwa tambayarshi duk inda takeso taje abinta. Tun daga wannan ranar idan taga an dan kwana biyu sai taje ta duba mahaifinta, amma ka duk da bata fadawa mahaifiyarta damuwarta ba Umma ta gane tana cikin damuwa, amma data tambayeta sai tace rashin lafiyar Abbanta ke damunta gashi kullum sai magani ake amma a banza kurjin na kara girma asibiti har sun gaji da basu magani sun sauya asibiti yafi goma gashi yanzu kudin maganin ma basu dashi duk jarin kayan miyar ya kare a jinya komai da suke dashi a kare a neman magani. Tabbas idan Allah ya baka RAI da LAFIYA ka gode masa dan duk dukiyar da kake tak'ama da ita da kadarorin da kake alfahri ka tara lokaci daya sai Allah ya jarabceka da jinyar da zata cinye gaba d'aya dukiyar da kake da ita🥲Allah ka kara mana lafiya wanda basu da lafiya na asibiti dana gida Allah basu lafiya👏👏Dama Daddy ke taimaka musu yana canja masu asubiti daga karshe ya yanke shawarar fitar dashi kasar India aikwa yana fadawa hajia ta shiga ta fita tasa aka mantar dashi suwaye iyayen Aysha ma gaba daya kai hatta Ayshan ma ya manta da ita kwata kwata.
A haka dai ciwo ke cin Abba dan har ciwon yazo y fashe yake zubar da ruwa, amma duk tsawon lokacin daya dauka yana jinyar sau d'aya Kb yaje dubashi shima Ummulkhairi tace su je su dubashi da ta ji Aysha tace bai da lafiya dan tanaso tayi tsegumi na ganin gidan su Ayshan. Itakwa Umma bata kawo komai dan duk randa Aysha ta zo sai tace Kb yana yiwa Abba sannu yace zai zo ya dubashi insha Allah. Koda sukazo da Ummulkhairi Umma bata kawo komai ba tunda Kb yace yar kanwar hajia sai dai bataji dadin yadsa Ummulkhairi ke yatsina ba, tana wani tofar da yawu. Ko Hajia da batazo duba Abban ba Umma bata kawo komai ba kuma daman tasan ba kowane mai kud'i keson zuwa inda talaka je rayuwa ba kuma ma ta fahimci Hajia ba da son ranta aka auri Aysha ba. Dan sun taba zuwa gidan bisa jagorancin Daddy amma bata ga wata alamar karbuwa a wurin Hajia ba.
Cikin Aysha ya tsufa tana zuwa awo ,wani lokacin ma daga asibiti take wucewa gidansu taga jikin mahaifinta. Saboda gaba d'aya ma batason zaman gidan nata domin idan namiji ya juya maka baya sai kaji gaba daya duniyar ta maka kunci dan ma dai tana hadawa da addu, a, ga cikinta da ya tsufa amma hakan bai damu Ummulkhairi ba dan tunda ta samu kan Kb ita Aysha bata gabanta, yanzu so take suyi aure amma yana cewa ta bari akwai abinda yake shiryawa. Itama Hajia yanzu ranta fari kal danta na son abinda take so.
Wata ranar larabace da asuba Allah ya karbi ran abinsa wato Abba ya amsa kiran mahalicci. Mutuwar data girgiza Umma da mutanen anguwa, ba, a sanar da Aysha ba sai kawai kawu Habibu daya dauki mai taxi suka je gidan Aysha domin ya taho da ita. Ya sanar mata jikin Abba ya matsa ne amma tana ta tambayarsa ko dai Abba ya mutu amma bai amsa mata ba, domin shima ya yi kokari soasi wajen ganin danne kukansa dan kar hankalin Ayshan ya tashi. Haka tasa hijabi duk ta rikice dan dama gaba daya yadda ta baro Abban nata jiya hankalinta bai kwanta ba haka ta kwana suk'uk'u duk damuwar Abban bata barta ta runtsa ba. Ga wata irin fad'uwar gaba dake damunta. Haka suka zo unguwarsu suna shigowa layinsu ta hango mutane maza a kofar gidansu sai mata dake ta tururuwar shiga domin yin sutura. Sosai hawaye ke zubowa daga idanunta amma bata yarda tayi kokan da manzo (S. A. W) ya yi hani a yi ba wanda ake k'walawa ana kiran an mutu an lalace, gata ya kare🙄 haka ta bud'e kofar motar ta fita tana ganin jiri ta shiga gidan yayin da wata mata da zata shiga gidan ta kama hannunta tana bata hak'uri Allah sarki rai bak'on duniya😭
tabbas kowace rai sai ta dandani mutuwa😭
Duk wanda ka ga ya muti shima bai san a ranar zai mutu ba😭😭
Haka za, azare ransa yana ji yana gani bashi da tsumi bashi da dabara, haka kawai zaiga mala, ikan mutuwa ya zo domin tafiya da ransa😭😭😭
Haka za, a wankeshi a sanya masa likkafani a daddaureshi, a dora a makara a sallata a kai a sanya a cikin kabari daga ranar ya koma rayuwa cikin kasa😭😭😭😭
A sanyaka a rami asa itace ganyen maina ,tukwane, kasa jik'ak'k'iya sannan bushashshiya, shikenan an shafeka a doran kasa daga kai sai halinka In kairan khairan in sharran sharran. Allah kasa mu aikata alkhairi😭😭😭😭
👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏
Aysha an bude mata Abbanta ta ganshi ta masa addu, a da ban kwana, haka suna ji suna gani aka daukoshi aka fita dashi daga gidan fita ta har abada fitar da ba, a sake dawowa. Ana fita da gawar Abba ciwon nakuda ya tashi wa Aysha........
MAMAN AFRAH🥰😍😘
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*_______________________________________*
🚨🚨GIDAN MIJINA🚨🚨
Short story
Story & written by
MAMAN AFRAH
Page
34--35
Ciwo ne ya sarke Aysha sosai wanda har bata gane su waye akanta, ga ciwo ga kuma damuwa. Suna so a fito a kaita asibiti wasu matane guda biyu suka fito domin samo abin hawan da za, a tafi asibitin a lokacin har an sallaci gawar Abba an dauketa domin kaita makwancinta. wasu maza ne guda hudu akan tabarma matan suka aika wani saurayi daga cikinsu ya samo abin hawan. Acan cikin gida kwa nakuda ce ta taso gadan gadan kakar Ayshan ce mahaifiyar Ummanta da wata makociyarsu ingozoma suke tare da Aysha kafin me wannan faya ta fashe har kan da ya dungo. Haka akayi ta taimaka mata har dai Allah ya sauketa lafiya. Ta haifi diyarta mace Allah sarki ga abin murna da farinciki ga kuma damuwa ta danne farincikin. Dan haka motar da aka samo domin kaita asibitin sai tafiya mai motar ya yi domin babu wata matsala ko k'ari bata samu ba.Haka Aysha da Ummanta suka saka diyar gaba suna kuka, kukan rashin ganinta da Abba bai yi ba kullum maganarsa Allah yasa kar ya mutu bai ga tsatson Aysha ba sai gashi ko kwana daya babu tsakaninsu a ranar da Abban ya bar duniya ita kuma a ranar ta diro duniyar. (shi yasa ake cewa mutum ya aikata alkairi,, dan idan mutum bashi da aiki sai neman mata to a ranar daya mutu wata macen ma a ranar zata balaga. Wata kuma a ranar zata diro duniyar kenan mutuwarsa bazata sa a daina komai ba ).
Ummulkhairi ce ta kira Hajia take sanar da ita Mutuwar mahaifin Aysha, dan ita Ummulkhairin akan idonta kawu Habibu ya tafi da Aysha tana kuka, sannan Kawu Habibun ya kira Kb a waya yana sanar masa rashin domin lokacin daya zo gidan kwata kwata ya manta da batun Kb domin a rikice yake. Kuma lokacin suna tare da Ummulkhairin aka kira shi, dan haka sai abin ya bata tausayi sosai ta ji tausayin Aysha.data kira Hajia ta shaida mata sai tace ita babu inda zata je, shi ne Ummulkhairin tace ta fadawa Daddy ya je wurin suturar tunda indai ba ita tace ya je ba to fa ba zuwa zaiyi ba tunda ba a hayyacinshi yake ba, sai abinda tace masa kuma indai bai je ba mutane zasu zagesu sannan duk ranar daya dawo hayyacinshi ya gane bai je wurin mutuwar ba rai ne zai baci. Da haka hajia ta fadawa Daddy ya je wirin mutuwar baban surukarsa kuma sai ta ga mutuwar ta dakeshi kamar dai yana cikin hayyacinshi. Haka direba ya daukeshi ya kaishi a lokacin ma ba, a dawo daga makabarta ba dan haka suka tafi makabartar. Itama Ummulkhairi data tisa Kb a gaba suka tafi suna zuwa ya wuce makabarta ita kuma ta shiga cikin gidan.
Ummulkhairi wuri ta samu ta zauna da yake gidan a cike yake, bata ga Aysha ba dan haka sai tayi zaton tana daki tana nan a zaune ta ji wasu mata suna hira hmmm gidan makoki ma yanzu hira ake tun ma ba, a dawo daga kai gawa ba.
"Kai Allah sarki kinga shi ana fita da gawarsa ita kuma nak'uda na tasar mata"
"wallahi kinsan haka lamarin Ubangiji yake, kana naka Allah yana nasa, gashi ko dawo wa ba, a yi daga kaishi ba har ta haihu"dayar tace tana kad'a kai alamar jimami.
"Wacece ta haihu? "Ummulkhairi dake kusa dasu akan kujera su kuma suna kan tabarma ta tambaya da mamaki a fuskarta.
"Diyar marigayin mana humaira"daya daga cikinsu ta bata amsa.
Kawai gani sukayi duk ta birkice, saurin daidaita natsuwarta tayi Tace"Allah dayyaba"
"amin "suka amsa a tare. Itakwa Ummulkhairi gaba daya so take ta tashi ta fita tasan yadda zatayi ta janye Kb su tafi gida kar labarin haihuwar ya je masa. Bayan an dawo daga kai mamacin anyi addu, a kowa kokari yake ya yiwa wanda mutuwar ta shafa gaisuwa, wasu kuma suna ta fita a gidan domin tafiya gida saboda suturace ta safe ana so aje gida ayi yan aikace aikace a samu ayi karin kumallo. Wasu kuma suna ta shiga dakin da Aysha take domin ganin abinda ta haifa sai dai hakan bai samu ba saboda har lokacin ba, a gama kintsa ta ba ita da jaririyarta.