← Book details Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 26

Sashe 19

Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya yi wani murmushi kafin ya ce “na gode da tunatarwa ” sai kuma ya maido dubansa gare ni yana jefo mini kallon so da ƙauna ya ce “ ki sa a ranki Banah yana sonki kuma zai zauna da ke ko da kuwa dukkan jikinki ciwo ne”

Wata ajiyar zuciya na sauke jin furicinsa ,kafin na dubi Deborah na ce “ba zan so ki tsani Banah ba saboda shi ɗin murfin rufin asirina ne.Deborah ki sani zuciyata ba za ta taɓa lamunta rashin miji ba”

Kai ta girgiza mini tana mai cewa “Banah ba mijinki ba ne,in ma dai akwai shi to ba na ce a jinsinmu ba ne don kuwa tarihi bai nuna hakan ba”

Da sauri Banah ya zo ya shiga tsakiyar mu yana mai ɗan ture Deborah ya ce “dama ba tun yau matsafan tarihi ke ƙirƙirar ƙarya ba domin cimma manufarsu” kallona ta yi,sai na kawar da kai ita kuwa da sauri ta fita.



“Ba zan taɓa lamunta ki auri ɗan maƙiyiyata ba,ki sani cewa ko bayan raina kika auri Naslam ban yafe miki ba“ Dadda ta faɗa tana yi wa A'ishah wani mugun kallo.

“Ki haƙuri Dadda amma ina son yarima fiye da raina,ki sani cewa in kika hana ni aurensa to tamkar kin yi mini shamaki da duk farin cikin duniya” A'isha ta faɗa tana hawaye.

Dadda ta yi mata mugun kallo kafin ta ce “da dukkan alamu har yanzu ba ki warke daga cutar haukan naki ba,ɗan matsafiya kike sha'awar aure ki haɗa zuri'a da shi?”

Ta dubi mahaifiyar tata da jajayen idonta kafin ta ce “ Dadda babu wanda ya tabbatar cewa Ummi Naslam na yin tsafi,kawai ƙage aka yi mata wannan dalilin ne ma yasa ta bi dare ta bar masarautar nan”

“Wato ƙage na yi mata? Don ubanki da idona na gani tana tsafi.Tashi ki ɓace mini ko na sabauta ki ” ta ƙarashe cikin tsawa,da wani irin sauri kuwa A'ishah ta fita daga ɗakin direct can baya ta nufa inda tantabarun yarima suke.Tana zuwa ta yi tsaye tana kallonsu yadda suke ciyar da junansu da kuma yadda suke yin wanka, murmushi ta soma yi tana jin sonsu ba don komai ba saboda yadda ta san muhimmancinsu a gun yarima.Daga bayanta ta ji muryar Barham yana mai cewa “har sai yaushe ne za ki bayyana asalin fuskarki? ”

Ba tare da ta juyo ba ta ce “ ranar da ka bar ɓoyen taka!”

“Amma ai kin san ni da ke ba ɗaya ne ba,magani nake bayarwa domin sanin wasu tsirrai dole sai na haɗa da Magic ”

A'ishah ta juyo tana wani murmushi kafin ta ce “me yasa kake saka mini ido a lamurrana? Bayan ni ai ka san waɗansu masu ɗauke da kambun baka me yasa ba za ka takura musu ba ?”

“Ki iya bakinki ko kuma...” ta yi saurin katse shi da cewa “ko kuma me? Ka je ka sanar da sarki? Hahaha! To bari ka ji abin da har zuwa yanzu tsafinka bai nuna maka ba,hatta yarima Naslam maye ne,yana ɗauke da kambun baka ”

Cikin zafin rai Barham ya ce “ ki sani cutar kambun bakan yarima daga Ubangijin Ka'aba take ba wai ta tsafi ba ce,ke kuwa uwarki ce ta saka miki ita.A kullum cikin yin ƙoƙarina nake na ganin na magancewa Yarima cutar nan saboda na san hankalinsa zai tashi muddin ya farga”

Shiru A'ishah ta yi tana nazarin kalamansa,wai ita Dadda ce ta saka mata maitar baka hakan na nufin kenan hatta Dadda matsafiya ce? Ba tare da ta ce masa komai ba ta yi saurin barin wurin ta koma can sashensu.Sai dai tana shiga ta tarar da Dadda cikin wani irin yanayi wanda da ace normal mutum ce ita da tabbas har taɓin hankali za ta iya samu.

Dadda ce cikin siffar maciya tana a tsaye gaban madubi idonta a rufe tana furzo kalaman tsafi tana haɗawa da sunan mahaifiyar yarima Naslam.
A'isha ta yi tsaye tana kallon cikin madubin wanda yake ta fitar da tiriri tamkar an ɗora shi kan wuta har wani hazo-hazo ke tashi.

Ummi ce ta gani wato mahaifiyar yarima Naslam tana zaune kusa da ruwa da alamu so take yi ta wuce amma ta kasa shiga ruwan.A kallon farko da za ka yi mata za ka fahimci cewa kaf illahin jikinta dabaibaye yake da mugun baƙin tsafi.

Dadda ta yi wata mahaukaciyar dariya tana mai fito da harshe waje tana yin wani tsafin A'isha sai gani ta yi Ummi ta faɗa ruwan,ba ta san lokacin da ta fasa ƙara ba ta ce “Ummiii?” hakan ya jawo hankalin Dadda matsafiya ta kuwa juyo da kanta ta kalli A'ishah tare da juya idonta suka fitar da wani haske ya je ya shiga A'ishah nan take ta faɗi ƙasa a sume.

Dadda ta yi saurin komawa normal kafin ta je ta dubi ƴarta,hannuwanta ta kama ta soma janta ƙiii har ta kai ta kan shimfiɗa.

Wata kwalba ta ɗauko ta gubar tsafi ta buɗe tare da dangwalo maganin ta shafawa A'ishah babu jima ta buɗe idonta tarau sai dai babu ɗigon baƙi.
Dadda ta soma sarrafa tsafi babu jimawa kuwa duk maganar da A'ishah ta yi ita da Barham ta shiga tariyo kanta.Dadda ta naushi iska tana mai cewa “ wato dai mugun tsohon nan ba zai taɓa fita hanyata ba” sai kuma ta luluɓa bargo ta fice ta bar masarautar.

A ɓangaren yarima Naslam kuwa a daren ranar haka ya kasa sukuni,yana kwance yana tunanin Naomi haɗi da yin surutunsa ba tare da ya san cewa ba zanen hotonta da ke ƙarƙashin pilow yana naɗar duk wata magana da zai yi ta yadda ita kuma za ta ji komai cikin ƙwaƙwalwarta.

Sai wuraren ƙarfe biyun dare ya samu bacci mai nauyi ya ɗauke shi,mafarkin Naomi yayi.Wannan karon ba mu'amala suke yi ba,a'a takobi yasa zai sauke mata kai bayan an ce ta miƙa wuya ta karɓi shahada ta ƙiya.Yana datsa mata takobin ta yi kururuwa wacce kai ka ce a gaske ne sai ya ji abin har kunnensa.Daidai nan ya farka yana jan numfashi tare da soma yin magana shi ɗaya.

★NAOMI

Duk da ban ji daɗin abin da ya faru ba tsakanin Banah da Deborah hakan bai sa na wani damu sosai ba saboda a ganina kowanne yana da hujjar da zai kalubalanci ɗan uwansa.Ita matsafiya ce mai rubutun tarihi,yayin da shi kuma matsafi ne mai ilimin jeji don maharbi ne.
Washegari haka muka zaga gari ni da Banah a matsayinsa na mijina,kafin kuma yasa shela mutane suka taru a ƙofar gidanmu.Sabbin dokoki ya ƙara kafawa kafin kowa ya kama gabansa,haka muka zauna ni da shi ina basa labarina yayin da shi kuma ya yi mini alƙawari sai da dare sannan ya bani nasa labarin.Wannan yasa ko da daren yayi a ƙage na ce masa “ina saurarenka bani labarinka ”

Maimakon yayi abin da na ce,a'a sai ma fatar dabbar da na suturce jikina da ita da ya yane ya soma yana shirin kai hannu kan jikina na zabura sakamakon kalaman nan irin na jiya da na soma ji suna ziyartar kwanyata ba tare da na san daga ina suke ba.

“Ya Rabb! Ka taimaka ka kuɓutar da ni daga dukkan wani tarkon sheɗanu da mabiyansu.Ya Ubangijin al'arshi ka bani kariya a duk lokacin da na fuskanci uƙubar mushrikai kamar yadda ka bai wa Annabinka Ibrahim.Ya Hayyu ! Ya Ƙayyum ! Ya zul...” da wani mugun sauri na toshe kunnuwana ina mai yin wata ƙara don tamkar ana ɗiga mini dalma haka nake ji, wannan dalili ne ma yasa ban bari na ji ƙarashe ba.Jikina na yin ɓari na ɗauki suturata na mayar kafin na buɗe ƙyauren ɗakin,sauri-sauri haka nake tafiya har na isa ƙofar gidansu Deborah .
A zaune na tarar da ita kan wani kututturen icce tana kallon sama,da alamu aikin nata ne take yi wato lissafin taurari.Gefenta na zauna ina mai cewa “ki yi haƙuri”

“Ki yi tambayarki kai tsaye” ta faɗa ba tare da ta dube ni ba.

“Wane ne Annabi Ibrahim ?” na tambaye ta a raunace don hatta faɗar sunan ma yana yi mini wani irin raɗaɗi.

“Yana ɗaya daga cikin masu isar da wahayin da Ubangijin Ka'aba ya umarce su da shi.Kamar yadda tarihi ya zo Annabi Ibrahim ya fito daga cikin al'ummar da ke bautar gumaka amma duk da haka shi tun tashinsa bai taɓa bautar wani Ubangijin ba sai na Ka'aba.Al'ummarsa sun so hallakar da shi ta hanyar jefa shi a cikin wuta amma sai Ubangijinsa ya cece shi ya mayar da zafin wutar sanyi mai daɗi ba mai cutarwa ba”

Shiru na yi ina nazarin bayanin da ta yi mini,ina shirin tambayarta wane ne shi Ubangijin Ka'abar sai ga Banah ya bayyana a gabanmu kamar walƙiya.Hannuna ya kama yana yi wa Deborah mugun kallo kafin ya ce “ina mai yi miki kashedi na ƙarshe ki fita idona na rufe”

Debora ta miƙe tsaye tana cewa “abin da nake da niyyar faɗa maka kenan ka guji wasa da wuta”

Tamkar wata sokuwa haka na tsaya ina kallonsu,sam hankalina ya ƙi tsayuwa wuri guda abin da nake son sani shi ne wane ne Ubangijin Ka'aba??????????
[28/04 13:15] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

06

Maimakon Banah ya kai mu gida a'a daga nan sai ya wuce da mu gaɓar ruwa.
“Shawoli narat kohi jayi!” ya furta kalaman tsafi cikin wata irin murya,babu jimawa wata irin ƙara ta karaɗe wurin kafin ruwan ya soma darewa yana fitar mana da hanya.Haka Banah ya ja ni muka shiga muka fara tafiya,ko tsakiya ba mu kai ba aka soma yin ƙasa da mu har muka dangane da ƙasan ruwa.A nan ne na yi arba da tsoffin garinmu waɗanda suka mutu,wasu tun banda wayo a labari ne na ji mutuwarsu yayin da wasu kuma da hankalina suka yi mutuwar.

Kamar yadda ake yi wa baƙo in ya zo a wuri haka suka karrama ni,a wannan lokaci ne na ida ganin ainihin ɓoyayyar fuskar Banah shi ɗin ba iya mutum ba ne a'a jinsi biyu ne.
Chapter 19 · 0% Book details