← Book details Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 26

Sashe 6

Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wurin babu gida ko ɗaya sai ciyayi,da na waiga ma hatta restaurant ɗin babu ta ɓace ma ganina.A nan take na fara jin tsoro duk da ni ɗin ba ma'abuciyarsa ba ce,tafiya na fara ba tare da na san inda nake jefa ƙafata ba har na isa wurin da hanya ta tsage ta rabu biyu.Wata irin ƙishirwa nake ji a cikin mintin da bai gaza goma ba,maƙoshina ya bushe ƙamas.
Idona suka fara ɗaukar caji,na lumshe su a hankali kuma bakina ya fara fitar da sautin wani Yare.Ban buɗe idona ba sai da na ji ƙarar motoci da zantukan mutane.
A bakin titi na tsinci kaina, Allah ya taimake ni na hangi wani gu ana sayar da ruwan leda na tsallaka na sayi leda huɗu a nan tsaye na shanye su.Na ja ajiyar zuciya kamar wacce aka dawo ma da ruhi haka na ji,daga nan na tari taxi sai gida.

A can restaurant kuwa sosai hankalin Mansur ya tashi,muryar Momah tamkar busar sarewa haka ta ratsa dodon kunnen shi.Ya so ya tsayar da Ayodele saboda hatsarin da ke da wurin,amma da ya tuna zuciyarsa ba ta aminta da lamarinta ba sai ya ƙyaleta tare da yaƙinin sai dai a yi labarin wata amma ba dai ita ba.
Bayan sun gama cin abinci ya ɗauki su a mota,sai da ya fara ajiye Fatimah sannan ya kai A'ishah.
“Wai wace ce ita? Wato abinci mai magani ba zai taɓa zama a cikinta ba shi yasa ta amayar da shi.Na tsane ki! Ita kuma uwarta ta wace ce? Ya aka yi har ta san na shirya plan akan ɗiyarta?” ya jero ma kansa tambayoyin ya na mai bugun sitiyarin mota a haka har ya isa tankaɗeɗen gidansa wanda ya ji komai na more rayuwa.Sai da yayi wanka ya sha madara mai sanyi sannan ya kira A'isha suka yi ta hirar soyayya a ƙarshe ya tambaye ta “ya labarin ƙawar ki?”
“Wace daga ciki?”
“Wannan mai siffar Inyamurai” ya bata amsa,ta yi dariya ta ce “don dai ta na da jar fata ne sosai amma ai ba ta kama da Inyamure ”
“Fatan ta je gida lafiya?”
“Wallahi ba mu yi waya ba”
“To ki kira ta mana,sam ban yi kirki ba da ban bata ko da kuɗin taxi ba ne”
“Jira na kirata to” cewar A'isha ta na mai kashe kiran,Mansur ya lumshe ido ya na jin zuciyarsa na ɗan dokawa burinsa guda A'isha ta kira ta ce masa ta mutu.

AYODELE

Ina isa gida Momah ta wani jawo ni a jikinta ta rungume bisanin ta fara duduba ni kamar wacce ke neman ko na samu wata illa ne.
“Daga yau kar na sake jin kin tafi yawo kin ji ko? ”
“To Momah ” na amsa.
“Ayodele ke ɗin ta daban ce,dole ki dinga taka tsantsan duk da ina da yaƙinin ababen bauta ba su taɓa bari a cutar da ke ba,domin su na tare da ke a ko ina amma ki dinga kulawa ba ko ina ba ne ake zuwa” Momah ta sake faɗa ta na mai kallona cikin ido.Kai kawai na jinjina mata bisanin na wuce ɗaki,kaya na cire na yi ɗaurin ƙirji na je na yi wanka .
Ina tsaka da cin dambun shinkafa da Moma ta girka kiran A'ishah ya shigo,gabana sai da ya faɗi a take duk abin da ya faru da ni ya dawo kaina,hakan yasa har kiran ya katse ban ɗauka ba . Lokacin da na biyu ya shigo kuma a daidai nan maƙociyarmu Asabe ta shigo ta na rangaɗa sallama.

Na amsa mu na gaisa wa,Momah ma ta fito .Godiya ta zo ta na ta faɗa mana yadda lamarin ya kasance da Zeinab nan muka yi ta hira kan Mayu da illolinsu.Sai bayan ta fita ne na duba wayata ,har zan maida kira kuma sai na fasa na tsunduma zancen zuci ‘tabbas da walakin goro cikin miya! In babu rame mi ya kawo zancen shi? Mine ne na biyana har toilet? Babu shakka akwai abin da ya saka a abincinmu,to shi kuma restaurant ɗin da ya zama kamar ɓatan wata? Hummm! Zan nutsu,na ankare komai sai na gano gaskiyar lamarin’
Abincin ma sai ya fita raina,tashi na yi na fiddo fararen rigunan da nake saka wa na likitanci na wanke su tasss bisanin na kwanta ina yin bacci don jiya mun sha aiki sosai.

Tamkar a mafarki na ga wasu mutane masu fararen kaya sun zagaye ni,idona sun min nauyin da ba zan iya ware su duka ba amma tabbas ina iya ganin abin da ke gabana.Kaina na ji an fara shafa wa yayin da sauran kuma ke yin hira cikin wani Yare wanda in ba zan manta ba shi ne na taɓa ji Momah ta yi.Cikin wannan yanayi na lula duniyar mafarki,yau ma kamar kullum sanye yake cikin kayan ƴaƴan sarakuna ya saka kayan yaƙi,daidai ƙugunsa kubai ne mai ɗauke da takobinsa.Gefensa kuma masu tsaron lafiyarsa ne a tsaye cikin shirin yaƙi akan duk wanda ya kawo masu farmaki.Murmushi yake sakar min ya na kallona daga nesa, cikin izzar da ban san yaushe na same ta ba na fara takawa izuwa inda yake muna facing juna.Da sauri na lumshe ido sa'ilin da ya tsaka ɗan yatsansa manuni ya dangwala min jininsa a goshi a nan take wani sanyi ya luluɓe ni yayin da kuma nake jin shigar wasu lamurran da ba zan iya fassara su ba su na ratsa ɓargo da tsokar jikina.

“Ayodele? Ayo....” a kasalance na buɗe idona na zube su kan Momah wacce ke faman jijigata da kiran sunana.
Ta sakiya wata nauyayyar ajiyar zuciya bisanin ta ce “daga yau kar na sake ganin kin yi bacci a daidai lokacin da tartatsin rana ke tsakiya ban so”
Dakyar na iya buɗa baki na ce “don me?”
“Lokacin babu wata albarka a cikinsa ,bacci ya haramta ga al'ummar Victoria Falls ”

Da mugun sauri na ce “su waye kuma al'ummar Victoria Falls ? A wacce ƙasa ce? Mine ne haɗi na da su?”
Da mamakina sai na ga Momah ta rikice,abin da na lura ma kamar suɓutar baki ce ta yi.“Ki na ji Ayodele mu bar wannan maganar,ke dai kawai ki kiyaye abin da na ce.Am...na ce ... Ki taso na koyar da ke saƙar hannu” duk a rikice take,ni kuwa na zuba mata ido.Lokacin baya babu yadda ban yi da ita kan takoya min saƙar hannu ba ta ƙiya,amma yau sai gashi yau take son koyar da ni.

Fuskata na wanke,na gyara zama ta fara nuna min yadda ake fara aza zaren farko na Foundation ɗin sannan a fara zarga wa gabanin ta miƙo min ƙarafan saƙar.
Abu guda ya ban mamaki yadda na iya tafiya da takun saƙar kamar wacce tun can farko na taɓa koyon ta ,Momah na daga gefe ta ƙure ni da ido .Ko shakka babu ta zurfa sosai cikin tunani duba da yadda na yi mata magana sam ba ta ji ba.Ganin haka yasa na je na fara cika bokiti da ruwa,“oh! Har kin gaji?” na tsinkayo muryarta, murmushi kawai na sakar mata bisanin na ɗauki bokitin ruwan.
Ina kai soso fuskata na ji wani irin uban raɗaɗi tamkar na zuba barkono ,da sauri na wanke na fito direct ɗaki na shiga na ɗauki madubi.Ɗigon ja na gani a goshina mai ɗauke da wani ƙaramin tauraro.Shiru na yi ina daɗa kallonsa,“Momah???” na ƙwala kiranta ,ta na shigo wa na ce,
“Dubi wannan abun mine ne? Zafi yake min”
Cike da kula wa ta ce min “ki jira har ranar da kika cika shekaru ashirin da biyu duk zan yi miki bayani”
Na turo baki gaba na ce “ni dai ki faɗa min yanzu”
“Ke ban fa son sakarci ,wai haihuwata ma kika yi da za ki tsare ni da tambayoyi ? To ban sani ba” ta na gama faɗa ta shige ƙurya ɗaki.

Yadda na matsa wa kaina sanin mine ne har Allah yasa na tuna da mafarkin da na yi,wato na masoyin ɓoye.Har ban san lokacin da na saki murmushi ba,cike da nishaɗi na shirya cikin riga da wando na fita ƙofar gida.

FATIMAH

Tun lokacin da ta ci abincin da Mansur ya saya masu a restaurant take jin wani mugun sauyi a jikinta.Tamkar wacce ba da lafiya haka ta samu wuri ta kwanta,wani irin tsoro da shakkar saurayin ƙawarta take ji ba tare da ta san dalili ba.Ummarta har tambayarta ta yi abin da ke damunta amma ta ce babu komai.Ta rufe kanta cikin ɗaki kawai ,domin wani irin son kaɗaici ne ya zo mata.Wayarta ta ɗauka ta tura ma Nasir saurayin ta text ,duk da ba ta son shi haka ta ji ra'ayin kula shi.Da wannan ta ɗan rage faɗuwar gaban da take ji,har ta samu ta ɗan saki jiki.

A can ɓangaren A'ishah kuwa haka ta kira Mansur ta shaida masa ta yi ta kiran Ayodele amma ba ta ɗauka ba.Har ƙasan ransa ya ji mugun daɗi don dama ya na tabbacin fatalen da ke kan hanya kawai sun isa su kasheta da tsoro.
Chapter 6 · 0% Book details