← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 18

PART 31 AND THIRTY TWO

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gaba daya mutanen dakin hankalinsu na kan television sakamakon hoton nainah da aka nuno a kasa a ka rubuta wanted,and ana yin bayani a jikin hoton,daga baya gaba daya idon kowa ya sauka akan nainah,ga makudan kudade da suka gani a kasa an rubuta,Dass ne ya kalleta yace ke kuma meye hakan,dariya nainah tayi dik da taga haka amma bata yi mamaki ba,domin tasan tabbas tayi ta'asa dole ma a nemeta,jin kara na agogon ta ne yasata fadin zanje toilet,ba Wanda ya kalleta ta tashi ta wuce,tana shiga ta rufe,daga kiran tayi sai kuma tai murmushi aunty ba matsala,nima yanzu nake gani,amma anam kinsan suwaye suka dora hoton nemanki ne,aa ta furta sannan sukayi sallama ta katse,zama tayi tana tinani can kuma ta fito,tana saka kafarta a bakin toilet take suka fesa mata wani abu a wajen ta fadi ta Sume,kallon kallo ake oga ne yace shi zai kaita address din da aka bashi,sauran ne suka nuna kin amincewarsu,daga haka gaba daya suka dunguma suka sakata a boot din mota,dass ne yace aa ku cirota kunsan yanzu darene,kuma akwai police Dan haka mu sakata a baya,daga haka suka dau hanyar kwatancen da akayi a jikin hoton.
Hammad zauna inason magana da kai,amma ummu kinga dare yayi ki Bari sai gobe mana,kallonsa tayi tace Hammad yaushe ka girma to ni yanzu nake son magana da kai,ganin ranta ya baci ne yasa shi fadin shikenan ummu na kiyi hakuri,murmushi ta saki domin a rayuwa tana matukar son hammad,zama yayi yana cewa to ummu na zauna,magana zamuyi dakai,inaso ne kaje Taraba dago kai yayi ya kalleta yace amma kuma ummu,tsaya hammad ta katsesa washa rabanka da taraba ne,shiru yayi yana saurarenta yayin da taci gaba da yi masa fada,kai wai Hammad ne yake damunka ne,kai kenan bazaka dinga zagaye dangi ba,yanzu washa rabanka da kaje kauye dagowa yayi yace yanzu ummu me ya kawo wannan maganar,nace fa zanje ko,hammad ka shirya ranar Saturday zaku tafi,amma ummu gobe jumua kenan jibi kike nufi,eaa ta bashi amsa kuma kai da muniba nake son kuje,rike kai yayi yace amma ummu kinsan dai ita muniba tasan hanya dole ne sai na bita,ok hammad wato ka girma ko,aa ummu ba haka bane shikenan zan je kamar yadda kike buqata,to shikenan Allah yayi maka albarka Hammad.
Aminu ne zaune a katon gidan da yake zaune,wata yar karamar waya ce take ruri a gabansa,kalla yayi tare da dauka ya kara a kunensa,hello sir wata muryace mai kama da ta zakuna,ya furta aminu wannan wane irin shashancin banza ne,yanzu yarinya ce zata gagareka kamawa,cikin inda inda ya furta wallah ba haka bane sir,yarinyar ce yanzu tayi wayo matuka ba kamar da can ba,kasani da cewa na baka nan da 3days ka kawo min ita idan ba haka ba wallahi sai na maka abinda baka tinani,mutumin banza kawai shashasha,kitt aka kashe wayar,bin wayar yayi da kallo yana mai tinanin mafita,k kallon yaran yayi yace kuna ji Na dik rintsi dik wuya inason yarinyar nan nan da 2days idan ba haka ba wallahi bazan biya ku ko sisi ba,daya ne ya Mike yace amma oga ai ka fada mana yadda ya kamata muyi,aminu ne yace kusan yadda zakuyi amma Ina buqatar ta kuma a raye nakeson ta,daga haka ya Mike ya shige toilet,gaba daya komai ya masa duhu ya rasa ta inda zai bi ya dawo da nainah,domin ya Riga da yasan halin sir,da wannan tinanin yayi wanka ya fito yabi lafiyar Katifa.
Tafiya suke a wannan Daren da yake sun san hanya sosai,karfe 3 suka iso Sokoto,address din suke bi,take sai gasu a wani katon gida mai matukar kyau,shiga sukayi sannan sukayi parking,biyu daga cikin su ne suka kama nainah tare da shiga parlorn da aka tanadar musu,basu dade da zama ba sai ga wasu mutane Manya Manya,zama sukayi sannan suka kalli nainah,vatare da sunyi magana ba,wata jaka daya ya Mika musu sannan su kuma suka mike suka bar parlorn,mutanen ne suka kalli nainah sannan sukayi murmushin samun nasara.yayin da mutanen Alhaji mahboob suka fito babban cikin su ne yace,ya kamata muje mu huta a hotel kafin nan sai mu wuce kano ko zuwa nan da 5 ne,daya ne ya kallesa hakane sir amma kuma me ya kamata mu fada wa Alhaji mahboob,dariya yayi yace aikin banza,rabu da shi mun riga da mun bada nainah an bamu naira million 1,idan yaso sai muce masa ai ta gudu ya zaiyi da mu,da wannan shawarar suka bar gidan.
Bayan tafiyarsu ne nainah ta farka,a zaune ta ganta gefe kuma ga wasu manyan mutane,bata damu ba kallonsu tayi tace zanyi sallah Ina bandaki,daya ne ya kalli daya sannan daya yazo kanta ya tsaya,muje a raka ki,kofar bandakin sukaje,shiga tayi bayan ta gama komai ta dauro alwala ta dawo,gyara jikinta tayi ta gyara mayafin sannan ta tada sallah,sai da ta gabatar da raka'atanil fajr sannan tai sallah asuba,sai a lokacin ta tsaya tana kallonsu,take bangon dakin ya fara haske,wasa wasa sai ga fuskar Alhaji DAYYIB a jiki yana mai kallon mutanen,good job mutane na,tabbas kunyi babban aiki,nainah ya kalla yace nasan baki gane ni ba,ni ne mahaifin kamal wadda Kika saka a ka karyawa kafa da hannu,dik da nainah najin tsoro amma ta danne tsoron,ta fara magana ka gode Allah ban kashe sa,iya hannu da kafa na karya masa,nan gaba idan ya ci gaba da abinda yake sai na rabasa da mazantakar sa,daya daga cikin mutanen ne ya wanka mata kykkyawan mari,take a wajen ya fara zub da jini dama ga dukan da mutanen Alhaji mahboob sukayi mata,alhaji DAYYIB ne ya kallesa ya isa Alex,ke a tinaninki zaki fita daga nan a raye ne,ai na rantse sai na kashe ki na kuma batar da gawar ki mutuniyar banza kawai,kallon Alex yayi yace kira Alhaji SALMANU,ko second 10 ba ayi ba sai ga Alhaji SALMANU shima ya bayyana,alhaji DAYYIB ne yace ga wadda ta karywa yaranmu kafa da hannu,alhaji SALMANU ne ya kalleta,sai kuma ya juya ya kalli zaid Dake kwance gefe kuma ga mahaifiyarsa,sai wata yarinya da suke kama da zaid da alama kanwarsa ce,zaid ne ya karbi wayar ya kalleta yace tabbas nainah,nasan nayi kuskure amma Dan Allah kiyi hakuri,bazan kara aikata hakan ba,kuma Ina mai baki hakurin rashin yar uwarki,nasan da cewa ni ne bani da gaskia Dan haka ga mahaifiyata zata baki hakuri,alhaji DAYYIB ne ya saki baki yana mai kallonsu,mahaifiyar zaid ce ke wa nainah godiya,daga karshe suka bata hakuri,nainah ce ke zubda hawaye domin tabbas ahalin sun birgeta,goge hawayen tayi sannan tace zaid kayi hakuri kaji Allah ya baka lafia,daga haka Alhaji DAYYIB yaja tsaki aikin banza,kai SALMANU anyi sakarai da kasan baza ka iya tinkarar wannan matsalar ba amma kuma,katsesa salmanu yayi yace DAYYIB ya isheka,ni yanzu bani da wata alaka da wannan yarinyar kuma nagode mata da tai sanadiyar shiryiwar da na,dayyib ne yace shikenan amma ka sani ni bazan kyaleta ba,alhaji salmanu yace dama ni ai bance ka kyaleta ba,daga haka ya katse wayar,dik wannan dramar akan idanun nainah akeyinta,nainah ce ta furta a hankali ya zama dole na ware domin zama na anan akwai hatsari,wata zuciyar ce ta furta to ke yanzu taya zaka gudu,dan karamin murmushi tayi.
Abeed ni yanzu zan wuce kano domin cigaba da bincikar nainah,allah ya bada sa a abinda abeed ya furta kenan,amma da ka kyale yarinyar nan Salim ka rabu da ita domin da alama ta fimu gaskia,hajiya areefah ce ta fito baza a kyaleta ba din,wai kai abeed me yake damunka ne,kai baka kishin kanka,i ta ce ta kashe maka mahaifi,kallon ta yayi yace mommy ba ita bace ba ita ta kashe daddy ba,to waye ya kashesa,salim ya tambaya,nasani amma bazan fada ba,kai kuma kace sai ka kamota ko to kasani bazaka taba iya kamata ba,sai da kasha wahalar banza ka dawo,salim cike da kuluwa ya kallesa kai abeed me yake damunka ne,tsaki yaja ni ba abinda yake damuna,ba komai kace fadin areefah,eaa ya furta mari ta kai masa,kai yaushe kayi girman Ina Fda kana fada,eye a zuciye ya furta shikenan mommy ki kashe ni,ki kashe kawai kamar shiru yayi yana huci,kamar me abeed ka karasa mana,hawaye ne ke zuba a idanunsa,karon farko da Salim yaga hawaye a idanun abeed kenan,cike da mamaki ya kallesa yace abeed tsaya me yasaka kuka,warce hannun sa yayi yana kallon hajiya areefah,wayarsa ya dauka ya haye kan upstairs ya huce dakinsa yana mai kuka.
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 16 · 0% Book details