← Book details Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banah ya ɓata rai yana shirin magana amma na dakatar da shi,na je na kawo mata ruwan.Sai dai tana saka hannunta ciki ta ce “waɗannan ai masu sanyi ne,masu ɗumi nake so” idona kawai na juya ruwan suka soma tafasa suna fitar da tiriri.Sai ta yi ƙuri tana kallona kafin ta ce “wannan tsafi ne kika yi kuma sarki ya haramta haka”

Sai muka kalli juna ni da Banah tare da haɗin baki wurin tambayar “wane sarki?”

Kai ta girgiza sai kuma ta soma yi wa jaririn wanka,ta saki murmushi ta ce “mace ce ashe” sai ta fito da ita daga cikin ruwan,ta cire uban kallabin da ta yane kanta da shi ta saka jaririyar a ciki.

“Wace ce ke?” na tambaye ta.

“Ni kaina ban sani ba,amma sai nake jin tamkar an aiko ni nan ne saboda isar da wani saƙo” ta bani amsa tana mai ɗago kai ta dube ni.Idona ya sauka kan goshinta nan na ga irin tabon nan da ke a goshin NASLAM ita ma yana fitar da haske sai dai bai cutar da ni ba,hakan kuma sai ya yi mini daɗi na ji a raina cewa ko da a ce ita ma wannan Ubangijin Ka'aba take bauta ma zan iya zama da ita.



Wuraren ƙarfe tara na safe daular abu NASLAM ta samu wani rikitacen labari.Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya yarima ya miƙe kan ƙafafunsa bayan ya yi wanka da magani ya kuma sha a cikin shayi.
Cikin tafiyar jarumta ya soma ratsa dakarun har ya isa inda Sarki ke tsaye yana jawabin yadda komai zai kasance,kamar kuma yadda Sarkin ya tsara jakariya Ali ne zai jagoranci tafiyar.

“Zan tafi ni ma don haka a shirya dokina” ya faɗa yana mai kallon mahaifinsa cikin ido.Sarki ya kawar da kai,don ya san ko da a ce ya yi yunƙurin hana shi ba zai ji ba.
Haka duk suka fito kowanne ya hau doki,da yarima zai hawa kan nasa sai da jakariya Ali ya taimaka masa amma a haka suka tafi.

Tun a bakin ƙofar shigar garin suka fara cin karo da kayan tashin hankali,babu shiri yarima ya diro yayin da kuma jakariya Ali ya soma take masa sawu.
Gawarwakin mutanen da aka kashe,Ali ya kalla sai ya ga duk kusan kalar mutuwar iri ɗaya ce.Ya kai hannu ya damtsi ƙasa sannan ya kai kusan hancinsa ya sunsuna,yarima ya dube shi tare da cewa “me ka fahimta?”

“Farmakin Mayu ne” ya basa amsa,ran yarima ya ƙara ɓacewa amma a haka suka ci gaba da duba ko ina har suka shiga gidan da matar nan ta haihu.

Cak jakariya Ali ya tsaya yana kallon ustaza Jamila,wacce ta bayar da dukkan lokacinta domin yin hidima ga addininta.Yarima ya ƙarasa yana mai cire rigarsa ta sarauta ya luluɓe ta,tare kuma da baiwa dakaru umarnin a ɗauke ta a kai ta can masarauta tun yanzu ba sai an jima ba......
[28/04 13:15] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

07

Ustaza Jamila ƙanwa ce ta jini ga jakariya Ali,mijinta ma ya mutu ne a wajen yaƙin haɓaka musulunci sai ga shi ita ma ta mutu wurin da'awar jawo hankulan waɗanda ba musulmi ba.Kamar yadda tsarin masarautar yake,suna aika maza da mata garuruwa don koyar da mutane karatu.

Yarima NASLAM ya dafa kafaɗar jakariya Ali yana mai cewa “ dukkan rai zai ɗanɗani mutuwa,ka sa a ranka lokacinta ne ya yi.Mu ma muddin namu yayi babu makawa a duk inda muke mutuwa za ta riske mu”

Idon Ali sun kaɗa sun yi ja sosai,muryarsa ma cikin wata irin sarƙaƙiya take fita.“Na yi imani ga Ubangijin Ka'aba,dukkan wata ƙaddara mai kyau da akasinta daga gare shi take.Sai dai babbar damuwata ɗaya ce ,cikin jikinta sam babu shi a yanzu hakan yana nufin kenan ta haihu in kuma ya tabbata haka ina jinjirin yake?”

Shiru yarima Naslam yayi na wani ɗan lokaci kafin ya ce “a duk inda yake Ubangijin Ka'aba ne zai tsare shi,ka dai kawai ka sa kyakkyawan yaƙini ga ubangijinka ” kalamansa suka yi tasiri a zuciuar jakariya Ali, wannan ya basu damar ci gaba da binciken ko ina.

Bayan sun gama haka suka haƙa rame aka rufe sauran kafin su juyo su dawo masarauta inda Sarki Haroon da sauran al'umma ke dakon jiransu.

Suna shigowa sarki ya je ya tarbi yarima tare da soma tambayarsa abin da ke faruwa.

“Farmakin Mayu ne,duk sun kashe mutanen gari da alamu kuma sun tafi da wasu.Babban baƙin cikin shi ne ba su bar wani sawu ba da zai sa mu gane ta ina suka fito ”

Barham da duk ya ji abin da yarima ya faɗa sai ƙara matsawo yayi yana mai cewa “a yadda ka yi bayanin ya tabbata cewa wannan rundunar Mayun ta samu jagoranci Banah maharbi”

Sarki da yarima Naslam sai duk suka maido dubansu ga Barham ɗin,shi kuwa kai ya jinjina kafin ya ci gaba da cewa “tarihin da ya fara zuwa na wannan ƙarnin ya bada labarinsa,Banah maharbi ne kuma babban matsafi wanda ya fito daga tsatson aljanar ruwa.Mahaifinsa ya kasance masinci ne,ya iya ruwa sosai a irin alƙawarin da mutane ke ƙullawa da ruhikan ruwa mahaifin Banah ya yi gamo da wata aljanar ruwa har yayi tarayya da ita suka same shi.Tun da aka haife shi a cikin jeji ya tashi tare da fatale da aljanu,kafin mahaifinsa ya mutu ya koya masa farauta da kuma baƙin tsafi na ƙarnin baya sannan kuma ya ɗora shi kan turbar yi wa aljana ZAƘUMA bauta” Barham na kawo nan da zancensa masarautar ta ɗauki wani salo,guɗa ce kamar an kawo amarya ta karaɗe ko ina kafin kuma iska ya soma tashi babu jimawa kuma aka soma yin wasu yayyafin jini.

Hankali a matuƙar tashe Barham ya ce “Attakbirrrr!”

Dukkan mutanen da ke wurin suka amsa da “Allahu Akbar!” nan take yayyafin jinin ya tsaya cak wanda duk ya ɓata fuskokin mutane.Sai kuma sararin samaniya ya soma ɗaukar launin ja yana nuno inuwar wata halitta marar kyawun gani can ita ma ta ɓace komai ya dawo normal.

Ran sarki da na yarima ya ɓace,saboda ba tun yau suka saba ganin ire-iren waɗannan surkullen ba.
Barham ya ce “ Aljana ZAƘUMA ce,wato uwar gijiyar Banah da ita yake tsafi.A kullum yana shayar da ita jinin mutane,ita kuma tana basa ƙarfin iko ”

“Ina zan samu shi Banah ɗin?” yarima ya tambaya.

Barham ya ce “Ubangijin Ka'aba ne kawai ya san daidai ina yake a yanzu,saboda tamkar guguwa haka Banah yake bai zama wuri ɗaya yawo yake yi gari-gari yana shanye jinin al'ummar yankin”

Yarima zai buɗa baki ya sake yin magana amma sarki Haroon ya dakatar da shi ta hanyar cewa “yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne yi wa ustaza Jamila sutura,don haka a kira gimbiya A'ishah ta yi mata wanka”

Sai a lokacin ne kawai Ayyub ƙanen sarki Haroon kawai ya saka bakinsa,“ gimbiya A'ishah tana kwance babu lafiya tun jiya,na so na sanar da kai sai kuma wannan al'amari ya danne niyyata ”

Hankali a tashe yarima ya ce “meke damunta?”

“Ciwon ido ne mai tsanani ,idanunta sun zama kamar gauta ” Ayyub mahaifi ga gimbiya A'ishah ya faɗa .

Yarima bai ƙara cewa komai ba ya shiga can ciki,direct kuma sashensu gimbiyar ya wuce.

A kwance ya tarar da ita don tun lokacin da Dadda ta fice ta bar ta take nishin azaba idonta sai ƙara ciwo suke yi saboda ta ga abin da bai kamata a ce ta gani ba.

Tana jin muryar yarima ta yi ƙarfin halin buɗe idon nata sai dai tamkar mai ɗauke da sabuwar makanta haka take ji dole ta ja su ta rufe.

“A'ishahhh?” ya kira sunanta cike da tausayinta.Murya na ƴar rawa ta amsa da “na'am yarima”

“Mene ne ya shiga idonki?” ya sake jefo mata tambaya,sai dai ba ta kai ga amsawa ba jakariya Ali da Barham suka shigo.

Barham ya matsa kusa da kanta yana ajiye jakar kayan aikinsa,bai ɓata lokaci ba ya soma zuba magani yana wanke mata idanunta duk da yana haɗawa da Magic babu wanda ya sani in ba ita gimbiya A'ishar ɗin ba.

Cike da aminci ta buɗe idonta da suka dawo normal tana kallon Barham da yake yi mata ta idanu.

“In yau na wanke miki ido kin samu lafiya ki sani gobe ba zan yi ba,zan bar ki da mugun halinki ”

“Ban taɓa ganin inda maye yake gorantawa ɗan uwansa ba sai kai Barham” ita ma ta basa amsa ta ido.

Ya ce “ni ba maye ba ne,ban taɓa yin maita ba hasali ma ina adawa akan duk masu yinta.Ke ma kin san cewa iya Magic kawai nake yi shi ma ba don komai ba sai don ci gaban masarauta”

“Me yasa dole sai ni kake son na bayyana kaina? Don me shi yarima ba ka damu da tasa maitar ba?” ta tambaye shi,sai dai shi Barham ɗin bai bata amsa ba ya juye kansa ya mayar da dubansa ga yarima Naslam yana mai cewa “ba wani babban abu ba ne ya same ta,kawai wani ɗan tsautsayi ne”

Yarima NASLAM ya dube ta yana mai cewa “ki kwanta ki huta” sai kuma ya fice jakariya Ali na take masa baya.

Wasu mata aka samu suka yi wa ustaza Jamila wanka.Sai da aka ma fito da gawar ne sannan gimbiya A'ishah ta san abin da ke faruwa,sosai ta ji zafin mutuwar har da zubar da hawaye.Ana yi mata sallah aka kai ta gidan gaskiya,sai kuma a wannan lokacin ne jakariya Ali ya nuna rauninsa ya soma yin hawaye waɗanda zubar da su ba ƙaramin sanyaya masa zuciya suke yi ba.

Sai da aka yi kwana uku ana jimamin mutuwar ustaza Jamila kafin kuma lamurra su ci gaba da tafiya.

A yau ne yarima yasa aka fito da matsafiyar nan da ta raira waƙa tsafi.Gaban sarki aka gurfanar da ita,tare da umartar ta da ta faɗi laifinta.

Amma ta yi shiru ta ƙi cewa komai sai yariman ne ya shaidawa sarki yana mai ƙara wa da “a yanke mata hukunci nan take ban son ajiyar mayya a cikin masarautata ”
Chapter 21 · 0% Book details