Sashe 24
Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɓangaren gimbiya A'ishah kuwa tsakiyar dare Dadda ta tashe ta,tana shirin yin magana amma Dadda ta toshe mata baki tare da janta suka je bakin window suka yi tsaye suna fuskantar farin wata da ke wasar ɓuya cikin giza-gizai.
Dadda ta soma yin magana a hankali tana cewa “a wurin Mayu dare shi ne lokaci mafi tsaro domin farauta,duk da cewa ana iya sarrafa maita safe ko rana amma irin wannan lokutan an fi yinta a cikin siffar bil'adama yayin da ita kuma ta dare ake ɗaukar ɓoyayyar siffa.Yau zan nuna miki romon da muke sha duk dare ni da sauran Mayu na wannan Daular ”
Cike da mamaki gimbiya A'ishah ta ce “dama bayan ke akwai wasu Mayu a cikin daular nan?”
Dadda ta yi wani irin murmushi kafin ta ce “idonki za su yi matuƙar mamaki in ki ka ga wasu mutanen” tana gama faɗar haka sai ta jimƙe hannun gimbiya A'ishah tana furta wasu surkulle nan take suka sama wasu ƴan ƙananu kamar sauro tare da tashi sama suka bi ta window.....
Za ku iya fara yin payment domin shiga paid group . 500 ta wannan account:
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
Shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[28/04 13:15] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️
```MRS SADAUKI```💫✍️
FCWA☀️
____________________________________________
09
Yana ɗaya daga cikin tabi'un Mayu yin yawon dare a lokacin da mutane ke yin bacci,saboda babu dare yana ƙunshe da sirrika dayawa.Gimbiya A'ishah baki da hanci ta buɗe tana kallon duniyar ƙasa,cike kuma da burge wa da ban sha'awa take ware idonta tana kallon gidajen da aka rufe babu bismillah.Kamar misalin tukunya ce babu murfi,haka idon Mayu ke gane gidajen da ba a ambaci sunan Allah ba a lokacin da ƙafa ta tsana za a kwanta.
Suna cikin shawagin suka yi ta haɗuwa da jiragen dare na Mayu, waɗanda suka kasance na tsafi ba wai zahiri ba.
“Duk ina za su je Dadda? Ya na ga mutane cikin gwangwanin kifi?” gimbiya A'ishah ta tambayi mahaifiyarta sai dai kafin ma ta bata amsa wani jirgin na tsintsiyar tsaye ya bi ta gabansu shuuu yana ɗauke da wata tsohuwa da kuma ƙaramin yaro.
Dadda ta yi murmushi tana mai cewa “A'ishah a duniyar ɓoye abubuwan da ba za su taɓa faruwa ba ne a duniyar zahiri suke gudana a nan ɗin.Muna amfani da duk wani abu da kika sani matsayin jirgin farauta,kamar irinsu turmi,jan zanen isimi,tsintsiyar tsaye da sauransu.Ke ma in kina sha'awa ai za ki iya hawa madadin ki yi yawo kamar leda”
“To mene ne banbancinsu Dadda?”
“Sauri! In kin hau jirgi kin fi saurin zuwa inda kike so,ko ba ki lura yadda mutane ke ta wuce mu ba?”
“Na gani,amma me yasa mu ba mu shiga ba?”
“Dama ina son fayyace miki komai ne,amma yanzu da zarar wata tawagar mayun za ta wuce zan tsayar da su don rage mana hanya”
Ai kuwa babu jimawa sai ga wata tsohuwa zaune kan baƙar akuya mai ƙahonni dogaye.Dadda ta tsayar da ita tare da neman alfarma,tsohuwar ta ƙara matsawa gaba gimbiya A'ishah ta fara hawa sannan Dadda daga ƙarshe.Kamar wani babur haka akuyar tsafin ke keta hazo da su.
Gimbiya A'ishah wacce duniyar ɓoye take sabuwa a wurinta sai cewa ta yi “ita ma akuya tana cikin jerin jiragen yawo?”
Wannan karon tsohuwar ce ta bata amsa bayan ta yi ƴar dariya mai fitar da zallar tsufanta,ta ce “ jikata ita akuyar nan protector ɗina ce,suna da banbanci da jirgin dare saboda ita tana numfashi sannan kuma tana kare ni daga dukkan sharri” gimbiya A'ishah ba ta kai ga cewa wani abu ba tsohuwar ta yi ƙasa da ƙahonnin akuyar sai ta yi shuuu ta fara yin ƙasa har ta sauka a wani babban gawo wanda ya cika tanƙam da Mayu da kuma matsafa.
Girki ake yi kan wata tunkunya wacce ke da zanen ƙwarangwal ta buɗe baki.Gimbiya A'ishah ta sauko daga kan akuyar tana wani riƙe Dadda ,ita kuwa sai cewa ta yi “ wannan ita ce TUKUNYAR MAYU ( ga mai son complete na Tukunyar Mayu yayi mini magana zan yi masa discount) duk dare muna haɗuwa a nan mu ci abin da wasu daga cikinmu suka yo farauta”
Sai kuma Dadda ta ja ta suka ƙarasa,hannu ta saka cikin tukunyar da ke ta faman tiriri ta tsamo wani abu mai kamar zare amma su a wurinsu nama ne,bakin gimbiya A'ishah ta kai ita kuwa ta buɗe ta saka mata sai ta soma ci tana jin wani irin yanayi na ratsa ta.
Dadda ta saki murmushi tana jin wani sanyi na luluɓe ta,a yanzu shirye take tsaf wurin tursasa ƴarta ta auri yarima Naslam ba don komai ba don ta san a cikin tabi'ar Mayu babu kara babu jin kunya,hatta uwar da ta kawo su duniya suna iya damƙewa ita kuma babban burinta shi ne ta bayar da yarima NASLAM a dafa shi kowa ci kamar yadda yasa aka yanke wa Ummarta hukunci kisa daga kawai asirinta ya tonu ta damƙe kurwar iyayen jakariya Ali.
Bayan sun gama cin naman sai idanun gimbiya A'ishah suka ƙara buɗewa ta soma gani tarau ,babu abin da ba ta iya gani da ke jikin mutum ko dabba.Rawa suka soma yi suna zagayen wuta,duk da mutane sosai hakan bai hana ta gane wasu fuskokin ba sosai kuma ta yi mamaki kamar yadda Dadda ta ce mata tun kafin zuwansu.
Alfijir na dab da ketowa suka koma gida,ta inda suka fita ta nan suka shigo.A gajiye duk suka zube suka ta yin rankon baccin da ba su yi ba.
A ɓangaren yarima Naslam kuwa tun bayan sallar asubah ya je ya samu sarki da maganar aurensa da gimbiya A'ishah.Ya yi haka ne duk don ya bar mafarkin Naomi,ba tare da ya san alƙaluman ƙaddara sam ba su rubuta masa auren wata mace ba bayan maƙiyiyarsa.
Gari na yin haske sosai sarki ya bada shelar baikon yarima zai kasance a yau bayan sallar asar in sha Allah.
Jakariya Ali ne ya dinga taimaka masa wurin shiryawa,yana daidaita masa hullar sarauta a kai ya ce “kana ganin kun dace kai da gimbiya A'ishah?”
“Me ya ja ra'ayinka wurin yin wannan tambayar?” cewar Yarima yana kallon mai tsaron lafiyarsa Ali .
Shi kuwa kai tsaye ya ce “na ga ba sonta kake yi ba”
“Haka kuma ban ƙinta“
“Duk da haka dai ya kamata a ce ka yi dogon nazari,na fi yi maka sha'awar auren soyayya gaskiya”
“Ita ma ina sonta tun da har na damu da ita” yarima ya faɗa yana mai zuwa bakin gado ya yi zaune,jakariya Ali ya duƙa ya soma saka masa takalmi yana mai cewa “in kana son mutum bai kai sai ka faɗa ba,ayyukanka ne za su bayyana hakan”
“Ko ma dai mene ne na yanke shawarar zan aure ta,kuma ta dace da ni tun da tana da addini sosai iya wannan ya wadatar” yarima ya faɗa yana tsayar da idonsa kan tantabarsa wacce ta yi wani saƙo kamar mai sauraren hirar da suke yi.
Jakariya Ali ya juya ya dubi inda yake kallo,sai ya saki ɗan murmushi kafin ya je ya ɗauko ta ya miƙawa yarima.Ya karɓa tare da soma shafar kanta,“zan je na duba na gani in sun gama shirya wurin taron” Ali ya faɗa tare da ficewa.
Yarima ya miƙe tsaye tare da zuwa bakin window yana kallon yadda ake ta kai komo cikin masarautar.Ko ina yayi kyau,hatta dawakai an yi musu ado na sarauta .Dokinsa wanda yake hawa a duk lokacin da zai fita yayi wani irin kuka,tantabarar hannunsa ta fizge tare da fita a guje tana kaɗawa yarima iskan fukafukinta da sauri ya lumshe ido kafin kuma ya ware su yana kallon yadda ta je ta hau kan dokin,duk wannan ɗin ma bai sa ya zargi wani abu ba kawai murmushi ya yi tare da fita.
Masjid ya fara zuwa,bayan an gama sallah ne duk aka dugunzuma zuwa wurin da aka ware domin gudanar da shagalin bikin baikon.
Zinare sarki ya ware masu yawa ya bayar matsayin kyautar mun gani muna so.Ayyub wanda ya kasance mahaifin gimbiya A'ishah da matuƙar farin ciki ya shaida wa dukkan taron jama'ar ya bai wa yarima damar auren ƴarsa,duk sai aka yi kabbara tare kuma da yin addu'o'i kafin a fita zuwa can inda za a yi wasar dawakai.
Ta madubin tsafi Dadda ke kallon komai,tun lokacin da aka yi shelar yin baikon ta shirya baƙin tsafi mai ƙarfi ta tura domin hallaka yarima.Ita dai gimbiya A'ishah cike take da farin ciki duk gajiyar nan ta jiya sai ta neme ta duk ta rasa,duk da cewa kuwa ta sha bacci sosai sai wuraren goma na safe ta farka.A bakin mahaifiyarta kuma ta ji abin da ke faruwa,sosai ta so a ce ta fita ta ga yadda komai ya wakana sai dai hakan haramun ne a masarautarsu zuwan mata a irin wannan taron.
Cikin rangaji ta ƙaraso ta zo ta yi tsaye ita ma tana kallon yadda ake wasar tseren .Wani irin murmushi ya suɓuce mata lokacin da ta ga yarima Naslam ya je kusa da dokinsa za su yi wasar tseren shi da wanda ya yi nasara akan dukkan dakarun da aka tsara wasar da su.Ita ma Dadda nata murmushin ta saki tana jin cewa saura ƙiris burinta ya fara cika don ta jefa kibiyar tsafi akan dokin yarima saboda in ya hau shi sai ya masakance.
Yarima ya hau kan doki yana mai ambaton sunan Allah tare da yin kabbara,Dadda ta ɓata fuska tana mai ɗan satar kallon gimbiya A'ishah wacce har yanzu murmushi ya ƙi barin fuskarta.
“Dadda dube shi ki ga yadda yake da ƙwarjini da cikar zati, wannan shi ne mijin A'ishah ”
“Haka ne ki yi fatan Allah yasa ya ci gasar kar ya kwabsa abin ya zama abin goranta miki” Dadda ta faɗa tana mai shafar madubin haɗi da yin wani surkulle daidai nan su yarima suka fara gudun.Ƙafar dokin ta ƙure da ido ta na shirin aika masa wata gubar tsafin kawai sai ganin bakin tsuntsuwa ta yi ya caki madubin ya tarwatse.