← Book details Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 21

Sashe 20

Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai kafin Ummulkhairi ta kai aya ya yi kan Aysha kamar zai kai mata duka, ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba, Aysha tana so ta masa bayani ya k'i saurarenta, Fauzy ma da zata yi magana ya dakatar da ita kai a tak'aice sai da Kb ya zagi Aysha ta uwa ta uba .Aysha kawai hawaye ke zuba a idonta itama Fauzy ba, a barta ba a baya dan tana da wayo sosai kuma tasan ba,a kyautawa mahaifiyarta ba, ta kuma san Mamanta bata zagi Hajia ba tana so ta yiwa Abban bayanin yadda aka yi amma yaki ya saurareta. Ummulkhairi kwa ranta fari kal ta had'a ta ji dad'i dan da sanin Hajia ma ta taho ta yi had'in wannan.

Wannan shi ne abin da ya janyo Kb ya sakeni lallai namiji duk hak'urin da nake k'unsa a cikin gidansa amma bai gani ba sai da ya ci wa iyayena mutunci!

Da asuba bayan na yi sallah na yi azkar, karamar trolly na d'akko na sanya kayana a ciki tare da abubuwan da zan buk'ata, fitowa na yi na je d'akin hindu mai kula min da yara na sanar mata zan tafi ta kulamin da yara na, na dauki kud'i masu yawa sosai ta ji babu dad'i jin sakin da na ce mata yaa shiga tsakaninmu. Haka na shiga d'akin yaran na gansu suna ta barci abinsu, na fito jin hawaye na neman kufce min ni kuma bana buk'atar yin kukan yanzu. Sashe na na dawo na dauki jakata da akwatin sai wayana, fitowa na yi na bude kofar na fita mai gadi na ta bani hak'uri domin ya san ba lafiya bace za tasa na fita da akwati da sassafen nan kuma ba tare da yaro ko d'aya ba.

Ina fitowa bakin titi na samu napep dan lokacin gari ya yi haske sosai akwatin na sanya a xiki nima na shiga na zauna na fad'a masa in da zai kai ni. A dede kofar gidan mu nasa ya tsaya na biyashi kudinshi na kinkimi akwatina na shiga buga kofar gidanmu, wata iya salame da suke zaune tare da Umma a gidan kanwar maman Ummance ita ta bude min kofar gani na da akwati yasa jikinta yin sanyi, jakata ta karba ni kuma na shigo da akwatin Umma dake shara ta yarda tsintsiya ta tsaya fuskarta da tsahin hankali tana kallona, jikina ne ya k'ara yin sanyi ganin damuwa k'arara a fuskar Ummana. D'aki na shiga da akwatin na ajiye, haka muka zauna jugum jugum na fad'a musu duk abin da ya faru ina fad'a ina kukan takaici dan gaba d'aya sai nake jin kamar ma yanzu ake min duk abin da aka mini.

BAYAN WATA UKU

Lokacin har Aysha ta yi iddah, dan haka kawu habibu yasa ta yi jamb kuma Allah ya taimaketa ta ci aka nema mata admission a B. U. K nan take Aysha ta fara karatu babu kama hannun yaro, dan dama tana son karatu gata da bala, in k'ok'ari sannan kuma ta hadu da k'awaye wayayyu suke koya mata komai na rayuwa dan idan ka ga Aysha ba zaka ganeta ba. Kamar ma ba ita ta haifi yaranta ba ba wanda zai ganta yace ba budurwa bace. Ta kwantar da hankalinta tana yiwa y'ay'anta addu, a tana karatun ta hankali kwance. Sai dai samari da manyan Alhazai da ke mata tururuwa ita kuma tana sallamarsu dan babu sha, awar aure a ranta yanzu dan kayan d'akinta ma tuni aka kwaso ta sai da wasu wasu ta jerawa Ummarta .Sannan ta kan sari takalma da pad ta mata da kayan shafa tana tafiya dasu makaranta tana siyarwa abinta.

*********

Bangaren Kb kwa tun da ya saki Aysha sai ya ji kamar ya yadda k'wallon mangwaro ya huta da k'uda. Dan yanzu ne yake cin karensa babu babbaka, sai ya kwana yana waya da y'an mata yara kwa ga hindu nan ita take musu komai dan ko gidan Hajiya aka kai su bata wani iya rikesu dak'er take bari su wuni, ta dai ce ya nemi mata ya yi aure dan murna fal cikinta da ya saki Aysha Daddy ne ma ya masa fushi ya kuma nuna masa bai kyauta ba. Amma abin da ya sa Daddy bai tsaurara ba sabo da yana so Kb ya gane muhimmancin Aysha ne.

Kb sai da ya zab'a ya darje domin kuwa wata kilalliya ya samu ana kiranta Hajara bai dai yar masu kud'i bace amma kuma iya daukan wanka da kuma kyau da take dashi shi ya ja hankalin Kb ya aureta. Bayan aure ansha amarci sosai dan Kb gani yake yanzu ya yi aure, ya samu mace dede da tsarinsa sai dai me😕 ashe amarya kwata kwata bata san in da mutunci ya dosa ba, bata ragawa Kb bare Hajiya bare kuma wata karan kad'a miya Ummulkhairi, sai ta taka har gida ta je ta yiwa Hajiya rashin mutunci kuma daga Hajiyar har Kb din babu wanda ya isa ya d'auki mataki dan gaba d'ayansu tsoronta suke. Abu d'aya ne bata yi shi ne tab'a masa y'ay'a, ba ruwanta da su Fauzy, dan tun da aka bata labarin irin zaman da Aysha ta yi ita kuwa ta ce wallahi duk sai ta gyara musu zama👍

A kwana a tashi sai ga Kb ya dawo yana da ya sanin auren Hajara,dan yanzu ta zame masa alak'ak'ai ko fita bai isa ya yi ba sai da izininta kuma ba boka ba malam kawai tsabar rashin mutunci ne. Gashi ko wane wuri zata je sai tare da Kb zasu je, sannan ya bud'e mata mota ta shiga ya bude'e mata idan zata fita🙄 Yan mata kuwa sai da ta sanya kowacce a black list ta sanya ya goge gaba d'aya numbers d'insu. Idan ya shigo gida wayarsa a hannun Hajara zata kasance bai isa ya danna waya ba kai ko kiransa aka yi sai ta fara d'auka ta tabbatar da mai kiran sannan zata bashi wayar. Gaba da gabanta aljani ya taka wuta🙃 Yanzu ne Kb ya fara ganin muhimmancin Aysha yanzu ne yake jin inama ya mai da hannun agogo baya, kai ba Kb ba hatta Hajiya yanzu tana dana sani akan abin da ta yi ta yiwa Aysha, yanzu sosai take jan jikokinta a jiki dan hajara bata basu dad'i ba daga ita har Ummulkhairi, Daddy kad'ai take ragawa dan gaskia sosai take girmamashi, dan bata kwana uku bata je gidan Hajiya ba idan kuwa ta je bata baro gidan sai ta sanya Hajiya damuwa,.Dan ita yanzu Ummulkhairi ta samu wani me mata uku zata aura sabo da ta gujewa rashin mutuncin Hajara da kuma gorin aure da take mata kuma dan Hajara ta d'aga hannu ta zabgawa Ummulkhairi mari ba komai bane a wurinta gata da tsawo da k'iba🤣.

BAYAN SHEKARA BIYAR

Aysha ta samu kammala karatun ta, ta karb'i result d'inta kuma alhamdulillah ya yi kyau sosai. Yanzu ta kara zama babbar mace ta yi k'iba abinta farinta ya dawo ha online bussiness da take yi shaddodi lesina atamfofi da sauransu, babu abinda bata siyarwa tana samun kudinta alhamdulillah babu abin da suka nema suka rasa dan dai Daddy ma yana taimaka musu.

Yanzu kawu Habibu ne Umma ta sanya shi ya sa Aysha ta fitar da miji ta yi aure, dan dama shi ya matsawa Umma ta barta ta yi karatu dan haka yanzu kuma Aysha ta kammala kuma ga manemanta nan masu mutunci shi yasa take so ta fidda wanda take gani ya dace ta aura. Duk da yau kusan shekara biyu Kb na zuwa wurinta yana bata hak'uri akan ta taimaka masa ta dawo dak'inta su cigaba da rayuwa🙄😕 amma ta ce babu ita babu gidansa amma duk da haka bai daddara ba kullum sai ya zo ko da kuwa ba zata kulashi ba. Dan wataran yana jikin motarsa zai ganta ta fito tana tare da wani wanda ya fishi komai da komai, duk da daman yanzu kud'in nashi ba kamar na da ba, dan Hajara ta gama tatik'eshi ta kuma rabu dashi👎 ba ciki ba goyo💃 ta karawa rigarta iska😄

Umma ce zaune da kawu Habibu Aysha sai kuma Daddy da shi ne sanadin had'uwar.

"Aysha inaso ki fidda mijin aure dan ni kamar y'ar da na haifa haka na d'auke ki"cewar Daddy.

Sunkuyar da kai Aysha ta yi dan kunyar Daddy take ji.

"Ba magana ake miki ba"Umma ta fad'a tana hararta dan tun jiya da Daddy ya cewa Umma a waya zai zo akan maganar ta gargad'i Aysha akan ta zab'i tsohon mijinta🤨 sabo da yanzu gaba d'aya Kb ya canja kuma ta lura har yau yana son Aysha ga nacin zuwa da yake kullum, sannan ta san Aysha ma taa son sa kuma idan ma wani ta zab'a ba tasan wayeshi ba sai ta je gidansa dan haka ta gaya mata ta zab'i wanda ta tab'a zama dashi ko dan y'ay'anta dan halin maza sai su gwara wanda ta san halinsa, zai fi wanda bata sani ba. Ta yi hak'uri da abin da ya mata a baya ta manta da komai.

"Ki yi magana mana kin yiwa mutane shiru"Kawu Habibu ya ce yana kallonta.

"Ku mata a hankali mana kun san...

"Assalamu Alaikum" sallamar da aka rangad'a ta hana Daddy k'arasa maganar, Hajiya ce ke sallama ita da Kb amsa musu aka yi tare da basu izinin shigowa. Mamaki ne ya kama Aysha da Umma na ganin Hajiya a gidansu abin da bata tab'a yi ba. ban da Daddy da daman ya san komai ka iya faruwa tun da Hajara ta koya musu hankali. Gaisawa aka yi a inda Kb da Hajiya suja shiga baiwa Aysha hak'uri musamman Hajiya da har da yafiya take nema a wurin Aysha. Aysha kunya ta ji anan take ta yafe musu, sannan Kb ya roketa alfarmar komawa d'akinsa har da durk'usawa da rok'onta yafe masa ta yi tare da fatan Allah yafe mana baki d'aya.
Chapter 20 · 0% Book details