Sashe 15
Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Sun fusata ba za su sake yin magana ba sakamakon shirun da kika yi yayi yawa.A matsayinki na shugaba ya kamata a ce kina bada amsa ne a kai ba tare da nazari ba” ƙawata Debora ce ta yi wannan furucin idonta na kallon tsakiyar ruwa.Dukkan matsafan sun yi amanna da furucinta,ban ce komai ba sai taku da na fara yi ina ɗaga kafaɗata gefen da ke da ƙusumbi na shiga can tsakiyar ruwan.Tafin hannuna na hagu na kalla ina yin wani furuci nan take ya tsage jinina ya soma ɗiga a cikin ruwan.Duk ɗigo ɗaya ina iya jiyo wani nishi daga can ƙasan ruwa,na ɗauki kamar minti biyu a haka kafin na dakatar da zubar jinin sai kuma na soma yin magana cikin sauti ƙasa-ƙasa “joliho kuntahee namaruju kalmari hanaighar kashmuh balbilancaaaa!” babu shiri na lumshe ido jin yadda wata irin guguwar ruwa ta tashi tana tunkuɗo duk wani masarafin tsafi izuwa gare ni.
“Ya ke ƴa ga Bazuka ki sani cewa kowanne tasiri da farashinsa,sannan mu halittun ruwa ba mu taɓa mance duk wata alaƙa da aka ƙulla da mu .Za mu bai wa garinki kariya kamar yadda kika buƙata sai dai ki sani a duk lokacin da kika take dokarmu za mu bayyana miki asalin me ake kira da masifa da annoba ” wata murya da ke kama da ta macijin ruwan ta yi mini jawabi.
“Hakan ba zai taɓa faruwa ba,zan kiyaye dukkan sharuɗanku” wannan karon na bada amsa kai tsaye.
“Mu ne za mu zaɓar hadiya da kanmu,a duk sa'ilin da lokaci ya yi za mu nuna miki mutumin da muke buƙatar jininsa ta mafarkinki ”
“Na amince!”
“Sannan kuma haramun ne shiga ruwa ranar Laraba ”
“Na amince!” ina furta haka kawai sai yanayin garin ya canza ya ɗauki wani irin launin duhu amma ba sosai ba,sararin samaniya ya cika da baƙaƙen giza-gizai yayin da kuma kukan tsuntsaye da kaɗawar bishiyoyi ya tsaya cak.
“Aroroke! Aroroke! Aroroke!” shi ne abin da sauran mutanen da muka zo suka fara faɗa cikin murna saboda dukkan alamomin nan da suka bayyana na nasara ne.
A hankali na fito daga cikin ruwan ina mai fuskantar su sai duk suka yi shiru tare da sauke idonsu ƙasa don nuna girma a gare ni.
“Daga yau na sama wa garinmu suna za a dinga kiransa YANKIN MUTUWA,duk wanda ya shigo sunansa gawa ba wai mutum ba ko dabbar da ba ta wannan garin ba ta shigo na bada izini kafin a zo a faɗa mini a kashe ta” nan ɗin ma jin daɗinsu suka bayyana a fili kafin na wuce gaba su mara mini baya muka koma can tsakiyar gari inda na sa aka ƙara ƙawata gidanmu.
Kan shimfiɗar da gawar Maa ta rushe na hau tare da yin kwanciya.Ina lumshe idona fuskar Naslam ta dawo mini da wani mugun sauri na buɗe su tare da tashi zaune ina jin zuciyata na harbawa da sauri.A fili na ja wani tsuki ina jin tsanarsa da su kansu mabiya addininsa.Yatsun hannuna na murza tare da furta kalmar tsafi nan take ragayar da ke maƙale a tsakiyar iccen rufin ɗakinmu ta yo ƙasa ta zo daidai inda nake wata ƴar ƙaramar takarda na gani mai ɗauke da haruffan tsohon asiri.Ban yi wani dogon bincike ba na fahimci cewa wannan takarda daga mahaifina take,mutumin da daidai da sakan ɗaya ban yi rayuwa da shi ba.Rubutun bai da yawa a ido,amma ma'anoninsa sun isa a rubuta dogon labari.Tsam na miƙe bayan na maƙale takardar a ƙuguna,daidai ƙofar da za ta ba mutum damar shiga uwar ɗaga na zube tare da shafar wurin nan take ya ɗau wani haske yana mai bayyanar mini da jan rubutu wanda aka rubuta da jinin mahaifina.
“Finstako Bazaku enfinstako naheee” ina furta haka ƙasar wurin ta tsaye sai ga wata ƴar madaidaiciya wuƙa ta bayyana mai ɗauke da sunan mahaifina,nawa da kuma na Maa.Sai da na tsaga jinina ya ɗiga a kai sannan na samu damar ciro ta.Wani mummunan iska ne ya taso daga sama ya cilla ni gefe kafin guguwa ta fara haɗuwa daidai wurin da na ciro wuƙar.Wata siffa ce ta bayyana a gare ni,tun a kallon farko na ga ne shi ɗin mahaifina ne duba da fuskarsa sak irin tawa ce.Hannu ya miƙa mini,daga wurin da nake zuwa inda yake da ƴar tazara amma hakan bai hana ni ɗora hannuna kan tafinsa ba sai ya janye ni muka ɓata cikin iskan guguwa.Wata tsohuwar maƙabarta ce mai zubin ta kiristoci,kowanne kabari da nasa sunan.
“Wannan ce hanyar da matsafa ke bi don kawar da maƙiyinsu ba tare da sun sha wahala ba.Da zarar kin ginawa mutum kabari to lissafin mutuwarsa zai dawo hannunki ,ke ce za ki zaɓar lokaci da kuma yanayin da zai bar duniyar bil'adama zuwa ta matattu” shi ne bayanin da Abbana ya yi mini ba tare da na tambaye shi ba.
Kallonsa na yi ina mai cewa “ni banda maƙiyi ko ɗaya”
“Shi kuma Prince ɗin da kuka haɗu fa? Kin yi tunanin cewa haka kawai ne kika fita daga duniyarmu ta tsakiyar ruwa zuwa duniyar turɓaya? Ya ke ƴata ki sani daga ranar da muƙamin iko na prophecy ya fara aiki a kanki to abu na farko da uwayen gijinmu suke nuna maka shi ne babban maƙiyinka”
Shiru na yi ina nazarin furicinsa ,so nake na san ta ya aka yi Naslam ya zama maƙiyina,don na fahimci sarai a kansa ne yake magana.
“Dalilin da yasa kika zama maƙiyiyarsa saboda ta silarki ce aka yi galaba a kansa,ba don a ce ya shagala da kallonki ba to da tabbas magauta ba za su harbe shi ba” ya ƙara faɗa kai ka ce shi ke sarrafa tunanina da har yake sanin abin da ban furta ba.
“In dai duk abin da ka furta gaskiya ne,to zan so a ce a duk lokacin da yake tsakiyar fafatawa da maƙiya ya zamana ni kuma na bayyana a wurin ta yadda zan zamo rauninsa,ya gane ya kuma fahimci cewa wutsiyar raƙumi ta yi nisa da ƙasa.Ta hakan ne kawai ba zai taɓa sha'awar farmakar yankina ba”
Bai ce mini komai ba sai wuƙar nan da ya cire daga gidanta ya miƙo mini tare da nuna mini wani buɗaɗen kabari wanda a jikinsa aka rubuta sunan Prince Naslam.
Hannuna na tsaga jini ya zuba a cikin ramen kabarin,babu jimawa wuta ta soma ci balbal.Daga nan kuma kawai sai tsintar kaina na yi a ɗaki,ba tare da na san alƙawarin jini ne na ƙulla Ni da aljanai ba.
★DAULAR ABU NASLAM
Tutar daular ce aka juye alamun babu lafiya a yankin.Dakaru haɗi da hadimai sai faman kai komo suke yi suna jiran tsammani na farfaɗowar jagoransu,madubi kuma gun babbar masarautar musulinci.
Sarki Haroon mahaifi gun Prince Naslam a tsaye yake a wata kusurwa wacce ta yi daidai da alƙibla.Idonsa a rufe suke,yayin da kuma ya haɗe hannuwansa wuri guda domin nuna ladabi ga Ubangijinsa.A hankali yake motsa bakinsa,duk da ba a jin furucin amma za a iya fahimtar abin da yake cewa shi ne “Ya Hayyu! Ya Ƙayyum! Wato ma'ana Ya Rayayye! Ya dawamamme!” iya shi kaɗai yake furtawa bai dakata ba kuma sai da ya ji murya jakariya Ali yana cewa “shugaba cikin amincin Ubangiji ka'aba Prince Naslam ya dawo hayyacinsa ”
“Shukuran Ya Rabb!” shi ne kawai abin da ya furta kafin yake juyowa yana kallon Ali wanda duk ya fita hayyacinsa tun ranar da suka dawo daga yaƙin tsibirin Mayu.
Murmushi sarki ya sakar masa wanda ya haifar masa da samun wata ajiyar zuciya nan take kafin cike da girmamawa ya ce “yarima na buƙatar ganinka”
“Mu je!” ya furta kafin sarki ya shiga gaba shi kuma Ali na take masa baya har suka shiga ɗakin yarima Naslam inda yake kwance yayin da kuma tsoho Barham ke kula da lafiyarsa.
Suna haɗa ido da mahaifinsa ya yi saurin yunƙurowa da niyyar tashi,sai dai raunin ƙirjinsa ya dakatar da shi da wani mugun sauri ya koma ya kwanta yana mai yin wani irin nishi.
Barham ya ce “na yi nasarar cire dattin garin mahalbiya,nan da kwana uku in sha Allah zai iya tsayuwa kan ƙafafunsa”
Sarki ya ce “Ubangin ka'aba ya albarka ce ka ya ƙara maka ɗimbin ilimin sanin magani”
Barham ya amsa da “ Amin ” kafin kuma ya yi wa Ali alama suka fice suka bar sarki shi da yarima.
“Ya jikin naka?” sarki ya tambaye shi yana mai dafa goshin Naslam ɗin.Maimakon ya basa amsar tambayarsa sai cewa ya yi “Abih aljanar da nake baka labari ita ce silar raunin da aka ji mini,na gan ta a zahiri tana tsaye gaɓar teku sanyen da kayan arna,ƙusumbin tsutsotsi maƙale a bayanta,idon sharrinta na fitar da gubar tsafi ”
“Naslam na sha faɗa maka ita ɗin ba aljana ba ce,wakiliyar duk wasu sheɗanun Mayu da matsafa ce.Ita ce aka damƙawa kundin prophecy domin cika wani baƙin ƙuduri nasu.Amma da ka gan ta wane yunƙuri ka yi?”
“Abih ta ya zan iya yin wani abu? Yanzu dai ina so a shirya dawakan yaƙi su ƙara komawa can domin binciko mini ita”
Shiru sarki yayi kafin kuma ya fita,cike da bayar da umarni ya sa aka shirya dawakai majiya ƙarfi da kuma dakarun yaƙi . Jakariya Ali shi ne ya shugabanci tawagar,sai dai sama da awa biyar suka kwashe ko kusa da ruwan sun kasa zuwa saboda tsantsan tsaron da aka shimfiɗa musu a dole ya jawo su suka dawo gida a lokacin tuni yarima Naslam ya kasa sukuni ya sa an kawo masa farin ƙyalle haɗi da abin zane haka ya zauna ya zana Naomi kai ka ce ta gasken ce .
Ido ya tsura mata cike da tsana yana tambayar kansa a zuci ‘ wace ce ke? Me yasa tun da na shiga zangon balaga kika addabi rayuwata?’
Jin an banko ƙofa yasa shi barin zancen zucin tare da maida idonsa kan ƙofar shigowa.Jakariya Ali ne sanye da kayan yaƙi,zanen ya fara kallo kafin ya cewa yarima “babu wata nasara dangane da tekun can,amma wai don Allah me yasa ka damu? ”
Cikin zafin rai ya ce “aljanar mafarkina ce”
“Amma fa ita ce ta cece mu lokacin da Mayu suka fara sarrafa tsafi ” jakariya Ali ya faɗa .