← Book details Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 26

Sashe 5

Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wunin ranar haka muka yi aiki sam babu walwala har Fatimah sai da ta lura kamar mun samu saɓani.Ta yi tambayar duk muka ce mata ba komai,wurin cin abinci ma haka A'isha ke ta min kallon ƙasa-ƙasa ban san mi take zargi a kaina ba har mu ka zo kwanciya.
Addu'o'i na ga ta na ta yi na neman tsari,sannan alamu sun nuna a tsorace take don motsi kaɗan sai ta zabura.Kasa haƙuri na yi na ce “ A'ishah ina son yin magana da ke”
Fatimah ta kalla wacce ta sharar bacci bisanin ta ce min “to”
Na saki wani murmushi sannan na ce “ki na tunanin ko wani na gani zai cutar da ke zan bari ballantana ni da kaina na cuce ki? Ban san zargin mi kike yi a kaina ba,amma ki sani ruhin Ayodele tsarkake ne .Burinsa kullum ya kawar da mugunta da masu yin ta,na san abin da ya faru a unguwarmu da kuma na mutumen nan sun saka miki shakku a kaina”
Ta ja wani dogon numfashi sannan ta ce “wallahi ni lamarin ki ne ya fara bani tsoro,abubuwa kike kamar ƴar autar aljan.Idonki fa har canza kala suke,kuma ba zan ɓoye miki ba wallahi na fara jin tsoron ki”
Na ƙyalƙyace da dariya na ce “wallahi ba muguwa ba ce ni ! Kuma ban san mike faruwa da ni ba.Abu guda nake so ki saka a ran ki shi ne Ayodele amanar A'isha ce”
Wani gamsashen murmushi ta sakar min ta ce “har na ji zuciyata wasai,yanzu kam zan yi bacci cikin aminci”
Sai da mu ka ɗan yi hira bisanin ta ɓingire bacci,na dube su cike da so da ƙauna irin ta jini.

Ina shirin yin kwanciya na ji an kira sunana “Ayodele?” na waiga ban ga kowa ba,sai na yi tunanin ko kunnena ne bai ji min daidai ba.Sai dai da mamakina haka aka sake kira a karo na biyu,kawai sai na fito.

Ci gaba da kiran sunan nawa aka yi,inda sautin ke fito wa na dinga bin direction ina ta tafiya har na ɓullo wata kwana.Nan na yi kiciɓis da allon sanarwa,sunan *GIDAN GAWA* ne ɓaro-ɓaro da manyan baƙi,a ƙasa kuma hoton gawa ne naɗe cikin farin likafani.

Waige-waige na fara ,har zan koma na ƙara jin sautin sunana,muryar ya ta namiji ce ba mace ba.Ɗakunan da aka tanada don ajiyar gawa na nufi na mazan,ƙofar da kanta ta buɗe hakan yasa na kutsa kai.

Ƙyalƙyal ! Aka kece da dariya,da sauri na fara dube-dube don tantance shin cikin wane akwatin ne ake dariya.
“Ga ni nan” na ji ya faɗa a bayana,na juya na yi tozali da mutumen da A'ishah ke ban labari an maido gawarsa.
Ido cikin ido muke kallon juna da shi,bisanin na ce “lafiya ka kira ni izuwa nan?”
“Kambuna nake so ki ban”
“Ba zan bayar ba doli ka mutu kamar sauran da ka kashe”
“Ki bani cikin lalama ko kuma na gayyato miki shugabanmu”
“Au! Har shugaba gare ku? Na tambaye ka mi yasa kuke son yin mugunta? Don me ba za ku zauna cikin duniya normal ba kamar kowa?”
“Saboda duniyar ɓoye ta matsafa ta fi daɗi,za ka sha jini ka yi ta siddabaru ka na tsoratar da mutane cike da nishaɗi ”
Hira ya fara yi min ta yadda suke kama kurwar mutum da kuma yadda suke yi in su na son bai wa mutum tsoro,hakan ya shagaltar da ni sosai sam ban fargaba sai mugayen esprit na ga duk sun cika ɗakin.

Ruhika ne na maras imani,wasu ma daga maƙabarta suka zo nan don taimakon ɗan uwansu.Kewaye ni suka yi,ba na ganin fuskokinsu.Wasunsu tamkar innuwa,wasu kamar dunƙulalen baƙin hayaƙi,wasu kuma cikin siffar fatalwa ne da farin likafaninsu.

“Auwushhh tangarrsinn,mahulujaaa.An yarhihum khaaaaa!” shi ne furicin da na samu bakina ya na furta wa,duk a tsorace suka ja ba shi kuwa tuni ya koma cikin akwatinsa.Idona na rufe na ci gaba da yin wani Yare ina yarfa hannu,a take wani haske duk ya game ɗakin wanda rufe wa idona bai hana ni ganin halin da suke ciki ba.
Tuni duk suka tsere suka bar ni da shi,akwatin da yake ciki na ɗora hannuna akai ya fara ihu ya na “cewa ki yi haƙuri zan tafi wallahi na yi miki alƙawari gobe zan bar gidan gawar nan zan je na kwanta kabar....” bai ida kai furucinsa ba wani haske ya fito daga bakina ya daki goshinsa tsit ya mutu a yanzu kuma na tabbata ko fatalwar ba zai iya yi ba.

Kaina yayi mugun sarawa,na dawo garas da sauri na fito waje sai kuma na ci karo da mai gadin wurin.“Wace ce ke?” ya jefo min tambaya,murya na ɗan rawa na ce “dama... Dama!”
Sai ya saki murmushi ya ce “yi tafiyar ki” ban san dalilin shi na yin haka ba amma sosai na ji,domin muddin maganar ta yi nisa ya tara min mutane dole a ɗora min Ayar tambayar mi ya kawo ni gidan gawa a wannan tsohon daren.
Ko da na koma ɗaki sai da na yi tunani bisanin bacci ɓarawo ya ɗauke ni.

Washegari bayan duk mun kimtsa na ga A'isha sai murna take,ban yi ƙasa da gwiwa ba na tambaye ta “wai farin cikin na mine?”
“Mansur zai zo ɗaukata,kin ga daga nan sai mu aje ki gida” ta ban amsa.
“Au haba? Fatimah ba ta zo da babur ba?”
“Ya samu matsala a jiya hanyar mu ta fiddo anko sai ta barsa wurin mai gyara”
Mu na tsaka da hira aka kirata,cike da murmushi ta ɗauka bisanin ta aje wayar ta ce “har ma ya iso mu je”
Sai da muka fito ne muka haɗe da Fatimah wacce ke zaune ta na shan love.Bakin ƙofar asibitin muka fita ,idona ya sauka kan wata ƙatuwar mota baƙa wuluk mai taya a baya.
A'isha ta buɗe mana gidan baya muka shiga ni da Fatimah yayin da ita kuma ta shiga gidan gaba.
“Baby ga ƙawayena da nake baka labari ka rage masu hanya” cewar A'isha .
“A gaishe ku fatan duk ku na lafiya?” ya faɗa cikin muryarsa irin ta siraran maza ,duk muka amsa da lafiya lau.
Ya dubi A'isha ya ce “ya maganar zuwa gidan abinci kenan?”
“Mu je mana ai su ma za su ji daɗi,ko ya kuka ce ƙawayena?”
Fatimah kawai ta amsa mata,ni kuwa na lula duniyar tunanin ta yaya ya samu kuɗi har haka cikin ƙanƙanen lokaci in dai yadda A'isha ta bamu labari ne Lagos ne ya je to tabbas akwai lauje cikin naɗi.

Ina cikin wannan tunanin har muka isa , restaurant ce ta sai wane da wane don ni ban ma san da zamanta ba.
Yadda aka tarbe mu kawai ya isa mu gane Mansur sananne ne a wurin.
Shi ya zaɓi abin da za a kawo ma A'ishah yayin da ya nemi mu zaɓa da kanmu,amma sai A'ishar ta nuna masa ko wurin aiki cikin plate ɗaya muke cin abinci don haka nan ɗin ma ba za a ware mu ba.
Shiru yayi ya na ɗan tunani,bisanin ya bai wa serveur ɗin umarni kan yayi yadda ta ce.Lafiyayen abinci ne,haka muka fara ci hankali kwance ba tare da wani tunani ba shi kuwa Mansur duk ya zama wani iri.
Tamkar wacce aka sa ƙugiya ana ƙoƙarin zaƙulo hanjin cikinta haka na fara ji cikina na min ciwo,da sauri na fidda hannuna na ce na ƙoshi.
Na tashi tare da tambayar masu kula da wurin ina ne toilet,aka nuna min na shiga.Amai na ta kwarara wa kamar raina zai fita,tsabar azaba har wata zufa ke tsatsafo min ina buɗe ƙofar toilet na yi kiciɓis da saurayin A'ishah...
[24/04 14:49] MRS SADAUKI: *FARAUTAR MAYU*

Page 5

Na yi tunanin ko banɗakin zai shiga hakan yasa na ɗan yi saurin ja baya na basa wuri.Amma da mamakina sai na ga yayi tsaye ƙiƙam hakan yasa na ɗago na dube shi.
Kamar mai son tantance wani abu haka yake kallona bisanin ya ce min “fatan dai lafiya?”
“Alhamdullah!” na amsa masa a takaice “okay!” ya faɗa tare da koma wa baya yayi tafiyar shi.Na bi shi da kallon mamaki bisanin na take masa baya,ina zuwa sai na tarar ya zauna kujerata wacce na tashi kawai sai na yi tsaye.
“Ki zauna mana” ya faɗa cike da kulawa,ban sani ba ko bai lura ba ne ya zauna a nan ɗin oho amma dai haka kawai na ji ban ra'ayin zama inda ya tashi .

“Ke ma ki zauna mana ga kujera nan,ki yi tsaye kamar wata soja?”cewar A'ishah,ganin haka yasa na zagaya zan zauna kan kujerarsa ba don na so ba don haka kawai nake jin akwai makircin da ya shirya,cikin ikon Allah wayata ta ɗau ringing,ina duba wa sai na ga sunan Momah .
Ina ɗaga wa ta ce “a ina kika tsaya har yanzu ba ki zo gida ba?”
“Momah gani nan zuwa yanzun nan” na faɗa cikin rawar murya.
“Ki na ina na ce?”
“Tare da su A'isha Momah ” na faɗa tare da mayar da wayar a hand free ta yadda za su ji abin da Momar za ta ce sai kuma na yi masu alama da su yi magana,sai dai kafin su kai ga yi Momah ta ce “ki dai yi sauri ki dawo gida sam jikina na bani babu hairan a ind....” ban bari ta kai Aya ba na kashe kiran ina muzurai “zan tafi sai gobe in mun haɗe”shi ne abin da na iya furta wa bisanin na yi tafiyata ba tare da na jira cewar su ba.

Bayan na fito daga restaurant ɗin sai na yi tsaye turus,don rasa ta ina zan bi na yi.Tamkar an sauya hanyar, lokacin da muna cikin mota lafiyayyar kwalta ce saɓanin yanzu da na tsinci kaina cikin jeji.
Chapter 5 · 0% Book details