← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 18

PART 15 AND SIXTEEN

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tashi tayi ta fara kokarin bude akwatin azwa,fito da kayan ciki take domin ko zataga abinda Azwa ta fada mata a cikin wasika amma bata gani ba,har ta fidda rai sai kuma Allah ya kai idanunta jikin zif din tsakiya tana budewa kuwa taga waya tare da wasu takardu data Adana,dauka tayi ta zauna a kusa da wajen takardun ta fara budewa wani rubutu ne ya bayyana kamar haka,aunty anam kin san menene musababbin abinda ya faru da ni tabbas fyade aka min amma kuma aunty ban mutu ba hasali ma nakai kara police station amma basu dau wani mataki ba,naje naje amma Ina aunty ba Wanda ya kulani kasancewata marainiya kuma talaka,amma aunty anam nasan idan na mutu zakizo kuma Ina farin cikin sanar da ke cewa Dan gidan Alhaji SALMANU yasan komai aunty ki Bini hakkina,wani kuka ne ya kwace wa nainah a lokacin data gama karanta takardar,t tashiu tayi tare da daukar wayar ta kunna videos ta duba sai ga wani video ya bayyana,saurin katsewa tayi tare da sakin murmushi Allah sarki Azwa Allah yakai haske kabarinki Allah ya ji kanki da haka ta tattare takardar da kayan ta mai da kayan ta dau wayar da takardar ta dora akan kayanta sannan ta saka kafa ta fice daga dakin tare da kulle babe da take ta kallon ta.
Tafiya take a cikin gidan amma ba ta da inda zata iya zuwa,can kuma sai ta dauki wayar ta da key ta fice daga gidan tafiya take a saman titi,dai dai wani Dan karamin gida ta tsaya a lungu,tana Kare masa kallo fitowa tayi ta shigo da sallama a bakinta,amsa mata akayi sannan aka shimfida mata tabarma,matar ta kalla ta gaishe ta sai kuma tace dama mama Ina Neman batula ne,ai kam yanzu yar nan batula na makaranta amma mai zai hana ki jirata ta dawo,murmushi ta saki aa mama shikenan kawai ni zan tafi,ga wannan wasu bandir din kudi ta ajiye mata idan ta dawo kice yayar Azwa ce tazo nemanta,sai a lokacin tsohuwar ta washe baki aa kardai kice min aunty anam ce,murmushi nainarh tayi tace eaa ita ce mama,dama nasan baki gane ni ba,to tsaya mana yar nan ai dole naki gane ki washa rabanki da gidan nan tin kafin ki koma kano da zama,dariya tayi sai tsohuwar ta kalleta tace idan akan kisan da akayi wa Azwa ne ba wani bane fa ce zaid,kallon mamaki ta bita da shi amma mama tayaa akai Kika sani,sallamar da akayi ce yasa su kallon kofar,tsohuwar ce ta ce shikenan ga batular ma nan ta dawo,batula kallon kallo aka shiga sai kuma ta rugo tare da fadin aunty anam ke ce a gidan namu,yaushe kikazo.
Aunty anam bara na baki labarin abinda ya faru kamar yadda nasani,aunty anam dani da Azwa tare muke zuwa makaranta kuma tare muke dawowa,mun kasance kullun hanyar mu ita ce ta kofar gidan Dan gidan Alhaji SALMANU wato gidan shan iskarsa inda yake sheke ayarsa,kullun Muna wucewa wani lokacin mugansu wani lokacin kuma muganshi da mata haka dai aunty anam komai ke tafiya,wata rana anyi ruwan sama mun taso daga makaranta a lokacin muna tafe Muna hira kamar yadda muka saba,kofar gidan zaid ne mukaga wani daga cikin abokansa Wanda suke sheke ayarsa ya bige wani tsoho ya fadi sannan ya takesa da kafa,azwa ce ta kalli wajen sannan ta tafi da gudunta dik da Ina kwala mata kira akan ta dawo amma Ina ta Riga data tafi,tashinsa tayi sannan ta juyo tana fadin sannu baba sannu,dafata yayi yana fadin yawwa yar nan sannunki,juyawa tayi wajen Wanda ya fadar da tsohon,kai wane irin dabba ne wato zalincin naku har ya kai kan tsofaffi wanna da kake sakawa ba uban wani abu,kallon ta yayi yace ke ni kike kira da dabba,cikin bacin rai tace nafada dabba,idan da akwai abinda za kayi to kayi daga hannu yayi sai a lokacin kuma zaid ya fito sai ya fasa,ganin Azwa a wajen take ya lumshe Ido ya kara sa wajenta,kamar yadda ya saba yiwa yammata ya ce ke nawane fara shin ki,cikin bacin rai ta daga hannu ta kwada masa mari sannan ta tofa masa yawu,yaran ne sukayo kanta zasu daketa sai yayi murmushi yace ku kyaleta domin wannan fansar ta babbace,tinda nake ba Wanda ya taba mari na bare har ya tofa min yawu amma yau ga wata ta mareni.Daganan kuma bayan kwana 2 shi ne wannan abin ya faru kuma na tabbatar da cewa zaid shi ne ya yi mata fyade sannan kuma bansan Wanda ya kashe ta ba,domin bayan dik wannan abin daya faru,tin daganan bata kara zuwa makaranta ba sai labarin mutuwar ta naji,anam ce ta share hawayen fuskarta ta ce nagode batula da haka tayiwa umma sallama ta wuce tana mai jin bakin ciki na abinda ya faru da Azwa.
Direct gidan Alhaji SALMANU ta nufa tin daga kofar gate din take dukan kyauren,gate man din ne ya bude yana zaro Ido wani kallo tayi masa tace Ina Alhaji SALMANU yake,tabe mata baki yayi yace ke kuma wa da zakizo kina Nema Alhaji cikin wannan duhun magariban,wani shahararren mari ta Basa Wanda sai da ya fasa masa baki take ya matsa ta shiga cikin gidan,da sauri ya bita,hajiya wallahi ba kowa a gidan nan dik Basa nan sun tafi amurika kuma bazasu dawo ba sai nan da wata guda wallahi hajiya daga ni sai masu gadi,wani tsaki taja yaushe suka tafi hajiya jiya ya bata amsa,to Ina zaid kuma hajiya ai wannan mai ganinsa sai ubansa da uwarsa amma badai mu ba,hajiya kije gidan sa,amma wallahi baya nan,tsaki taja ta fice daga cikin gidan tare da shiga motarta ta bar wajen.Kofar gidan zaid nan a kulle tsaki ta ja amma kuma har ta tafi ta juya ta dawo ganinsa a rufe ne yasa ka sakin baki tana fadin wallahi sai na shiga gidanan,kamar haka kuwa tai tsalle ta dare Katanga ta haura,bata dade ba ta fito tana Jan dogon tsaki.
Asubar fari ta fito daga cikin gidan hannunta rike da babe,motarta da tazo da ita ta shiga,ta fice daga gidan,tafiya take tana tinanin me ya kamata tayi,wayar ta ta dauka tai dialling number abeed ka saurara gani nan na taho sannan Ina mai tabbatar maka da cewa dik yawan jami'an Yan sanda da zaka baza bazasu iya kamani ba,domin tin farko na fada maka kuma na nuna maka a aikace Dan haka ka saurari zuwa,da haka ta katse wayar tana mai cigaba da driving.Abeed ya kalli mommy yace mommy tana hanyar dawo da babe,kallonsa tayi tace to sannan ta tashi ta shige daki,wayarta ta janyo tace tana hanyar zuwa garin Abuja karku bari ta fita daga garin nan ba tare da kun kama ta ba sannan kuma kunsan dokar da haka ta katse waya ta zauna,salim ne ya daga waya ya ce ku tabbatar da kun bace da mutane domin tana hanyar zuwa Abuja sannan daga tazo ku cafketa batare da wata matsala ba,da yes sir suka bishi sannan suka katse.
Garin Abuja ta shigo sai da ta tsaya wani boutique ta ja hannun babe suka shiga,kaya ta Siya mata Riga da wando sai facing cap shirya ta tayi take ta zama kamar namiji,wani black shoes ta saka mata take ta koma namiji,ita kuma ta sayi abaya black mai ratsin yellow ta saka sai gasu sun fito kamar ba su ba,mota ta koma ta shiga tare da janyo laptop din ta,take ta fara chanja location din ta maida shi na jigawa,salim na zaune yaga location ya chanja take ya Mike tsaye yana fadin shikenan ta gane mu,da haka nainah ta taho har kofar gidan su abeed,a cikin mota ta kalli babe tace idan Kika sake kikayi kokarin magana wallahi sai na kasheki,fitowa tayi a lokacin kowa na aikinsa,yansandan waje sunga namiji kuma basuyi tinanin babe bace saboda ance musu macece za a kawo,gidan ta shigo a lokacin Salim ya fito da sauri ya bigeta,juyowa yayi yace ya hakuri madam,murmushi tayi masa ta juya,har inda ta dauki babe ta maida ta tace ta zauna,anan kuwa ta zauna yayi da ita kuma take kokarin fitowa,haka kuwa akayi sai ga nainah a mota tana tada ta,har ta bata wuta ta fara gudu a titi kira ne ya shigo kaduba na ajiye maka kanwarka kuma na tafi,salim ne ya karba waya gaya miki kinsha juya bayanki tana juyawa taga gungun motoci na binta take ta karasa wuta.
ASHU
Secret Writer
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 8 · 0% Book details