← Book details Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 26

Sashe 23

Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta dire kalamanta sannan Banah ya ɗago,idonsa sun kaɗa sun yi ja kamar na baƙin maye.Aljana ZAƘUMA ta soma saukowa daga can saman ta zo dab da shi ta na hura ƙirjinsa wanda ya fitar da sawun haƙoranta,sai kuma ta ci gaba da cewa “a jefa jiragai cikin ruwa domin fara saye da sayarwa tsakaninku da wasu garuruwa,ta wannan hanya ce zan samu yadda nake so” tana gama faɗar haka ta cillo shi tsakiyar gari.Bai ma koma can gida ba ya wuce gaɓar ruwa,sai ya tarar da manyan jiragai guda biyu.Tsaye yayi ya lumshe ido tare da soma yin magana da ruhikan ruwa,bayan sun amsa masa ne ya tsaga yatsansa jini ya zuba a cikin ruwan da kuma jiragen.

★Naomi

Bayan fitar Banah kalar nawa tsafin na yi don binciko su wane ne suka fara yi mini zamba cikin aminci,sai dai babu wanda aka nuna mini fuskarsa illa aljana ZAƘUMA.Banda ilimin tarihi wannan yasa ban san wace ce ita ba,haka na fito na samu Ummilo na tambaye ta.

“Babu matsafin tarihi a wannan yanki naku?” ita ce tambayar da ta yi mini.

Na ce “akwai sai dai mun yi kare jini,biri jini da ita kwanan baya”

Ta ce “ke ce shugabar duk wani da ke garin nan,don haka ki aika kawai ta zo” na yi shiru na wani ɗan lokaci kafin na ga kuma eh ta yi gaskiya.

Takarda na nemo da tawada na soma yin rubutu,bayan na gama sai na dinga murza ta ina yin furucin tsafi a hankali babu jimawa kuwa takardar ta fita daga hannuna ta yi sama.Ido na birkice ta yadda komai zai wakana ina gani,cikin aminci Deborah ta samu wasiƙar na yi tunanin ba za ta zo ba sai ta bani mamaki kuwa yadda ta ɗauko hanyar zuwa nan tana tafe iska na ƙara yin gaba da ita.

Tana isowa ciki sai na ga ta yi tsaye tana kallon Ummilo kafin da sauri ta buɗe kuɗin da ke rungume a ƙirjinta.Sai ta rufe shi tare da sake kallon Ummilo cikin wani irin yanayi ,kamar wacce ba ta son taka ƙasa haka ta ƙaraso tare da yin tsaye.

“Ranki shi daɗe ga ni na samu saƙonki ne a yanzu” ta faɗa cike da ladabi,sai kuma na ji babu daɗi yadda ta zubar da duk wata dangantaka da ke tsakaninmu ta bani matsayin shugabarta.

Da ido na yi mata nuni da ta zauna,ta cire takalminta na fata ta zauna tare da maida hankalinta a gare ni.

“A cikin tarihi wace ce aljana zaƙuma?”

“Aljana ce mai matuƙar santsi da farin fata,tana ɗauke da kambun Maitar shan jini.Lokutan da ta fitowa shi ne dare musamman wuraren jeji ko kusa da rijiya.Tana jan hankalin mazaje musamman maharba don su ne suka fi shiga jeji,tana fitowa cikin siffar barewa haka za ta yi ta wasa da hankalin maharbi har sai ya faɗa tarkonta sai ta ja shi izuwa duniyarta” Deborah ta faɗa tana mai buɗe littafinta sai ta nuno mini hotonta,kallo ɗaya na yi masa na kawar da kai.Sosai ta fito a siffar mayyar shan jinin kuwa don bakinta kaca-kaca yake da jini.

“Kika ce maharba sun fi shiga tarkonta ?” na tambaya.

“Eh haka tarihi ya zo da shi”

“Meke faruwa bayan ta kama mutum?”

“Tana kai shi wani kogo ne,sai ta basa zaɓi biyu.Na farko zai bauta mata,in kuma ya ƙi zaɓi na biyu shi ne za ta kashe shi”

Ummilo na duba ina mai cewa “dukkan alamu sun nuna ita ce ta zo yau don har yayyafin jini aka yi”

“Hakan na nufin tana son jan ra'ayin wasu mazajen ne ,don haka mu zama cikin shiri” Ummilo ta faɗa .

Deborah ta girgiza kai tana mai cewa “ Aljana ZAƘUMA ba ta taɓa bayyana a wurin da ba a ambace ba ko kuma sunan ɗaya daga cikin waɗanda ke baƙin tsafi da ita.Tun da kuka ga ta zo to tabbas a garin nan akwai mai yin aiki da ita”

Da wani mugun sauri na dube ta,a cikin ƙwayar idonta na hango tana zargin mijina Banah da wannan ɗanyen aikin.Ban san me ta gani ba ita a nawa idon sai ci gaba ta yi da cewa “ta yiyu kuma wucewa ne kawai ta zo yi,don haka za ki iya yin watsi da lamarin mu gani in za ta sake dawowa”

Numfashi na furzar tare da jinjina kai,Ummilo ta karɓi littafin tarihin tana mai cewa “ina mugun son labarun tarihin ƙarnin da ya wuce musamman a kan maita,shin a page lamba ta nawa ce zan samu tarihin Mayu da kuma yadda suke rikiɗa daga bil'adama zuwa dabbobi?”

Deborah na shirin yin magana Banah ya shigo hannunsa riƙe da manyan kifaye,da dukkan alamu kuma ya ji tambayar da Ummilo ta yi duba da yanayin yadda fuskarsa ta cika da tsantsar mamaki.

“Jira na zo na fayyace miki komai Ummilo ” ya faɗa yana mai miƙawa wata hadima kifin ya zo kusa da ni ya zauna sannan ya karɓi littafin tarihin ya mayar wa Deborah da kayanta sannan ya kamo dukkan hannuwan Ummilo ya ce “a duk lokacin da mutum yake son rikiɗa zuwa dabba da farko zai ɗan rage tsayi sannan ya furta kalaman tsafi yana mai tsayar da ƙwayar idonsa wuri guda ba tare da ya ƙyafta ba.Bari na nuna miki ta yadda za ki gane sosai” sai ya saki hannuwanta tare da yin tsugunne ya soma magana a hankali amma duk muna iya jiyo sautin.Cak kuwa ya tsayar da idonsa suka bar motsi,babu jimawa ya koma narkeken kare baƙi ƙirin yana wani fito da harshe waje.

Duk da ni ma yau ne karon farko da na ga canjin siffa sam ban ji wani tsoro ba sai ma burge ni da lamarin ya yi na soma yin murmushi.

Cikin firhici Ummilo ta furta “ Ya Ubangijin Ka'aba ka tseratar da ni daga sharrin wannan halittar” sai kuma ta soma yin ihu tare da tashi za ta zuba a guje,ni da Deborah muka yi saurin taro ta yayin da Banah ya yi baya yana haushi cikin hassala.

Hakan da yake ba ƙaramin ƙara firgita ta ya yi ba,ni kuma lura da hakan yasa na juya na yi masa tsawa sai a lokacin kawai ya dawo cikin siffar bil'adama.

Ummilo ta soma furzo wani zance “kar ki cutar da ni Ummu A'ishah ki sani ban taɓa aikata maita ba,wacce ke maƙale a ruhina ba sayenta na yi ba kyauta ce daga wasu ruhikan da ke zuwa mini cikin MAFARKI (MRS SADAUKI akwai littafin nan na MAFARKI complet mai so zan barsa shi a 700 maimakon 1k) .Ban so ki bari in ba haka ba zan tona miki asiri na faɗa kowa ya sani ke ce mai yin Maitar dare” tana kawowa nan sai numfashinta ya tsaya cak sai da muka tallabe ta tare da shimfiɗe ta.

Deborah ta ce “ da dukkan alamu ita ma ta fito a yanki da ke maita duk da dai a yadda take furuci Maitar ba ta yi ƙarfi ba.Sannan ita wannan Ummu A'ishar tana ɗaukar siffar kare ne a duk lokacin da za ta yi maita ”

Banah ya matso yana cewa “ai da na san haka ne da na ɗauki wata siffar,amma sam ban yi haka da wata manufa ba”

Na ce “kar ka damu na fahimta,daga yau sai ka kiyaye” ya jinjina kai.

Deborah ta ce “ni zan koma,in ta farka ki ce ina yi mata sannu da jiki” haka muka rabu.



Yarima NASLAM ne kwance yana yin bacci yayinda tantabarsa ke tsaye ƙiƙam tana kallonsa sai da ta gaji don kanta kafin ta ɗaga fukafukinta ta je ta sa ƙafafunta ta ciro shi sama tare bi ta window da shi ta fita.Haka ta dinga zaga duniyar ɓoye da shi yana cikin wani yanayi wanda shi ba bacci yake yi ba kuma idonsa ba a farke ba.

Cikin wani jeji mai cike da dragon ta sake shi ,shuuu yayi kamar zai faɗi amma sam jegaran ba su bari hakan ta faru ba haka suka buɗe fukafukinsu wuri ɗaya ya faɗo a sama. Kafin kuma su kai shi kan wata lafiyayar shimfiɗa da aka yi da ganyen furen floris.

Yarima NASLAM ya ja wani dogon numfashi tare da ɗan ware idonsa,nan ne ya yi arba da sarauniya Naomi cikin shigar ganye,ta rufe ƙirjinta da fatar lemun zaƙi kugunta kuma ta suturta shi da bayan albasa.Gashin kanta kuwa ya ci ado da ganyen lemu,tafiya take yi cikin yanga da jan hankali har ta zo gare shi.Kan shikinsa ta kwanta tare da yi masa rumfa kafin wasu lamurra su biyo baya waɗanda suka kusan sheƙa shi lahira.Yana gama samun nutsuwa ya farka daga baccin,a kan shimfiɗarsa ta asali ya samu kansa ƴar tantabarsa na can gefe tana bacci.

Ya dafe kansa yana jin wani irin takaici na rufe shi,saboda shi babu wacce ya tsana irin aljanar mafarkinsa.A gajiye kamar wanda yayi mu'amalar a gaske ya ƙoƙarta ya tashi tare da shiga toilet,sai dai fa babu ruwa ba ciki babban bokitin ruwan ba.Ya ja tsuki ya fito kafin ya soma ƙwala kiran sunan jakariya Ali,dama ɗakinsa yana kusa da nasa babu jimawa kuwa ya shigo hannunsa riƙe da sharɓeɓiyar takobi duk a tunaninsa farmaki ne aka kawo musu.

Turus yayi ganin iya yariman ne kawai a ɗakin,ya yi saurin ajiye takobin yana mai cewa “ranka shi daɗe me kake buƙata?”

“Babu ruwa a banɗaki” yarima ya faɗa yana jin ƙyanƙyamin kansa,da sauri jakariya Ali ya fita babu jimawa ya dawo jaye da baro an lodo ruwa a ciki.Banɗakin ya shiga ya juye ruwan kafin ya fito,sai a lokacin yarima ya shiga sai ya ga hatta bahon wankan Ali ya cika masa shi da ruwan.

Kwanon da ake zuba ruwa a ciki domin yin alwala ya ɗauka ya soma wanke hannunsa sau uku bayan ya ɗauki niyyar wankan.Daga nan yayi ɗahara sai ya wanke kansa tasss kafin ya game jikinsa duka,daga ƙarshe ya kurkure bakinsa ya kuma yi shaƙar hanci.Sai a lokacin kawai ya ji nutsuwa ta ratsa shi sai ya shiga bahon wankan ya kwanta a ciki,tunanin gimbiya A'ishah yake son yi amma da zarar ya fara cankar surarta sai fuskar Naomi ta zo ta yi fakan-fakan a dole ya haƙura ya fito ya ɗaura alwala ya zo ya fara yin sallar nafila.
Chapter 23 · 0% Book details