Sashe 14
Gidan Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka Aysha tayi wunin gida a ranar ranta kwata kwata babu dadi domin ganin mahaifinta cikin ciwo mahaifiyarta cikin damuwa yasa taji gaba daya duniyar bata mata dadi. Haka ta bar gidan zuciyarta cike da damuwa domin gaba d'aya ma shi ciwon Abban nata an kasa tantance wane iri ne wani k'aton k'urji ne wanda girmansa ya yi mutum ya hada hannayensa wuri d'aya ya dunk'ule tauri k'igir dashi kamar dutsi😭 haka dai Ummarta tayi ta kwantar mata da hankali kafin ta musu sallama ta kama hanyar gida. A lokacin karfe shida ma tayi, sai bayan ta hau dan sahu ta tuna cewar lokacin dawowar Kb gida ma ya wuce. Tana sauka ta baiwa dan sahun kudinsa, karamar kofar get din ta tura ta shiga ta maida ta rufe mai gadi dake zaune kan bencinshi yana jin redio ya gaisheta ta amsa masa sama sama dan gaba daya jinta take kamar ba a duniyar mutane take ba, damuwar dake ranta ta hanata ta ji dadi a zuciyarta koda k'ankani ne. Har ga Allah tana son Abbanta tana kuma tausayin Ummarta gashi basu da wani d'a me debe musu kewa tunda ita kadai suka mallaka sai kawu Habibu dake zuwa lokaci zuwa lokaci domin taimaka Ummarta wajen jinyar Abban nata kamar yadda Ummar ta sanar da ita yau, a cewar Umma anki sanar da itane saboda kar ta shiga damuwa saboda abinda take dauke dashi tabbas! kwa Umma tayi gaskiya domin gashi yanzu tunda ta yi arba da halin da Abbanta ke ciki bata samu sukuni ba ko miskala zarratin. Tana tafiya tana zancen zuci bata anakara ba sai ganinta tayi har tazo sashinta, bude kofarta ta yi ta shiga ta je ta ajiye jakarta da mayafinta, ta fito domin zuwa sashen mijinta dan ta ga motarsa alamar yana nan kenan tunda tasan matsawar ya dawo to fita kwa ta zama dole, amma kuma tunawa da tayi jiya ma ba Inda ya je wannan yasa ta fara tunanin ya fara gyara halayensa. Sai dai kuma in ko Aliyu ne ya zo suka fita tare a motarsa. Tura kofar tayi ta shiga amma kuma bata ga Kb a ko ina ba hatta bayin ta duba baya ciki, hakan yasa ta fara tunanin ta tambayi me gadi ko ya fitane bayan ya dawo? To amma kuma me yasa be kulle part din nashi ba? Tunda ya san yanzu ba su kadai bane a gidan akwai Ummulkhairi. Fitowa tayi da niyyar zuwa tambayar me gadi, shaida mata yayi Alhajin yana ciki bai fita ba,garden ta nufa wai ko can ya je yake hutawa, tun daga nesa ta hango inda kujerun suke amma babu kowa a kansu. Cikin lambun tabi ta dan zagaya amma babu shi babu alamarsa,abun ne ya daure mata kai haka ta kamo hanya ta dawo har zata shiga daki sai wata zuciyar tace ta tambayi Ummulkhairi dan jim tayi tunda tasan ba wani shiri suke ba amma a haka ta doshi dakin Ummulkhairin tana fargabar kar ta mata rashin arziki. Tana zuwa kofar dakin ta fara jiyo tashin sautin dariya data kasa banbance mamallakan muryan, kwankwasa kofar tayi amma ba, a mata magana ba kuma tasan an ji, sake nocking din tayi a karo na biyu, jin ba, a mata magana ba yasa ta tora kofar, abinda idanunta suka gani👀 shi ya sanya ta razana Ummulkhairi ce da Kb zaune akan kujera daya kanta akan kafadarsa suna kallo a waya yayin da wayar take a hannun Kb suna ta dariya abinsu hankalinsu kwance, kamar ma basu san da shigowar Aysha dakin ba. Wani kululun bakin ciki da takaici ne suka taru suka mamayewa Aysha ranta take ta ji wani kishi ya hayayyako mata hawaye ne suke neman zubo mata amma kuma basu samu dama ba domin kwa tayi namijin kokari wajen ganin ta danne su, bude baki tayi da niyyar yin magana amma kuma maganar da Kb yayi ita ta hanata furta tata maganar.
"Dalla malama ya zaki fadowa mutane daki ba sallama? ko irin tarbiyar gidanku kenan? " ya fada yana wani hade rai tare da zaro mata idanu.
"A, a toh kai ma dai ka fada Ya Kb, tunda idonka ya nuna maka yanzu"Ummulkhairi tace tana dariyar shekiyanci.
"Yanzu dan na shigo dakin nan kake kiran babu tarbiya a gdn mu? Kafin in shigo sau nawa na kwankwasa kuka kyaleni?bayan na shigo na ganku manne da juna bayan ku ba ma, aurata bane ba kuma muharraman juna bane, kai koda ku muharraman juna bai kamata kuyi irin zaman da kuka yi ba yanzu amm.......
"Ke dakata ke har kin isa kizo har dakina kice zaki gaya min maganar banza nawa ma ilimin naki yake da har zaki yiwa mutane wa, azi ko nasiha"Ummulkhairi tace tana aika mata harara.
"Yauwa! Sisina fada mata dan tun kan ta san hanyar makaranta muka sani"cewar Kb
"wlh dan d'an iliminta da baifi cikin cokali ba"Kb yace tare da fashewa da dariya, Ummulkhairi ta mika masa hannu suka tafa🤝
"wannan haka yake Yayana"tace tana maida kanta kafadarsa.
"Ki fice kiba mutane wuri wama yasan daga ina kike"yace yana maida hankalinsa kan wayar dake rike a hannunsa.
"Wallahi kwa Ya Kb kana fita itama ta saka kafarta ta fice, sai yanzu ta dawo"Ummulkhairi tace tana fakar idon Kb ta yiwa Aysha gwalo. Hawayen takaici ne suka cika mata idanu gaba daya ta daina gane komai haka ta juyo ta baro musu dakin tana tafiya ba tare da ta san inda take saka kafarta ba har ta karasa kan gadonta ta kwanta tare da fashewa da kuka mai taba zuciyar mai sauraro. Salloli kawai t gabatar ta yiwa mahaifinta addu, ar samun lafiya tare da duk musulmi sannan ta rokawa kanta sauki da sassaucin halin data tsinci kanta a ciki.
Abin da Aysha bata sani ba shi ne tun da ta saka kafarta ta fita, itama Ummulkhairi ta tafi gidan kawar Hajia da ta hadata da ita zasu je wurin wani malami domin a shawo kan Kb yake kula Ummulkhairin domin a cewarsu itama fitar da tayi wurin boka ko malam ta tafi.Haka suka bada kudade masu yawa aka basu magani wanda nan take zai fara aiki sannan magani ne na shiga tsakanin Kb da Aysha. Haka barci barci ya k'auracewa idanun Aysha har wajajen karfe biyu na dare da taga dai babu abinda zuciyarta keyi sai sake sake tashi tayi ta dauro alwala ta ringa nafiloli tana kai kukanta gurin wanda baya barci sannan gyangyadi bai kamashi,bayan ta idar da sallolin ta karanta sunayen Allah 99 sannan ta karanta Alqur, ani mai girma.daga hannayenta tayi ta ringa jero addu, o, i bayan ta gama ta like abin sallar ta maida Alqur,an din ma ajjinsa. Komawa tayi ta kwanta lokacin har karfe uku da arba, in, cikinta ne ya fara k'ugi alamar yunwa fresh milk ta dauko mai sanyi tasha ta koma ta nkwanta nan take barci ya yi awon gaba da ita.
Washe gari
Bayan ta yi wanka ta gama shiryawa ta shiga kicin ta hada breakfast doya ta soya sai tayi miyar kwai, sai ruwan shayi mai kayan kamshi, dakkowa tayi ya nufi sashen Kb dan lokacin karfe takwas da kwata jerasu tayi a kasan capet dan Kb bai fiya san cin abinci a dinning ba.bedroom dinsa ta nufa,lokacin har ya shirya yana taje gashin kansa, shigowa tayi bakinta dauke da sallama Kb dake tsaue gaban mirror yaji kamar ta doka masa guduma a kansa.
"ke! me ya kawoki dakina? "
"kayi hak'uri abinci na kawo maka"
"banason cin abincin naki ki fice min a d'aki banason ganinki, kuma kar in sake ganinki kin shigo min daki"yace yana nuna mata kofa.
"Ya Kb,Ya Kb"sukaji Ummulkhairi na k'wala masa kira a falo.
"Gani nan k'anwata"ya fad'a tare da daukan wayarsa ya gota Aysha dake tsaye kamar gunki ya fice, itama bayansa tabi suka karaso falon tare Ummulkhairi na zaune ta dora kafa d'aya kan daya sanye take da doguwar riga yar kanti jikin rigar roba gaba daya ta kamata.sai k'aramin mayafi data yafa tana ganin Kb ya fito ta tashi ta nufoshi sukayi gaisuwar larabawa suna ta murmushi abin su,
"Allah tun jiya daka taho wajen karfe goman nan ban samu sukuni ba sai yanzu dana ganka"Ummulkhairi tacw tana wani mak'ale kafada tare da zunburo bakinta mai kama dana sauro.
"Sorry nima haka na kasance amma yanzu ai gani ko? "ya fada cikin lallashi.
Aysha da ranta ya matukar b'aci ta rab'a su ta fice daga falon, haka ta koma falonta ta zauna tana jin lokaxin da mai gadi ya wangale musu get suka fice.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji, un "kawai take furtawa,har ta ji zuciyarta ta yi sanyi. Tun daga wannan ranar Aysha bata kara sumun wata dama ba a matsayinta na mata a wurin Kb. Haka suke fita tare da Ummulkhairi shi ya san inda yake kai ta ya wuce kasuwa idan zai dawo haka tare zasu dawo, su shigo da take away ba ruwansu da neman abinci haka kawai ma sai su tafi yawo tare a gida suna tare kamar dai mata da miji soyayya suke zubawa abin su, sai barci kawai ke rabasu duk wannan shak'uwar daje tsakaninsu baisa Aysha ta musu zargin zina ba.
Haka rayuwa ta ci gaba da kasancewa amma koda wasa Aysha bata taba sanar da kowa abin da ke faruwa ba. To wama zata fad'awa mahaifiyarta dake cikin damuwar jinyar mahaifinta ko kuma Hajia da ba k'aunarta take ba kuma ma ai da saninta abin ke faruwa tunda tasan da zaman Ummulkhairin a gidan, sannan bataso ta fadawa su hafsa saboda kar su ma su dauki abin a bai bai dan duk wanda zata baiwa labarin zai dauki mijinta mazinaci ita kuma bataso sunan uban y'ay'anta ya baci ko ba komai su y'ay'a a wurinsu mahaifine duk lalacewarsa, sannan kuma shi yaro bashi da laifi ba shine ke da alhakin zabawa kansa mahaifi ba dan haka tana ganin koma menene laifinta ne,kuma bai kamata take sanar da wani abin da ya zama sirrinta ba.