Sashe 4
Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Kayiii! Mace a wannan lokacin? ” tako ɗaya na ƙara duk suka ja baya tare da ɓoye wa ƙarƙashin gadajen maras lafiya aka bar mai yi min magana.
Abu guda na yi nasarar gane wa,shi a siffar mutum yake yayin da sauran kuma innuwarsu kawai ake gani.
“Su wane ne ka gayyato mana a nan ana zaman lafiya?” na jefo masa tambayar .
Muryarsa na ɗan rawa ya ce “abokaina ne! Umm.Sun zo ganina ne”
Sai a yanzu na ƙare masa kallo,hannunsa na ɗauke da tiyon da ake yi wa mutum ƙarin ruwa.
“Don sun zo ganin ka shi ne za su hana mutane bacci? Ce maku aka yi nan gidan caca ne? ” na sake faɗa cikin tsawa.
Shiru ya ɗan yi bisanin ya ce “madam ke ɗaya ce kawai kika ji mu,amma normal mutum basa ji ”
“Ka sallame su maza kar na sake ganinsu a nan har lokacin da za ka bar asibitin nan in kuma ba haka ba zan yi mugun saɓa maku” ko gama rufe baki ban yi ba ya ce “an gama ranki ya daɗe!”
Har na juya zan koma sai kuma na tsaya tare da jefo masa tambaya “shashekar kukan wa nake ji a ɗazu?”
Kame-kame ya fara,can cikin ikon Allah idona ya sauka kan wani ɗan yaro da ke kwance kan gado.Esprit ɗinsa na gani a ɗaure ana tsoratar da shi haka kawai,“wane ne yayi masa haka?” na yi tambayar tare da shaƙe mutumen wanda aƙalla zai kai shekar sittin .
Cikin magagin wahala ya ce “abokina ne! Wallahi sai da na hana shi amma ya ƙiya”
Yadda yake magana zan iya hangen wani koren abu daga cikin bakinsa,ban san da me na yi amfani ba na ciro shi daga bakinsa bisanin na je na saki yaron nan da suke cutar wa sai kuma na koma ɗaki.
Ina kwanciya kan bed sai na ji nutsuwata ta dawo daidai saɓanin a ɗazu da nake jin kamar mu biyu ne a cikin gangar jikina.
Washegari
Da na tashi na yi zaton mafarki ne na yi wannan yasa ban bai wa abun muhimmanci ba.Ɗakunan maras lafiya mu ka fara shiga mu na duba su,na zo daidai gadon wannan mutumen na jiya da dare na ji muryarsa ya na cewa “madam don Allah ki taimaka ki bani kambuna”
Da mugun mamaki na dube shi na ce “mi kake magana a kai? Ko wani abu yake ma ciwo ne?”
Ya waro ido ya ce “kambun maitata da kika karɓe a daren jiya ”
Ras gabana ya faɗi,a fili na furta “kenan ba mafarki ne na yi ba?”
“Ki ban abina don Allah na yi miki alƙawari har na fita daga nan ba zan ƙara cutar da kowa ba” ya sake faɗa a karo na biyu,wani baƙin ciki ne ya turnuƙe ni nan take.“Wato ka ma taɓa cutar da wasu kenan?”
Muryarsa na ɗan rawa ya ce “wallahi yara biyu ne kawai na shanye ma jini bayan su babu wanda na cutar”
Na lumshe ido,nan take abun da yake kira da kambun maita ya bayyana gare ni daga nan inda nake zan iya hango shi cikin jakata wacce ke can ɗakin baccinmu.
‘Duk wanda ya kashe shi ma a kashe shi,don haka kai ma dole ka bi su’ na faɗa a zuci ina mai juya wa zan fita hargaginsa ya tsayar da ni na juyo.
Duk hankalin kowa ya koma kansa,nishi kawai yake ya na zarar ido.
A'isha ta nufe shi ta fara dubasa,kafin wani lokaci ya ce ga garinku nan ya mutu.
Wani kallo na ga ta na jifata da shi na tuhuma,sai kuma ta fita babu jima wa suka shigo ita da Dr . Rubuce-rubuce aka yi bisanin a sanar da ƴan uwansa suka fita da shi.
Har muka sauka daga aiki A'ishah ba ta bar min kallon nan ba,tuni na tsargu.Ko da na je gida hankalina kasa kwanciya yayi,haka na wuni sukuku Momah ta yi tambayar duniya amma na ce da ita babu komai.
Da dare bayan duniya ta yi tsit na buɗe jakata na ciro kambun maitar nan,wata ƴar ƙaramar halitta ce mai rai sai motsi take.Sai da na ƙura idona da kyau sannan na fahimci Kunkuru ne,hannuna na rawa na ɗauko shi nan take ya ɗauki wani irin haske kamar an kunna ƙwan lantarki.
Muryar Momah na ji daga sama ta na mai cewa “kambun wane ne?” na juyo a razane ina kallon ta,sai dai abin da ya fi ɗaga min hankali shi ne iya muryar ce kawai ke ta Momah amma fuskarta ta canza .....
[24/04 14:49] MRS SADAUKI: *FARAUTAR MAYU*
Page 4
Fuskar Momah sak ta tsohuwa irin uwanda sun ga jiya da yau.Tuni tsoro yayi min dabaibayi ya ɗaure min zuciya,cikin wata irin murya wacce ba tata ba take shaida min “wannan halittar da ke hannunki ta na da matuƙar haɗari ki yi gaggawa mayar masu ita kayar su.Kin san kuwa mi ake kira da Kambun Kunkuru? Maita ce mai shegen naci masu ita za ki ga ko mutuwa suka yi sun dinga yin fatalwa kenan domin son duniya ba zai taɓa gushe wa ba daga zuciyarsa” Momah na gama faɗar haka kamar ƙyaftawar ido ainahin fuskarta ta dawo normal.
Wani numfashi na ga ta ja ta na mai kafe ni da ido,da sauri na mayar da Kunkurun cikin jaka ina mai cewa “Momah ke ce?”
Maimakon ta ban amsa sai kawai ta fashe da kuka,hankalina ya ƙara tashi na shiga tambayarta can ta tsagaita da kukan tare da yi min umarni na je na kwanta.
Ban musa ba na kwanta sai dai fa ko kaɗan babu ɗigon bacci a idona.Tunani kawai nake,zuwa yanzu na fahimci akwai wani ƁOYAYYEN SIRRI(MRS SADAUKI) da Momah ke ɓoye min sai dai ban san shi ba.
Kamar wacce take karantar zuciyata na ji saukar furucinta “Ayodele ban ɓoye miki tarihin ki ba don wani abu ba,sai don kiyaye ki daga mumunar ƙaddarar da mahaifin ki ke son ɗora ki a kai”
Da sauri na yunƙura na tashi zaune na ce “Momah don Allah ki faɗa min wane ne mahaifina? Sannan ya na raye?”
“Da ransa duk da na fi shekara ashirin da baro ƙasarmu ta gado,amma ina ji a jikina bai mutu ba”
“Mine ne dalilin ki na guduwa to?”
“Zan faɗa miki sai ranar da kika cika shekara ashirin da biyu cicif”
“Nan da wata biyu kenan?” na faɗa don birthday ɗina ya kusa.Ta jinjina min kai alamar tabbatar wa,cike da farin ciki na kwana.
Washegari da zan tafi makaranta Momah ta jadadda min kan cewa na mayar da Kunkurun nan inda na ɗauko shi “to” kawai na ce mata ba wai don ina da niyyar yin haka ba.
Da na fito waje a ƙofar gida na yi rame daidai inda ruwa ke kwanta wa na saka Kambun Kunkuru na mayar da ƙasa,ina ganin yadda yake kallona da manyan idonsa amma Allah na gani ba zan barsa ba ya cutar da mutane.
Ko da na isa asibiti na tarar ana ta ɗaga ankon bikin A'isha ,ban ware kaina ba na shiga duba wa tare da tambayar inda suka fiddota.
Muna tsaka da aiki A'isha ta zo kusa da ni ta ce “Ayodele kin tuna mutumen da ya mutu jiya?” duk da na fahimci wanda take nufi bai hana ni neman ƙarin haske ba “wane fa?”
“Wanda kafin mu sauka ya mutu,gadonsa kusa da na yaron nan mai cutar sikila”
“Oh! Na gane shi”
“Hum! In faɗa miki an sake maido shi asibiti”
“Bai mutu ba?” na tambayeta da sauri,har sai da ta min wani kallo bisanin ta ce “ya mutu! ”
Na sauke ajiyar zuciya,ita kuma ta ci gaba da cewa “sai dai fa gawarsa ta ƙi shiga kabari ” A'ishah ta faɗa cikin wani yanayi.
Dukkan nutsuwata na bata tare da tambayarta “ban gane ba? To ya su ka yi da gawar?”
“Sun maido ta mana! Ta na can MUTUWARE cikin sanyi”ta ban amsa.
“Can shi ya sani! Mugun halinsa ne yasa Ubangiji ya nuna masa ishara” na faɗa zan ci gaba da aikin cika takardu don mun ɗan tsaya hutu ne .
“Amma Ayodele na tambaye ki mana”
“Ina jin ki” na faɗa ba tare da na dube ta ba.
Ta ce “mine ne haɗin ki da shi?” na ɗago na zuba mata na mujiya sai na ga ta ɗan rikice da sauri ta ce “ah! Ina nufin mi ya haɗa ku,jiya da ina ƙoƙarin taimakonsa na ji ya na cewa ki yi masa rai kar ki muzanta ni ban shirya zuwa ɓoyayyar duniya ba”
“Sai kuma ya ce miki da ni yake?”
“Sunan ki na ji ya faɗa”
“To ki je ki tambayesa” na faɗa cikin fushi tare da tashi na barta ma wurin.