← Book details Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 26

Sashe 20

Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abu aka shayar da ni wanda ya dagula mini lissafi ya juye mini hankali na ji tausayi,so,ƙauna da duk wani abu da ya shafi mutumci sun fita daga zuciyata.Sai dab da za mu fitowa ne sannan aka kawo Maa zuwa gare ni,tana tsaye cikin siffar nan ta matattu sai dai yanayin fuskarta ya nuna tana cikin damuwa kamar ba ta jin daɗin rayuwar wannan duniyar.

“Maa” na kira ta ina mai shigewa jikinta,yadda na ratsa ruhin nata na fita shi ya sa ni saurin janye wa na koma kan ƙafafuna.

“Naomi me yasa har zuwa yanzu ba ki yi wani aikin bajinta ba wanda zai sa ruhina ya mori aikinki? Dube ni yadda na rame har yanzu ruhikan ruwa ba su yi amanna da ni ba” ta faɗa cikin wani irin yanayi.

“Maa sam ban gane abin da kike nufi ba” na faɗa .

Ta ce “Ta hanyar kashe mutane ne kawai zan samu abinci Naomi ” ta bani amsa ,wato so take yi na fara sarrafa maita ina damƙe kurwar mutane ina kawo mata jininsu.

Tana gama bani amsa aka zo aka tafi da ita,Banah ya kamo hannuna muka fito daga ƙasan ruwan.A lokacin da muka isa gida tuni gari ya soma yin haske,cikin son sake kasancewa da ni Banah ya soma yi mini wasu abubuwan amma na dakatar da shi ta hanyar yi masa wani kallo da idona da nake jin tamkar an yi mini musayarsu.Cikin wata shakkata ya janye daga gare ni kafin ya koma gefe yana kallona,murya a dake na soma magana “ka nemo baƙar akuyar da za a yi hadaya da ita,yau laraba ruhika na buƙatar jini” sai kuma na yi shiru kafin can kuma na ci gaba da cewa “ina son jinin mutum domin shayar da mahaifiyata”

Sai da na kai karshe sannan Banah ya ce “domin samun jinin mutum ya zama dole ki fita farautar dare,don yin maita da rana tsaka ba halayyar shuwagabanni ce” sai kuma ya taso ya matso kusa da ni ya tallabo haɓata yana mai ci gaba da cewa “matata zafafa ce,na san ta kowanne fanni jaruma ce kuma ƙwararriya.Zan baki shawara mai kyau amma sai in kina so”

“Ina jinka ” na faɗa a dake.

Ya ce “ki shirya gagarumin yaƙi domin samo tataccen jini mai tsabta wanda ba a gurɓata shi da maita ba”

“Su wa zan yaƙa kenan?”
“Garuruwan da ke maƙwabtaka da mu mafi akasarinsu ba su sarrafa tsafi ballantana maita,in muka yaƙe su sosai za mu samu alkhairi ”

A cikin bayaninsa sosai na tsinci kishin garinmu da kuma son ci gabansa, wannan dalili yasa na ce “bayan an gama ƙaddamar da hadaya,zan so ka haɗa hankulan dukkan mutanen garin nan sannan ka shaida musu a yau ba sai gobe ba za mu je farauta ruhika”

Banah ya yi wani murmushi yana mai cewa “an gama” sai kuma ya fice.
Ido na lumshe ina tunanin yadda na ga shugaban nan NASLAM da tawagarsa suna yaƙar Mayu.Da wani irin sauri na buɗe idona ina mai yin magana a fili “ yaƙi cikin tsakiyar dare ya fi ɗaga hankali kan da safe,don haka farmakin dare za mu kai musu” sai kuma na yi wani murmushin mugunta wanda hakan ba ƙaramin sanyaya mini zuciya ya yi ba.

Kamar yadda na umarci Banah haka ya kawo mini baƙar akuya har da ma zakaru su ma duk baƙaƙe ne.A gaban al'ummar gari muka je muka shayar da kogi jinin dabbobin kafin kuma mu juyo,Banah ya laƙanci tsafi sosai wannan yasa bai sha wuya ba wurin aiwatar da shirinmu na kai farmaki a garuruwan da babu maita.

Dab da shigowar duhun dare Deborah ta zo inda nake,haka kawai na ji ban buƙatar ganinta duk da kuwa wani sashe na zuciyata yana tune da ƙawancenmu.

“Abin da kike shirin yin sam bai dace ba! Babu wani sarki da ya zo mana a tarihi cewa ya nuna ƙarfin tsafi ya janyo wani yanki izuwa nasa” Deborah ta faɗa ,ba tare da na kalle ta ba na ce “wannan garina ne,ni ce ke da ikon yin duk abin da ya dace ga al'ummar ciki ba ke ba.Ruwanki ne ki rubuta tarihina a cikin littafinki,in kuma ba ki ra'ayi za ki iya barinsa”

“Naom...” ban bari ta kai ƙarshe ba na juyo a harzuƙe cikin hargowa,sai kawai ganin Deborah na yi ta yi sama tare da faɗowa ƙasa cikin rauni.Na nuna ta da yatsa ba tare da na ce mata komai ba,amma sosai ta gane kashedi nake yi mata.

Wani irin kallo ta soma jefo mini kafin ta ce “ta yaya kika yarda har wani baƙon haure ya raba mu? ”

“Shi ɗin mijina ne,don haka na san ba zai yi abin da zai cutar da ni ba kamar yadda ke kike ƙoƙarin danganta ni da masifar rashin yin aure”

Hawaye suka zubo kan kumatunta ba tare da ta goge su ba ta ce “na san kin karanta littafin tarihi,kin gani da kanki muddin shugaban tawagar Mayu ta fito a mace babu ƙaddarar aure a rayuwarta,in kuma ta yi shi to ki sani akwai ranar da mulkin sai suɓuce mata.Sannan yadda tarihi ya nuna ke dai babu aure a tarihinki da ya zo da wanda ma zai zo gaba, sannan na faɗa miki sharaɗi in ma kin yi auren to ki sani ba a wannan duniyar ta ruwa ba”

Cike da tsana da takaici nake sauraren jawabinta.Da a ce za a tambaye ni babban maƙiyina a duniyar nan a yanzu to babu makawa zan ce Deborah ce,saboda duk wanda ke da ja da lamarin aurena to ban ɗauke shi masoyi ba.

Baya na juya mata a karo na biyu kafin na ce “ina shawartar ki da ki bar gidan nan kafin na yanke miki ɗanyen hukunci”

Ba tare da ta ce komai ba ta tafi,babu jimawa kuma shi Banah ya shigo hannunsa riƙe da ƙwallon kwakwa ƙwaya ɗaya.Tsakiyar ido ya dube ni kafin ya ce “muddin kina gama baki da matsafin tarihi to mulkinki ba zai taɓa ci gaba ba saboda a kullum so suke su canza maka ra'ayi akan abin da kake buri”

“Me za ka yi da kwakwa?” na tambaye shi ba tare da na bai wa abin da ya gama faɗa muhimmanci ba.

“Jirgin dare ne na Mayu ,a cikinsa za mu tafi” ya bani amsa.Kallon mahaukaci na yi masa don sam ban san komai ba game da maita saboda ban taɓa gwada yi ba.Sai da dare ya zo tsakiya ne na ga abin al'ajabi yadda Banah ya mayar da kwallon kwakwa jirgi,kuma ma ni ce farkon shiga bayan shi sai kuma ya soma zagayawa da mu yana ɗibar jama'ar gari waɗanda ke ɗauke da kambu maita ko tsafi.
A wani gari jirgin namu ya yi dirar angulu,tsit garin yake kowa na yin bacci .Haka muka zagaye shi kafin mu soma sarrafa mugunta muna fito da su daga gidajensu muna cillawa cikin jirgi,duk wanda ya yi gardama a nan take muke aika ransa ga ruhikan ruwa.Cikin ƙanƙanen lokaci garin ya hargitse da ihuce-ihuce da kukan mata da ƙananun yara,gefe ɗaya kuma wuta ce ke tashi.
Har mun shiga jirgi za mu koma sai idona ya sauka kan wani gida,shi kaɗai ne ba mu rogaza ba.Kukan jinjiri na soma ji,cikin azama na dire tare da zuwa na ratsa bango na wuce saboda yadda duk ƙwayoyin tsafi suka game jinina.

Wata mata ce na tarar a ciki,gefenta jinjiri ne sabon zuwa duniya don ko cibi ba a yanke masa ba.A hankali na duƙa na ɗauki yaron,sai a lokacin kuma na ji muryar matar na cewa “kar ku kashe mini yaro ” yadda na ga soyayyar uwa da ɗa a cikin ƙwayar idonta shi ya tuna mini tawa mahaifiyar.
Ban kai ga cewa komai ba Banah ya shigo,kafin ƙyaftawar ido ya soma jan ragamar ruhinta.Cikin gargardar murya na ji tana cewa “ Ash-hadu an la'ilaha illallah! Wa'ash-hadu anna Muhammadu Rasulullah!” wata irin walƙiya ce haɗi da zubar ruwa suka zo a nan take,yayin da kuma ni da Banah muka zabura muka yi baya saboda ɗacin amon sautin abin da ta furta yayin da shi kuma yaron da ke rungume a hannuna ya ci gaba da canyara kuka.

“Mu bar wurin nan yi sauri kafin alƙawari ya karye” Banah ya furta cikin wani irin tsoro wanda ban san dalilinsa na yin haka ba.Ina ɗaga kafaɗa haɗi da sake rungume jaririn a ƙirjina na fito,ina shiga cikin jirgin Banah ya jefo mini wani mugun kallo yana kallon jaririn.Na ƙankance ido ina mai ce masa “kar ma ka fara,ka tuƙa jirgi mu tafi”

Ba don ransa ya so ba ya ja ragamar jirgin namu na matsafa har muka isa yankinmu,a ƙofar gidanmu aka zube dukkan mutanen da muka kwaso kafin ni na shiga can ciki na bai wa sauran umarnin su tsaya su tsare mutanen.

Kan gado na shimfiɗe jaririn,ina shirin kwanciya na ji wata murya a cikin ƙwaƙwalwata tana shaida mini an samu baƙon haure a yankina.
Ba tare da na fita ba na yi surkulle na aika Banah can gaɓar ruwan,bai dawo ba sai da gari ya yi haske sai ga shi saɓe da wata mata.

Kan tabarma ya shimfiɗe ta,kallo ɗaya na yi mata tal na ji ƙaunarta ba don komai ba sai don na hango tabon ruhaniya a jininta.

Fuskarta na shafa nan take ta buɗe idonta,sai kuma ta tashi zaune tana mai kallona da kuma inda take.

“Su wane ne ku? ” ta yi tambayar tana ajiye idonta kan gado inda na shimfiɗe jariri.Da sauri kuma na ga ta miƙe tana cewa “me yasa har yanzu ba a yanke cibi ba?”

“Ban san ya ake yi ba” na bata amsa.

“Bani wani abu mai kaifi” ta furta,na zaro wuƙata na miƙa mata,da ita ta yi amfani ta yanke cibin kafin kuma ta ciri suturar jikinta ta kulle daidai wurin da ta yanke ɗin.

“Gefen cikin jaririn duk yayi baƙi saboda mahaifa ta taɓa shi,a kawo ruwa na yi masa wanka” ta sake faɗa .
Chapter 20 · 0% Book details