← Book details Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 26

Sashe 25

Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tare suka ja ba,kafin su kalli juna.Da wani irin gudu kuma gimbiya A'ishah ta fita don jikinta ya bata babu lafiya,mayafinta ta ja ta rufe fuskarta lokacin da ta isa filin sukuwar.

Yarima NASLAM wanda ya lashe wasar tseren dokin ya juyo yana kallon inda take a tsaye,suka haɗa ido da sauri ta sunne kai tana wani murmushi kafin ta juya da sauri ta koma.Ya ja numfashi yana jin a ransa ya yi dacen mata.



An ɗauki tsawon lokaci kafin Ummilo ta farfaɗo wannan karon ma tana yin wasu kalamai a cikin Yaren da ban fahimci me take nufi.

“Alhamdulillahi lazhi ahayana ba'ada ma'amattana wa'ileyhi nushur” ta furta tare da ware idonta a kaina,na sakar mata murmushi na ce “sannu Ummilo” ba ta amsa ba sai martanin murmushin da ta maido mini tana mai shafar gefen fuskata kafin kuma ta miƙe ta fita.Haka na take mata baya sai na ga ta shiga banɗaki,can kuma ta fito ta soma wanke hannuwa da baki da fuska da hannuwanta hatta kai da kunne sai da ta shafa haɗi kuma da wanke ƙafafu.

Mayafinta ta gyara kafin ta zo ta fara yin wata irin bauta da ban san ta mece ce ba,ni dai ido kawai na tsura mata da na ga ba ta da niyyar idawa kawai na je gun baby Mila na ɗauke ta dama tun ɗazu ta tashi.Madara na soma bata tana sha tana kallona cikin ido, murmushi na saki ina jin sonta na ratsa ni.

Banah wanda tun bayan abin da ya faru ya koma can ƙofar gida yayi tsaye,sai yanzu ya shigo yana mai tambayata “mene ne can Ummilo ke yi?”

“Ina kifin har yanzu ba a gama dafawa ba?” na tambaye shi ,don sau tari in yayi mini tambayar da raina bai so ba nuna masa nake yi kamar ban ji ba sai na ɗauko masa wani zancen.

Fita ya yi ba tare da ya ce mini komai ba,can kuma sai ya dawo riƙe da kwano yana tiriri.Kamshin kifin ya daki hancina,nan take yawuna ya tsinke sai na shimfiɗe Mila na karɓa na soma ci shi kuma Banah yana aukin kallona.Ina gama ci na ji wata kasala ta rufe ni,sai na kwanta ni ma sai a lokacin kuma Ummilo ta shigo.

Banah ya ce “ga kifi nan da Naomi ta rage ki ci”

Da fara'a kuwa ta karɓa tare da gyara zama ta sa hannunta,sai dai fa ta gagara ci sai yamutsa fuska take haɗi da yunƙurin kai shi bakinta.Can dai ta haƙura tare da ajiye kwanon tana mai girgiza kai ta ce “in na ci wannan ai tamkar na cinye kaina ne,a'a sam maita ai ba hauka ba ce da zan ci jinsina ”

Banah ya ƙanƙance ido yana kallonta kafin kuma ya fice ya bar mu.Maƙoshina ne na ji yana wani irin zafi kamar ana hura wuta,murya kamar ta mai koyon magana na ce “Ummilo sanyi nake ji ki rufe ni” sai kuwa ta miƙe ta ɗauko bargo ta luluɓa mini.Daga wannan kwanciyar ban ƙara farkawa ba sai washegari da zakara ya fara cara,na buɗe idona da suka yi mini nauyi kafin na yunƙura zan tashi sai dai na kasa sakamakon bayana da na ji ya riƙe kafaɗata ta ƙara nauyi.

“Banah?” na kira sunansa kasancewar ni da shi ke kwana a ɗaki ɗaya,Ummilo kuwa cikin jerin ɗakunan da aka yi daga baya take kwana ita da Mila.

Shiru ban ji motsinsa ba,sai na ƙara yunƙurin tashi a wannan karon gangar jikina ta baro shimfiɗar sai dai na gagara tsayuwa kan ƙafafuna na faɗi kwacaaa.Jeren kwanukan da ke ɗakin duk ya baje,ƙarar ta jawo hankalin Ummilo ta shigo tana tambayar lafiya sai dai muna haɗa ido da ita ta ɗau haske.Da sauri ta zo ta taimaka mini na miƙe tsaye tare da riƙe ta gam,murya na ɗan rawa na ce “ki kai ni banɗaki na yi wanka” ita ce ta kai ni,sannan kuma ba ta fito ba sai da ta yi mini wanka.Bayan ta saka mini kaya sai ta miƙo mini wani icce ta ce na riƙe,na karɓa ina jin ƙusumbina da ya ƙara girma ya rinjaye ni na yi mini wani motsi.....

My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[28/04 13:15] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

Daga yau discount ya ida.
Last free page

10

Wata rusunawar dole ce ta zo mini saboda girman ƙusumbina ya wuce a yi kwatance sam tsayuwa ko tafiya babu sanda ba zai yiyu a gare ni ba.A haka na fito daga banɗakin ina jin wasu canje-canje na daɗa ƙaruwa a jikina,ban zame ko ina ba sai a ƙofar gida inda mutane birjit ke a wurin dukkansu kuma a ƙarƙashin ikona suke.Tamkar sun ga ubangijinsu haka duk suka tsaya da abin da suke yi suka zube ƙasa tare da yin kwanciya suna yi mini wani irin kirari da ba a taɓa yi mini shi ba.Idona na ƙanƙance ina kallon Banah da ke can ɗan nesa da ni yana wani irin murmushi da ban san mene ne ma'anarsa ba,don ko kaɗan ban zargi cewa a cikin kifin da ya bani na ci ba ne wannan girman ƙusumbin ya ƙaru.

“Sabbin dokoki sun sauka,don haka al'ummar gari ku kasance cikin shiri ga dukkan abin da shugaba za ta zartar” Banah ya faɗa yana mai takowa yana doso inda nake hannunsa riƙe da kwari da baka.
Sai da ya zo dab da ni sannan ya saita kibiyarsa a sama yana mai furta ɗalasiman tsafi,ji kake shuuu kafin wata wuta ta baje a sama.Babu kuma jimawa sauran jama'ar gari suka fara ɓullowa ta kowace kusurwa,tuni wurin ya ɗauki harama ya cika tanƙam.Sai kuma a lokacin ne na soma yin magana,“daga yau an zartar da yin hadaya duk ƙarshen mako,ruhikan ruwa su ne ke da alhakin zaɓar wanda suke so ko dai mu ɗauke shi mu bayar ko kuma su da kansu su kira mutum zuwa can domin ɗaukar ransa.Abu na gaba shi ne duk wani jinjiri da za a haifa sai an kai shi bakin kogo uwa gijiya ta saka masa albarka tare da ƙa'ide masa adadin shekaru ko watannin da zai yi a duniya”

Yanayin fuskokinsu duk sun nuna ba su ji daɗin wannan sabon tsarin ba,sai dai babu wani mai zarrar yi mini magana duba da irin ƙarfin ikon da ya ƙara hawa kaina ba tare da ni kaina na shirya masa ba.

A haka aka watse na koma ciki na tarar da Ummilo a zaune ta yi uban tagumi.Tana ganina ta miƙe tsaye tare da nufo ni,“na tuna wace ce ni ” shi ne abin da ta furta mini.Cike da jin daɗi na ce “kin tuna? Kai wannan babban abin farin ciki ne amma ya na ga ba ki murna?”

Idonta ya kawo ruwa tana mai cewa “na fito a yankin da aka haramta maita da kuma tsafi,ba tare da shuwagabannin sun yi la'akari cewa ba babu wani babban tarihi da magabatanmu suka shuɗe suka bari kamar Magic,ita Maitar ma ba ta fiya ƙarfi ba. Surukina kafin mutuwarsa ya yi matuƙar ƙoƙarin wurin ganin ya daƙile duk wata baƙar shirka,sai dai abin takaici Mayun ne suka haɗin gwiwa wurin kai shi barzahu.Wannan ya fusata mijina har ta kai shi da yin wani tsari shi ne kafa masarauta,yasa an gina babban wuri tare da yin shelar duk wanda ya shirya karɓar addinin gaskiya to ya shigo a cikin sabon ginin da aka yi.Ta wannan hanyar ce aka yi walƙiya aka gano mayu da matsafan cikinmu,sai ya soma yaƙarsu har ya yi nasara a kansu.Sai dai abin da bai sani ba ita maita bibiyar jini take yi,ga shi dai ya kashe tushenta amma bai cire inda ta yabanya ba.Sannu a hankali lokaci na tafiya mace-mace ya fara yawaita a daular,a bisa binciken wani mai bayar da magani ya gano cewa cutar maita ce sai kuma aka ƙara ƙarfafa tsaro.Tun ana yi wa mutum afuwa in an kama shi da cutar maita har aka zo zamanin yarona inda ya yanke ɗanyen hukuncin cewa duk wanda aka kama da laifin maita ko tsafi kisa ne kawai” tana kawowa nan ta yi shiru tare da kamo ni tana cewa “zo ki zauna hakan za ki gaji sosai,ya kamata ma Banah ya nemo miki sanda mai kyau”

Kan kujerar da aka sassaka da icce ta zaunar da ni kafin ta ci gaba da bani labarin.

“Mahaifin matar ƙanen mijina shi ne mutum na farko da ɗana ya fara cirewa da hannunsa saboda laifi mafi muni da ya aikata ya kashe mahaifan hadiminsa wanda ya ɗauka tamkar amininsa.Ƙarfin wannan raɗaɗin ya saka ita kuma matar ƙanen mijin nawa ta ɗauki tsanar duniya ni da ɗana ta ɗora mamu” nan ɗin ma shiru ta yi tana kallona tsakiyar ido da dukkan alamu akwai wani sirri mai nauyi da take son sanar da ni wanda baki ba zai iya furtawa ba.

Ta idonta kuwa ta shaida mini cewa “ni mayya ce! Ina ɗauke da kambun Maitar prophecy” sai kuma ta yi saurin janye idonta daga cikin nawa kafin ta je da sauri ta shige ɗakinta.Na lumshe idona tare da buɗe su kafin na yunƙura dakyar ina dogara sanda na take mata baya.

A zaune na tarar da kan shimfiɗarta,na ajiye sandar hannuna ni ma na zaune tare da kamo hannunta.Sai ta ɗago ta dube ni tana wani irin murmushi da ya fi kuka ciwo kafin ta ce “ban taɓa yin maita ba,ban taɓa cin ɗan wani ba kawai dai abin da na sani wani lokacin ina rikiɗa na zama kifi a irin haka ne har ita Dadda ta ganni cikin wannan siffa shi kenan ta je ta sanarwa sarki ai ni ma mayya ce.Ba tare da maganar ta fita waje ba aka titse ni sai na faɗi gaskiyar magana,in kuma na yi shiru na ƙi faɗa gobe gaban al'ummar gari za a yanke mini hukuncin kisa bayan an tabbatar shi ne kawai na yanke shawarar bin dare na gudu.Amma duk da haka bai ishi Dadda ba sai da ta jefe ni da baƙin tsafi ta haukata ni”
Chapter 25 · 0% Book details