← Book details Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 26

Sashe 13

Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangaren Momy kuwa shiru har yanzu ba ta ji ihun A'ishah ba ,ta yi zaton shegen duka Mansur zai lakaɗa mata.Ganin haƙar ta ba ta cimma ruwa ba yasa ta tashi ta rufe ƙofa da key,kayan jikinta ta cire ta ɗaura wani jan ƙyalle a ƙugu.
A cikin jakkar kayanta ta fiddo wata ƙaramar tukunyar laka mai ɗauke da layu da sauran abubuwan shirka sai kuma wani bokitin roba fari mai ɗauke da korayen ruwa,nan ta fara yin surkulle a nan take hayaƙi ya turniƙe ɗakin ba ka jin komai sai hucin narkeken kwaɗo da kukansa.
Ta ɗauki lokaci da dama bisanin ta tsaya,murmushin mugunta ɗauke a fuskarta ta ce “ A'isha tun da ki ka yi sanadin shigar ɗana ƙungiyar asiri wallahi ke ma sai na gulala miki,sai kin gwammaci kiɗi da rawarki.Da ni da ke shege ka fasa” ta gama faɗar haka ta buɗe bokitin nan fa kwaɗon nan ya yi tsalle ya fito kamar mai jira.
Shegun idonsa tulu-tulu sai faman juya su yake ya na ƙoto.Ba tare da jin tsoro ba Momy ta shafi kansa ta na mai cewa “na wakilta ka a matsayin mai ɗaukar fansata,ina so ka fitini A'isha cikin mafarki da kuma zahiri ka zame mata hawainiya ka na sauya kala kamar yadda aka bani Kambunka” ta na zowa daidai nan ta furta wasu surkulle a take ya ɓace bai bayyana ko ina ba sai a ɗakin A'isha.

Ta na zaune kan gado kunnenta maƙale da waya ta na cewa “wallahi Fatimah in faɗa miki har yanzu ma Mansur ya ƙi yin wanka,ban san dalili ba in kuma na yi magana ya yi fushi”
Can ɓangaren Fatimah ta ce “to ke kamar ba mace ba,ki rasa dubarar da za ta sa yayi wankan? Kawai ki bari sai ya na kwance ki cika bokiti da ruwa ki zuba masa ai doli ya yi wankan ”
“Katifata ta jiƙe?”
“Ai ta na da leda”
“Ok to zan jarraba na gani” sun yi hira sosai bisanin ta kashe kiran, lokacin ƙarfe takwas na dare bai gota ba.
A'isha ta sauko ƙafarta ƙasa da niyyar zuwa toilet sai ta ji wani bala'in sanyi tamkar ƙanƙara,“innalillahi!” ta fusrta da mugun sauri a take kuma ta ji normal .
Toilet ta shiga ,ta hau WC kenan ta fara jin kukan kwaɗo ta saki ihu ta fito a guje sai kuma ta ci karo da Mansur ya shigo.
Ko tambayarta bai yi ba lafiya take ihu ya zube kan bed,saboda ya gaji sosai ya sha yawo a gari ko zai samu ƴan mata huɗun da aka buƙata sai dai ko guda bai samu ba.

Baccin da ya fara da ninshari ya saka A'isha da ke can takure saurin dubansa,shawarar Fatimah ce ta zo mata a kai.Da mugun sauri ta fita waje ta ciko bokiti da ruwa ta malala masa a jiki.Hargowar da ya yi ya saka A'isha sakin bokitin ta na mai dafe ƙirji.

★AYODELE

Duk yadda na so in danne muradina akan sanin tarihina kasa wa na yi.Bayan mun gama cin abincin dare na ce “Momah wai mine ne sunan Abbana? Na ga ko lokacin da na yi makaranta Ayodele kawai ake kira na” shirun da ta yi ya saka ni ci gaba da cewa “ko dai shegiya ce ni banda uba?”
“Da ubanki Ayodele! Jarumi mai zubar da maza ko a fagen yaƙin wasa.Ke ɗin sauraniya ce ɗaya tamkar dubu,a kaf cikin ƴaƴansa maza da mata,manya da ƙanana ke ce ƴar baiwa” Momah ta faɗa wanda a ƙarshe sai da ta saki murmushi.
“To ya na ina? Mi yasa ba mu rayu a tare ba?”
“Don na tseratar da ke daga uƙubar da ababen bauta ke shirin tsoma ki yasa na gudo” ta bani amsa ta na mai kallon cikin idona, ta ci gaba da cewa “ko da na ji kin ambaci sunan Lassey na fahimci lokaci ya yi da za ki san tarihin ki,sai dai fa ba komai zan sanar da ke a yau ba sauran sai ranar birthday ɗin ki”
Cike da jin daɗi na matso, Momah ta saki murmushi wanda a cikinsa ina iya hango tsantsar farin ciki wanda ban san mi ya wanzar da shi ba sai dai na fi alaƙanta shi ƙila ta na son mahaifina irin sosai ɗin nan.

Sai da ta jawo ni jikinta kamar wata ƙaramar yarinyar,kaina na kan cinyarta hannunta kuma na shafa ƙananun kitson da ta yi min.
Momah ta ce “kamar yadda na shaida miki ke sarauniya ce to mahaifin ki shi ne Sarkin Victoria Falls inda ya gaji sarautar ne a hannun Yayarsa na manta sunanta ”
Da mugun sauri na ce “ Déborah ” ambaton sunan ya saka ƙwan lantarkin ɗakinmu fashe wa ji kake ɗuuuu.
Momah ta zabura ta miƙe tsaye,“wa ya faɗa miki sunanta? Wa ya ce miki ana ambaton sunanta a ko ina? Da na ce miki na manta a tunanin ki gaske manta war na yi?” Momah ke faɗa cikin wata irin murya wacce ba ita na santa da ita ba,idonta kuwa wani irin haske suke fitar wa kamar an kunna glov har wani canza kala suke.
Jikina ne ya ɗauki rawa ainun, musamman da ƙofofin gidanmu suka fara yin wata irin buga wa su rufe kansu su buɗe ji kake faaa-faaa!
Rufin ɗakinmu kuwa kamar zai kware har ɗaga wa sama yake,wata da ban manta inda na ɗora ta ba na lalubo tare da ƙoƙarin kunna fitila ita ma ta yi bindiga ta fashe har ɗiyan hanjinta da garin batirinta na ji a hannuna.
Tashin hankali,gobarar gemu Momah ta canza Yare ta shiga suratai.In ba gizau idona ke min ba wasu fararen siffofi ne ke faman shigo wa ɗakinmu tamkar duniyar fatale.........

A nan kawo ƙarshen free page,duk wacce ke son complete za ta biya 800 ta akwatin nan
2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank
sai ki tura shaidar biya ta WhatsApp +22795045822

MRS SADAUKI NIJAR 🇳🇪
[28/04 13:15] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCRW☀️
____________________________________________

01

Cikin duhun dusar ƙanƙara wata mata mai ƙusumbi ke ta ɗangala sanda cikin sauri har ta isa wani ƙaton kogo mai cike da hayaƙi kamar an yi gobara.Tana shiga kogon ya fara rawa yana fitar da wani sauti,baƙin bargon da ta luluɓe kanta da shi ta sauke kan kafaɗunta hakan ya bayyanar da shafafar fuskarta wacce babu ido,babu tsinin hanci sai iya baki kawai.Bakinta ta buɗe tana yin wani gurnani mai fitar da magana cikin wani yare na ƙarnin baya “ uleja naho kajulu ramhakaya fyayal!” cak kogon ya tsaya da rawar da yake tare da ɗaukar wani irin shiru kamar mutuwa ta ratsa,babu jimawa kuwa wasu fararen halittu suka fara shawagi ko ta ina.

Da sauri ta zube kan gwiwanta tana mai buga gundulalun tafukan hannunta a ƙasa tana mai daɗa furzo wasu kalaman.

“Za ki iya gabatar da abin da ke tafe da ke” wata murya ta ratso iska ta bata umarni.

“Naomi!” ta furta cikin rawar murya.

“Alƙaluman doka sun riga da sun ƙafe babu wani canji da za mu iya yi miki” aka bata amsa.

“Ita ɗin yarinya ce ƙarama ƙwaƙwalwarta ba za ta iya ɗaukar wannan hatsabibin tashin hankali ba” tana gama rufe bakinta wata tukunyar ƙasa ta faɗo a gabanta ,“ki bata waɗannan ruwan ta sha daga nan komai zai tafi kan tsari”

Tukunyar ta ɗauka kafin ta gyara luluɓinta sai kuma ta fito,bai wuce tako uku da ta yi ba sai ta furta wani furuci wanda ya haifar da wata hatsabibiyar guguwa tashi ta zo ta zagaye ta tana fitar da wani iska,sannu a hankali guguwar ke daɗa yin sama da ita a haka ta ɓace ɓat kamar walƙiya ba ta bayyana ko ina ba sai a ƙofar gidanta.

Ina zaune ina ƙulla garin magunguna na ji motsi,da sauri na ɗago kai sai na hangi Maa na daidaita rufin ƙyauren gidanmu.Murmushi ne ya wanzu a fuskata ba tare da na ce mata komai ba na ci gaba da kallonta har ta ƙaraso ta zauna kusa da ni tana mai miƙo mini tukunyar hannunta.Na karɓa,sanyin haɗi da wani shock suka ratsa ni yayin da na ji kwaɗayin shan ruwan ciki.Baki na kafa na soma shan abin da ya kasance a ciki don sai bakina ne kawai ya iya tantance mini kallon kitse na yi wa rogo don kuwa ba zallar ruwa ne ba. Ina ajiye tukunyar sai na ji tamkar wacce aka yi wa wankin ƙwaƙwalwa,wasu abubuwa da suka keɓancin mahaifiyata nake son sani.

“Maa me yasa ake kiranki da mayya?”
“Saboda ababen bauta sun mallaka mini baiwar da ta keɓanta da ta sauran mutane”
“Kina nufin makantar ido?”
“Eh! ”
“Amma ai kina gani duk da babu gurbin ido a fuskarki ”

“Naomi??” muryar ƙawata ta katse zaren tambayoyin da nake yi wa mahaifiyata wacce ta kasance jigona,bango abin jiginata.

Miƙewa na yi da sauri ina ƙara gyara zaman fatar dabba wacce ta suturta tsaraicina ina mai duben Debora wacce ke sanye da wani tsohon bargo duk ta yane jikinta da shi.Murmushi ta sakar mini kafin ta yi mini alama da hannu,Maa na duba ina mai cewa “zan yi wa Debora rakiya ne”

“To kar ki jima saboda lokacin zuwa farauta ya kusa” Maa ta bani amsa,ba tare da na ce komai ba na kama hannun Debora muka fito ƙofar gidanmu wanda ya kasance na kara.

“Ya meke labari?” na tambaye ta .
Kamar munafuka ta yi ƙasa da murya ta ce “zo mu je na nuna miki wani abu” sai kuma ta fara ɗan gudu-gudu tana nufar bayan gari yayin da ni kuma nake take mata baya har muka isa bakin Teku .Da wani irin kallo na bi ta da shi ina mai cewa "me kuma za mu yi a nan?”
Chapter 13 · 0% Book details