Sashe 22
Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sarki Haroon ya kafe ta da ido yana kallo kafin ya ce “ki amsa laifinki sannan ki tuba ki rungumi addinin Musulunci domin tsira da ranki”
“Babu wani addini da zan shiga,na fi son zama babu alƙibla.Sannan kuma ni ba mayya ba ce duk da ina da ilimin sarrafa maitar,maganar ƙarshe kuma ita ce zan koma gida”
Rai ɓace yarima Naslam ya zaro takobinsa da niyyar sauke mata kai amma jakariya Ali yayi saurin riƙe shi yana cewa “ka nutsu yarima kar ka yi saurin yanke mata hukunci jira na kira Barham”
Zuciyarsa na ƙuna ya ce “ba ka ji yadda take magana ba sam babu ɗa'a?” bai ma kai ga cewa wani abu ba Barham ɗin ya shigo.
Kallo ɗaya ya yi wa matar ya gane wace ce ita,hakan yasa ya ƙarasa gun sarki yana mai yin ƙasa da murya ya ce “kar ku kashe ta,za ta yi mana amfani a nan gaba” sosai sarki yake ɗaukar shawarar Barham saboda shi ɗin aminin mahaifinsa ne sannan kuma dattijon arziki na masarautar.
“Ku mayar da ita” sarki ya faɗa wanda hakan sam bai yi wa yarima daɗi ba sai kawai yayi zuciya ya fita daga wurin.
Jakariya Ali ya bi bayansa yana mai cewa “ gaggawa aikin sheɗan ne,matar can tana ɗauke da wani ɓoyayyen sirri wanda nake jin cewa ita ce makullin da za mu yi amfani da shi wurin buɗe duk wata ƙofa da ta yi mana wuyar shiga”
Ba tare da yarima ya ce masa wani abu ba ya soma cire kayansa na sarauta yana ajiye wa.Toilet ya shiga ya soma yin wanka ko zai ji sassauci,har ya fito jakariya Ali na nan.Shi ne ma ya taimaka masa wurin tsane jikinsa ya saka kayan zaman gida,daga nan sai suka wuce can inda tantabarunsa suke.
Yana son tsuntsaye, wannan yasa ko ƙunci yake sai ya ziyarce su yake jin daɗi.Jakariya Ali ya buɗe su,da gudu kuwa duk suka shiga fitowa suna nufo shi,ɗaya ta sauka kan kafaɗarsa ya kai hannu ya damƙo ta yana shafar jikinta yana murmushi.
Sai ya ji kamar ana kallonsa,ido ya baza cikin tantabarun nan idonsa ya sauka kan baƙuwar tantabara idonta ƙurrr kansa.Kasancewar bai yarda da canfi ba sam bai kawo komai a ransa ba,haka ya ratsa ya je ya ɗauko ta wani irin shock ya ratsa shi nan ɗin ma bai sa a ransa wai lamari ne da ya shafi sprituality ba.
Jakariya Ali ne kawai ya farga da abin da ke faruwa,amma kuma sai ya ja bakinsa yayi shiru.Duk yadda yarima ya so tantabarar ta saki jikinta amma abu ya cuttura kawai sai ya wuce da ita can ɗakinsa yana mai cewa “ban san daga ina ita wannan ta zo ba,da alamu ta ƙi sabawa da sauran ne”
Jakariya Ali ya ce “ dama ai kullum cikin samun baƙi tantabaru ake yi,ita ma za ta saba”
Cikin ɗakinsa ya sake ta,ai kuwa sai ta shiga yin walwalar.
A can ɓangaren gimbiya A'ishah kuwa abubuwa ne duk suka dagule mata,ga rashin ƙawarta Jamila ,ga ɓatan Dadda kusan kwana uku har yanzu ba ta dawo ba,ga kuma yanayin jikinta da take jin ya sauya.Zaune ta yi cikin halin ƙaƙanikayi tana wasiƙar jaki,sai ta ji ana magana ƙus-ƙus ba ta jin abin da ake cewa, da ta nutsu sosai sai ta gane a cikin drower kayanta.A hankali ta je ta buɗe,ɓerayen da suke gurgurar kayanta suka saki ihu a tare wannan karon sarai ta ji abin da suka ce.
“Wayyo an kama mu yanzu an yi ƙoƙarin kashe mu” shi ne abin da ɓerayen suka faɗa kafin su fara gudun tsira,har kan ƙafarta ɗaya ya faɗo amma ta kasa yin motsi saboda shock.Ita maitarta iya ta juya baƙi ya dawo fari ce,sai ga shi yau ta ƙara samun matsayi.Jikinta ne ya hau rawa,babu shiri ta nufi ƙofa don zuwa wurin Barham ta sanar da shi sai kuma ta yi kiciɓis da Dadda wacce ta dawo daga jejin Mayu.Da sauri ta ja baya,ita kuwa murmushin mugunta ta sakar mata tana mai cewa “Allah yasa dai ba ƙoƙarin tonawa kanki asiri kike yi ba? To ki sani muddin yarima ya ji labarin ke mayya ce to zai fasa aurenki, ba kuma zai yi jinkiri sauke miki kai ba kin fi kowa sanin halinsa fiye da ni yadda bai da tausayi akan mayu”
Idon gimbiya A'ishah ya kawo ruwa,yanzu ne kawai ta yarda da maganar Barham .Tabbas a matakin da take a yanzu ta riga da ta makaro babu ta yadda za a yi ya cece ta.
Dadda ta ci gaba da yi mata gargaɗi mai ban tsoro,“ in kuma kin shirya yin mutuwar kare sai ki je ki faɗa ,sanin kanki ne hatta sarauniya Sarat ta bar masarautar nan saboda laifin maita ballantana ke karan kaɗa miya ”
“Amma Dadda ni ban ce miki ina son zama mayya ba,don me za ki bani kambunta?” gimbiya A'ishah ta faɗa .
Dadda ta bata amsa da “saboda duniyar nan muddin babu maita da Magic to tamkar miya ce babu magi,ki zo na nuna miki mece ce ainihin rayuwar Mayu na tabba in kika ga irin shagalin da ake yi ke kanki za ki ji daɗi ki kuma gane gata ne na yi miki ” shiru gimbiya A'ishah ta yi kafin ta je da gudu ta rungume Dadda.
★YANKIN MUTUWA
Zuwan baƙuwar haure daga duniyar turɓaya shi ya canza mana yanayin shigarmu.Na ajiye fatar dabba na koma saka kaya,waɗanda Banah ne da kansa ya shiga duniya shi da sauran matsafa suka kwaso su a can duniyar tuɓaya.Kai tsaye za a iya cewa suka sato,saboda dare ne suka bi suka dinga shiga kanti suna ɗebo kaya bayan an kawo haka aka zube su aka rabawa kowa ciki kuwa har da ƴar jaririya da na samo wacce har zuwa yanzu ba a saka mata suna ba.
Ummilo shi ne sunan da nake yi wa matar wacce duk ƙoƙarin Banah na son saka mini tsanarta bai yi nasara ba.
Zaune na yi ina kallon yadda take bai wa baby madarar da aka tatso daga dabbobi.Hannu na kai na shafi fuskar Babyn ina mai cewa “Ummilo wane suna kika zaɓa mata?”
Ta yi wani murmushi mai ƙayatarwa kafin ta ce “ina son sunan Jamila saboda na riƙi ƴa mai irin sunan nan” sai kuma ta yi wani irin shiru kamar mai yin nazari,a nan ne na fahimci cewa kamar ƙwaƙwalwarta na son tuna wani abu da ya danganci rayuwarta.
Ina shirin yin magana sai gani na yi gari ya ɗau wani irin duhu,yayin da kuma mutanen da na zube suna yi mini hidima suka soma yin ihu.Duk yadda na so yin tsafi abu ya cuttura,kamar minti biyar sai komai ya dawo normal.Idona na sauke ƙasa sai na ga duk ɗigon jini ne ta ko ina kamar an yi ruwansa,ina ɗago kai kuma muka haɗa ido da Banah fuskarsa kicin-kicin kafin ma na kai ga tambayarsa sai cewa yayi “ tun da kika shigo da jaririyar nan a yankin nan bala'i ya soma sauka,don haka mun yanke shawara ni da sauran matsafa za mu bayar da jininta matsayin hadaya ga ruhikan ruwa........
[28/04 13:15] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️
```MRS SADAUKI```💫✍️
FCWA☀️
____________________________________________
08
“Ta ya za ka ce a ɗauki jaririya a kai wa Teku matsayin hadaya? Wannan sam ba mai yiyuwa ba ne.Wannan al'amarin da ya faru kuma ko kaɗan bai da haɗi da da jaririya Mila wani baƙin ƙulli ne daga maƙiya kuma zan binciko na gani duk masu hannu a ciki” na faɗa .
Banah ya ƙanƙance ido yana kallona,na je da sauri na ɗauki Mila daga kan cinyar Ummilo na goge mata fuskarta da yayyafin jini ya ɓata.Can ɗaki na yi tsinke,ina daidaita mata kwanciya ya shigo yana mai cewa “ita kuma Ummilo sai yaushe za ta tafi tun da kin karya doka kin ce ba za a kashe ta ba”
Ba tare da na juyo ba na basa amsa da “ nan ɗin masarautata ce,Ni ke da ikon barin wanda zai zauna da kuma wanda zan kashe,ka tsaya iya matsayinka na mijina in ina son shawarinka ni ce da kaina zan neme ka”
Cike da takaici Banah ya fito daga ɗakin ya jefi Ummilo da wani mugun kallo wacce yake jin tsanarta sai dai fa alƙaluman tsafinsa sun kasa rubuta sunanta .Direct can bayan gari ya nufa,bai yi nisa ba ya soma furzo kalaman tsafi nan take busashen ganyen da ke zube a ƙasa ya soma tashi sama kafin kuma ya haɗa wata baƙar guguwa wacce ta yi ambaliya da gangar jikinsa ya ɓata .Cikin wani kogo ya bayyana mai ɗauke da kunamu baƙaƙe ƙirin kuma ga su manya-manya.Suna ganinsa duk suka soma basa hanya,shi kuwa haka ya dinga ratsa tsakiyarsu har ya isa can ƙarshen kogon inda wata halitta ke kwance tana ƙyafta ido kamar mai jin tsoron buɗe su ɗin.
Zubewa yayi yana mai yi mata sujuda ba tare da kuma ya ɗago ba yake cewa “kin ce in na dinga shayar da ke jini za ki ɗaga martaba ta fiye da duk wani mai iko a duniyar nan,amma me yasa Naomi ke yi mini gardama akan hukuncin da na zarta alhalin hatta maganin laƙani na sa an shayar da ita shi”
Ba ta basa amsa ba,sai fara saukowa da ta yi daga kan dutsen da take kwance ta zo ta fara hawan bayansa tare kuma da laulaye shi da bindinta.A hankali ta zagayo kanta kan ƙirjinsa,babu ɓata lokaci kuma ta buɗe bakinta tare da kafa masa haƙoranta masu mugun tsini ta soma tsotsar jininsa na wani lokaci kafin ta tashi sama tana wani irin kuka kamar jiniya.Dukkan kogon ne ya tsaya cak kamar babu wata halitta mai numfashi,muryarta ta soma fitowa “ka karya dokata,na faɗa maka duk wacce za ka aura to ya zama dole ka yi tarayya da ita a wannan daren sannan ka bani jinin budurcinta.Tun da har ka bijire to ya zama dole a gare ka da ka yi haƙuri da wasu ƙananun al'amurra.Sannan ita wannan mata da kake tsana ta kasance shugaba ce a wata mazaɓar duniyar ruhaniya muddin ka yi kuskuren cusa kanka a lamarinta to za ka tsinci litininka a laraba ”